Wednesday, November 27, 2013

SHARUDDAN HIJABI A MUSULINCI



 ABUBUWAN DA SUKE CIKI

                                                                            Shafi
Godiya           -           -           -           -           -         1

Taqarizi         -           -           -           -           -         3

Matsayin Mata                      -           -           -         5

Ma’anar Hijabi         -           -           -           -           8

Sharuddan Hijabi     -           -           -           -           9

Niqabi            -           -           -           -           -       -      -    38       

Niqabi Yana da Asali    -     -        -     -               39

Fahintar malamai a kan Niqabi      -      -             44   

Nasiha Ga Isah Hassan Tikuma     -           -         55

Mahimmancin Sa Hijabi     -           -           -           58

Illar Rashin Sa Hijabi          -           -           -          59

Yadda Ake So Mace ta yi tafiyarta           -           59

Hattara Mata -             -       -        -         -            60

Kammalawa  -           -           -           -           -           63       
GODIYA
بـسـم اللـه الـرحـمـن الـرحـيـم                                                                
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره  ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادى له، وأشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله.   
أما بعد: فإن خير الحديث كتاب الله، وخير الهدي هدي محمد، وشر الأمور محدثاتها، وكل محدثة بدعة، وكل بدعة ضلالة، وكل ضلالة في النار.
Haqiqa ina wa Allah godiya da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi taqaitacce Wanda yake Magana a kan “Sharudxan hijabi a Musulunci” da bayani akan Niqabi da yadda ake so  tafiyar mace ya kasance, Ina rokon Allah daya anfanar da shi.  Dubi ga halin da muke ciki na ga ya kamata a yi rubutu da ke bayanin tufafin mata a Musulunci ta yadda kowace ‘yar uwa musulma  zata karanta ta gane haqiqanin tufafin da Allah ya ce, wa manzansa ya gaya ma matayensa  da ‘yayansa da matayen mumuinai su riqa sanyawa  (wato shigarsu ta kasance ko da yaushe yadda Allah ya ce[1]).  Domin Yahudawa maqiya  addinin musulunci kullun qoqari suke yi safiya da maraice wajen ganin sun lalata mana tarbiyyarmu masamman mata domin sun san in suka lalata mata to kamar sun lalata al’uma ne, da ma burinsu kullun so suke musulunci ya karye a daina jin labarinsa da tasirinsa a bayan qasa, kuma su Yahudawa so suke shigar matayenmu ta zama shiga ceta kafirce.                                                      
Wannan littafin shi ne bugu na huxu (4) ya taqaitune qarqashin Qur’an da Hadisi da maganganun sahabbai da magabata na qwarai (salafusSalih) ina roqon duk wanda ya karanta wannan littafin da ya yi ma ni addua ta alheri, kuma duk wanda yaga kuskure to kofa a buxe take ya aiko da gyaransa in sha Allahu za a gyara kuma muna farinciki da gyaransa.   Ba zan gushe ba ina mai godiya ga malam Abubakar Jumare Gixaxo Zaria da ya duba littafin tundaga farko har qarshe ya gyara kurakuran da ke ciki da kuma ba da shawara, Allah yasa ka ma shi da Aljanna amin. Ba kuma  zan manta da malami na ba malam Ahmad Bello Dogarawa   wanda  koda yaushe yakan qarfafaman muhimmanci  yin rubutu domin ‘’yanuwa su anfana shima Allah yasa ka ma shi da Aljanna   amin.                                                              
  Malam Haruna Ishaq Shika Alqali da Malami na malam  Mikail Isah Imam da Malam Muhammad Amin Jumare Maqarfi Alqali suma Allah ya sakamasu da Aljanna amin.  Da duk wanda ya taimaka wajen ganin wannan littafi ya fito Allah yasa kama shi da alheri amin.                                        

                                             .                                                                                 
A qarshe ina wa mahaifiyata Fatimatu Dalhatu Zaria da mahaifina malam Abubakar Ibrahim   adduar Allah ya saka masu da Aljannatil Firdaus   amin.                                          
                                          Wassalamu alaykum                                                                 Harun Abubakar Shika
                                            25 Ramadan 1429 / 24/9/2008
                                                           harunaabubakar99@yahoo.com
                                         08030582333 -08054533361-08020900001     

بسم الله الرحمن الرحيم
TAQARIZI
  Lallai gaodiya ta tabbata ga Allah muna gode masa  muna  neman taimakonsa kuma muna neman gafaransa muna roqon Allah ya tsaremu  daga  sharrin kawunan mu da munanan  aiyukanmu, Duk wanda Allah ya shiryatas ba bu mai  vatar da shi, haka kuma wanda Allah ya vatar dashi babu mai shiryar da shi ina shedawa babu abin bauta na  gaskiya sai Allah shi kaxai  ba shi da abokin tarayya, kuma ina  sheda cewa lallai Annabi muhammadu sallalahu alaihi wa,alihi wasallam bawansa ne kuma Manzansa ne. Naga littafin da xan uwa malam Harun Abubakar Shika (Izzah) ya wallafa wanda yake magana a kan Hijabi da Niqabi da wasu nasihohi da faxakarwa ga nau’oin jama’a daban-daban kamar mata masu fita irin ta jahiliyya da masu kuskuuren fahinta da jahilai masu sanya rigar ilimi da ‘yanBidia da sauran su babu Shakka mawallafin ya kyautata bayani kuma ya ilmantar kuma yayi nasiha Allah ya qarfafe shi don ci gaba da yin talifi, ya kuma yawaita mana irinsu. Dukkan wani mumini masoyin Allah mai kishi akan shiriyar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa’alihi wasallam zai yi farinciki da irin bayanin da littafin ke xauke da shi ganin cewa littafin bai qetare hujja daga Qur’ani da Sunnah da maganganun magabata na qwarai da suran Malaman musulunci ba, sai dai  shaixan da rundunarsa  za suyi baqin ciki da abin da ke cikin littafen.                                                       
           ومن يرد الله فتنته فلن تملك له من الله شيئا
Kuma kowane mumini zai burin Ina ma ace duk matayen musulmi zasu qawaci wannan littafi kuma suyi aiki da shi. Allah yasakawa malam Haruna da alheri duniya da lahira ya kuma taimakemu wurin Neman gaskiya da aiki da ita ya kuma shiryi matayen mu.                                                                               .
AbuAbdurRahaman             
                                                        Abubakar Jumare Gixaxo                                        4/1/1430 - 31/12/2008




بسم الله الرحمن الرحيم
                        MATSAYIN  MATA
Haqiqa Allah ya yi wa  muminai baiwa da ya aiko  masu manzo a cikinsu, ya bayyana  masu  shariar Allah, haqiqa Mata suna xaya daga cikin al’ummar da Allah ya karrama su ya kuma  girmamasu ya kuma  ba su kariya, kuma manzon Allah sallallahu alaihi wa,alihi wasallam   ya yi umarni da a kyautata ma su, kuma a karrama su kuma a ba su kariya kuma musulinci ya bayyana mana cewa idan mace daya ta yi karatu kamar an koyar da al’umma ne idan kuma  ta gyaru kamar al,uma ce ta gyaru,.mata suna da daraja mai girma.  A na cin nasarar al, uma ne in  aka lalata ma su matansu   kuma musulinci yana alfahari da mata, ba kuma zai manta da gudunmuwar da suke bayarwa ba tun, daga zamanin Nana khadijah Allah ya qara ma ta yarda,  da   Sumayyatu  har ya zuwa yau.   Iyayenmu mata sune makaranta ta farko da ke tarbiyar yara, shi ya sa musulunci kullun ya ke qarfafa kulawa da su kulawa ta masammam.[2]
            Yahudawa maqiya addinin Allah  kullun yaqi su ke yi  safiya da maraice wajen ganin sun lalata mata domin sun san su ne  qashin bayan al’umma sun san cewa mata suke bada tarbiyan yara, kuma sune tubalin gina  al’umma. Idan muka lura da kyau zamu ga yadda suke fito mana da abubuwan  lalata dabi’u kamar fina finai, ( fim)  da waqe – waqe da tufafin tsaraici da   qyaman aure,  da  kuma yadda Yahudawa suke wulaqanta su (mata) wajen sa hotunan su kan tituna kamar ِAllan bakin Titi (signbol) da  kayan sayarwarsu kamar sa hotonsu a jikin sabulu ko kayan sawa da  manshafawa da kwalaye don wulaqanta su, da sa su tsaran shago cikin shiga ta baxala, da kuma  qoqarin nuna masu  shiga ta addinin muslinci qauyanci ne kuma ci baya ne[3], saboda mata a wajen maqiya addinin Allah ba su da qima[4].  Lura da halin da muke ciki na ga ya kamata a yi ma yan’ uwa bayani yadda Allah ya umurci mata su rinka sa tufafinsu da kuma sharudxan hijabi, da yin bayani akan kayan da suke haramun ne ga matan musulmai su sa, da kuma bayanin kayan mata ‘yan wuta, da manzon Allah sallalahu alaihi wa, alihi wasalam  ya ce, al’ummar sa za su rinka sa wa a qarshen zamani, kuma za mu yi bayani kan Niqabi ta mahangar Kur,an da Hadisi da maganganu magabata na qwarai.
 Lallai yana daga cikin kariya ga mata da Allah ya yi masu wajen kare su daga dukkan tozarci, ya ce su sanya hijabi in za su makaranta ko aiki ko asibiti ko ziyara kai duk in da zata, ta sa cikakken hijabi wanda Allah yayi umarni da a sa cikakke wanda zai nuna    cewa ita mace ce kamammiya, mai mutunci da sanin ya kamata, mai bin Allah da Annabinsa sallalahu alaihi wa,a lihi wasallam. Hijabi Aqida ce wadda dole ne musulma ta sa shi in dai ta yarda da Annabi (sallalahu alaihi wa, alihi wasallam.)  kuma shi hijabi kamar sauran shari’o’ine wanda Annabawa suka yi bayani, to shi ma Annabi  Muhammad (sallalahu alayhi wa alihi wasllam) ya yi bayanin  yadda  ake so Hijabi ya kasance, kuma yana da sharudxan  sa  kamar yadda sallah da zakka da aikin hajji da azumi  da sauran ibadu Suke da nasu sharudxan, shi ma hijabi yana da na sa wanda dole ne hijabi ya cika  su  sannan ya zama hijabin musulunci, wanda Annabi sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya yi umurni da a sanya, idan har waxan nan sharudxan ba su cika ba, to haqiqa hijabin  bai cika hijabi karvabve ba.
Haqiqa kunya tana cikin kyawawan dabi’u wanda Allah ya aiko Annabi (sallalahu alaihi wa, alihi wasallam) da ita, [kunya] ta na da ga xabi’u kyawawa wanda   manzon Allah sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya sanya ta yanki da ga cikin rassa na imani[5] kuma babu mai inkari (musu) a kan kunya abar so ce, kuma sharia ta yi umurni da ita, sanya hijabi yana daga kyawawan xabi’u wanda Allah ya yi umurni da a sa sannan   manzansa yayi bayani   yadda ake sa shi kuma ibada ce  sanya shi (hijab).
Idan mu ka bibiyi tarihi za muga ba a ci nasarar Daular musulunci ta Qasar ANDULUS (SPAIN) ba sai bayan da matayen qasar suka daina Sanya hijabi suka riqa fita, fita ta fitsara Wanda haka ya jawo lalacewar xabi’un mutanen qasar ta sanidiyar rashin Sanya hijabi har aka ci nasara a kan su. Don haka ya zama dole mu kula da matan mu da yaran mu, mu tabbatar suna sa hijabi cikakke wadda shara`a ta yadda da shi.
MA, ANAR HIJAB
 Hijabi a cikin harshen larabci yana nufin shamaki ko  kariya, amma a ma’anarsa ta shara’a. Hijabi shi ne dukkan wani mayafi mai kauri da mata suke amfani da shi wajen rufe jikinsu baki daya har da fuskarsu duk da cewa akwai savani tsaqanin malamai kan rufe fuska.[6]
Manufar  umurnin  da Allah  ya  bayar na sanya hijabi shi ne domin mace ta voye kwalliyar ta (ado) kar wani ya gani sai dai mijinta ko xaya daga cikin waxanda Allah yayi wa izini a cikin suratun Nur domin tsare mutuncinsu da kuma toshe kofar varna da fitina ( fasadi.)[7]
An wajabta sanya hijabi ne bayan hijrar manzan Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallam   daga Makka shi da  sahabbansa Allah ya kara  masu yarda. Wato a garin Madina ne aka wajabta sanya hijabi. Ibn Qayyum Allah ya jiqan shi da gafara ya ce an saukar da ayar hijabi ne bayan shekara ta uku dayin hijran Manzan Allah sallallahu alaihi wa, alihi wasallam, ko kuma a shekara ta biyar bayan hijaran manzan Allah sallahu alaihi wa,alih, bayan kuma Annabi ya auri Zainab kuma lokacin da ya yi bina,i(tarewa) da Nana Zainab bintu  Jahash Allah ya qara yarda da ita [8]

SHARUDXAN HIJABI
Ga sharudxan Hijabi a jere Kamar haka.[9]
1.       Ya rufe dukkan jiki sai abinda aka togace.
2.       Ya Zama mai kauri ba shara- shara ba.
3.       Kada hijabi ya zama mai ado(kwalliya)
4.       Ya zama yalwatacce ba mai kunci ba.
5.       Ka da a sanya masa turare.
6.       Kada hijabi ya yi Kama da tufafin maza.
7         Kada hijabi yayi kama da tufafin  Arna (Kafirair                              
8        Kada ya zama tufafin alfahari.
9        Kar a sa masa hoto.
10    kar ya yi kama da na  ‘yan bidi’a
11   kar ya kasance yana da janjami (Cross)
Idan a aka  bibiyi ayoyin Alqurani da hadisan ma’aiki sallalLahu alaihi wa alihi wasallam da maganganun sahabbai  da sauran magabata na qwarai (salafusSalih) zakaga waxannan sharudxa baki xaya da suke nuna mana    sharudxan hijabi a muslunci.

1-  SHARAXI NA FARKO YA RUFE DUKKAN JIKI SAI INDA AKA TOGACE
 Yana da ga cikin sharudxan hijabi dole ne ya rufe dukkan jikin mace kamar yadda  Allah  ya faxa a cikin suratul Ahzab.

يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن ذلك أدنى أن يعرفن فلا يؤذين وكان الله غفورارحيما

Ya kai wannan Annabi ka ce ma matayenka da ‘ya’yanka da matayen muminai su kusantar da manyan kayansu da ke kansu zuwa kasa (wato hijabinsu tun daga saman kansu har  zuwa kasa) wanna shine ya fi dacewa da a gane su (matan mumina) bakuma za’acutar da su ba, kuma   Allah yakasance maigafara ne kuma mai jinqai,
Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da ya zo bayanin jilbab a wannan ayar a Tafsirin sa sai  ya nuna ta rufe jikinta duk kan sa ta bar ido xaya domin ganin hanya in zata fita.[10]
Sannan ayar da ke cikin suratu Nur  ita ma ta nuna mana mace ta rufe duk kan jikin ta sai dai in da  aka  togace. Haka shi ma Imamu Dabariy  ya kawo a tafsirin qarashin wannan aya.[11]                                                                                                                          
وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا
 ‘’Ka ce ma  muminai mata  su runtse daga ganinsu kuma su tsare farjinsu,kar su  bayyanar da  kwalliyarsu  sai dai abin da ya bayyana daga gare ta……...[12]
Manzon Allah Sallalahu alaihi wa, alihi wasallam ya ce ‘’wanda ya ja tufansa yana mai girman kai Allah ba zai ma shi kallo , kallo na rahama ba ranar Tashin kiyama.Sai Ummu salma matar manzon Allah sallalahu alai hi wa,alihi wasallam, Allah ya kara mata yarda ta ce yaya za mu yi da hijabanmu da ke janqasa ?’’ Sai Annabi sallalahu alaihi wa,alihi wasallam  ya ce to ku sake shi yana jan qasa dani xaya (tikan hannu). Sai  ta ce ‘’Qafafuwanmu zasu bayyana.’’ sai Annabi (sallalahu alaihi wa,alihi wasallam.) ya ce, to ku ja shi  qasa kamu xaya kar ku qara a  kan haka (wato kada a qara ya wuce kamu xaya a qasa)[13]
Sheikh Nasiruddeenil Albany  ya ce, a cikin  littafinsa ’Jilbab’ wannan hadisin yana nuna mana  a fili cewa lalle dole ne hijabi ya rufe qafafuwan mace, wannan dole  ne sai ya rufe mata qafa[14]
Shi ma Imamu Baihaqi haka  ya ambata  ya ce wannan hadisin dalili ne a kan dole ne mace ta rufe qafafuwanta.
Wani hadisin ya nuna cewa ko da ya tava qazanta ba komai qasar gaba ta tsarkake shi (hijab)  haka Annabi sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya faxa.   Hadisin  ya zo cikin Muwadxa                          
عن أم ولد لإبراهيم بن عبد الرحمن بن عوف أنها سألت أم سلمة زوج النبي صلى الله عليه وسلم فقالت : إني امرأة أطيل ذيلي وأمشي في المكان القذر ؟ قالت أم سلمة : قال رسول الله صلى الله عليه وسلم  يطهره ما بعده                                                                                                                                                                 An karbo hadisi daga Ummu Ibrahim bn AbdurRahaman bn Auf ta tambayi  UmmuSalama matar   Annabi sallalahu alaihi wa, alihi wasallam ta tambaye  ta ta ce,   ‘’Ni  na kasance mace ce mai dogon hijabi  yana jan qasa kuma ina tafiya a wuri mai najasa ? Sai  Ummu salama ta ce, Tsarkinsa (hijabin) qasar gaba manzan Allah sallalahu alaihi wa, alihi wasallam   yace qasar databiyo baya ta tsarkake shi[15]
Wannan bayanin a fili yake  ba komai don hijabi ya tava  qazanta, wata mata  wata rana ta ce ma manzan Allah sallahu alaihi wa, alihi Ni hanyar da na kebi zuwa masallaci  a kwai qazanta  yaya zan yi da hijabina da ke jan qasa ? Sai Annabi sallalahu alai wa alihi wasallam ya ce,’’ Ashe ba  akwai wata mai tsarki ba bayan ta  to wannan da wancan’’ (wato qasar gaba ta tsarkake ta baya) 

وعن امرأة من بني عبد الأشهل قال ( قلت : يا رسول الله إن لنا طريقا إلى المسجد منتنة فكيف نفعل إذا مطرنا ؟ قال : أليس بعدها طريق هي أطيب منها ؟ قالت : قلت : بلى قال : فهذه بهذه
 Don haka wannan hadisin ya nuna mana don hijabin da ya taba qazanta ba Komai a gare ki. Jeki muwadxa babin da ke bayani a kan kayan da a ka hana mata su sa na tufafi, Imam Malik ya kawo hadisin da Hafsatu ‘yar Abdulrahaman ta shiga wajen Nana Aisha Allah ya qaramata yarda, da  hijabin da baidace ba xan qarami,  sai taqwace shi ta yayyaga shi, sai ta sa ma ta hijabi mai kauri babba.[16]
Don haka yana daga cikin sharaxin hijabi ya rufe dukkan jikin mace kuma ya ja qasa.
Ya rufe ma mace qafafuwanta wannan dole ne bai halasta  a ga   qafarta ba.
Sheikh Nasurudin Albani ya ce[17] ‘’ ya yin  da aka tambaye shi game da qafar mace. Sai ya amsa da cewa, ‘’qafar mace al, aura ce da bai halasta  ta buxe ba   ko da a wajen sallah ne,  kuma matayan sahabbai sun kasance suna rufe qafafuwansu.Yace ya zo a cikin Sunan na Abi Dauda dake nuna  mace idan ta zo sallah ya zama dole ta rufe qafanta baki xaya.
 Babban malami Sheihk bn Baz shi ma yayi bayani mai gamsarwa  inda yace duk matar da tayi sallah qafarta a waje bata da sallah ko tana sallah qafarta ta fito bata da sallah.[18]
Shima Sheikh  Usaimin fahintarsa  kenan haramun ne mace tafitar da qafarta waje  yayin da ta fito daga gida ko kuma tana sallah.[19]
 Shieikh Muhammad Jamil Zaynu ya ambata a cikin littafinsa cewa lalle dole ne mace ta rufe qafarta in tana sallah ko kuma in zata fita waje, ya qara dacewa idan Mace tayi sallah qafarta a waje Allah bazai amshi sallarta ba ya ce ko ta sanya safa ta rufe qafarta. Haka hadisi ya nuna ruwayar Abu Daud.[20]Idan mace tayi sallah qafarta a waje  bata da sallah  wannan itace fahintar  Nana A’ishatu Allah ya qara mata yarda da  Nana Maimunatu  da Ummu Sallama  dukkan su matayen manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam sun ce idan mace ta yi sallah qafarta a waje bata da sallah  sai ta sake  sallarta.[21]
Don haka dole ne hijabi ya rufe qafar mace wannan sharaxi ne. Haka nan hadisi ya zo mai lamba 173 cikin lttafin Tirmidhi  da littafin sunan na Imam Nasa’i mai lamba 29 wanda  Ibn Umar yaruwaito  duk suna nuna mana   dole ne mace ta rufe qafarta a waje  ko yayin da take sallah.
 Amma mata masu fitar  da qafafuwan su a fili ga mazajen da ba suna aure dasu bane kuma ba muharransu ba lalle sun sava ma Allah da manzon sa, kuma suna cikin fushin Allah. Haka nan ma yana daga cikin abin baqin ciki za ka ga mata musulmai suna tuqa mashin qafafuwansu a waje wannan haramun ne kuma bai dace da su ba a matsayinsu na musulmai  masu mutunci, sannan wata babban musiba da ke damun duniyar musulman Arewacin Nijeriya itace yadda mata suke hawan ‘’yan acava  wanda yake haramun ne namiji ya goya matar da ba tashi ba  a  kan mashin wannan babu savani a tsakanin malamai cewa haramun ne mace ta hau (Expresss) acava ;  shi ma haramun ne ya xauke ta  ya goya ta a mashin. Ya kamata masu yin acava da su ji tsoron Allah, su sani fa da su haxa jikinsu da jikin matar da ba tasu ba ; yafi masu sauqi su sa jikinsu  a garwashin wuta kamar yadda hadisi  ya zo a kan hanin na miji yahaxa jikin sa  da matar da batashi ba. Wani  hadisin ma cewa ya yi gara ya sami qarfe mai tsini ya sossoke idonsa ya fi mashi da  ya haxa  jikinsa da mace wadda batasa ba[22],  wani hadisin manzon Allah cewa  ya yi da mutum ya haxa jikinsa da matar da bat asa ba ya fi mashi sauki ya je ya rungumi aladen da ya  cakuxu da tavo qazanta (kwata) da ya haxa jikinsa da wata mace.[23]  Allah ya kare mu. Balle masu fita, fita ta fitsara gashin kansu a waje. Masu tafiya ko hijabi babu sai gyale, wanda ko munsani cewa sa gyale haramun ne ”ya mace tasa gyale ta fito waje. Lalle mata masu sa gyale su ji tsoron Allah su  sani  fa  cewa  addinin Allah  bawasa ba ne kuma su tuna  mutuncin da qima da martaba da Allah ya yi ma su, su kiyaye dokokinsa.[24]

2. SHARAXI NA BIYU KADA YA KASANCE MAI KWALLIYA
Yana daga cikin sharaxin hijabi ya zama ba mai kwalliya ba, (wanda babu ado a jikin sa) babu cin baki, mai daukar hankali ko wani ado a jikin shi, domin faxan manzon Allah (sallallahu alaihi wa,alihi wasallam). Mutane uku kada  kayi tambaya a game da su, domin halakakku ne : mutumin da  ya rabu da jama’a ya saba ma shugabansa, ya mutu mai sabon Allah. Da kuma bawa ko baiwa da ya guje ma uban gidansa sai ya mutu. Da matar da mijinta ya yi tafiya ya bar mata abin da zai wadace ta na buqata, amma sai ta yi tabarraji ta fitar da kwalliyarta a bayan shi, to manzon Allah sallahu alaihi wa,alihi wasallam  ya ce,  ‘’kar ka yi tambaya a kansu domin suna wuta.[25]’’
Bai halasta ba a yi ma hijabi ado ba. Duk wani nau’i na kwalliya bai dace mace ta yi ma hijabinta ba.  Allah ya kawo mu wani  lokaci da mata ke sa wani irin gajeren hijabi mai santsi bai da kauri wai sunansa sorry ustaz, Alhamdu lilLahi shi dama Ustazu baya  sha’awar fasikai balle a ce  masa sorry,
الخبيثات للخبيثين والخبيثون للخبيثات والطيبات للطيبين والطيبون   للطيبات                                                          
Ko a tsokani shari’a, ko kuma suna kiran sa Rubber  hijab ko Jahannama ga fasinja ko please call me.  Da kuma wani wai shi made in France, ko Half breast ko Breast line[26]da wani wai shi show me your breast, ko half sunnah  da Baba na balaga da talaka bai da rabo Zura hannunka masoyi subhanallah لا إلَهَ إلا اللهُ  wallahi ‘yar uwa abin kiyi kuka ne haba ! haba ! haba ! don Allah ki tuna darajar da Allah ya yi maki, dukkan waxannan hijaban dai  ba su halasta mata su  sanya su ba.
Kamar yanzu za ka  ga  waxansu mata da hijabi mai  kyalkyali, wannan bai dace ba domin wannan qyallin  kwalliya ce.Ko wasu ka ga sun sa ma  hijabinsu fulawa, ko kuma ka ga an yi ma shi aiki kamar irin wanda suke kira da suna Made in France  ko wanda su ke yayi a yanzu kamar wanda suka yi  yayinsa da wannan Sallar bana  a shekara 1429 (2008).kuma kowace  shekara su kan fito da wani sabon salon na savo.
Shi yasa ma wasu malaman suke ganin bakin hijab yafi dacewa  a ko wane zamani da lokaci koma shi ne mafifici domin bai da ado ko wani kwalliya a jikinsa.[27] Shi yasa wasu Malaman suke ganin rashin dacewar mata masu aikin Hajji da suke xinka fararen kaya don ihrami kuma gashi bai cika wannan  sharrudxan ba, da mata  za su dinka bakin Hijabi wajen aikin hajjinsu da yafi kamar yadda sauran alhazan duniya suke yi. Ya kamata muma namu matan su daina xinka fari  domin dacewa da alkhari.
Wani abin ban takaici da baqin ciki da mamaki  shi ne a kwanakin baya mata  suna qoqarin   shiga    yadda Allah da manzansa suka yi  umurni. Idan kai  tafiya cikin garuruwanmu  zaka ga  ‘’yan kaxan  ne daga cikin mata  ba sa sanya  hijabi   cikakke  yalwatacce.  Kuma zaka ga sun zama daban kuma suna jin kunya.  Amma wannan sallar abin ya canza inda mata suka sa qananan hijabai masu kwalliya abin gwanin ban takaici. Allah ya kyauta kuma muna roqon Allah ya ba ‘’yan uwan mu mata damar gyara shigarsu amin.
Haramun ne uba ya bar yarinyarsa ta sa irin wannan hijabin  da  a ka yi yayinshi da  wannan sallar(Rubber hijab ko sorry ustaz, ko please call me ko a tsokani shara’a ko sai na shiga ko jahannma ga fasinja ko half sunnah)  mai qyalli ko xan qarami ko shara-shara    idan uba ya bar ‘’yarsa tana sa hijabi mai kwalliya ko gajere wanda bai rufe qafa ba  yin haka zai haifar masa da  shiga  cikin  fushin Allah  shi da ‘’yartasa. Don haka ya zama dole uba ya kiyaye kar ya faxa cikin azabar Allah shi da ‘’yartasa.
Manzan Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce duk matar da tafitar da kwalliyarta a waje to ita mazinaciyace. Hijabin da su ke kira da suna please call me kamar tana cewa ita mazinaciya ce a kirata, Allah ya tsare mu.

3.  SHARAXI NA UKU  YA ZAMA  MAI KAURI BA SHARA-SHARA BA
 Dole ne hijabi  ya zama mai kauri  ba mai shara-shara  ba.   Manzon  Allah  sallahu alaihi  wa,alihi wasallam  ya ce, ’Da sannu a qarshen al’ummata, wasu mata  zasu  saka tufafi amma tsirara suke, wato a tsiraice  su ke,kawunansu kamar tozan rakumi, manzon Allah ya ce’’ Ku la’anance su, domin la’anannune.’’ A wata ruwaya manzon Allah ya ce, Ba za su shiga al’ jannaba (waxannan matayen masu sa kaya shara – shara), ba kuma za su ji qamshim al’janna  ba.    Qamshinta  a na samu  na tsawon shekara kaza  da kaza[28]
 Dole ne hijabi ya kasance mai   kauri wanda bazai nuna jikinta ba. Wannan hadisin yana nuna mana cewa mata masu karin gashi ko masu sa gwaggwaro ko masu sa matsatsun kaya duk sun shiga cikin wannan siffar da Annabi  sallahu alaihi wa, a lihi wasallam ya ce  a tsine masu   a cikin hadisinsa.[29]

4.  SHARAXI NA HUDU  YA ZAMA                     YALWATACCE.       
 Ya  zama  yalwatacce mai faxi sosai  banga-banga,  ba  mai  qunciba,  saboda kada ya nuna wani abu na jikinta kamar ;    Ya siffantar da wani abu daga jikinta kamar ya nuna  alamar  tudun nonanta ko tudun duburarta. Ko cinyarta ,ko dai wani wuri da zai iya jawo fitina  ga maza ,Usama   bn zaid   ya ce,’’ manzon Allah (sallalahu alaihi wa,alihi wasallam) ya tufatar da ni wata riga mai kauri daga abin da  Dhiyatul  kalbiy ya  ba shi kyauta, ni kuma sai na tufatar da mata ta  ita sai manzon Allah Sallalahu alaihi wa, alihi wasallam  ya ce me ya sa baka sa ba ?, sai   nace na tufatar da matata ita. Sai manzon Allah sallahu alaihi wa,alihi wasallam  ya ce.’’To ka umurce ta da ta sanya wata a qarqashin  ta domin ina tsoron kada ya   siffanta  nauyin gavuvuwanta.[30] Wanan yafito da maganar a  fili ta buqatar hijabi ya kasance yalwatacce mai fadi so sai.
Hafsatu yar AbdirRahan tashigo wajen Nana Aisha Allah ya kara mata yarda da wani dan qaramin mayafi mara kauri kuma gajere. Nana Aisha ta kwace shi ta yayyaga shi, sannan ta sa mata mai kauri babba[31]
Don haka sharaxi ne hijabi yazama mai faxi sosai kuma mai kauri ba fake-fake ba.

5.  SHARAXI  NA BIYAR  KADA A SA MA SHI     TURARE 
Ka da a sa ma hijabi   turare, turaren nan na ruwa ne ko turaren wuta ne da sauransu hadisai   masu  yawa sun zo suna  haramta ma    mata  su  sanya  turare in za su fita daga gidajensu.
Ga wasu hadisan   kamar   haka:   Abu Huraira ya ce manzon Allah   sallahu alaihi wa,a lihi wasalam    ya ce “Duk matan da  ta  sa   turare kada ta je sallar Isha’i    tare da mu.’’’[32]
Abu Musa al’ ash,ariy    ya ce   manzon Allahsallahu alaihi wa,alihi  wasallam   ya ce, Duk matar da ta shafa turare ta wuce wajen wasu  mutane domin   su ji  qamshinta, to ita mazinaciya  ce.’’’ [33]
 Manzon Allah sallalahu alaihi  wa,a lihi wasallam ya ce, idan xayarku zata masallaci kada  ta kusanci turare[34] … Don haramun ne mace ta shafa ma hijabinta turare ta fita waje, ko  ta shafa man shafawa  mai  qamshi ta fita waje, kuma mun fahimci  abin da hadisin   ya ce idan mace tasa turare to ta zama tamkar mazinaciya  ce in dai da ta sa ta fito waje. Allah ya kyauta. Don haka mata ya kamata ku ji tsoron Allah,ku san ce wa Allah yana ganinmu,ku bar shafa turare a tufafinku in za ku bar gidajenku, domin  sa turare in za ku fita bai halasta  ba  a gare ku(mata), saboda    hanin  da  Manzan Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya yi.
Wani hadisin ma manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam cewa ya yi “Duk matar da ta sanya turare ta fito waje ta wuce ta wajen wasu mutane don suji qamshin turarenta to ita mazinaciyace[35]
Amma kuma akwai hadisin da Annabi sallallahu alaihi wa`alihi wasallam yace turaren mata wanda launasa ya bayyana amma qamshinsa ya voye (wato turaren mata su kaxai suke jin qamshin abinsu in sun sa wani ba zai ji ba  sai dai su kaxai  kawai za su ji qanshin). 
Waxanan hadisan ba suna hani ba ne a Kan mace tasa turare baki xaya ba. A’ a zata Sa abinta a cikin gidan ta don mijinta yaji qamshin turaren nata don ta burge mai gidanta, bai dace ga matar aure da ta zauna a cikin gidanta tana wari ko biji-biji ba kyan gani.[36]

6. SHARAXI NA SHIDA KADA YAYI KAMA DA TUFAFIN ARNA.
Kada ya yi kama da tufafin Arna [kafirai] An samo hadisi daga Abdullahi bn Ummar Allah ya qara masa  yarda, ya ce, ‘’Manzan Allah sallahu alaihi wa,alihi wasallam yaga  tufafi masu ruwan zinariya [gold] a jiki na sai ya ce “Haqika wannan yana daga cikin tufafin kafirai, don haka kar ka sanya  su.[37]
Wannan hadisin ya haxa har da maza, su ma haramun ne su sanya kayan arna.
Sannan wani hadisi daga Ali Allah ya qaramasa yarda ya ce ‘’Manzan Allah sallahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce”Na hane ku daga sa tufafin fastoci ,fada-fada, domin duk wanda ya yi shigar ta su ko ya yi kama da su to shi yana  tare da su[38] kamar Academic gown da ake sawa a makarantu ranar bukin rantsar da su (Matriculation)
 wannan rigar asalinta daga Coci take, yakamata “yanuwa su guji sa wannan rigar.
Wannan hadisin shi ma  ya  game gaba dayan musulmai  da su daina   shiga  ta Arna Kayan da a ka san Arna da su haramun ne shi musulmi ya sa. Kamar wanda a kan sanya yayin yayen dalibai a makarantun gaba da sakandere da kuma Lauyoyi a kotuna. (Sai  ai hattara)
Wani hadisin cewa ya yi wanda yayi kama da wasu jama’a  yana tare da su.
  Ibn Taimiyya ya yi bayani sosai kuma mai gamsarwa kan haramci sa kayan Arna da koyi da su[39]

         7-SHARAXI  NA BAKWAI KADA YA YI KAMA DA TUFAFIN MAZA.
          Kada ya  yi  kama da tufafin maza, Manzon sallahu alaihi wa,alihi wasallam  yace ‘’Bashi  tare  da ni namijin da ke  kamantuwa da mata wajen sa tufafi.  Da mace da ke sa tufafin maza’[40].
          Hadisai ingantattu sun zo suna tsine ma matar da ke sanya     kayan maza.’’’ 
          Abu Dauda ya ruwaito hadisin da manzan Allah sallallahu   alaihi wa’alih wasallam, ya ke tsine ma namijin da ke sa tufafin mata,da matar da ke sa kayan maza[41].
          Allah yakare  mu.  Yanzu zaka ga mata na sa kaya matsattsu da wanduna su fita waje ba sa jin kunyar Allah da Manzansa. ko kuma su xinka yadi da yake maza kawai a ka san su da  shi balle uwa uba Xan daudu wanda mazon Allah sallahu alaihi wa, alalihi wasallam ya tsine ma shi,   Allah ya shirye smu baki xaya.
           Manzon Allah sallallahu alaihi wa`aihi wasallam ya ce a wani hadisin ‘’ Allah ya tsine ma matar da ta kamanta  kanta da maza da namijin da ya siffanta kansa da mata’’[42]
           Sabo da haka yana da ga cikin sharaxin   hijabi  ka  da ya yi kama da kayan maza.

           8-SHARAXI NA TAKWAS  KADA  YAZAMA  TUFAFIN   ALFAHARI.
         Kada ya zama tufafi na alfahari wato mace ta sanya kalan hijabin da yake  yadin na  kece  raini ne  ko na alfahari  ko  na  nuna isa da ji-ji da kai  Manzon Allah  ya ce ‘’wanda ya  sanya tufafin alfahari a duniya, Allah zai sanya masa tufafin qasqanci a ranar alqiyanah, kuma sannan a hura wuta a cikin ta"[43]
            Kuma dama musulunci ya hana girman kai   wani hadisin yana gaya mana bazai shiga  Aljannah ba wanda yake  a cikin zuciyarsa   akwai  qwayar zarra na  girman kai[44] .
           An samo hadisi daga  Abi Huraira Allah ya qara mashi yarda  ya ce ‘’’Mazan Allah sallalahu alaihi wa’alihi wasallam  ya ce ‘’wata  rana wani mutumi yana tafiya rigarsa (ta alfahari) ta burge shi nan take Allah ya girgiza qasa da shi yayi qasa  manzon Allah ya ce, Har yanzu yana cigaba da tafiya cikin qasa har ya zuwa tashin qiyama.[45]

           9-SHARAXI  NA TARA KADA YAKASANCE YANA DA KUROS.
           Yana daga cikin sharaxin  hijabi kar ya kasance yana da Kuros gecciye (cross) a jikinsa. Ba ya halasta a  sa tufafin da ya ke akwai kuros a  jikinsa, hijabi ne ko riga ce, domin  kuros alama ce ta Nasara  kiristoci ,kuma suna raya cewa Annabi Isah ne suka gicciye wanda  ko karya ce suke yi, Allah ya qaryata su a cikin suratu Nisa kuma Annabi Isah bai  mutu ba zai  dawo a karshen duniya haka Annabi ya yi bayani kuma kur’ani ma bai ce Annabi Isah ya mutu ba yana a raye a sama  manzan Allah ya ganshi lokacin daren Isra’i 

وقولهم إنا قتلنا المسيح عيسى ابن مريم رسول الله وما قتلوه وما صلبوه ولكن شبه لهم وإن الذين اختلفوا فيه لفي شك منه ما لهم به من علم إلا اتباع الظن وما قتلوه يقينا   بل رفعه الله إليه وكان الله عزيزا حكيما   
Ka nemi Tafsirun Imamun Nasa’i zakaga bayani                                                                                  gamsasshe kan cewa   Annabi Isah bai mutu ba kuma zai dawo.[46]                                         .
          Abin da ke qara nuna mana haramcin sa  tufa da ke da    Janjami (cross) korus  a jikin sa shi ne hadisin da Iman bn Haddan ya ruwaito Nana Aisha Allah ya kara ma ta yarda ta gaya ma shi cewa haqiqa manzon  Allah sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya kasance ba ya barin wani gida da yake da kurus face ya  kawar da shi[47]
           Yana da kyau musulmi  in zai sayi kaya  ya tabbatar babu  Janjami kuros (cross) ko alamarsa ajikin kayan kafin ya saya akwai wata akwatin kamo qasashen waje (Receiver) mai xauke da Kurus sunanta PAUXIS, duk wani abu daya ke da kuros haramun ne musulmi  ya kawo shi gidan sa.   Anan  zamu fahinci ‘’yan uwan mu da ke sa rigar qwallon (Jesi) na BERCELONA da na REALMADRID da ke xauke da kuros da su ji tsoron Allah su daina sanyawa tun da bayani yagabata  da ke nuna mana haramcin sa kaya mai Janjami (cross).[48]
                 Abin da ke qara nuna mana haramcin sa  tufa da ke da janjami (cross)  korus  a   jikin sa shi ne hadisin da Iman bn Haddan ya ruwaito Nana Aisha Allah ya qara ma ta yarda ta gaya ma shi cewa haqiqa manzon  Allah sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya kasance ba ya barin wani gida da yake da kurus face ya  kawar da shi[49]
            Shi yasa Ibn hajr a cikin ‘’Fathul Bari’’ ya ce wanna hadisin yana bayani ne har da kayan sawa haramun ne musulmi ya sa kaya mai janjami (cross) kuros.
           Shi kuma bn Malhi almaqdis ya ce abin qyama ne ga musulmi  ya sa tufan da ke da  kuros. Shi  kuma bn Hamdan ya ce haramun ne. [50]
           Imamu Safaarani ya ce haramun ne sa tufa mai kuros a jikinsa. Ya yi  bayani mai tsawo. Ya kuma kawo maganganun magabata  da ke nuna haramcin sa kaya masu kuros.
        Akwai makarantar da yake janjami (cross)ne  bajen su bai halasta musulmi ya kai xansa wannan makarantar ba.

           10- SHARAXI NA GOMA KADA YA KASANCE YANA DA HOTO.
           Sharadi na goma kada hijabi ya kasance yana da hoto  a jikinsa, gabadayan junhurun malamai sun tafi kan haramcin rike wani abu da yake xauke da hoton abin da ke da rai wannan hoto na Xan Adam ne ko  Dabba ce  wannan hoto a  bango akasa shi ko a jikin tufafi ne.  Ko a labule akasa shi kai ko mene  haramun ne a  sa hoton abin da ke da rai.[51]
           An samo hadisi da  ga Xalhatu Allah ya qara masa yarda ya ce manzan Allah sallallahu  alaihi wa, alihi wasallam ya ce, ‘’Malaikun  rahma ba sa shiga gidan da ya ke akwai hoto ko kare[52]
           Hadisi ya  zo daga Nana Aisha Allah ya qara mata yarda ta ce, ‘’ manzan Allah sallalahu alaihi wa, alihi wasallam ya shigo xaki na  na sa  labule mai xauke da hoto  da ya gani  idon sa ya canza  fuskarsa ta canza yasa hannu ya yayyaga shi  san nan yace ‘’haqiqa waxanda suke shiga azaba mai tsananin ranar kiyama sune  ma su yin kwaikwayon  halittan Allah.[53]
          Bai halasta a sa ma hijabi hoton wani Shehi ba, ko wani malami ba ko wani irin hoto ne dai haramun ne,  in dai hoton halittar tana da rai  ko da wannan hoton ba na abin da ke da rai  ba ne,  ba  a  yarda a sa shi a jikin hijabi ba.   Shi ya  sa wasu malaman suke cewa baje (na alamar makaranta)   shi ma ya shiga domin zai kasance ya bada  kwalliya a jikin hijabin.[54]
          Yazama  dole Alhazan  su gyra su daina xika kayan aikin hajji da hoton Gwabnonin su  wannan kuskure ne kuma bayyanar da jahilci ne a gaban musulman duniya ga kuma sava wa Allah da Annabinsa.
11.      SHARAXI NA GOMA SHAXAYA KADA YAYI KAMA DA TUFAFIN  ‘’YAN BIDI’A.                                                                                                        
          Ya na daga cikn sharadin hijabi kada yayi kama da hijabin  ‘‘yan Bidi’a kamar masu bin addinin Shi’a  dake sa hijabinsu,  su  tsaga qasansa su matse fuska bai kaiwa qasa.   Fuskarsu a matse, ba ya kaiwa kasa.
          Kamar ranar Ashura 10 ga watan Muhararram[55] suna da hijabin da suke sanyawa  na masammam domin wannan ranar baqaqe  suke sawa domin baqin cikin wannan ranan, Sheikh Usaimin ya ce yin haka Bidia ce[56]
 Wadannan su ne sharuddan hijabi wanda ya ke dole  ne ko wane hijabi sai ya cika su sannan ya zama hijabi wandaAllah ya ce a sanya, dama mun san cewa sa gyale haramun ne, Nana A’ishatu taga wata mata da gyale ta ce mata Allah wadanki’’[57] kuma lalle mata su ji tsoron Allah, su sani fa  manzon Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce mata, su ne suka fi yawa a gidan wuta, don haka  su rinqa shiga wanda  Allah Ya yi umurni  da shi. Kuma su guji yawon banza - da kallon fitsararru 'yan firm xin Hausa   masu yada varna a bayan kasa masu lalata  tarbiyan yara marasa kunya masu koyar da zina da yaxa ta.

إن الذين يحبون أن تشيع الفاحشة في الذين آمنوا لهم عذاب     أليم في الدنيا والآخرة والله يعلم وأنتم لا تعلمون                                 
Kuma iyaye su sani fa Allah ya ba su amana ne kuma zai tambaye su, sannan su tuna da cewa Allah yace ku kare kanku da iyalanku daga wuta wadda makamashinta  duwatsu ne da mutane[58].Yana da kyau uba ya tabbatar yaransa nashiga  wadda  Allah ya yi umurmi da  ita, domin kokarin sauke nauyin da Allah ya xaura masa na kula da tarbiryar yara.[59]
Kuma hatta ranan sallah a tabbatar sun sa hijabi   kar a barsu da hijabin da su ke ce ma shi sai na shiga ko sorry ustaz  ko robber hijab ko please call me’ ko half sunnah ko Jahannama ga fasinja, ko half  lenght ko have breast ko baba na balaga ko saka hannunka masoyi ko Alhaji kar ka bar banza ko talaka bai da rabo ko karuwa a Masar ko tayani gantali ko maraba da Aljanu waxannan  hijaban haramun ne  Mace musulma ta sa su, haba ‘’yar’uwa ke da ga jin sunan kinsan akwai izgili da tozaci da wulaqanci ga addini Allah, bayan  ko Allah yana cewa :

أبالله وآياته ورسوله كنتم تستهزؤون                    
“shin Allah da ayoyin Sa da manzon Sa ne ku ke ma isgili”

 Tarbiya dole ne iyaye su kula da ita kula   ta masammam  kuma Annabi ya ce wanda bai  da kishi bazai shiga Aljanna ba yana daga rashin kishi kabar matarka ko ‘’yarka tana fita ba hijabi cikakke wanda Annabi yayi umurni da a sa. [60]
Kuma yanzu bincike ya tabbatar da cewa mata masu sanya hijabi  sun fi saurin samun mazajen Aure kuma anfi son su.
                                         NIQABI
Niqabi  wani kyalle ne da mata ke amfani da shi wajen rufe fuskarsu daga maza. Baki ne  ko fari ne ko wane  irin qyallene. Nikabi  da safar  hannu sanannu  ne ga mata tun zamanin Annabi sallalahu alaihi wa, alihi wasalam, Ana sa Niqabi da safan hannu  kamar yadda yazo a cikin Bukhari, manzon (Sallallahu alaihi wa,a lihi wasallam) ‘'ya ce ‘’Masu aikin Hajji mata  kada su sa Niqabi da safar hunnu. Wannan yana nuna  mana cewa akwai Niqabi da safan hunnu ga mata tun zamanin manzo  Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.   Kuma wannan niqabin ba ace sai kyakkyawa ba. Domin kai ne a wajen ka mummuna amma wajen wani ita kyakkyawa ce.  Akwai karin maganar   Larabawa  da suke cewa kowace tsintuwa akwai mai xaukarta.
Kuma yadda aka umurci maza su cire hula ko rawani a lokcin aikin hajji. Kenan idan ba aikin hajji  sananen al’amari ne namiji zai sa hularsa a koina. To haka itama mace game da sha’anin Niqabi.[61]
  matayen manzon Allan sun sanya Niqabi, matayen sahabai suma sun sanya niqabi matayan Tabi,ai, suma sun sa  Nikabi sunna ce a wajen wasu malaman, wasu kuma suka ce sunnace mustahabbiya, wasu malaman  su kace suna ganin wajibi ne sa Niqabi, muna iya cewa Malaman  Musulunci sun kasu kan NIQABI kamar haka.
1-     SUNNA CE
2-      SUNNACE MUSTAHABBIYA
3-     WAJIBI NE (Dole ne mace  ta rufe fuskanta).

NIQABI YANA DA ASALI
Da farko dai  ga hadisai dake nuna mana kasancewar  Nikabi yana da asali tun zamanin Manzan Allah sallahu alaihi wa, alihi wasallam.[62]
1.      An samo daga Nana      Aisha     Allah yaqara mata yarda     ta ce "Mun kasance a wajen aikin Hajji tare da manzon Allah sallallahu alaihi wa’alaihi wasallam idan mahaya suka zo wucewa ta wajen  mu sai mu saki Niqabin mu, mu rufe fuskarmu, idan sun  wuce sai mu bude fuskarmu"[63].
2.      Haka  ma hadisi yazo a cikin Bukhari yayin da                                                                                        aka tafi  aka bar Nana Aisha  Allah ya qarama ta yarda  a kan ba a sani ba, domin ta  tafi neman abin wuyanta,da ta dawo ta taras sun  tafi sai ta zauna a wurin da take,sai barci ya xauke ta. A kwai wani sahabi mai suna Safuwan bin Mu'adilassalami yakan biyo baya ko wani ya bar kayansa sai ya xauko ya taho da shi.   A ne mi mai shi a ba shi. Daya zo sai ya ganni dama ya san  ni  kafin a saukar da ayar Hijabi sai ya ce subhanallahi sai nafarka da istirja'insa sai na rufe fuskata da hijabi  na.[64]Wannan hadisi ne shahararre Wanda a ka fi sani     da Hadisatul ifki.
3.        Nana Asma'u 'yar Abubakar Saddiq ta ce,’’ Mun kasance muna rufe fuskarmu daga maza kafin haka a wajen aikin hajji ba ma rufewa.’’[65]
4.         Haka nan da matar Ikirama ta musulunta, ita ma ta sa Niqabi ta rufe fuskarta domin ta musulunta a wannan lokaci  ta  je wajen manzon Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam’ [66]
5.        Hadisi ya zo daga Anas a cikin qissar Nana Safiya a lokacin yakin khaibar, manzon Allah ya zavi Nana Safiya ma kansa [a matsayin matarsa   sai Annabi ya fito bayan ya sadu da ita sai ya sa ta a kan rakumi, kuma yasa bargonsa ya rufe mata bayanta da fuskanta.[67]
6.        An samo daga Nana Safiya ta ce "Na ga Nana Aisha tana dawafi a wajen aikin hajji tana sanye da Niqabinta.’’[68]

7.        An samo da ga Fadhimatu bin munzir ta ce,’’ Mun kasance muna rufe fuskarmu kuma mun kasance wajen aikin hajji muna tare da Asma'u yar Abubakar Siddiq [da niqabi ba wanda ya yi mana inkari.’’[69]
Imam Baydawi ya faxi qarqashin ayar da Allah ya ce "Ku yi qasa da jilbab" ya ce su rufe fuskansu da dukkan jikinsu[70].
A Mazhabar Shafi`iyya da Malikiyya, da Hanabila sun tafi kan cewa fuskar mace al'aura ce kuma dole ne ta rufe fuskarta wajibi ne,  bude fuska haramun ne   Albany ma ya kawo wannan maganar a littafinsa Jilbab  shima mai Tarbiyatul Aulad Nasihil Ulwan yakawo wannan maganar.
Mazhabar Hanafiyya sun ce fuskar mace ba dole ba ne ta rufe fuskarta ya halasta ta buxe fuskarta In dai ba'a tunanin faxawa cikin fitina. In an tabbatar ana lokacin aminci to ba komai tana iya buxe fuskar ta.  Tambaya anan  shin yanzu muna lokacin aminci ?  
8.         Abdullahi bin Umar " ya ce, Nana Safiya ta ga Nana Ai'sha da Niqabi a tsakiyar mutane kuma  ta gane ta[71]
9.     Ummu Salma matan manzon Allah (S.A.W) " ta ce ‘’Mun kasance ba ma rufe fuskanmu idan muna gida, amma idan zamu fita sai mu rufe fuskarmu [72]
10.     Manzon Allah ya ce, ‘’Masu aikin hajji mata ba sa  sa Niqabi ko safar hannu.’’[73] 
Shaikhul Islam bn Taimiyya ya ce wannan Hadisin yana nuna mana a fili qarara cewa lalle  akwai Niqabi tun zamanin manzon Allah kuma shara'ar Allah ce mata su rika sa Niqabi. Yace waxanda basu je aikin hajji ba suna sa Niqabi da safar Hannu.[74] Kuma matayen Annabi  suna sa Niqabi suna rufe fuskarsu daga maza. Kuma  matayen Annabi suna sa Niqabi kuma  matayen sahabbai suna sa Niqabi, kuma matayen tabi'ai su ma suna sa Niqabi.
11.     An samo daga Asim xan Ahwal ya ce, "Mun kasance muna shiga wajen Hafsatu 'yar Sirin wadda ta haddace Qur'ani tana da shekara goma sha-biyu, ta mutu tana da shekara saba'in. I dan  muka shiga sai ta ja Jilbab xinta ta rufe fuskarta da Niqabinta.’’[75]
12.       Wata mata tazo wajen manzon Allah sallallahu alaihi wa,alihi wasallam ana kiran ta da suna UmmuKilad                                                                   
ta zo tana sanye da Niqabinta, tana tambaya  game  xanta. Manzon Allah  sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce’’ Xanki na da lada ta shahidai biyu. Sai ta ce ‘’Sabo-da mene ? Sai Annabi ya ce saboda Ahlul kitabine suka kashe shi’’.[76]
Sahabi Abdullah ibn Abbas Allah ya qara masa yarda  ya ce  Allah ya umurci matan mumuinai  idan za su fita da ga gidajensu  domin wata  buqata  su  rufe fuskokinsu da jalabib din su  su bar ido daya.[77]
13. An samo  hadisi acikin al-Musannaf na Abi Shaybah idan sahabi Umar yaga baiwa da Niqabi dokanta yakeyi ya ce ta cire shi domin ita baiwa ce ba ‘ya ba ce. (idan mace  ta fito ba niqabi ana xaukanta baiwa ce  ba ‘ya ba  shi yasa sahabi Umar ya ke dukan wadda ta sa niqabi in baiwa ce) wannan ya nuna mana a fili niqabi yana da asali.[78]
Waxannan hadisai suna nuna mana falalar Niqabi  da kuma nuna mana yana da asali  a addinin musulunci kuma ta’adace [dabiace] ta masu karamci da kunya,[79]  kuma manzon Allah ya tabbatar. Kuma  da  sanya  Niqabi ba sharia  ba ce da manzon Allah yahana  da  kuma matayan sahabbai basu sa  ba  kuma da an samo wani magabaci ya yi  rubutu yana nuna cewa babu kyau, ko bidiace ko kuma su yi  rubutu suce sai kyak kyawa.  Babu masu cewa sa niqabi ba kyau  ko su faxi maganar da ba tadace ba sai yan bidia "yan Bidi'a ma kiya sunnar Annabi sallahu alaihi wa’alihi wasallam da kuma Yahudawa makiya addinin Allah, da Jahilai.
Waxannan su ne Hadisai da suka zo suna mana bayani a kan sa Niqabi akwai shi (tunzamanin manzon Allah, kuma matayen masu karamci  da mutunci da daraja sun,sanya(niqabi),   masu cewa sa Niqabi Bidi'ace   su ji tsoron Allah su sani cewa ilimi yana da faxi,  idan baka karanta ba karkace babu, domin yin haka zai nuna ma duniya cewa     kai jahiline kuma, ka na suka ne kan matayen Annabi sallallahu alaihi waalihi wasallam da matayan sahabbai da matayan Tabiai Allah ya qara yarda da su bakixaya,kuma halin   da muke ciki bai dace a hana mata sa Nikabi ba,  don Annabi bai hana su ba, kuma sahabbai ba su hana su ba,   kai  ma yanzu baka da ikon hana su  kuma kar ka ce sai kyakkyawa   duk wadda ta sa ta kyauta  kuma ta yi koyi ne da matayen Annabi sallalahu alaihi wa,alihi wasallam da kuma matayen sahabbai da Tabiai waxanda  suke su ne mafifitan  al,uma ta harshen kur’ani da Annabi sallallahu alaihiwa,alihiwasallam, don haka nasiharmu ga masu zagin masu sa nikabi   su daina  su ji tsoron Allah, in ka duba tafsirin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Raddul azhan ila ma’anil Kur’an  cikin suratul Ahzab aya ta 59, za ka ga bayani  da ke nuna tabbatar dasa Nikabi.[80]
Malamai na  da   da na yanzu sun kasu kan matsayin sa   niqabi shin wajibine ko kuwa sunnnace ko kuwa mustahabbi ne.
Waxannan  kashi ukun  basu da na hudu  a  matsayin niqabi a wajen malaman mu na Musulinci, wasu  na da fahinta dole ne mace ta rufe fuskanta wasu kuma suka ce sunna ce wasu kuma suka ce mustahabbi ne sa Niqabi.

 FAHINTOCIN MALAMAI  KAN  NIQABI
1.    SHEIKH MUHAMMAD NASIRUDDEEN ALBANY.
Babban malamin hadisi ya ce sa Niqabi   ba  dole  ba ne wato mace ta rufe fukarta ba wajibi ba ne amma  sunna ce mustahabbiya. Ya  ce halin da muke ciki da mata:za su  sanya Niqabi   daya fi domin yin haka yafi da'cewa kuma ya  fi  alkairi yaci gaba da cewa da za su rufe fukar su da Niqabi to wannan abin da muke so ne a  gare su kuma muna kiran su da  su sanya   (Niqabi) ya ce  amma muce wajibine bamu da hujja, fuskar mace ba al'aura bace.amma su rufe fuskar  na su shi yafi, domin yin hakan alamace ta matan kirki[81]  
Albani ya yi bayani a  cikin littafinsa na qarshe  akan hijab mai suna ''RADDUL MUFHIM) ya ce fuskar mace ba dole ba ne ta rufe ta, sunna ce kuma mustahabbi  ne amma  ba dole ba ne, amma da zasu rufe   da Niqabi to da ya fi,[82]   
 An tambayi  Sheikh Nasiruddeen Albany Allah ya ji kansa game da hukuncin rufe fuskar mace, sai ya ce,  ‘’Ba musan wani daga cikin sahabbai ba wanda ya ce dole ne mace ta rufe fuskarta? Sai dai abin da yake mafifici shine mata su rufe fuskar su shi yafi da cewa ya fi mutunci. Amma mu ce wajibi ne bai dace wani mutun ya ce wajibi ne ba ya ce ya zo daga Ibn Abbas  nassi  inganttace da ke nuna cewa fuskar mace da tafin hannunta  ba  al'aura ba ne[83]. Masu cewa fuskarta al'aura ce su ne 'yan kaxan daga cikin malamai, amma masu cewa ba al'aurabane sune suka fi yawa da ga cikin malamai.  Ya qara da cewa Hadisin da ke cewa "Mace al'aura ce in ta fito shaixan yana qawata ta (wato maza su ganta kyakkyawa) " ingantattace ne, amma ba haka ya kamata  a fahimce shi ba.[84]
Sheikh Albany  ya ce amma da za su rufe, an fi son haka.   Sheikh  ba ya kushe sa  nikab  ko hanawa shi abin da bai yadda ba a ce wajibi ne  amma  sa  niqabi shi yafi alkhairi. Ya yi  ma Sheikh Tuwaijari raddi mai tsawo a cikin littafinsa  Raddul mufhim.

الرد المفحم
على من خالف العلماء وتشدد وتعص
وألزم المرأة أن تستر وجهها وكفيها وأوجبئ ولم يقنع بقولهم : إنه سنة ومستح
           Kai da jin suna littafin kasan Albany yana da fahintar Niqabi sunna ce kuma yana kira da a sanya Niqabi ne, Sheikh har yabar duniya bai taba cewa kar a sa niqabi ba.[85]        


2. SHEIKH bn BAAZ.
 Babban malami shugaban masu ba da fatawa na  qasar Saudiya Allah  ya ji qan sa. Shi  a wajensa wato a  fahimtarsa
SHEIKH  MUHAMMAD SALIHIL UTHAMIN,
 Allah ya ji qansa ya tafi a kan cewa niqabi wajibi ne, ya ce, Kasani yakai musulmi mace ta sa hijabi tsakaninta da maza tarufe fuskanta umurni ne wanda yake wajibi ne wanda Qur'ani da hadisai suka nuna da Qiyasi ya ce manzon Allah yayi umarni da mata su rufe tafin kafansu kar su buxe qafansu, kuma duk malamai baki xaya sun yi ittifaki akan qafar mace haramu ne ta buxe  ta, sai yace to ai fuska nan ne wajen fitina, kuma kowa fuska ya ke fara kallo kafin qafa domin nan ne wajen fitina to ai ya isa hujja mace ta rufe fuskanta tunda akace ta rufe qafarta, ya qara da cewa     hadisi da yace mace al aurace gaba xayanta sai dai fuskarta da tafi hannuta yace bai inganta ba,  kuma hadisi ya inganta da ya yake cewa mace  al'aura ce don haka, Usaimin yana da fahimtar dole  mace  ta rufe fuskarta ko don (saddu zari,a) wato toshe kafar varna.[86]
A  cikin fatawarsa an tambaye shi hukuncin buxe fuskar mace ya ce bai halasta  ba yace da za a ce ma ga wata mata mai kyan qafa amma mummunace  a fuskar ta, yace baza ka so ta  ba, sai ya kara da cewa ai Annabi ya ce a rufe qafa to ai fuska ita tafi cancanta da a rufe.[87]
Usaimin ya ce fuskar  mace nan ne matattarar fitina kuma nan ne wurin farko da mace zata rufe  kuma mutane da dama suna sakaci wajen barin yaran su na fita fuskar su a buxe wanda bai kamata ba[88]
Shi kuma sheikh Muhammad bn AbdulMaqsud yana da fahimtar mace ta rufe dukkan jikinta baki daya kar ta bar komai sai dai idonta da za ta ga hanya, hujar sa hadisin  bn Mas`ud  wanda Imamu Tirmidhi  yaruwaito da isnadi igantacce ‘’’ Mace  al`aurace  mu kuma an umurce mu da  mu rufe al`aura ’’’[89]

SHEIKH MUSTAFAL ADAWI 
Ya faxa  a cikin littafinsa Jami’u ahkamul Nisa ya kawo                     wannan ayar
{وإذا سألتموهن متاعًا فسألوهن من وراء حجاب ذلكم أطهر لقلوبكم وقلوبهن                                                     
Sai ya kawo hadisin da imamul Bukhari ya kawo da wasu hadisan  a qarshe dai bai wajabta ba  amma yana ganin waxanda suka ce wajibi ne suna da hujjojinsu kuma masu qarfi.Sai ya rufe maganar sa da cewa ko da mutum bai yarda  niqabi dole ba ne, to amma sa shi  shi ya fi dacewa,  kuma mafi kusanci ga tsoron Allah.

أن الأفضل
والأقرب للتقوى ومرضاة الله ورسوله: هو ستر كل البدن بما في ذلك الوجه والكفين.
‘’Mafifici kuma mafi kusanci ga tsoron Allah da neman yardansa dana Manzonsa : shine mace ta rufe dukkanin jikinta da  abin da ya haxa da abin da ke tare da shi  na fuska da tafukan hannu !!
Ya dai fi karkata  wajen  waxanda suke ganin wajabcin rufe fuska[90]
Haka Immul Qurdubi shima yaxan karkata wajen rufe fuskar mace a cikin tafsirinsa cikins suratul Ahzab aya ta  59.

        SHEIKH BAKR  bn ABDILLAHI ABU ZAID
  Ya ce  a cikin  Littafinsa  Hirsatil Fadhilah[91]
shi ma yana da fahimtar Niqabi, wajibi ne domin kamar yadda  ya ce ayoyi da hadisai suka wajabta sa Hijabi ga mata Muminai, to gaba daya tana nufin har da fuskarta da tafukan hannuta za'ta rufe.  Bai halasta ba ta buxe fuskarta a gaban maza. Ya qara da cewa Allah da ya ambaci .Jilbab ma'anar Jilbab  a Larabci tufa yalwatattace wadda zai rufe gabaxayan jiki tun daga sama har qasa. Shi ma Bakar yana da fahimtar Niqabi wato mace ta rufe fuskarta wajibi ne. Bayan haka ya ce ba'a samo daga wani ba a cikin musulunci da ya halasta ma mace ta buxe fuskanta ba a zamanin da  musulunci ya ke da rauni da lalacewa. Ya ce yadda mutane suka lalace a yanzu to ya zama dole mata su rufe fuskansu ga maza, kuma rufe wan  ita ce za ta toshe kafar varna  balle ma a halin da muke ciki.[92]
 Ku san gaba xaya malaman Saudiyya suna ganin wajibi ne mata su rufe fuskansu. 
   5.    ALIYU SABUNI 
  Ya faxi a cikin "Rawa'i ul Bayan, ba wai an wajab ta ma mace ta rufe fuskarta  ba ne don a quntata mata ba,    sai dai don kariya da kunya.Imamul Bagawi yana da fahintar mata su rufe fuskansu domin su bambanta kan su da bayi mata ya ambaci haka ne a cikin Tafsirinsa har ya kawo maganan Ibn Abbas Allah ya yarda da shi  in da yake cewa :

·       ثم نهى الحرائر أن يتشبهن بالإماء فقال جل ذكره عليهن من جلابيبهن} جمع الجلباب وهو الملاءة التي تشتمل بها المرأة فوق الدرع والخماروقال ابن عباس وأبو عبيدة: أمر نساء المؤمنين أن يغطين رؤوسهن ووجوههن بالجلابيب إلا عينا واحدة ليعلم أنهن حرائر
An hana mata ‘’yaya su kamanta Kansu da mata bayi wajen sa hijabi Allah yafadi haka  ne qarqashin  fadansa  “ su saukar da jilbab xinsu” yace Jalabib shine tufar da mace zatayi amfani da shi a saman mayafin  ta ya qara da cewa ibn Abbas  da Abu Ubaydata  sun ce “An umurci mata Mumine  su rufe kawunansu da fuskokinsu da jilbab xisu sai dai ido daya da za su bari domin  ganin hanya kuma ta  hakane  za`a gane su “yaya ne  ba bayiba.
Shi ma dai Imamul Bagawi yana da fahintar sa Niqabi shine umurnin Allah.

6.       SHEIKH NASIRUS SA’ADIY
            Ya ce a cikin, tafsirinsa. Tafsiru KarimurRahaman  mannan  ya ce mace ta rufe Jikinta baki xaya kar ta bar komai sai idonta guda xaydon ganin hanya..

                7 SHI MA ABUBAKAR JABIR AL JAZAIRI
            Mawallafin littafin Minhajul muslim ya ce
mace kar ta buxe fuskarta,   ba a so ta bayyanar da fuskarta, sai dai wajen    
lalura, kamar karvar wani  abu da hannu ko ido xaya ko biyu domin ganin hanya. Hadisi yazo mace gaba xayan ta alaurace sai dai fuskanta da tafukan hannunta ama a wajen Sallah.[93]

8.      SHEIKH TUWAI JIRI
            Ya yi magana gamsasshiya  bisa  muhinmancin sa Nikabi da kuma raddi ga masu cewa ya halasta mace ta buxe fuskarta, domin shi a wajensa sa Niqabi wajibi ne, sannan kuma ya yi ma Albany raddi da ya ce mace ba dole ba ne. ta rufe fuskarta ya ce dole ne ta rufe fuskarta  a cikin littafinsa (Assarimul mas shur alat tabaruj wassufur wa fi  Raddu al  kitabul Albany). Duk da cewa Albany bai yarda da cewa wajibi ne rufe fuska  ba amma kuma matansa da 'ya'yansa suna sawa.  Ya  ce kuma'sawan shi ne mafi alkairi.Tuwaijari yafi kowa tsanantawa wajen  fahintar  mata sai sun rufe fuskar su  kuma sai  sun   sa safar hannu kuma shi ne ya fi yin ma Albany raddi kan nikabi[94].

                       SHEIKH  FAUZANIL FAUZAN
            Sheikh yana da fahintar rufe fuskar mace dole ne yafaxi haka a littattafansa da dama   ya fasassara Hijabi da cewa:
 الحجاب الشرعي هو أن تستر المرأة ما يجب عليها ستره من الوجه والكفين، ومواضع الزينة من بدنها، كموضع الكحل والخضاب والسوار والقلادة وغير ذلك مما يستلزم النظر إليه رؤية موضعه من بدن المرأة. فستر هذا كله وإخفاؤه داخل في مفهوم الحجاب الشرعي،                                                            
  Sheikh Abdullahi Salihil Fauzan  ya  fasassara Hijab  da cewa shine  mace ta rufe  abin da yake wajibi ne rufe shi a gareta wanda ya haxa da fuskarta da tafukan hannunta  da qafafuwanta da wurren  kwalliyanta na jikinta kamar  Tozali qunshi da sarka da sauransu, ga abinda yake  yana jawo kallo ya zuwa gareshi na daga jikin mace................................[95]
           Yana da fahintar dole ne mace tarufe fuskarta  kamar yadda ya yi bayani a wani  littafinsa mai suna  Tanbihatun  ala Ahkamin taktassu bil muminat.   Wato shima a wajen sa sanya  niqabi dole ne.  Malaman  da suke  ganin sa  Nikabi ba dole bane  amma sun yarda sa nikabi shi ne mafi alkhari  kuma mafi kusance ga tsoron Allah, kuma sun yarda a sa Niqabi a wannan zamanin  shi yafi dacewa  ga ko wace ‘’ya mace. 
            Kuma   har ila yau sun yadda  cewa Nikabi  na zama wajibi ga dukkan macen da tasa Tozali ko hoda ko jan baki ko ja gira  ko dai wani nau’in kwalliya a fuskarta to dukkan   macen data yi  daya da cikin wadannan abubuwa to niqabi yazama  dole  a gareta wato dole ne ta rufe fuskarta.
             Haka nan ma duk wadda tayi Dayis (kwalliyar da mata suke yi da lalle ko taki) a hannu ko tasa jan kunba  to itama dole ne tasa safan hannu ta rufe hannunta. Kuskure ni ki sa niqabi amma qafarki a waje dole ne ki rufe qafarki.

            SHEIKHUL ISLAM BN TAYMIYYAH
            Yana da fahintar wajabcin mace ta rufe fuskanta wato sanya Niqabi  dole ne ya yi bayani mai tsawo acikin littafinsa majmu’ul fatawa ya fara da cewa haqiqanin al’amari shine Allah ya sanya kwalliyar mace (qawa) kashi biyu  akwai kwalliya ta bayyaane, kwalliya ta bayyane ya halasta mace ta buxe ga wanda ba  mijinta ba, ya qara da cewa mata kafin saukar da ayar Jilbab sun kasance suna fita fuskan su a buxe amma tun da aka saukar da ayar da ke cikin suratu Ahzab mata in za su fita suna fita ne  fuskansu a rufe, a qarshe ya ce “hannun mace da fuskanta da qafanta bai halasta ta buxe su ba ga wanda ba mijinta ba, ba kuma muharraminta ba. Ya ce jilbab shine  abin dake rufe jiki baki xaya har da fuska shine Allah ya ambata acikin suratu Ahzab.[96] Wannan ne fahintarsa mata su rufe fuskansu, Allah ya jiqansa amin. Shima xalibinsa ibn Qaym shima fahintarsa kenan, da kuma ibn Rajab al-Hambali shima yana da fahitar wajabcin  mace ta rufe fuskanta .[97]
           Babban malamin malikiya al-Qadhi Abubakar  al-Arabi al-Andalusi  ya ce  “mace dole ne ta rufe fuskanta ka da maza su ganta in zata fita waje,  awajen aikin hajji ne kawai aka yarda ta buxe fuskarta.[98]
           In ka na son ganin bayani sosai sai ka duba littafin Imamul Kurdubi ko Tafsirin  Baydawi  ko ibn Kasir ko Mahasinu Tanzil  ko ka duba  Jilbabul mar atil muslimah na Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albany  ko Audatul hijab da  Libasul Yaum na Ammru da Sarimul mashur alt Tabarurj, gaba xayan malaman Tafsiri sun tafi akan cewa rufe fuskan mace wajibi ne.[99]
Bincike ya tabbatar da cewa sanya Niqabi yana bada kariya daga kamuwa daga cutar  T B (Tarin fuka) cutar da ake  kamuwa da ita ta iska, kuma Niqabi yana gyara ma mata fuskar su da kariya daga cutattukan da ake kamuwa da su ta iska. Bala’i ne da musiba mai girma mace ta sanya Niqabi sannan kuma ta hau Acava (xan yasfiris) wannan mata ta shiga uku, ko ba ki sanya Niqabi ba ai haramun ne ki hau acava balle kin yi shiga ta matan kirki.

NASIHA GA ISAH HASSAN TIKUMA DA MASU MUMMUNAN RA’AYI IRIN NA SA.
Isah HassanTikumah wani mutum ne mai koyar da social studies a Jamiar Ahmadu Bello Zaria wanda asalinsa xan Ghana ne zama ne ya kawo  shi  Zaria.
   Yarubuta littafi da ke cin mutuncin masu sa niqabi da  wulaqanta musulmai a  fuskar kafiran duniya baki xaya da karya ta ilimi da qago maganar da take bahaka take ba kan Albany wanda acikin littafin nasa  shi Tikuma yana ganin bai kamata a rika barin mata suna sa nikabi ba sabo da a yanzu masu sa nikabi suna yin aikin banza   har ya kawo wani misali wanda ya faru a  Jama’a Hospital wanda a qarshe ya nuna shi ma bai da tabbas akan  labarin amma ya kawo shi a littafin nasa  da labarin abin da yafaru a Pakistan a Red mosque da wani  labarin qanzan kurege kan masu koyan karatun Kurani da niqabi wanda a littafin ya  nuna malaman Nigeria basu da amfani  kuma ya qara da cewa bai kamata a bar mata su riqa yin Defence na Masters da niqabi ba, kuma ya  nuna sa niqabi kamar wani imani ne na qarya. Nayi mashi nasiha ni dashi a ofis xinsa amma ya qi ji na kuma nuna ma sa kurakuren da ke cikin littafinsa hujja daga Kur’ani da Hadisi amma ya qi yarda a qarshe sai yana ceman wai su wane ne malamai na girman kai ya kamasa.                       
Isah Tikumah da farko dai ka ji  tsoron  Allah ka tuba kan littafin da ka rubuta kuma ka sani idan wani ya yi shiga ta mutanen kirki yaje ya yi aikin banza  ka sani baka da daman  da za kace a daina wannan shigar kuma kai a yanzu ba ka isa ka hana sa niqabi ba tunda Annabi bai hanaba kai yanzu a wane za ka hana , Isah ga wani masali yanzu wanda suke da gemu suke zuwa suna aikin banza sai muce yanzu a daina barin gemu   tun  da a na  samon mutanen banza suna bari gemu,  kuma yanzu sai a daina aure sabo mata na zina, kamanta da cewa  manzon Allah sallalahu alaihi wa alihi wasallam ya ce, “Alumarsa basa haxuwa kan vata  ko da yake ba mamaki tunda kai ba addini ka karanta ba kuma tunda Allah ya  sa  an  san cewa kai xan Bidia ne  kuma jama’a ma suna tunanin mai yiwa   Yahudawa suka saye ka don kai ma  su aiki tun da labari ya tabbatar da qasar da kayi karatunka. Allah  ya shiryeka.
Game da magananr da ka kawo kan Albany da sanadiyar barinsa Madina to ba haka maganan take ba  kuma ba Jilbab ba ne yafara rubutawa kan hijab kaje ka tambeyi malaman da ke kusa da kai don samon bayani, kuma ina so ka sani shi Sheikh Albany bai da mummunar  fahimtarka ta hana sa niqabi jeka ka duba littafin sa Hijab ko Jilbab ko Raddul mufhim za kaga  yana goyon bayan sa niqabi shi abin da ya ce  ba  dole ne ba, kai ko kana so ne a hana sawa kamar yadda  kai  mawata yarinya   a  ajinka .
Kana ta kawo magananr Sheikh Qardawi to ka je ka duba  littafinsa  da ya yi kan hijab za kaga shima yana goyon  bayan sa niqabi shi  ma Qardawi  matsayin Albany ya xauka.   Ina   ma da kai ma ka xauki fahintar waxanda suke ganin sa niqabi   ba dole ba ne amma a sa shi ne alkhari,   amma  ina sai ka xauki kanka matsayin Malami, malamin ma babba,    Kai   yanzu a fahintarka yanzu har hijabi ma bai kamata a riqa sawa ba. Kuma kai ka xauki  malaman Najeriya matsayin marasa  amfani  sabo da kai    malaman   ka  basa   Najeriya  kuma  ka nuna ma duniya kai baka  da kunya kuma baka da tarbiya  shi yasa    ka ci mutuncin  malaman   Najeriya     kasani   malami   duk inda yake  ya wuce wulaqanci  a wurin  mai  mutunci mai  tarbiya, muna maka  adduar Allah ya shirye ka  kai da masu irin wannan  mummunan   ra,ayin   da bai  da  magabaci, abin ban mamaki sai ga shi  ya qara rubuta wani littafin daya ke qoqarin kiran niqabi da cewa fasiqanci ne ko bidia, Allah ya tsare mu daga shiga cikin wannan ta’addanci  ne mi littafina da na rubuta ‘’Guiding principles of Hijab /Nikab and Nasiha to Isah Hassan Tikuma’’ za kaga nasihar da nayi ma shi kuma muna roqa mashi Allah ya shirye shi ya tuba daga yin ma Yahudawa aiki.
Ka duba littafin da na rubuta mai suna ‘’Guiding principle of hijab’’ na yi mashi nasiha  da kuma nuna masa kurakuran da yayi a cikin littafin sa mai suna (The Abuse of Islam and the dormancy of Islamic scholars Evidence from the misuse of nikab (face veil) in Nigerian society”.Malamina malam Ahmad Bello Dogarawa yayi masa raddi acikin littafinsa “Tarbiyyar ‘ya’ya a muslinci”. Abin  vacin rai da baqin ciki sai gashi ya rubuta wani littafin da ya kira Niqabi da abin qyama mummunar bidia  ya sanya ma littafin suna “NIQAB (FACE-VEIL) AN EXEMPLARY SUNNAH OR A REPUGNAT INNOVATION” a wannan littafin nasa ya nuna zindiqancinsa a fili Allah ya shirye shi amin.[100]

    MUHIMMANCIN SA HIJABI

1.   Bin umurnin Allah da Annabi
2.   Kariya daga fitina
3.   Alama ce ta tsarkin zuciya
4.   Kyakkyawan xabi'a ce
5.   Alamar mumina ce
6.   Yankewa daga hanyar Shaixan
7.   Kare kunya
8.   Garkuwa daga  faxawa cikin halaka
9.   Sutura ce daga al'aura
10. Kariya daga mazaje marasa mutunci
11. Kariya daga Aljanu
12. Kariya daga shiga cikin azabar Allah
13. Bautar Allah ne sanya hijabi
 ILLAR RASHIN SA HIJABI.               
 1            Rashin sa Hijabi sava ma Allah ne da Annabi                     
2.            Rashin sa Hijabi Zunubi ne mai halakarwa
3.         Rashin sa Hijabi Sifface ta 'yan wuta
4.            Rashin sa Hijabi alfasha ce
5.            Rashin sa Hijabi ta, addanci  ne da rashin kunya
6.            Rashin sa Hijabi Koyi  ne da Yahudawa
7.         Rashin sa Hijabi Koyine da Nasara (Kiristanci)
8             Rashun sa  hijab`shiga  ce   ta Jahiliyya
9.            Rashin sa Hijabi Dabbbanci ne
10.          Rashin sa Hijabi ci baya ne
11.          Rashin sa Hijabi sharri ne
12.       Rashin sa hijabi rashin kunya ce
 13.      Rashin sa Hijabi  qauyanci ne.[101]
14.      Rashin sa Hijabi alamace ta munafinci.

     YADDA   AKE  SO MACE  TA YI TAFIYARTA
Lalle ya isa mutumtawa da karramawa da  muslunci ya yi wa  mata  yadda bai qyale su haka nan ba.  Hatta tafiya sai  da   ya nuna ma su yadda ake so su yi don dai karrama su da mutuntasu. Hadisi yazo cikin Bukhari,    Manzan Allah sallalahu alaihi wa,a lihi wasalam yace ‘’ Mata wajen tafiyarsu,  su   bi  gefen hanya.’[102]  Mata a zamanin Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam sabo da bin gefen hanya har hijaban su yana yagewa saboda tava bango[103]   Don  haka ana son mata in suna  tafiya subi gefen hanya kuma   kansu na kallan qasa    kuma suna tafiyansu cikin sanxo banda sauri.[104]
Wani  lokaci waxan su matan sukan sa Niqabi amma qafarsu a waje  ko hijabin nasu bai rufe masu qafaba  wannan kuskure ne. Dole ne mace tarufe qafarta indai za ta fita daga gida.  Kuma ta  yi tafiyarta yadda  Annabi sallallahu alaihi wa, alihiwassalam.yace.  Waxansu  matan zaka ga ba sa sanya  hijabi in kai magana sai suce wai tsoran Allah a zuciyatake  wannan maganar kuskure ne  domin ba matar da ta kai matayen Annabi sallahu alihi wa, alihiwasallam tsarkin  zuciya amma kuma suna sanya niqabi. Ma su yin wannan magana Allah ya shiryesu wasu kuma suna cewa hijabi  a zuciya yake suma masu yin wannan maganan qarya ce tsantsa sukeyi domin abin dake zuciya shike fitowa gangan jiki, Bahaushe ma yana cewa labarin zuciya a tambayi fuska.   Suma muna masu adduar Allah yashiryesu amin.

 HATTARA MATA                                                                              
 Haba ‘’yaruwa musulma ai ya ishe ki   darajar da Allah ya yi maki da ya ce ki sanya hijabi kuma aka nuna maki yadda akeso kiyi tafiyarki  kuma aka hanaki ki nuna kwalliyarki sai ga wanda shara’a ta yardam mashi da ya gani. To amma duk da wannan mutunci da Allah ya yi ma ku  sai ki ga wasu sunyi watsi da wannan darajar, sun shigar da kansu cikin fushin Allah da tsinuwarsa da kuma tsinuwar Annabi sallahu alaihi wa’alihi wasallam suna cire kayansu suna shiga cikin fitina da abin da zai kai su wuta suna yin qwallo.
                             إنا لله وإنا إليه راجعون
  wai  a ce mace zata yi qwallo, ke da aka hanaki ki cire kayanki a ka hana wani ya ga jikin ki  sabo da qimar da jikinki yake da shi, sai mijinki kawai, amma kuma sai ki ka qi yarda da abin da Allah ya ce ki  ka shiga cikin waxanda Annabi ya ce ba za su shiga Aljanna ba manzon Allah sallallahu alaihi wa alih wasallam yana cewa ‘’Duk ya yin da wata mace ta cire kayanta ba a cikin gidan mijinta ba ta ruguza suturar da  ke tsakanita da Allah’’[105] kinji abin da Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce kin ruguza kariyar da Allah ya yi maki da ga  shiga wuta, kin shiga cikin layin masu shiga wuta don haka qwallon mata shari ne yahudawa maqiya addinin Allah  suka kawo mana don su ruguzamana tarbiyar mu da addininmu da kuma jefamu cikin bala’i.  Mun sani Annabi ya hana maza su buxai cinyarsu ya ce cinya al’aurace[106] maza kenan balle  ke mace da aka ce kirufe gaba xayan jikin ki sabo da qimarki da darajarki da mutuncinki amma sai  ki sanya gajeran wando  ki  fito gaban maza ana ganin cinyarki da nonan ki da duburarki haba ‘’yar uwa ki yi kuka wannan abin kiyi kuka ne domin kin shiga cikin waxan da Annabi ya ce  baza su shiga Aljannaba wani hadisin Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce, ‘’Siffar mutane biyu ‘’yan wuta ne   mata ne sun sanya tufafi amma tsirara suke (saboda rashin kaurin tufan nata ya nuna wuraren fitina dake jikinta)…………… a qarshen hadisin Annabi ya ce baza  su shiga Aljanna ba[107]
Wani hadisin Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce, ‘’ Mata ma sharranta sune masu nuna tsaraicinsu (masu sanya kaya matsattsu) ma su yin yanga  su ne munafukai  baza su shiga Aljanna ba sai dai misalin hankaka mai jan baki’’[108]  idan muka kalli yadda addini ya ce mata su rufe jikin su  kuma su yi tafiya a hankali a kwai hikima cikin wannan umurni.
Akwai  wasu abubuwan   da ke cire ma mace budurcinta, idan tayi aure mijinta  yajita tamkar wani namiji ya tava saninta a ‘’ya mace (wato kamar ta tava saduwa da wani na mijin) sune mace tariqayin gudu, gudu  yana cire  ma mace budurcinta gabanta ya lalace, da kuma yin tsalle yin tsalle-tsalle yana cire ma mace budurcinta da kuma xaukan kaya mai nauyi shima yana cire ma mace budurcita[109] da kuma sauri shima yana cire ma mace budurcita da kuma yin magana da qarfi shima yana cire ma mace budurcinta idan ki ka kalli waxannan za ki gane  musibar da ke cikin qwallon mata domin waxannan abubuwan da ke xauke ma mace budurcita duk sun taru a qwallon mata  suna da yawa  kije ki tambayi malaman fiqihu zakiji bayani sosai.     To  idan muka kalli waxannan abubuwa za mu qara fahintar sharrin qwallon mata da kuma muni ta Allah ya kare mu da shiga cikin waxanda Annabi  sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya tsine masu, agaskiya  duk  yarinyar ko mu ce duk matar da tayi qwallo ta shiga cikin waxanda Annabi ya ce baza su shiga Aljanna ba  kuma sun shiga cikin waxanda Annabi ya ce tsinannu ne kuma ta shiga cikin waxanda Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce sun ruguza suturar da Allah ya yi masu, haka duk wanda ya taimaka wajen yin qwallo mata shima ya shiga cikin tsinuwar Ma’aiki sallallahu alaihi wa’alihi wasallam haka  suma masu kallon qwallon mata suma tsinannu ne kuma yana da cikin abin dake kawo  bala’i a bayan qasa da xauke albarkan abinci shi ne  qwallon mata . Duk uban da ya qyale yarinsa ta yi qwallo ya nuna bai da kishi kuma manzon Allah ya ce wanda bai da kishi ba zai shiga Ajanna bar ranar tashin qiyanma.[110]An tambayi babban Malami Sheikh  Ibrahim bn Muhammad  game da qwallon mata  sai ya ce haramun ne  qwallon mata, bai haasta ba kwata kwata haramun ne bai halasta ba.[111]
A qarshe muna kira ga iyaye  da su  ji tsoron Allah su hana yaransu mata yin qwallo da kuma shuwagabannin makarantun sakandire suma su hana mata yin qwallo domin kar su faxa cikin bala’i da musiba ya Allah ka shirye mu baki xaya.  

YANCIN MATA
Maganganu sun yawaita aduniya musamman a wannan lokacin akan yancin mata wanda wannan maganar har ta fara tasiri acikin zukatan matan musulmai, duk yayin da mace tafara tunani akan musulunci ya danne mata haqqinta to lalle ba bu ko tantama Yahudawa sun yi nasara akanta kuma ta kama hanyar halaka. Idan muka binciki tarihi za muga cewa addinin musulunci ne yaba mata ‘yanci cikakke sauran addinai  sun tauye ma mata ‘yancinsu ne kuma sun takura su, misali kafin zuwan musulinci mata ba abakin komai suke ba mata wulaqantattune  gadon su ake yi ana sayar da su yadda ake sayar da dabbobi ana rufe su daransu, idan uba ya mutu xanta zai gajeta ya ci gaba da saduwa da ita, idan za ai tsafi mata ake samu a yi tsafi dasu[112]idan zata yi aure ita take ba da sadaki ba namiji ba kuma mata ke zuwa gona ba maza ba.[113]
 Da musulinci ya zo sai ya haramta rufe mata ya hana kashe su da ake yi  musulinci ya yi umurni da aba mata gado ya haramta xanta ya aureta, ya ce abata sadaki yace ta zauna agida aciyar da ita ayi mata sha tara ta arziqi.
Idan muka kalli Yahudawa sun xauki sa hijabi a matsayin quntata ma mata ne tauye masu haqqi ne  shi ya sa su ka kiri bikin qona hijabi a qasar Misra a shekara ta 20/3/1919 matan duniya su ka haxu suka nuna kyamar su ga hijabi da mata musulmai su ke yi, bayan qasar Misra ta yi nata sai kuma qasar Turkiyya itama tayi nata bikin qona hijabin lokacin mulkin Mustafa Kamal Atatur, shi na shi yafi muni domin daga baya ya hana sanya hijabi a waxansu yankunan qasar nasa. Bayan Turkiyya daga baya qasar Tunisia itama  tayi abin da Masar tayi qarqashin mulkin Burgeba, shi Burgeba yayi hauka domin har kiran sallah sai da ya hana ya ce a rage yawan sallolin da akeyi abar guda biyu subahi da Isha’i wai kar a taqura ma jama’a ya ce arage azumi abarshi daga safe zuwa shabiyu.[114] Wannan ita ce haukan da Burgeba ya yi.
A shekaran 1995 matan duniya sun haxu a qasar China a Peking a dandalin Teanerment nan ma suka yi magana akan ‘yancin su anan kasar tamu Najeriya matar shugaban qasa na wannan lokacin ta halarci taron ita da tawagarta, wannan fa duk da sunann ‘yanci  kuma kamar mu manta sun xauki hijabi a matsayin tauye ma mata ‘yanci ne, idan muka lura za muga mata waxan da ba su da addini sai dai boko kawai za mu ga suna qyaman hijabi, ba wani abu yasa suke qyamansa ba face sai don wai takura ne sun manta da cewa dokar Allah ne sanya hijabi kuma  akwai katafaren lada  ga wadda ta sanya hijabi, kuma zunubi ne  mai girma ga wadda ta qi sanya hijabi, muna roqon Allah ya shirye matayen da basa sanya hijabi amin.
 Kuma duk yana cikin ruxin da Yahudawa su ke yi na  ‘yancin mata  suka qirqiro masu da qungiyoyi misali akwai women empawerment da women in politice da what a man can do women can do even better da women society da Jam’iyar matan Arewa da women right da sauran su dukkanin waxan nan qugiyoyin Yahudawa ne suka qirqiro su da nufin su kawar da mata daga addinin Allah, Allah ya ganar da mu amin.[115]
                 KAMMALAWA
Wannan shi ne abin da ya sauqaqa  kan sharudxan hijabi    Allah ya  taimake mu, kuma Allah ya ba mu ikon aiki da abin da na rubuta,  Allah ya sa ya anfanar da ‘’yan uwa baki xaya.
Ga masu zagin mata in sun sa hijabi yana jan qasa ko sun sanya Niqabi da suji tsoron Allah    su sani cewa duk ya yin da kazagi mai niqabi to kana neman aibanta matayen Annabi ne da     matayen sahabbai. KumaAllah ya hana isgilanci ga masu addini, Allah ya faxa cikin suratul Tauba  "yanzu  Allah da   ayoyisa da manzonsa  ne  ku ke ma isgili babu wani uzuri da za Ku  kawo  kun  kafirta  bayan da  kun kunyi   Imani’’ kuma dubi da halin da muke ciki bai kamata ka hana matarka ko "yarka ko qanwarka ko ‘’yar uwar ka sa Niqabi ba. In ka zagi mai sa niqabi wannan zagi  ko tozarcin zai koma zuwa ga matayen
 Annabi ne da Sahabbansa, Allah ya kare mu da ga aibanta matayen magabata amin. Iyaye su tuna da girman haqqin da ke kansu na ‘ya’yansu, su ba su tarbiyyah ingantacciya domin tsira gaban Allah[116]  kuma yana da kyau iyaye  su lura da sharrin da ke fuskanto mu na koya ma yara ilimin jima’i a da Gwanati ta ke qoqarin kawo wa a cikin  manhajar (curriculum) makaranta boko za a kira yaro ace  ya tava nonon  mace  ita kuma ta kama gabansa sai malamin ya tambaye su me  suka ji
إنا لله وإنا إليه راجعون               
Wannan abin muyi koka ne wallahi domin musifa ce a fili Yahudawa suka kawo  mana domin su lalata mana tarbiyar mu, kuma so suke zina ta yaxu ta zama ruwan dare, iyaye ya zama dole su kula da ‘ya’yansu.[117]
Allah ka taimake mu baki xaya kuma ka gafarta mana zunuban mu, amin.
Wanda ya ga  kuskure ko gyara  ko shawara qofa a buxe take yana iya kirana  insha Allahu zan amsa masa kuma zan  gyara kuskuren da yardan Allah. Xan uwanku  a cikin addinin   Allah.
Wassalamu alaykum warahamatullahi Barakatuhu Daren 25 Ramadan 1429 wanda ya yi daidai da 24/9/2008.
‍ والله تعالى أسأل أن يجعل هذا العمل مقبولاً، مباركاً، خالصاُ لوجهه الكريم، وأن ينفعني به في حياتي وبعد مماتي، وأن ينفع به كل من انتهى إليه؛ فإنه سبحانه خير مسؤول، وأكرم مأمول، وهو حسبنا ونعم الوكيل، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم      وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لاإله إلا أنت  أستغفرك وأتوب إليك                                      
                                       والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته
Harun Abubakar shika
08030582333-08020900001- 08054533361
harunaabubakar99@yahoo.com


[1]  Suratul Ahzab
[2] Shi ya sa malaman  muslinci  kullum suke  rubuce- rubuce domin ba su kariya  wajen ganin  yahudawa maqiya addinin Allah  ba su  lalata tarbiyanr su  ba da aqidarsu ba.
[3] In zamu iya tunawa anyi wani fim Na Hausa da ke wulaqanta mata masu sanya hijabi inda fim din ya nuna mata masu sa hijabi zina suke yi.Wannan duk aikin Yahudawa ne na cikin gida maqiya addinin Allah.
[4]  Mata a wajen Yahudu  kamar haja ce  ta  sayarwa kowa na  iya  zuwa ya gani  kuma ya taba kuma ba sa ba su wata qima sai dai qimar tozarci da wulaqantawa, suna  qyamar  zaman auren  da matan musulmai suke yi a gidajensu  shi ya sa suke qirqiro ma su qungiyoyi da sunan  nema ma mata yancinsu.   Ko su ce kar su yi aure sai sun kai wani lokaci ko wani matsayi na duniya ko muce wani matsayi na karatun Boko, wannan duk maqircin Yahudawa ne maqiya addinin Allah, mace ta yi aurenta da wuri shine mutuncinta, aure ba ya hana karatu, karatu ba ya hana aure.
[5] Manzon Allah sallalahu alaihi wa ‘alihi wasalam ya ce,” kunya da Imani tare suke idan daya ta tafi ita ma dayar zata tafi “Kunya da imani tare suke ba a raba su.Wani hadisin  ma cewa ya yi kunya alkhai ri ta ke jawo wa  kuma duk wanda bai da kunya kamar wanda bai da imani ne.
Don haka yana da kyau mata su kula da kyau kar su rudu da kiran da Yahudawa su ke masu  na su nemi ‘’yancinsu. wanda wannan da,awar ta su  karya ce da yaudara. Duk duniya ba addinin da  ya ba mata ‘’yanci kamar Muslinci, ya kuma ba su kariya.
[6] Muqaranatu baynalhijab wassufur
[7] Allah ya ba da umurni ne na sanya hijabi domin darajar da mata suke da shi, kuma da ma duk abin da yake da daraja zakaga voye shi akeyi a na ba  shi kula kula  ta     musamman  domin darajar sa.sannan duk abin da yake a rufe ya fi daraja kuma ya  fi kyau.  
[8] Bukhari da Zadul ma,ad da Isaba.
[9] Jilbabul Mar’atil muslima  da Hijabulmar,atil muslima  da Raddul mufhim  dukkansu  na  babban  malami Sheikh Nasirudden Albany da  Iqtiyaratul fiqhiyah  inda  Sheikh Albany   Jilbabul Mar’atul muslima  Na  Amru AbdulMun’im
[10] Raddu Azhan ila ma’anil Kur’an Suratul Ahzab.
[11] Ya kawo maganar  Ibn Abbas  kan fassarar wannan  ayar.
[12] Suratun Nur 31 da kuma tafsirn Imamul Xabari za a qaru da bayanin  magabata masu daxin karatu.
[13] Tirmizi da Ahmad da Abu Dauda
[14] Jilbabul mar,atil muslimah  da hijabulmar,atil  muslima
[15] Muwadxa ta Imam malik
[16]Muwadda ta Imam Malik
[17] Fatawa Madina
[18] Majmu’ul Fatawa na  Baz  10/409
[19]  Majmu’ul Fatawa
[20] Adxaaharatu was Sallatu 54
[21] Bidayatu mujtahid na ibn Rushid 124
[22] Asalin acava Arna mata ke hawa, an fara yin acava  ne a Kaduna ,amma yanzu abin bakin ciki ya canza har mata musulmai  suma suna  hawa acava, abin da yasa ake ce masu ‘’yan  Acava  shi ne in sun dauki mata su ka  yi  gudu dasu  suka taka birki  Nonan  matar   ya taba jikin sa  sai  ‘’yanuwansa su ce mashi ya CAVA yar’uwa  kin ji  asalin dalilin da yasa ake cewa “YAN ACAVA,  Kuma babban abin baqin ciki har da masu sa Niqaabi za kaga suna  hauwa  ِ  Acava. ِِAllah ya kyauta  sai dai lalura mai qarfi to ta  iya hawa Acava , kamar  mace tana cikin rashin lafiya  na fitan hankali wanda in bata hau acava ba  tana  iya mutuwa .
[23] Xabarani Mu’ujamul Kabir
[24] Haka nan ma haramun ne mace ta buxe kanta ga matar da take kafira,  wato babu kyau mace ta bude gashin kanta ga Arniya kafira da sunan kitso, ko wani abin  sai dai lalura mai qarfi,  kuma wani sharri da bala’i da ke faruwa sai kaga mata a makarantun Sakandire malamai maza na buxe masu kansu  wai da sunan  duba tsafta wannan bala’i ne da masifa  kuma hramun ne mace ta bari kafiri yana kallan gashin kan ta, namiji musulmi ma an hana  shi   ya ga kanki balle kafiri ko kafira don Allah mata kuyi  qoqarin gyarawa tun kafin lokacin nadama  Allah ya kyauta amin. Ana iya duba littafin  Fauzan mai suna Hijabul shar’i ko Littafi Albany  Hijabul Mar’atul Muslimah ko Jami’u Ahkamin Nisa’i ko Littafin ibn Taymiyyah Hijabul Mar’ah
[25]  Ahmad 19/6 da Bukhari  Adabul mufrad da Ibn Hibbans
[26] Breast lenght shine hijabin da mata masu karatun Anguwan zoma su ke sanyawa a (school of Nurses) shima haramun ne sanya shi don haka mata masu karatu  a wannan waje su yi qoqari su gyara.
[27] Fiqhu Sunna lil Nisa Kamal Abu malik da Sheikh Mustaphal Adawi Jami’u Ahkamun Nisa
[28] Muslim da Xabarani (Dukkan mata masu sanya tufafi amma ana ganin jikinsu sun shiga la`antar manzon Allah kuma  tsinannu ne Allah ya kauta.  
[29] Nisa’u Ahlunnar  na Mustafl murad
[30] Dhiya’ul Maqdis
[31] Muwadda Malik 2/913
[32] Muslim da AbuDauda
[33] Nasa’I 12/203 da AbuDauda
[34]  Muslim 328  da Imamu Nisa’I 8/154
[35] Ahmad 4/394
[36] Don haka mata in za su makarantan Islamiyya ko boko ko kasuwa  suji tsoron Allah su bar sanya Turare  ko shafa mai  mai qanshi
[37] Muslim
[38] Dabarani fil Ausad
[39] Iqtidau siradil mustaqim
[40] Ahmad 2/199-200
[41] Abu Daud
[42] Ahmd
[43]  Abu Dauda da ibn Majah 
[44] Sahihu Jami’usSagirs 7674
[45] Bukhari 4/54   Muslim 3/1653-1654.
[46] Manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam  ya ambata ya ke  cewa  wata rana Annabi Isah yana zaune a gidansa shi da xalibansa su goma shabiyu  sai  yace ma    Dalibansa yanzu haka  anzagaye  gidana da nufin kashe ni   waye zai fita, Allah zai sa mashi kamanni na za a kashe shi mu haxu a Aljannah  ba wanda ya tashi sai wani yaro ma fi  qanqantar shekaru a cikin su Annabi Isah ya faxi haka sau uku sai dai wannan yaron yake  tashi  sai Annabi Isah ya ce mashi  to je ka,  yana fitowa  sai Allah yasa mashi siffar Annabi Isah su kuma da suka ganshi sun xauka Annabi Isah ne  sai suka kashe shi, shi kuma  Annabi Isah sai Allah yasa mashi barci   ya buxe saman rufin xakin nasa ya yi sama da shi… da AbuHuraira mai riwayar hadisin ya kawo nan sai yace ku karanta in kun  so وما قتلوه وما صلبوه ولكن شبه لهم وإن الذين اختلفوا فيه لفي شك منه ما لهم به من علم إلا اتباع الظن وما قتلوه يقينا   بل رفعه الله إليه وكان الله عزيزا حكيما                                                                
Don haka Annabi Isah zai dawo kamar yadda hadisai suka nuna  wanda  ya  ce  ba zai dawo ba yana karyata Kur’ani  ne da hadisan  Annabi kum  hadisai ingantattu.                             .                 .                                                                                                                                                                                       
 
[47] Bukhari da Ahmad
[48]  Su ‘yan qallon Ture suna yin wasanin su ne da manufar su ta kafirci shi ya sa suke   sa alamar kuros  a  jikin kayan wasanin su don su, sun xauki qwallansu tamkar suna coci ne   kuma su nuna ma duniya manufar su ta kafirci.    Yakamata mu kula mu daina  sa irin wadannan kayan kuma zaka ga  mutum musulmi ya hardace  sunayan ‘yan qwallo amma bai hardace sunayen Sahabban Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam  ba ko kuma kaga yadda yake son ‘yan qwallo ya fi yadda  yake  san Annabi sallalahu alaihi wa,alihi wasallam   lalle wannan  musiba  ce  Allah ya  kare mu. Kwanaakin baya ansami wani Xan Qwallo mai suna BECCHAM   aka tambaye shi wa yafi so ya ce Matarsa akace mashi to wa yafi qi sai ya ce Musulunci da Musulmai,   ya faxi wannan Magana kowa yaji a duniya amma   zaka ga musulmi da hotan shi a rigarsa sabo da rashin sanin ciwon jikin sa, Allah   ya shiryemu baki xaya  amin. Balle  kuma bala,i  na qarshe Qwallon Mata da a keyi a  sakandere (secondary)  duk wadda ta yi qwallo tsinarniya ce haka shima wanda ya taimaka wajen yin qwallon  Mata shima tsinanne ne da masu kallon qwallon mata suma tsinannu ne haka hadisin Imam  muslim ya ambata.
Wannan musibar ta fara yaduwa  a makarantun  gaba da firamire  wato makarantun Sakandire Allah ya tsare ma na matayen mu da yaranmu da yin qwallon mata
[49] Bukhari da Ahmad
[50] Adabu shari’a 3/512
[51] Bn Baz     Jawabul mubin  fi hukmu taswir
[52] Bukhari da Muslim.
[53] Bukhari da Muslim     in ki ka duba Adabuz zifaf zaki ga Magana mai kyau kan sa hoto a tufafiko labule.
[54] Malaman musulimci na Ahlussuna sun tafi kan xaukar  hoto haramun ne wannan it ace Magana ingantatciya kuma ita  ce bn Baz da Albany da sauran malaman sunna  su ka xauka, ki duba littafin Riyadussalihin da Adabuzifaf da jawabul mufid na bn Baz da silsilatul AhadisusSahiha da ikrtiyaratulfiqhiya na Albany da Bukhari da muslim da  Gayatul maram   ko Iziya littafin fiqhulMalikiya zaki ga bayani kan harmcin xaukar  hoto  don haka bai kamata ki xauki hoto ba , balle ma  in zaki yi aure ki yi KALANDA wannan yafi tsananin haramci da muni. Hadisin da manzan Allah ya yaga labule Nana Aisha bai da inuw don haka kowane irin hoto ne haramun ne ki xauke shi ko ki manna a Xakin ki ko a kayan ki indai wannan hoton wani abu ne mai rai. Ba a fara yin shirka ba a bayan qasa sai ta sanadiyar hoto wannan Magana ce shahararriya maganace daga ibn Abbas   kuma duk kusan littafan tauhidi sun yi bayanin wannan. Za ka ga wasu hijabin  da hotonan  wasu mutane da sunan malamai ne ko masu mulki ,ko sarauta duk bai halasta a sa ma hijabi hoto ba ko na wane malami ne  bai halasta  a  sa   hotonan su  a jikin hijabi ba. Ko taurariya da wasu su ke sawa hijabin su  suma duk sun shiga cikin hanin.
[55] Ranar  goma ga watan Muharram ita ce ranar da a ke ce mata ASHURA,Manzon Allah ya yi   umurni ne da a yi    azumi   amma  a wajen  masu bin addinin‘’Yan SHIA rana ce ta baqin ciki shi ya sa suke sa baqaqen  kaya.Su kuma mara sani‘’yan Bidia  ranar suna yin cika-ciki ne, shi kuwa cika-ciki Bidiace domin ba shi da asali a shari’ayar Annabi da Sahabbai da sauran magabata na qwarai.. Su kuma NAWASIBA ranar farin ciki ne a wajensu  shi ya sa suke yin abinci  suna rabawa gida-gida suna farin ciki su ma  abin da suke  yi Bidia ce. Su kuma AHLUL SUNNA suna yin Azumi ne kamar   yadda Annabi sallahu alaihi wa alihi wasallam ya yi umurni da a yi nemi littafina na “Tasu’a da Ashura da Cika-ciki”.
[56] JilbabulMartul muslima   Ammru Abdulmum’in 47
[57] Musannaf Abi Shayba
[58] Suratul Taharim.
[59] Sanannen abu ne cewa ilmin addini da kwatanta aiki da shi, sanya sutura  ta Musulunci da tarbiya ta zahiri, alamomi ne da ake lura da su wajen kyautata wa mace zaton cewa tagari ce (المرأة الصالحة). To amma kasancewar ana samun akasin haka bayan an yi auren, wajibi ne kowane Musulmi ya riqa yin addu’a tare da roqon Allah Ya taimake shi wajen samun mace ta kwarai, mai tsoron Allah, wadda za ta iya yin tarbiyar kanta da na `ya`yansu, 
[60] Iyaye su umurce su da hijabi cikakke idan za su fita gida zuwa makaranta ko kasuwa ko gidan buki ko asibiti ko ziyara   ko wani wuri dabam. Haramun ne a kyale `ya`ya mata su riqa sanya tufafi shara-shara ko kuma su fita ba tare da hijabi cikakke ba, da zaran sun balaga – sun fara jinin al’ada. Maganar cewa hijabi wajibi ne kawai a kan matar aure, ba ta da asali a cikin Musulunci. Allah (Mai girma da daukaka) Ya ce: “Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana qawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su sanya da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna qawarsu face ga mazansu, ko ubanninsu…”[60] Kuma Ya ce: “Ya kai Annabi! Ka ce wa matanka na aure da `ya`yanka da matan muminai su kusantar da manyan tufafin da ke kansu kasa……… , bai halasta a ga wani bangare na  jikin tab a. in dai ta balaga Haka nan, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: “Daga qarshen al’ummata, za a samu wadansu mata (na yawo) sanye da tufafi (amma kuma saboda shara-sharansa), tsirara (suke a zahiri)… Ku la’ance su, domin kuwa la’anannu ne. A cikin wani hadisin, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce: “Ba za su shiga aljanna ba, kuma ba za su ji qamshinta ba.Ke nan, da zarar yarinya ta balaga (ko da ba ta yi aure ba), wajibi ne ta sanya hijabi na Musulunci idan za ta fita. Amma kasancewar itace ana tanqwara shi ne tun yana danye, ya kamata iyaye su himmatu wajen koya wa `ya`yansu sanya hijabi da saba masu da fita da shi, maimakon gyale ko abin tatan qullu.  Shaykh Muhammad Saalih ibn al-‘Uthaimeen ya ce: “Ya ku `yan’uwa, iyayen `ya`ya mata! (A yau) Sanya wa `ya`ya mata gajejjerun tufafi ko tufafi matsattse da ke siffanta jiki ko tufafin da ke bayyana launin jiki saboda shara-sharansa, abu ne da ya yadu a tsakanin mutane kuma aka dauke shi da sauqi. (Ku sani cewa) wanda duk ya sanya wa `ya`yansa mata irin wadannan tufafi ko kuma ya ke qyale su da  gyale, to yana sanya masu tufafin `yan wuta ne, kamar yadda ya tabbata daga Annabi (tsira da aminci su tabbata a gare shi).s Ya kai uba musulmi! Yanzu za ka so wa `yarka kuma masoyiyarka shiga wuta? Ka yarda ka riqa sanya wa `yarka tufafin da zai nuna rashin kunyarta, bayan kuwa kunya na daga imani? Ka yarda `yarka ta mayar da kanta kamar wata hajar (kayan) sayarwa…?
[61]  Sa hula xabiace ta mutane masu mutunci da karamci da sanin          yakamata da kamala, Tafiya kai ba hula xabiace  ta Arna haka yafarune bayan zuwan Turawa qasashen musulmai duba Tamamul minna za ka ga Magana gamsasshiya, don haka ‘’yan uwa su kiyaye su daina tafiya kai ba hula.   Hadisin da aka ce Annabi ya cire hularsa ya yi sutura da ita lokacin da yazo sallah ba sutura wannan hadisin bai tabbata daga Annabi ba hadisi ne na qarya,duba Silsilatul Ahadisul Dhaifa da Tamamul minna fi taliqi ala fiqhu Sunnah.
[62] Yana da kyau masu aibata mata masu sa nikab da su yi hakuri su fadada karatun su ko kuma su je su tambayi malamai   ma su     ilimi su bar fadin abin dab a su da ilimi a kan shi  dasu bar maganar da ke bayyanar da jahilcin su.
[63] Bukhari.
[64] Bukhari.  9365
[65] In ki ka duba Suratu Nur  zaki ga wannan kissar ko ki duba  Bukhari zaki ga bayani.
[66] Audatul hijab
[67] Ahmad 6/30
[68] Ibn Said  49
[69] Muwadda ta Imam Malik 
[70] Tafsirul Baydawi
[71] Ibn Said
[72] Ibn  Majah
[73] Bukhari
[74] Hijabul mar,atul muslima
[75] Bayhaqi  8/93
[76] Imamun Nawawi yana da fahintar sanya Niqabi wajibi ne idan dai ana gani zamani ya lalace kuma ana tsoron faxawa cikin fitina  to mata su rufe fuskokinsu shi ya fi alkhari.
[77]  Fafirru ilallah na Abi Zaid
[78] Musannaf  Abi Shaybah  2/231-6294 isnadinsa  sahihi ne
[79] Wadannan hadisai da muka kawo  sun nuna mana  a fili karara  cewa Niqabi yana da asali kuma mata masu daraja sun sa , nasihar mu ga masu aibata niqabi   da suji tsoron Allah su sani yin haka   zai ja masu haxari  ga   imanin su    kuma aibata masu sa Niqabi  zai koma ne zuwa ga matayen Manzan Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam da matayan sahabbai da Tabi’ai, domin sune farkon waxan da suka fara sa Nikabi kafi  kowa ko kafin  wata ta  ta sa. 
[80] Raddul azhan ila ma,anil Kur,an
[81] Hijabul mar, atul muslima.
[82]  A cikin littafin sa Raddul mufhim yagoyi bayan sa nikabi  domin ya kawo hadisai da su ke nuna sharia ce mace ta rufe fuskar ta kuma matayen Annabi sallalahualaihi wa,alihi wa,sallam da sahabbai sun sa amma a ce dole ne ba mu  da hujja a kan haka sai dai sunna ce kuma mustahabbi ne mata su sa niqabi amma ba dole ba ne amma su sa shi ya fi.
[83] Abu Dauda 4/41 sai dai wasu malamai sun ce hadisin mai raunine saboda  a cikin  isnadinsa   a kwai illoli guda hudu
1Khalid bn Dharayk  bai hadu da nana Aisha ba isnadinsa Munkadi’I ne.
2Qatada yayi  an an  kuma mudalis ne.(yaiy jurwaye a cirato hadisin kuma gashi shi kansa dama mai mguxe ne)
3 Sa,id bn Bishir Dhaif ne musamamam ta wajen Qatada.
4. Khalid  bn Muslim yayi an an kuma shima  mudalis ne.
[84] Fatwa Madina 10
[85] Imamun Nawawi yana da fahintar sanya Niqabi wajibi ne idan dai ana gani zamani ya lalace kuma ana tsoron faxawa cikin fitina to mata su rufe fuskokinsu shi ya fi alkhari.

[86] Risala fil hijab
[87] Majmu’ul fatawa usaimin.
[88] Usratul muslima. Sheikh usaimin ya yi Magana mai yawa  kan dole ne mace ta rufe fuskarta yana da kyau a duba littafinsa wanda  muka kawo a baya.
[89] Fatawaa  Mar`atul Muslimah 602
[90] Ahkamun Nisa da Hijab adillatul nujibina wa shubuhul mukalifina.
[91] Hirsatul fadhilah 77
[92] Hirsatulfadhilah 45-65
 [93] Assarimulmashur alat tabaruj wassufur wafi raddul ala kitabul Albany
[94]  Assarimul masshur al tabaruj wassufur wa fi  Raddu al  kibabul Albany
[95] Dhawabidul Hijabi Shar’i
[96] Majmu’ul fatawa 22/110-114
[97] Fathul Bari na  ibn Rajab al-Hambali 1/507 da Tahzibuz Sunanan 5/198 da I’ilamul Muwaqqi’ina
[98] AaradhatulAhwaziy 4/56
[99] Dukkan wadannan malaman ba su yi wannan fihinta tasu kan ra’ayi ba sai dai don Allah da kuma kyakkyawar niya   don haka wanda ya ce sa nikabi dole ne  dogaransa da hujjojin wadanda suka ce wajibi ne  ba za a zarge shi ba don yana da magabaci kan fahintarsa in kuma ka ce ba dole ba ne amma sanyawan shi yafi alkhari shima ya na da magabaci kuma shima yana da na sa hujjar.Inda illar ta ke kace ba kyau ko bai da asalin ko bidia ne nan ne fa malamai za su yi maka raddi kan bayyanar da jahilcin ka a fili.
[100] Babu ko shakka Yahudawa suke amfani da shi wajen cin mutuncin musulici.
[101] Duba Nisau Ahlinnar
[102] Bukhari
[103] Bukhari
[104] Wani abin ban takaice a yau sai kaga mata suna tafiya tsakiyar hanya ba sa ko jin kunya, wani lokacima har ka ga suna haxa jikinsu da maza sabo da matsatsin hanya, a gaskiya yin haka kuskure ne muna roqon ‘yan uwanmu mata da su gyara don girman Allah  in suna tafiya su bi gefen hanya kamar yadda  Annabi sallahu alaihi wa’aihi wasallam ya koyar da mu, Allah ya taimake mu amin.
[105] Ahmad
[106] Ahmad. Sheikh Mashur Hassan Salman ya rubuta littafi wanda ya ke nuna harancin qwallon qafa sunan littafin ‘’Kurratul Qadam”qwallo dai ga maza ma ba ta halasta ba balle mata.IbnTaymiyyah yayi bayanin hukunci qwallo a Majmuol Fatwa da asalinta yana  da kyau aduba bayaminsa.
[107] muslim
[108] Baihaqi
[109] To ma su xaura ma yaransu mata talla sunji xaukan kaya mai nauyi yana kawar ma mata budurcinsu sai abi a hankali. Kuma dama talla tana cikin abin da ke lalata tarbiyar yara mata har ma ya kai su shiga zinace- zinace ta sanadiyar talla, wulaqanta mata ne ariqa xaura masu talla, iyaye su ji tsoron Allah su kula ‘ya’yansu, su tuna da cewa amana ne Allah ya basu zai kuma tambaye su akan amanar ‘ya’yansu.
[110] Ahmad
[111] Fatawaa Mar’atil musimah 603
[112] Za mu iya tunawa a qasar Hausa sarakuna da mata suke tsafi a yave su da rai ajikin gida ko ganuwa kafin jihadin Xanfodio.
[113] Har yanzu a qasar Indiya akwai masu yin haka, kuma aqasar Indiya har yanzu mace zata iya auren maza fiye da guda xaya Allah ya kyauta amin.
[114]  Burgeba ya mutu a wulaqanci haukacewa  yayi Allah ya tsare mu, a lokacin sa ya  kasha maya-mayan malaman Musulinci, malaman duniya sun bad a fatawan cewa Burgeba ya kafirta, haka ya faru da shi ne saka makon neman ‘yanci
[115] Matan har yanzu a Turai basu da qima domin kuwa acikn  tsarin mulki (consitution) na Faransa ya halasta ma magidanci idan yana fama da taulauci ya xauki matarsa ya jinginar da ita, ‘yar uwa ina ‘yanci yake anan, an tava shiya tattaunawa a qasar Ingila wai shin mata dabbobi ne kuma mutane ne  ina za a sa su, ina ‘yanci yake, a Amurka mata sun tava kai qara akan wai ana taqura masu da ake cewa su riqa sa rigan mama in za su shiga wanka a rafi (swiming pol) su ka ce baza su qara sawa ba sai in suma maza za su riqa sawa, irin wannan ‘yanci ne ake so ki nema !. yana daga cikin ‘yancin mata awajen Yahudawa abar mata su riqa  auran junan su mace ta auri mace لا إلَهَ إلا اللهُ Allah ya tsare mu.
[116]  Nemi littafina ‘Haqqoqin ‘Ya’ya akan Iyayensu” muna ruqon iyaye da su kula da ‘ya’yansu masamman mata domin yanzu wani bala’i ya faxo mana yadda ‘yan Film xin Hausa suke vata mana tarbiyyar ‘ya’yanmu muna roqon Allah ya kare mu daga sharrin ‘yanfilm da ‘yan maxigo (lessbianism) Allahumma amin.
[117] Jaridar Weekly Trust ta  tattauna da malamai akan koya wa yara ilimin jima’i  (sex education) abin farin ciki  dukkanin malaman mu na musulinci ba su yarda ba kai  har da na Kiristoci suma ba  su yarda ba, amma abin baqin ciki wani daqiqin malami na musulinci a Kaduna ya ce a koya wa yara ba komai yana da kyau Allah ya kyauta  Allah ya shirye shi.

1 comment: