Friday, February 11, 2011

YADDA AKE SANYA SUNAN 'YA'YA A MUSULINCI

SABUWAR SHEKARA TASU'A DA ASHURA DA CIKA-CIKI


ABUBUWAN DA YAKE CIKI

Gabatarwa…………………………………………………2
Godiya…………………………………………………….3
Asalin watannin Musulinci………………………………..4
Qalu bale ga ‘yan Qalaqato……………………………….7
Duniya ta kasu kasha biyar………………………………..9
Mushirikai………………………………………………….9
Nawasiba…………………………………………………..11
Matayen Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam……12
 ‘Ya’yayan Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam…..18
Jikokinsa……………………………………………………19
Ahlul Bayti a dunqule…………………………………….22
Haqqoqin Ahlul Bayti…………………………………….23
‘Yan Bidia da hukuncin cika-ciki a musulinci……………24
Masu bin Addinin Shia……………………………………26
Ahluls Sunnah da Siffofinsu da tsarin su………………….30
Azumin Tasua da Ashura………………………………….31
Hukuncin Hutun sabuwar shekara………………………...34
Hukuncin faxin Happy New Year………………………...35
Hukuncin Bikin Kirsimeti…………………………………35
Hukuncin cin abincin Kirsimeti…………………………..37
Bikin Ranar Masoya ta Duniya (Valentine’s Day)…..38
Bikin Ranar Masu Dariya ta Duniya……………………..40
Kammalawa…………………………………………………………42



GABATARWA
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
إنَّ الحَمْدَ لله، نَحْمَدُه، ونستعينُه، ونستغفرُهُ، ونعوذُ به مِن شُرُورِ أنفُسِنَا، وَمِنْ سيئاتِ أعْمَالِنا، مَنْ يَهْدِه الله فَلا مُضِلَّ لَهُ، ومن يُضْلِلْ، فَلا هَادِي لَهُ.
وأَشْهَدُ أنْ لا إلَهَ إلا اللهُ وَحْدَهُ لا شَرِيَ لَهُ، وأشهدُ أنَّ مُحَمَّدًا عبْدُه ورَسُولُه أما بعد:    
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Ya Allah kai daxin aminci ga sahabban Annabi sallallahu alayhi wa alihi wa sallam. Wannan wata ‘yar taqaitacciyar maqala ce wadda ta qunshi bayani kan azumin Tasu’a da Ashura da bayani kan cika-ciki da kuma bayani kan sabuwar shekara ta musulunci da bayani akan Kirsimeti da hukuncin cin abincin kirsimeti da bayanin ranar masoya ta duniya, ina roqon Allah ya anfanar da mu amin. Kuma kamar yadda yake ta’adata ce bayanina ya na kasancewa ne qarqashin qur’ani da Hadisi da maganganun magabata na qwarai, Allah ya taimake mu amin. Kuma qofar gyara a buxe take ko shawara ko qarin   bayani.[1]

GODIYA
Bazan gushe ba  ina wa mahaifiyata Fatimatu Xalhatu Zaria da babana Abubakar Ibrahim adduar Allah ya ba su Aljannah amin. Haka shima Malamina marigayi Sheikh Imam Mika’il Isah Shika Allah ya gafarta mashi Allah ya bashi Aljannah amin.Malamina Malam Haruna Ishaq Shika Alqali Allah ya saka ma shi da Aljannah, haka shima Malamina Malam Ahmad Bello Dogarawa Allah ya yi mai sakamako da Aljannah, yana qarfafa na matuqa wajen cigaba da talifi. Dr Ahmad Bello Sardauna Shugaban Tsangayar qidaya da lissafin kuxi na Jami’ar Ahmadu Bello Zaria (HOD Accounting Department) babu abin da zan ce a gare shi face Allah ya bashi AljannatilFirdausi shi da mahaifansa yana taimaka man sosai wajen ganin duk littafin da na rubuta an fitar da shi domin amfanar musulmai, Allah ya taimake shi. Godiya ta masamman ga Malam Musa Sahabi da Malam Abubakar JumareGixaxo Zaria.Kofa abuxe ta ke ga mai shawara ko gyara, za a iya samun littattafan dana rubuta a mudawwanata ta yanar gizo mai alamar  http://harunaabubakarshika.blogspot.com ina roqon addua ta alheri ga duk wanda ya karanta littafi na nagode. Kuma amincin Allah ya tabbata ga duk wanda yaga gyara ya nuna mani.  Wassalamu alaykum warahatul Lahi wabarakatuhu
                                 Harun Abubakar Shika
                       harunaabubakar99@yahoo.com
24- Zulhajj-1430/ 11-Dec-2009
+2348030582333-08054533361-08020900001





                ASALIN WATANNIN MUSULUNCI.
Asalin watanni a wajen Allah guda goma sha biyu ne (12) kamar yadda ya ambata a  cikin littafinsa mai girma.[2]

إِنَّ عِدَّةَ الشُّهُورِ عِنْدَ اللَّهِ اثْنَا عَشَرَ شَهْرًا فِي كِتَابِ اللَّهِ يَوْمَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ مِنْهَا أَرْبَعَةٌ حُرُمٌ ذَلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ فَلَا تَظْلِمُوا فِيهِنَّ أَنْفُسَكُمْ وَقَاتِلُوا الْمُشْرِكِينَ كَافَّةً كَمَا يُقَاتِلُونَكُمْ كَافَّةً وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ مَعَ لْمُتَّقِينَ[3]                                        
Allah ya na cewa “Haqiqa qidayar watanni a wurin Allah guda goma sha biyu ne a cikin littafin Allah tun ranar da Ya halicci sammai da qassai, daga cikin waxannan watanin (12) akwai watanni huxu masu alfarma.[4] Wannan shi ne addini madaidaici, saboda haka kada ku zalunci kawunanku a cikinsu, kuma ku yaqi Mushirikai baki xaya kamar yadda suke yaqar ku baki xaya. Kuma ku sani cewa lalle Allah yana tare da masu taqawa (masu kiyaye dokokin Allah). Wannan aya ta nuna mana cewa watanni a cikin littafin Allah guda goma sha biyu ne haka shi ma manzon Allah sallallahu Alayhi wa alihi wa sallam ya ce, Shekara watani goma sha biyu ne ake samu,  a cikinta (shekara) akwai watanni huxu masu alfarma,  guda uku haxe suke da juna: Zulqida da Zulhajji da Muharram da Rajab na qabilar Mudar  wanda yake tsakanin Jumada  da Sha’aban.[5]
وقال النبيُ صلى الله عليه وسلم: "السنةُ اثنا عشر شهرًا منها أربعةٌ حرم ، ثلاثٌ متواليات: ذو القعدة ، وذو الحجة ، والمحرم ، ورجبُ مضر الذي بين جمادى وشعبان"
 Malaman musulunci sun ce an ambaci watan muharram da suna Muharram ne saboda Allah ya hana yaqi a cikinsa. Wasu kuma malaman suka ce Allah ya ambaci watan muharram da suna Muharram ne saboda a cikinsa ne Allah ya haramta ma Ibilis (Shaixan) Aljannah.[6]  Zai yi matuqar kyau mu kawo watannin Musulunci guda goma sha biyun da Allah ya ambata a littafinsa mai girma, ga su kamar haka;
1. Muharram.
2. Safar.
3. Rabiul Awwal.
4. Rabiut Thani.
5. Jimadal Ula.
6. Jimada Thani.
7. Rajab.
8.  Sha’aban.
9.  Ramadan.
10. Shawwal.
11. Zulqada.
12. Zulhijja.
Waxannan su ne watannin Musulunci waxanda ya kamata a ce kowane musulmi ya haddace su, kuma ba za ka same su a cikin Qur’ani ba dole sai ka dawo ma sunnah, wannan shi ne yake qara nuna mana cewa ba za ka tava fahimtar Qur,ani ba sai ka yarda da Hadisi, domin Hadisi shi ne yake fasassara Qur’ani, wanda ya ce ba ruwansa da Hadisi Qur,ani kawai, to wannan ya bar musulunci, haka Allah ya ce a cikin  Qur,ani.[7]
 إِنَّ الَّذِينَ يَكْفُرُونَ بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ وَيُرِيدُونَ أَنْ يُفَرِّقُوا بَيْنَ اللَّهِ وَرُسُلِهِ وَيَقُولُونَ نُؤْمِنُ بِبَعْضٍ وَنَكْفُرُ بِبَعْضٍ وَيُرِيدُونَ أَنْ يَتَّخِذُوا بَيْنَ ذَلِكَ سَبِيلًا أُولَئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ حَقًّا وَأَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا مُهِينًا         

Allah yana cewa “Lalle ne wanxanda suke kafirta da Allah da ManzanSa kuma suna so (nufi) su rarrabe  tsakanin maganar Allah da maganar ManzanninSa, kuma suna cewa mun yi  Imani da sashe, (Qur’ani) kuma muna kafirta da sashe,(Hadisi) ( wato suna cewa sun yarda da Qur’ani ba su yarda da hadisi ba) kuma suna nufi su riqi  hanya a tsakanin wannan.  Waxannan sune kafire tsantsa  (masu qaryata hadisi suna cewa sun yarda da Qurani kawai) kuma mun yi tattalin azaba mai wulaqantarwa ga kafire.[8]
Wannan aya ta nuna mana cewa duk wanda ya qaryata hadisi ya bar musulunci.Nemi fassaran ta wajen malamai. Maganar wata ya zo cikin Qur,ani amma bayanin su filla-filla ya zo cikin Hadisi ne”.[9]
 Gaskiya abin kunya ne a ce mutum musulmi ya hardace watannin kafirci tun daga January zuwa December amma bai san na Musulunci ba, wanda asalin watannin kafirci guda biyar ne, daga baya suka kwaikwayi na musulunci suka maida nasu zuwa goma sha biyu. Kuma dukkanin watannin kafirci sunaye ne na gumakan qasar Girka [Greak].[10] Lalle ya kamata yara su tabbatar sun hardace watannin musulunci.
 Zamanin Manzon Allah sallalllahu alayhi wa alihi wa sallam babu cewa an shiga sabuwar shekara. An fara qirgar sabuwar shekara ne zamanin Khalifa Umar Allah ya qara masa yarda, shi ne ya tsara hijira har  aka sami tarihin hijira ta musulunci.[11]  Idan  an fahinci wannan za’a fahinci cewa duk wata magana  da ta zo a kan yin wata sallah ko wata addu’a a sabuwar shekara ba gaskiya ba ce.








 DUNIYA TA KASU KASHI BIYAR.
Game da watan Muharram ko mu ce sabuwar shekara ta musulunci duniya ta kasu kashi biyar, ga kasuwar ta su kamar haka;
1.      Akwai Ahlul Sunnah.
2.      Akwai Yan bidi’ah.
3.      Akwai Masu bin addinin Shi’a.
4.      Akwai Nawasiba.
5.      Akwai Mushirikai.
Waxannan su ne kason mutane game da watan muharram,  ga kuma bayaninsu xaya bayan xaya kamar haka;

1.       MUSHIRIKAI: Shirka shi ne haxa Allah da wani a cikin Ibada. Su waxannan kashi a farkon, watan Muharram suna aikata abubuwan da suke ba musulunci ba ne, suna yin wani abu wai shi buxar takarda wanda suke cewa an buxe takarda an ga a wannan shekarar za a yi fama da cututtuka da masifu da fari, wannan da’awar gaibu ce babu kuma wanda ya san gaibu sai Allah. A farkon watan Muharram   bayan sun yi buxar takarda sai su riqa zuwa daji suna yin waxansu surkulle,  shi ne da a qasar Hausa waxansu jama’ar sukan je daji su yi wani tsafi mai suna ‘Bukin budin daji’ da “Bukin giwa shallaka, a wajen qasar Gusau”waxannan duk sun sava ma koyarwar musulunci. Wasu kuma a watan Muharram suna shiga gida-gida suna ba da ruwa wai ga ruwan sabuwar shekara wanda ya sha ba zai yi ciwo ba har qarshen shekarar, suna yawo da takarda, wadda a cikinta akwai rubutun Larabci, a cikinta wai akwai hatimin Annabi Musa, yana maganin tsafi, sannan kuma suna ba da addu’o’in sabuwar shekara wai duk wanda ya karanta wannan addu’ar ba zai mutu ba  a wannan shekarar. Waxannan maganganu duk qarya ce tsantsa ba gaskiya ba ne.[12]
Ta sanadiyar buxar takarda da ake yi a sabuwar shekara,  in an gaya ma jama’a  za a yi qarancin ruwa sai su je daji su riqa qona bunsuru da ransa, da farautar qananan bisashe, in sun kama su sai su fexe su, idan suka sami ruwa a cikinsu, to buqatarsu ta biya idan ko ba ruwa sai tsafi, idan an faxa masu za a yi fama da  masifu, shi ne ya sa a qasar Zaria  a  da  ake zuwa Dutsen madarkaci, a Kano kuma suna da Tsunburbura, su kan je dutsen Dala su yi sur kulle Barbushe ya zo sannan a yanka ma Tsunburbura karya duk da sunan sabuwar shekara. Dukkan waxannan ba  gaskya ba ne qarya ce kuma shirka ne, Allah ya shiryi masu yin wannan aiki, waxanda kuma suka yi alhalin  ba su sani ba Allah ya gafarta masu, mu kuma sai mu kiyaye tunda mun sani lallai babu kyau Shirka ne.







2.      NAWASIBA:
Nawasiba wata muguwar qungiya ce daga cikin qungiyoyin ‘Yan bidi’a, masu wannan qungiya sun kafu ne kan zagin Ahlul Baiti musamman ma Sahabi Aliyu Allah ya qara masa yarda. Su kuma dalilin da ya sa suke zagin sahabi Aliyu shi ne  saboda su baqanta wayan Shi’a rai a kan wai yan Shi’a sun ce suna son sahabi Aliyu kuma suna baqin ciki a ranar goma ga watan Muharram, to sai su kuma Nawasiba suka riqa zagin sahabi Aliyu saboda su vata wa yan Shi’a rai. A ranar goma ga watan muharram Nawasiba suna dafa abinci suna kaiwa gida-gida suna shagali suna murna don an kashe sahabi Hussain jikan manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam a wannan rana ta 10 ga watan Muharram, wato a ranar yaqin Karbala.Waxannan qungiya su ma vatattu ne kuma hallakakku domin duk mai zagin Ahlul Baiti vatace ne[13].
Allah ya umurci dukkanin Musulmi da su so AhlulBaiti (Dangin Manzo sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam).  Allah Ya  faxi haka ne a cikin Qur’ani.[14]

ذَلِكَ الَّذِي يُبَشِّرُ اللَّهُ عِبَادَهُ الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ قُلْ لَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَى وَمَنْ يَقْتَرِفْ حَسَنَةً نَزِدْ لَهُ فِيهَا حُسْنًا إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ شَكُورٌ
 Allah yana cewa, “Wannan busharar Allah ce zuwa ga bayinSa, ga waxanda suka yi imani kuma suka aikata aikin qwarai. Ka ce bana tambayarku wata ijara, face soyayya ta cikin zumunta.” Kuma wanda ya aikata aiki mai kyau , za mu qara masa da kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai godiya.”[15]
Wannan aya ta kira baki xayan duniyar musulmai da su so dangin Annabi Muhammad sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, kuma shi kansa Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, Ina tunatar da mu Allah, mu so dangisa’’[16] yana da kyau mu san su wane ne dangin Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, wato Ahlul Baiti, ga su kamar haka;
 MATAYEN ANNABI sallalLahu alayhi wa alihi wasallam.
Matayen manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam suna cikin Ahlul Baiti kamar yadda aya ta faxa a cikin suratul Ahzab aya ta 31-33
يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآَتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا
Wannan aya a fili ta nuna mana qarara cewa matayen Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam suna cikin Ahlul Baiti[17] ga sunayensu kamar haka:
1.      Nana Khadijatu binti Khuwaylid[18].
2.      Saudatu binti Zam’ah[19]
3.      A’ishatu binti Abubakar Sidiq[20].
4.      Hafsatu binti Umar alFaruq[21].
5.      Zainab binti Jahash[22]
6.      Hindatu binti AbiyUmayyah(UmmuSalma)[23]
7.      Juwairatu binti Haris alKhuza’iyyatu[24]
8.      Safiyyatu binti Huyiy bin Akhdab[25]
9.      Ramlatu binti AbiSufyan (Ummu Habibatu)[26].
10. Maimunatu binti Haris alHilaliyyah[27].
11.  Zainab binti Khuzaimah[28].
12. Mariyatu alKibdiyyatu(Ummu Ibrahim)[29].
13. Raihanatu binti Sham,un.[30]
Waxannan su ne matayen Manzon Allah sallallahu alayhi wa alihi wasallam, duk wani mai son Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, babu shakka  zai hardace sunayen waxannan matayen na shi da ‘ya’yansa in dai da gaske ne son na sa.
‘YA’YANSA;
1. Abdullahi.[31]
2. Qasim.[32]
3. Ibrahim Mu’azzam.[33]
4. Zainab.[34]
5. Rukayyatu.[35]                                                    
6. UmmuKulsum.[36]
7. Fatimatu Zahara.[37]
JIKOKINSA;
1.      Hassan.[38]
2.      Hussain.[39]
3.      Muhsin.
4.      UmmuKulsum (matar Sahabi Umar).[40] Duk waxannan Nana Fatimatu ce ta haife su.
5.      Ummatu, ita kuma Nana Zainab ce ta haife ta.
6.      Abdullah xan Usman, shi kuma xa ne a wajen Nana Ruqayyatu.
AHLUL BAYTI A DUNQULE
A taqaice, muna iya cewa Ahlul Baiti ga su a dunqule, Matayen Annabi (sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam) da ‘Ya’yansa, da Jikokinsa, da Iyalin gidan Sahabi Aliyu[41], da Iyalan gidan Aqilu, da Iyalan gidan Ja’afar, da Iyalan gidan Abbas, da Hamza shugaban shahidai.[42] Duk wani mai son Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam zai hardace waxannan dangi na Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Kuma dole ya qaunace su ba zai qi su ba kamar yadda Nawasiba suke yi. A qarshe, muna addu’a ga Nawasiba Allah ya shirye su su bar zagin dangin Annabi  sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam.




Haqqoqin AhlulBayti akan dukkan Musulmi
1-Soyayya da qauna a gare su, soyayyanka ga Ahlul Bayti zai bayyana ne ta hardace sunayen matayensa da ‘ya’yansa da jikokinsa da daginsa musulmai da kuma  sanya sunayen  su.
2- Yin masu salati duk salatin da ba a sanya Ahlul Bayti ba, wannan salatin bai cika ba dole sai an sa  su, wajibi ne in kazo tahiya a sallah sai kai ma Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam salati, a cikin salatinsa akwai Alihi[43]
3- Biyayya da girmama su da mutunta su da basu kariya.

3.      YAN BIDI’A
Su kuma yan bidi’a a ranar goma ga watan Muharram suna yin abinci suna yin ginsami suna cika-ciki[44] wai suna cewaDuk wanda ya yalwata ma iyalinsa a wannan ranar Allah zai yalwata masa.Shi ne a qasar Hausa a ke ce ma ta cika-ciki (sallar Mata). Allah sarki! Su waxannan suna yin cika-ciki ne ba su san asalin wannan aiki ya samo asali ne daga masu qin Ahlul Baiti ba. Yin cika-ciki Bidi’a ne. Ibn Taymiyyah ya ce cika-ciki  ba addini ba ne,  jahilci ne, sava ma koyarwar Annabi (sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam) ne da ya ce a yi azumi a wannan ranar.[45]
Ibn Jauzi da Shaukani da ibn Qayyimul alJauziy da Imam Daru Quxini da Albany da Usaymin  sun ce duk wata magana da ta zo take nuni da a yalwata ma iyali a ranar goma ga watan Muharram ba gaskiya qarya ce.[46]  Wasu garuruwan har buki suke yi gaggarumi sarki ya fito ya yi hawa suna kiranta da suna Sallar-Gani da a ke yi a  garin Daura da Kazaure. Wannan duk bidi’a ce ba addini ba ne. Sai ka ji wasu su na cewa wanda bai cika cikinsa da abinci ba za a cika ma sa da wutar Jahannama, wannan maganar qarya ce tsantsa. Wasu kuma a wannan ranar za ka sami matasa suna shan taba da wiwi da kunna tazargade duk da sunan cika-ciki. Wasu yaran daga wannan ranar suke koyon shan taba da wiwi. A ranar dai mata suna sa kayan maza, maza su sanya kayan mata duk da sunan cika-ciki. Wannan savon Allah ne a fili qarara domin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wasallam ya tsine ma matan da ke sanya kayan maza, haka shi ma namijin da ya sanya kayan maza.[47]  Kuma a ranan goma ga watan Muharram wasu su kan je gidan wani malami su leqa rijiya wai za su ga burakar Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alhi wa sallam a cikin rijiyar, sannan su ba da kuxi su sha ruwan. Wannan duk haramun ne kuma damfara ne wasu masu danganta kansu da malanta su ka qirqiro don cuta. Don haka dai cika-ciki bidi’a ce ba addini ba ne. Allah ya ganar da mu, amin. [48]

4.      MASU BIN ADDININ SHI’A.
Kashi na huxu su ne masu bin addinin Shi’a: Asalin addinin Shi’a daga wani mugun Bayahude ne mai suna Abdullahi bn Saba’i.[49] Ya shigo addinin musulunci ne da niyyar ya haifar da matsala a cikinsa.Masu bin addini  Shi’a sun ginu ne a kan la’antar sahabban Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam da yin qazafi ga matayen Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, kai har ma da zaginsu masamman Nana A’ishatu da Nana Hafsah da mahaifansu Abubakar da Umar kai ya kaima har cewa suke Nana A’ishatu ta yi zina,[50]  da halasta zina wai da sunan Mutu’a,[51] da kuma raya cewa Qur,ani an canza shi, da kuma cewa qasar duniya baki xayanta ba ta da tsarki sai qasar Karbala. Sannan su masu bin addinin Shi’a suna ganin Limamansu sun fi Annabawan Allah daraja  da matsayi AyatulLahi Khomen ya tabbatar da haka a littafinsa Hukumatul Islamiyya ga abin da ya ke cewa’’

وإن من ضروريات مذهبنا أن لأئمتنا مقاماً لا يبلغه ملك مقرب ولا
                                   نبي مرسل"                                     

[52],”Ya ce haqiqa wajibi ne a tafarkin mu cewa shuwagabannun mu suna da darajan da yake wani  Mala’ika na kusa da Allah bai isa ya kai wannan matsayin ba balle Annabi ko Manzo”[53] Allah ya kyauta domin duk musulmi ya san ba wanda ya kai Annabawa da Manzanni da Mala’iku daraja, amma ga shi AyatilLahi Khomeni ya ce shuwagabannin Shi’a sun fi Annabawa da Mala’iku. Kuma su ma’asumai ne da kuma cewa Nana Fatimatu ce kawaiyar da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alaihi wa sallam wanda ya haifa”   wai sauran agola ne wannan magana hatta ma su bin addinin Shi’a na Najeriya su ma su na da wannan mugun tunanin har ma rubutawa su ke yi a jaridarsu shugabansu da kansa ya ce, “ Sayidina Fatimace kawai ‘yar da Manzon Allah ya haifa” duba  JARIDAR ALMIZAN 23-Jumadathani 1429 shafi na 4. Rafida (masu bin addinin Shi’a) a ranar goma ga watan Muharram suna xaukanta rana ce ta baqin ciki saboda a wannan ranar ce a ka kashe jikan Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam a yaqin Karbala, wato Sayidna Hussaini da qannansa Abubakar da Umar da Usaman dukkan su ‘ya ‘ya ne ga sahabi Aliyu[54] a wannan ranar suna sa baqaqen kaya suna kuka suna saran jikinsu da wuqa ko adda suna fitowa layi-layi suna kuka da baqaqen kaya  suna saran jikinsu suna la’antar sahabbai, suna xaukar ranar AShura amatsayin ranar baqin ciki.[55] Farfesa (Professor) Imam Musa Musawi ya ce “Kafirai ‘yan mulkin mallaka sune su ke qarfafa ma ‘yan Shi’a ranar Ashura su yi ta zubar da jini wai da sunan addini amma ba addini ba ne yin baqin ciki da kuka da saran jiki a ranar Ashura”.[56] Wannan malami babba ne a cikin addinin Shi’a kuma xan uwa na jinni na shugaban qasar Iran AyatulLahi Khomeniy amma ga abin da ya faxa nemi littafisa. Idan mutum yana kallon  Akwatin talabishan na qasahen waje zai ga wannan aikin na saran jiki da zubar da jinin a ranar Ashura sunce ranar kowa sai ya zubar da jininsa, yana da kyau mai karatu ya kalli waxannan Akwatinan talabishan na MANAR ko ALKWATHAR ko  ko AL-ALAM ko ALFORAT ko AL ANWAR ko ASC ko AHLULBAITI ko gidan Akwatin talabishan na Pakistan ko kuma ranar  ya zo Zaria zai ga yadda suke yi a kan titi mazansu da matansu zai ga yadda  masu bin addinin Shi’a suke yi a  ranar Ashura abin ban mamaki da tausayi zaka ga har da qananan yara ana fasa goshinsu duk da sunan juyayin ranar Karbala. Masu bin addinin Shi’a suna ganin duk qasar duniya bata da tsarki sai qasar Karbala shi yasa suke sa goshinsu a kan wani Qodago wai Turbatul Hussainiya da sunan wai qasar Karbala, ko su shafa ma wanda ya rasu a cikinsu.[57]  Waxannan suma abin da suke yi kuskure ne domin ya sava ma koyarwar Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam muna roqon Allah ya shiryi masu bin addinin Shia su gane cewa Shia ba addini ba ne. Sahabi Aliyu da kansa ya tura ‘ya’yansa Hassan da Hussain su je suyi gadin gida sahabi Usman wannan duk ya nuna mana babu tatavurza   balle tirjiya tsakanin sahabi Aliyu da Usman. Zaka ga masu bin addinin Shia suna tsine ma sahabi Mu’awiyaha bayan ko Mu'awiyah ya rasu da shekara biyu sannan aka kashe sahabi Hussaini a Karbala, to shi kuma Mu’awiyah mena laifinsa?

5.      Ahlus Sunnah:
AhlusSunnah su ne masu bin Qur,ani da Hadisi  a kan Fahintar magabata na qwarai, suna son Annabi Muhammad sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam da matayensa da sahabbansa daAhlul Baiti (Danginsa) da duk wani mumini mai bin Qur’ani da Hadisi bisa fahimtar magabata na qwarai, Ahlus Sunnah duk inda suke suna faxa da Shirka da Bidia, ubangidansu shi ne manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam.[58]
Ibn Taymiyyah ya ce dukkanin qungiyoyin baya vatattu ne kuma suna kan kuskure ya ce Ahlussunnnah sune matsaikaita basa komai sai bisa kan maganan Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, ya qara da cewa su suna yin azumi ne a wannan rana kamar yadda sunnah ta yi umurni da ayi basa buxan takarda ba sa cika-ciki ba sa baqinciki basa zagin sahabbai a’a girmama su suke yi da mutunta su da yin masu addua ta alheri,  Ahlussunnah azumi suke yi a wannan rana saboda shi ne umurni da Annabi sallallahu alayhi wa,alihi wasallam ya bayar kuma su dama umurninsa suke bi”.

  AZUMIN TASUA DA ASHURA
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, Mafificin azumi bayan azumin Ramadana shine azumin watan Allah mai alfarma Almuharram.”  Ya cigaba da cewa mafificiyar sallah bayan sallar farilla ita ce sallar nafila cikin dare.[59]  Sheikh Usaymin ya ce, “Azumin watan Muharram wanda ya ke bayan Zulhajj wanda Sahabi Umar ya sa shi a farkon shekara ta musulunci, ya ce “wannan azumin shine mafifici bayan azumin Ramadan”.[60]Da  a farkon musulunci azumin Tasu’a wajibi ne amma daga baya ya koma ba wajibi ba. Bayan an wajabta azumin Ramadana sai ya zama wanda ya so ya yi wanda bai yi ba bu laifi a gare shi.[61]
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, Azumin Tasua yana kankare zunubin shekara.[62]
 Wata ruwayar manzon Allah umurni ya bayar da umurnin  a yi azumin Tasua.[63]
Asalin azumin Tasua manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya zo garin Madina ya taras da Yahudawa suna azumi ranar goma ga watan Muharram, da ya tambaye su dalilin yin azumin  sai suka ce a ranar ne Allah ya tserar da  Annabi Musa daga Fir’auna da rudunarsa. Sai manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “mu ne muka fiku cancanta ga Annabi Musa sai ya azumci wannan rana ya kuma umurci al’umma da su azumci wannan rana ta goma ga watan Muharram, kuma da ma Qureshewa suna girmama wannan ranar.[64] 
Ranar goma ga watan Muharram ce Allah ya tserar  da Annabi musa  daga sharrin Fir’auna, kuma a dai goma ga watan ne Allah ya tserar da Annabi Nuhu da jama,arsa daga ruwan xufana sai su ka azumce ta saboda godiya ga Allah.[65] Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya azumci, azumin Ashura ya ce baxi in Allah ya kai mu zan azumci Tasua wato tara ga watan Muharram.[66]
Yahudawa sun xauki ranar Ashura ranar farin ciki manzon Allah sallallahu alayhi wa,alihi wasallam ya ce “Ku kuma musulmai ku sava ma su ku yi azumi a wannan ranar.[67]Ibn Abbas ya kasance yana yin azumin Tasu’a da Ashura ko yana cikin halin tafiya ne, sunnah ce yin azumin Tasu’a kamar yadda azuminAshura yake Imamu Shafi,i da Ahmad bn Hambal sun kasance suna yin Azumin Tasua da Ashura  domin su sava wa Yahudawa su Yahudu goma ga muharram kawai suke yi basa yin tara, don haka ana buqatarka da kayi Tasua da Ashura domin ka sava ma Yahudu.[68]Ibn Taymiyyah ya ce, “sunnah ce mustahabbiya yin azuminTasu’a da Ashura ajere yin guda biyun shine bin umurni Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam.[69]
 Sheikh Usaymin ya ce yana da matuqar mahimmanci yin azumin Tasu’a da Ashura wato azumin tara da goma ga watan muharram ya ce a qarfafi  jama’a da su azumci waxannan ranaku, domin a wannan rana ce Allah Ya halaka Fir’auna Ya tserar da Annabi Musa. Usaymin ya qara da cewa wasu malaman ma suna ganin makaruhi ne  yin azumi xaya ka bar xaya suka ce idan ka yi Tasua ba, ka yi Ashura ba ko kayi Ashura ka qi yin Tasu’a baza ka sami cikakkun lada ba.[70] Yin azumin Tasu’a da Ashura shi ne ya tabbata  amma yin azumin watan Muharram  baki xayansa bai tabbata ba ko yin wata sallah ta daban a ranar Ashura bai tabbata ba.[71]
Yin cika-ciki bidia ne kuma cikin bayanin a baya za mu iya fahimtar ba bu wani abu wai shi “happy newyear” don sabuwar shekara ta shiga, wannan koyi da Kiristoci, abin da dai ya tabbata babu wani baqin ciki ko farin ciki ko cika-ciki ko wata sallah ta musamman ko shan wani rowan sabuwar shekara ba, abin da ya inganta shi ne yin azumin Tasu’a da Ashura.

HUNTUN SABUWAR SHEKARA
Akwai wani abin ban mamaki da ban takaici idan akace watan Muharram ya shigo zaka samu wasu mutane suna cewa a ba da hutun sabuwar shekara, wai saboda suma Kafirai suna yi hutun sabuwar shekara na January  wannan babu ko kokonto bidiace kuma koyi ne da Kiristoci,[72] zamanin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa,alihi wasallam babu wata sabuwar shekara,kuma ba a samo daga magabata ba inda aka ce yau suna hutun sabuwar shekara. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wasallam ya ce “ Wanda ya kamanta kansa da wasu mutane to ya na tare da su”
من تشبه بقوم فهو منهم"
     Ibn Tamiyyah ya ce “ Wannan  hadisin ya nuna  mana cewa bai hasta koyi da Kafirai ba ko ta  wace hanya, haramun ne koyi da Kafirai wajen sanya tufafi  ko abincin da ya ke na kafirai ne kawai bai halasta ka ci ba ko koyi da su wajen yadda su ke wanka  ko koyi da su wajen gaisuwa[73] ko shiga sabuwar shekara ta wajen kunna wuta,[74] ko murna ko biki.”[75] Wannan Magana ta Sheikul Islam ta fito da bayani a fili na haramcin koyi da Kafirai kuma ya nuna mana babu kyau murnar shiga sabuwar shekara ta musulinci ko yin biki ko hutu kamar yadda Gobnatin jahar Kano ta bayar da hutu don sabuwar shekara wannan bidiace kuma koyi ne da Yahudawa da Kiristoci maqiya addinin Allah, yana da kyau mai karatu ya ne littafin Ibn Taymiyyah mai suna Iqtida’u Siradil Mustaq…..  Ibn Qaym ya ce haramun don sabuwar shekara ta shiga a riqa cewa Happy New year/ ko happy Xmas[76]

  HUKUNCIN BIKIN KIRSIMETI
Kirsimeti shine bikin da Kiristoci su ke yi wai suna tunawa da ranar da aka haifi Annabi Isah ta zagayo wannan ranar ita ce ishirin da biyar 25 ga watan Disemba (25-December) da kuma haxawa da bukin shiga sabuwar shekarar su ta Kafirci za su riqa dafa abinci suna shagali suna murna da zagayowar ranar haihuwarsa (Annabi Isah) suna buki suna bayar da kyauta suna hura wuta wanda a yanzu sun zamanantar da shi suke yin kock out su haxu a majami’unsu su  yi ta tunvele.
Wanda ya yi Kirsimeti ko ya yi shagalin Kirsimeti Ibn Turkamiy alHanafi ya ce indai bai tuba ba to ya zama Kafiri domin ya yi daidai da su Allah kuma yana cewa.
يا أيها الذين آمنوا لا تتخذوا اليهود والنصارى أولياء بعضهم أولياء بعض ومن يتولهم منكم فإنه منهم              
 “Ya ku waxan da su ka yi imani da Allah ka da ku riqe Yahuda da Kirstoci masoya, sashinsu masoya sashi, wanda ya jivincesu to yana tare da su” ya ce wannan ayar hujja ce.[77]
Abu Hanifa ya ce wanda ya ba da kyauta ga kafiri(Kirista) ranar Kirsimeti saboda girmama Kirsimeti ya zama Kafiri a wane wajen ya ce wanda ya ba da kyautan kwai ga mushiriki sabo da girmama ranar (Kirsimeti) ya kafirta .[78]
      "من أهدى فيه بيضة إلى مشرك تعظيما لليوم فقد كفر بالله تعالى                                    
Ibn Taymiyyah ya ce ijima’i ne cewa haramun ne zuwa wajen Kirsimeti wannan ita ce mazahabar Abu Hanifa da Malik da Shafi’i da Ahmad.[79]
Imam Malik da ibn Qasim sunce musulmi ya nisanci abin hawa na kirsimeti in dai abin hawan don kirsimeti ne makaruhi ne kai musulmi ka hauta.[80]
Sheikh Usaymin ya ce haramun ne zuwa wajen Kirsimeti ko ka ce Happy New Year ko Happy Xmas wannan maganar ijima’i ne kuma harmun ne musulmi ya aikata su.[81]

HUKUNCIN CIN ABINCIN KIRSIMETI
Ya halasta cin abinci Kirista ko Bayahude ba tare da ka tambaye shi wa ya yanka masa ba indai abinci nan halas ne a gareka kamar naman kaza ko saniya ko rago sun halasta in Kirista ya baka ka ansa ka ci ba komai a gareka, ba a ce ka tambaye shi waye ya yanka masa ba.[82]
Amma game da cin abincin ranar Kirsimeti wannan haramun ne bai halasta  ba  babu wani malami daga cikin malaman sunnah da ya halasta cin abincin ranar Kirsimeti. [83]
 Ya kamata dai musulmai su kula mu gane cewa ba wasa muka zo yi duniya ba kuma muna da tsari wanda bai buqatar na Kafirci, kuma ya na da kyau mu gyara  aiyukan mu zaka ga wasu ba sa xaura aure sai ranar kirsimeti wasu malaman suna ganin xaura aure ranar kirsimeti haramun ne, kuma suna da hujja mai qarfi ya kamata mu kula.


  BIKIN RANAR MASOYA (VALENTINE’S DAY)
Bikin ranar masoya ta duniya ana yinta ne sau xaya a shekara, a ranar 14 ga wata Fabareru (14 Febuary) ta samo asali ne daga masu bin addinin kiristanci a shekaru xari biyar 500 bayan tafiyar Annabi Isah alayhi salatu wassalam aka fara shi, wanda ya qirqiro wannan tunvelen shi ne wani qaton kafiri ne mai suna Fafaroma Gelasius  Sanadiyar kiranta da wannan suna shine da  an hana sojojin kiristoci yin aure ne daga baya aka basu izini da suyi auran su..[84]
 A wannan rana ana yanka karnuka da awaki da aladu sai a samo qartai majiya qarfi guda biyu su shafe jikin su da jinin waxannan dabbobin, bayan haka sai su wanke jikinsu da madara, waxannan qartin za a karramasu  saboda shafa jinin da suka yi sai a basu ‘yan mata su zava.[85] A wannan ranar suna sanya jajayen kaya da jan takalmi suma dabbobin jajaye  suke samowa, suna  sayen jajayen furanne ana aikawa da su ga masoya da takardan gaisuwa  (Greeting card) xauke da huton Mala’ika da fikafikai guda biyu (wannan qarya ce domin ba bu wanda ya tava ganin mala’ika acikin su) a wannan rana zina ba laifi ba ne a wuri su. 
 Haramun ne a musulinci yin bikin ranar masoya (Valentine’s Day) domin shi musulmi kullun yana nuna soyayya ga matar sa, kuma mu a wajen mu haramun ne yin zina Allah Ya yi tattalin azaba mai tsanani ga mai yin zina in bai tuba ba kuma harun ne mu a musulinci cin naman  alade balle har mu shafa jinin alade ajikin mu, shima cin naman kare haramun ne balle a shafa jininsa. Shafa jijin  dabobi ajiki ya iya bayuwa ya zuwa ga shirka, Allah ya kyauta. Sayan Greeting card shima  bai halasta ba ko ba a wannan ranan ba domin koyi ne da Kafirai sune su ka qirqiro Greeting card,  haka sanya jan tufafi a ko wane lokaci haramun ne, haramun ne inji Annabi sallalLahu alayhi wa alhi wasallam ya ce jan kaya na  kafirai ne  duba Zadul Ma’ad bai halasta ba musulmi ya sanya jan kaya.[86]
An tambayi babban Malaml Sheikh Muhammad Usaymin hukuncin bikin ranar masoya ta duniya sai ya amsa da cewa haramun ne yin wannan bikin kuma limamai su gaya wa mutane haramcinsa da bala’in da ke cikin ta.[87]
Abin baqin ciki a yau ‘yan mata da ke makarantun gaba da sakandire (University)   da maza waxan da basu san addini ba zaka ga suna sayan Greeting card suna  ba ‘yan mata yin haka haramun ne.  Yin wannan bikin ya sava wa musulinci ya kamata a tsoratar da ‘Yan Boko su gane sharrin shi, kuma dasisa ce ta maqiya addinin Allah, Allah ya kyauta amin. kuma muna kira ga iyaye su kula da ‘ya’yansu domin kuwa koyi  ne da kafirai  yin wannan biki, Allah  ya shirye mu.[88]
Abin baqin ciki zaka ga a makarantun gaba da sakandire (Universities) maza da mata suna wa junan su murnan zagayowar ranar masoya, ko kaga an rubuta a Allan sanarwa (Notice Board) ana ma xalibai murnan zagayowar ranar masoya (Valentine’s Day) yin haka kuskure ne babba kuma sava ma koyarwan manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ne, ‘yan uwa maza da mata su ji tsoron Allah su bar wan tunvelen, na kafirai ne ba nanu ba. Sheikh Munajjid ya yi littafi masamman mai magana akan haramcin bikin ranar masoya ta duniya, jeka yanar gizan sa zaka samu littafin nasa (www.qa.com).









KAMMALAWA
 A qarshe ina roqon Allah da ya amfanar da ‘yan uwa wannan yar taqaitacciyar   maqala, kuma duk wanda ya ga kuskure ko gyara ko shawara, qofa a buxe take, kuma ina maraba da gyaransa ko qarin bayaninsa. Sannan ina roqonsa don Allah ya yi man adduar ni da iyaye na ta alheri nagode.
    Jazakumul Lahu Khairan. والله أعلم
وصلى الله وسلم وبارك على عبده ورسوله محمد النبي الأمي وعلى آله وصحبه أجمعين ومن تبعهم بإحسان إلى يوم الدين.       
هذا وما كان فيها من صواب فمن الله وحده، وما كان من سهو أو خطأ أو نسيان فمني ومن الشيطان، والله ورسوله منه براء، وهذا بشأن أي عمل بشري يعتريه الخطأ والصواب، فإن كان صواباً فادع لي بالقبول والتوفيق، وإن كان ثمّ خطأ فاستغفر لي.
وإن وجدت العيب فسد الخللا
جلّ من لا عيب فيه وعلا
فاللهم اجعل عملي كله صالحاً ولوجهك خالصاً، ولا تجعل لأحد فيه نصيب
                            والحمد لله الذي بنعمته تتم الصالحات.                                                        وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين،
هذا والله تعالى أعلى وأعلم.........
سبحانك اللهم وبحمدك، أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك
Wassalamu alaykum warahamatulLah
Harun Abubakar Shika
                   24- Zulhajj-1430/ 11-Dec-2009
               08030582333- 08054533361-08020900001            


[1] Idan na ce magabata na qwarai ina nufin sahabban Annabi sallallahu alayhi wa alihi wa sallam, da tabi’ai, da masu bin ma su, da kuma dukkanin malaman fiqihu baki xayansu.
[2] suratul Tauba aya ta 36:
[3] Suratul  Tauba aya ta 36.
[4] Ba a yin yaqi acikin waxannan watanin  guda huxun tun zamani Jahilyya kuma   da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wasallam ya zo Allah ya tabbatar da wannan hukuncin na hana yaqi a cikin su sai dai in Kafirai suka yaqe mu acikin su babu laifi muma mu yaqe su muyi masu biji-biji, haka Allah ya ce a cikin Baqara.
[5] Bukhari da Muslim, ba a yin yaqi a cikin waxannan watannin. Abin da yasa ake danganta watan Ranar da Qibilar Mudar shine saboda suna girmama watan tun Jahiliyya basa yaqi acikinsa da Musulinci ya zo sai ya tabbatar da hana yaqi acikin watan, duba FathulBari ibn Hajar ya yi bayani mai daxi mai gamsarwa.
[6] Ma sahha wa ma lam yasihhu Min Siyami Tasu’a wa Ashura 2-3 na Abi Anas Maajadil Islamil al-Bankani.
[7] Nisa,i aya ta 150
[8] Nisa,i aya ta 150 mai karatu ya nemi littafin  Sheikh Mustafa Saba’i  mai suna ‘’Assunnatu wa makanatuha Fittashri’ilIslamiy’’ zai ga hujjojin da ke nuna duk wanda ya ce bai yarda da Hadisi ba ya bar Musulunci, Allah ya kyauta.
[9] Littafina mai bayani kan ‘Yan Qala-qato ya kusa fitowa bayanin su yana ciki ‘yan uwa su yi ta addu’ar Allah ya fito da shi. Amma cikin abin da ya zo a Qur’ani wanda bayaninsa na cikin hadisi, ga tsakure daga cikinsu: Maganar watanni ta zo a cikin Qur’ani amma sunayensu na cikin hadisi, Sallah a Larabci tana nufin addu’a amma a shar’ance ita ce wadda muke yin karatun Qur’ani da ruku’u da sujada da yawan raka’o’i wannan duk sai a Hadisi zaka sami yawan raka’o’i, haka lokutan sallah sai a hadisi, me ke vata sallah sai a hadisi, Qur’ani bai ce tusa tana  karya sallah ba hadisi ne ya yi bayani. Allah ya ambaci kiran sallah a Qur’ani amma yadda sigarsa take sai ka koma ma hadisi, Allah ya ambaci sallati, amma sigar  salati sai ka koma ma hadisi, Allah ya  ambaci Azumi amma bai faxi kwana nawa za a yi ba, haka nan ma bai faxi abubuwan da ke vata azumi ba, Allah ya ambaci aikin Hajji amma bai faxi watan  da ake yi ba, Allah  Ya ambaci wanda ya yi sata a yanke hannunsa amma bai ce ga iya inda za a yanke ba hadisi ne ya yi bayani inda za a yanke, da yawan abin da in aka sata za a yanke  hannunsa, haka bayanin zakka shi ma hadisi ne ya bayyana qimar zakka da adadin abin da za a bayar, qur’ani bai faxi yadda za ai ma gawa ba hadisi ne ya yi bayanin yadda ake ma  gawar mutum  idan ya rasu. Abubuwan suna da yawa, gaskiyar labari dai dole ne yarda da hadisi, muna addu’a Allah ya shiryi masu cewa ba ruwansu da Hadisi, waxannan misalai kawai sun ishe su hujja balle ma abubuwan suna da yawa. Haka duk wanda ya ce bai yarda da hadisi ba ya bar musulunci, Allah ya shirye su amin.
[10]  Encarta Encyclopaedia
[11] Majmu’ul Fatawa 25.
[12] Sunan wal mubdaia 94
[13] Majmu’ul Fatawa 25/308.
[14] Suratu Shura Aya ta 23.
[15] suratu Shura Aya ta 23.
[16] Muslim
[17] suratul Ahzab aya ta 31-33.
[18] Nana Khadijatu: Ita ce Khadijatu  binti Khuwailid,it ace farkon wadda ta musulinta, matarsa ta farko  ta auri manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam tana da shekara 28 shi kuma  manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yana da shekara 25. Sun zauna tare da manzon Allah tsawon shekara 25 ita kaxai, kuma ba ta tava sava masa ba har ta bar duniya (Ka ji matayen qwarai). Bai mata kishiya ba har ta rasu, ita ce ta haifar masa ‘ya’yansa gaba xaya banda Ibrahim. Nana Khadijah har ta bar duniya bai mata kishiya ba, ta rasu tana da shekara 50, wannan shi ne gaskiyar labari, riwayar Abu Ishaq ita ce kuma Imamuz Zahabi ya tabbatar, haka shima Hakim ya kawo ruwaya ingantatta da ta nuna ya aure ta tana da shekara 28 ba 45 duba Mustadarak na Hakim. Amma maganar cewa ta aure shi tana da sheka 45 ruwayar Waqidi ce, ba gaskiya ba ce, domin malaman hadisi sun yi ittifaqi a kan cewa Waqidi tataccen maqaryaci ne. Ta ba musulunci gudunmawa mai yawa wadda duniya ba za ta tava mantawa  da  ita ba.  Manzon manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya qaunace ta matuqa yana da dangantaka da ita ta kakanta Kusel ya yi baqin ciki matuqa ranar da ta rasu, ta rasu ranar Asabar 10 ga watan Ramadan shekara ta 10 kafin hijira bayan fita daga qangin kafirai da kwana 18, an rufeta a Hajun lokacin ba a wajabta sallah ba, balle ta janaza.
[19] Nana Sauda binti Zam’ah: Ita ce amaryarsa ta farko bayan rasuwar Nana Khadijah. Ta zauna tare da shi tsawon shekara 3 bai yi  ma ta kishiya ba. Ya aure ta a matsayin dattijuwa. Yana daga cikin karamcin ta, ta yafe kwananta ta bar wa Nana A’ishatu, dama kuma ta kwana biyu, sai ta bar wa A’ishatu Allah ya qara mata yarda. Ta rasu zamanin khalifancin sahabi Umar.
[20] Nana A’ishatu: An haife ta shekara ta tabiyar (5) ko huxu (4) bayan manzanci, ta auri manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam a cikin watan Shawwal shekara ta tara, tana da shekara 6 da haihuwa. Ita kaxai ce manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya aura tana budurwa ‘yar shekara shida kuma ita ce wadda ya fi so daga cikin matansa. An tambaye shi wa ka fi so?  Sai ya ce, “Nana A’ishatu a cikin maza kuma babanta Abubakar Siddiq”. Mala’ika Jibril ya zo ma sa yana barci da wani qwanso na Hariri a cikinsa ne Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ga Nana A’ishatu, sai Mala’ika Jibrilu ya ce “wannan matarka ce duniya da lahira”. Ta bada gudummawa wajen yaxa ilimi na tsawon shekara hamsin bayan rasuwar Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Ya aure ta tana da shekara shida, ya tara da ita tana da shekara tara (9).Kana kuma ya rasu ya bar ta tana da shekara goma sha takwas 18 (savanin matayen yanzu sukan wuce shekara 18 ba su yi aure ba, sun faxa tarkon Yahudawa, Allah Ya kyauta.)  a shekara ta58 bayan hijira Sahabi AbuHurairah Allah ya qara masa yarda,  shi ya yi mata sallar Janaza, shima kuma a wannan shekarar ya  rasu Allah ya qara rahamarsa a gare su baki xaya.
 [21] Hafsatu binti Umar alFaruq:  ta auri manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  a shekara ta 3 bayan hijira. Ita ma Allah ya ce a gaya ma Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam cewa ita ma matarsa ce duniya da lahira. Ita ce abokiyar takarar Nana A’ishatu. Ta kasance mai yawan azumi ce kuma mai yawan Sallar dare ce, mace ce mai qarfin hali da juriya. Ta rasu shekara ta Arbain da xaya (41) bayan hijira zamanin kalifancin sarkin Musulinci Muawiyya ta rasu a garin Madina,Gwabna Marwan  ya yi mata sallar janaza aka rufeta a maqabartan Baqia.

[22] Zainab binti Jahash: Ta auri manzon Allah a shekara ta uku ko biyar bayan hijira, sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Allah ne ya xaura aurenta daga saman bakwai wannan daraja ce Allah ya bata. Ta kasance mace ce mai saurin fushi da kuma saurin hucewa (yafewa), kuma ta fi duk  sauran ‘yan uwanta qasqantar da kai ga Allah da yawan ba da sadaka da gaskiya kuma mace ce mai tsabata ta sanadiyarta ne Allah Ya saukar da ayar hijabi. Ita tana xaya daga cikin masu takara da Nana A’ishatu wajen nuna qauna ga Annabi, Sallal Layhi wa alihi wa sallam. Ta rasu shekara ta ashirin bayan hijira a garin Madina Sahabi Umar ne ya yi mata sallar Janaza.

[23] Hindatu binti Abiy Umayyah (UmmuSalma): Baquraishiya ce  kuma dattijuwa ce.  Yana daga cikin darajarta cewa ta tava ganin mala’ika Jibrilu tare da manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam suna tattaunawa, shi kuma yana cikin siffar wani Sahabi kyakyawa Dahiyatul Kalbi. Ita ce ta ba da shawara lokacin yaqin Hudaibiyyah kuma Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi amfani da shawararta aka kuma ci nasara ta sanadiyar wannan shawarar ta.Ta kasance mace ce mai kaifin hankali.
[24] Juwairatu binti Haris alKhuza’iyyatu: Ta auri manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam shekara ta biyar ko ta shida bayan hijira bayan yaqin da Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi mai suna Yaqin Muraisi’u. Ta sanadiyarta ne musulmai suka ‘yanta bayi xari daga qabilar ta wato Banul Musxalaq, ta sanadiyar haka su kuma qabilar ta suka musulunta baki xayansu. Ta rasu shekara ta hamsin (50) bayan hijira.
[25] Safiyatu binti Huyiy bin Akhdab: Annabi sallallahu alayhi wa’alihi wasallam ya aure ta a shekara ta shida bayan Hijira bayan yaqin Khaybar .‘Yar uwar Annabi Harun bn Imran xan uwan Annabi Musa (AS) ce. Mace ce kyakkyawa matsakaiciya mai haquri kuma  ta iya girki kuma ta iya kwalliya da tarairayan Manzon Allah sallallahu alayhi wa,ali wasallam. Mace ce jaruma ta bada mamaki matuqa lokacin yaqin Gwalalo, ita ce ta kashe wani mugun Bayahude ya yin da ya yi qoqarin shigowa cikin mata. Allah Ye mata cikawa a shekara ta sabain (70)bayan hijira tana da shekara sabain da xauriya (70) Allah ya qara tsira a gareta
[26] Ramlatu binti AbiSufyan (Ummu Habibatu): Ta auri manzon Allah sallallahu alayhi wa’alihi wasallam bayan mijinta ya rasu a Habasha.  Ya mutu yana musulmi shi mijin nata na farko. ‘Yar sarkin Makka ce. Da ita aka yi hijirar farko zuwa Habasha, ta kasance mai girmama mijinta Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wasallam mai tsantseni mai gudun duniya. Ta tava hana babanta zama kan tabarmanta saboda lokacin bai musulinta ba dole ya zauna a qasa. Ta rasu shekara ta arbain da huxu bayan hijira zamanin khalifancin Muawiyya.
[27]Maimunatu binti Haris alHilaliyyah: Asalin sunanta ‘’Barratu’’ Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya canza mata suna ya sanya mata  Maimunatu. Manzon Allah sallahu alayhi wa alihi wasallam ya aureta a shekara ta bakwai bayan hijra, Nana Ai’shatu ta ce duk ta fi su taqawa da kuma sadar da zumunci. Ta rasu bayan ta gama aikin hajjinta, an rufe ta  a Sarif  a wurin da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi angunci da ita daren farkon  na aurenta da Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam. Amincin Allah ya tabbata a gareta.
[28] Zainab binti Khuzaimah:  Allah sarki! Wannan baiwar Allah Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya aureta bayan wata uku ko biyu Allah yayi mata rasuwa. Allahu Akbar! Ana yi mata alkunya da Uwar marayu sabo da yawan kyautanta da sadakanta mace ce mai kyauta ba marowaciya ba ce, Allah ya qara mata yarda amin.
[29] Mariyatu alKibdiyatu (Ummu Ibrahim): ‘Yar kabilar Kibxu ce, qabilar da ke Misrah. Ta kasance kuyanga ce aka ba manzo Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wasallam ita da ‘yar uwanta a matasyin kyautan bayi.  Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya bayar da kyautar ‘yar uwanta ga Has-saan bin Thabit. Ita kuma ya mayar da ita saxakansa har ta haifar ma sa Ibrahim, sanadiyar haihuwarta ne ya ce xanki yasa kin zama ‘yantacciya. Nana A’isha ta kasace tana kishi da ita saboda ta kasance kyakkyawa  ce. Ta rasu bayan mutuwar Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wasallam da shekara biyu.
[30] Ya Allah kai daxin aminci ga matayen Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam.
[31] Abdullahi: Ana masa laqabi da Xahir da Xayib abin da yasa ake masa laqabi da Xahir da Xayib saboda an haife shi cikin musulinci, ya rasu yana yaro xan qanqani.
[32] Qasim:  Wannan xa na manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasalam da shi ake masa alkunya (AbulQasim) an haife shi kafin manzanci ya kuma rasu kafin manzanci yana yaro.
[33] Ibrahim Mu’azzam: An haife shi a madina ya rayu shekara biyu babu wata biyu ya rasu kafin rasuwar Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam da wata uku, ranar da ya rasu rana tayi kusufi, Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya tashi ya yi huxuba mai tsanani domin kada mutane su xauka rana ta yi kusufi ne saboda mutuwar xansa. Ibrahim Mu’azzam ba Nana Khadija bace ta haife shi, Nana Mariyatu Kibxiya ce mahaifiyarsa.
[34] Zainab: Ita ce babba acikin ‘ya’yansa an haifeta shekara goma kafin Annabta xan innanta ya aure ta (Haulatu bintu Kuwailidu) sunan mijinta Abu Asim ta rasu a Madina shekara takwas bayan hijara.mijinta ya rasu zamanin kalifanci Sahabi Umar.
      Ruqayyatu: Ta auri Usman ibn Affan Khalifa na uku, ta haifan masa xa AbdulLahi wanda ya rasu yana da shekara biyar ko huxu. Ruqayyatu ta rasu bayan yaqin Badar da kwana  uku.
[36] UmmuKulsum: Ita ma bayan rasuwar ‘yanta Nana Ruqayyatu sai ta auri mijin ‘yanta wato sahabi Usman ibn Affan ta rasu a wurin sa shekara ta uku bayan hijira, ba ta haihu da shi ba.Saboda auran ‘ya’yan manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam guda biyu yasa ake ma sahabi Usman laqabi da Zunnurain, amincin Allah ya qara tabbata a gare su baki xaya.
[37] Fatimatu Zahara: Mace ce wadda take duniyar kallo ce a wajen kyau, saboda Allah ya yi mata tsananin kyau. Ta yi kama da Manzon Allah sallahu alayhi wa alihi wasallam kama  ta qarshe da ka ganta kaga Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam, tafiyarta irin na Annabi ta auri sahabi Aliyu ta haifan masa ‘ya’ya guda biyar  Hassan da Hussain da Zainab da UmmuKulsum da Muhusin, Muhusin ya rasu yana qarami.Zainab ta auri AbdulLahi xan Jaafar wan sahabi Aliyu, ita kuma UmmuKulsum ta auri sahabi Umar bn Kattab kalifa na biyu. Ta rasu bayan mutuwar babanta da wata goma sha shida, shekara ta sha xaya bayan hijira ranar talata uku ga watan Ramadan. Nana Fatimatu ita ce shugaban mata agidan aljanna.
[38]Hassan ibn Aliyu ibn Abi Xalib: mahaifiyarsa ita ce Nana FatimatuzZahara ‘yar Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam an haife shi a Madina 15 ga watan Ramadana shekara ta uku bayan hijira, Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ne ya raxa masa suna Hassan ya kuma yanka masa rago da hannunsa, Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam yabar duniya sahabi Hassan na da sheka goma. Sahabi Hassan kyakkyawa ne matuqa ya yi kama da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam daga fuska zuwa cibiya, yana da fara’a sosai ga haquri da kwarjini, kuma mutum ne mai kyauta. Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam yana tsananin sonsa sosai har yana yin masa kirari da shugaba yana cewa “Wannan xan nawa shugaba ne zai sasanta tsakanin jama’ar musulmai. Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya ce shi ne shugaban matasa a Aljannah yana da hangen nisa da kaifin tunani, lokacin da babansa sahabi Aliyu ya yi niyyar zuwa Kufa sahabi Hassan ya hana shi zuwa ya ce “ina mai baka shawa baba kar kaje. Shine kalifa na biyar bayan mutuwar Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya zama kalifa ne bayan mutuwar babansa, kuma da kansa ya sauka ya ba sahabi Muawiyya  shugabanci domin maslaha.Ya rasu shekara ta arba’in da biyu 42 bayan hijira sakamakon guba da ya ci a abinci, ana zargin  tsohuwar matarsa ce tasa masa guban. Kafin ya rasu ya roqi Nana Aishatu da tayi  masa alfarma a rufe shi a xakinta kusa da kakansa Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam Nana Aishatu ta yarda a rufe shi kusa da kakansa, amma Marwan ya hana a rufe shi kusa da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam sai aka kai shi maqabartan baqia.
[39]Sahabi Hussaini an haife shi shekara xaya bayan haihuwar wansa Hassan, shima ya yi kama da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam daga cibiya zuwa qasa, shima Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ne ya sanya masa suna Hussaini. Lokacin da ‘yan tawaye suke qoqarin kashe sahabi Usman bn Affan sayidina Aliyu ya tura Hassan da Hussaini su je suyi gadin gida khalifa Usman bn Affan. Ya yi shada 10 ga watan Muharram a Karbala sakamakon wasiqu da ‘yanShia suka aiko masa ya zo za su yi mashi mubaya’a da ya zo sai ya gane yaudaran sa suka yi, bai ga kowa ba sai rundinar UbaidulLahi ibn Ziyad,ranar 9 gawatan Muharram  sahabi Hussaini ya ce ma jama’arsa gobe akwai yaqi tsakani na da gwabnan Kufa duk mai son komawa gida ya bi dare ya tafi, rundunar gwabnan Kufa su 4000 shi ko sahabi Hussaini ‘yan rikiyarsa 72, gari na waye wa sai yaqi ya varke, aka fafata aka fafutuka sahabi Hussaini ya nuna shima barde ne domin ya kashe jama’a masu yawa kafin yayi shahada. Ga sunayen waxanda suka kashe sahabi Hussaini (1) Zur’atut Tamimi ya fara saransa a kafaxa daga nan sai (2) Sinanu xan Annas ya soke shi da mashi a maqogwaronsa ya kuma qara cakansa da mashin a qirginsa (3) kafin Sahabi Hussaini ya kai qasa sai Khuli al-Asbahi ya sa takobi ya sare kan sahabi Hussaini.( Ya Allah kar kai rahama ga waxannan mutanan da suka kashe sahabi Hussaini Ya Allah ka tabbatar da la’antarKa ga waxan da suka kashe Hussaini) kafin a kashe sahabi Hussaini ya nuna jarunta matuqa. Wannan  yaqin ya faru ne bayan mutuwar sahabi Muawiyya da shekara biyu shi kuma Yazidu xan sahabi Muawiyya yana Sham. Bayan sun sare kansa sai suka xauki kan sahabi Hussaini suka tafi da shi Sham daga baya aka kai kan Sahabi Hussaini Madina aka rufe shi bayan kusan sati da faruwan yaqin. Ya Allah ka qara aminci ga jikan Annabinka ya Allah Ka qara xaukaka darajansa amin. Ibn Taymiyyah ya yi mummunar addua ga waxanda suka kashe sahabi Aliyu da xansa sahabi Hussain duba Minhajuj Sunnah na bn Taymiyyah.
[40] Wannan ya nuna mana a fili cewa sahabi Aliyu da sahabi Umar babu tirjiya tsakaninsu domin ga shi har sahabi Aliyu ya aurar da ‘yarsa Ummu Khulsum ‘yar Fatimatu jikar Mazon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wasallam ga abokinsa Khalifa Umar Allah Ya qara ma su yarda baki xayansu, har kuma  ta haifar masa yara guda biyu Zaidu da Ruqayyah,suma Ahlul Baiti ne kuma  ta kasance matarsa har lokacin da aka kashe shi kisan gilla yana sallah a masallaci da subahi.
[41] Sahabi Aliyu ibn Abi Xalib: An haife shi shekara ta 13 kafin annabta, Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya girme shi da shekara 30.shi ne farkon wanda ya fara musulinta a cikin yara, shi ne mijin Nana FatimatuzZahara, barde ne jarumi bai da tsoro bai tava gaba da kafiri ba face ya kashe shi, ya je yaqin Badar, shine wanda ya kashe babban kafirin nan Walid xan Utbah a yaqin Badar, a yaqin Gwalalo shine ya yi fito na fito da Amru bn Wuddu wanda barada ke tsoronsa ya kuma kashe shi nan take, shine ya jagoranci yaqin Kaibar kuma aka ci nasara da sauran yaqoqin da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya je,  yaqin Tabuka ne kawai bai je ba shima an bar shi  ne a gida  ya kula da iyalan Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam, yana xaya daga cikin waxanda akai musu bushara da Aljannah tun a duniya. Kalifa na huxu bayan rasuwar Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam, ya tava hawa raqumin Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam tun daga Madina har Makka shi kaxai, Manzon sallalLahu alayhi wa alihi wasallam yana masa alkunya da AbutTurab ya ce ba suna da yake so kamar AbutTurab.  Mutun ne mai yawan ibada da sallar dare ga yawan zikiri kuma Allah ya bashi zaka’i da yawan ilimi da hangen nisa.Ya yi shahada ranar Juma’a 17 ga watan Ramadana  shekara ta 40 bayan hijira yana cikin masallaci yana zikiri wani mugu Tsinanne azzalumi, la’ananne mai suna  AbdurRahaman ibn Muljam al-Kharij ya caka masa wuqa a maxigarsa (tsakiyar kansa) sai da wuqar ta nutse gaba xayanta a kansa. Sahabi Aliyu ya yi nadamar zuwansa Kufa har yake cewa inama da na anshi shawaran xana Hassan da ya ce kar in zo. Ya Allah kai daxin aminci ga sahabi Aliyu, Ka tabbatar da azabar Ka ga wanda  ya kashe sahabi Aliyu.
[42] sahih Muslim. Sahabi Hamza: Allah Akbar Hamza shine xan AbdulMuxallibu xan Hashim xan AbdulManafi shugaban barada zakin Allah shugaban shahidai baffan AnnabisallalLahu alayhi wa alihi wasallam an shayar da su tare. Musuluntarsa ya sa musulmai sun sami kariya da xaukaka, ya musulunta shekara ta shida bayan Annabta, wato bayan Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya shiga gidan Arqam xan Abi Arqam. Ranar yaqin Uhudu da takbba biyu yake yaqi yana saran Arna a gaban Annabi  sallalLahu alayhi wa alihi wasallam yana cewa nine “zakin Allah” ya rasu ranar yaqin Uhudu, Wahashiyu ne ya kashe shi, amma daga baya wahashiyu ya musulunta kuma ya kyautata musulincinsa har ya yi shada aqarshen rayuwarsa.Lokacin shugabancin sahabi Mu’awiyya ya sa  a yi hanyar ruwa ta hanyar Uhudu da aka zo gina wajen qabarin Hamza an taras da shi lafiyar sa lau cikin kama kyakkyawa Allah Akbar, bayan shekaru fiye da Hamsin amma yana cikin kamarsa ya Allah kai daxin aminci ga zakin Allah ya Allah Ka qarama sa karama.
[43] Ibn Qaym ya yi bayani gamsasshe akan  ingantattun salatai  ga Annabi  sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam  acikin littafinsa Jila’ul Afham fis salati wassalami ala kharil Aanam da kuma Siffatu Salatin Nabiy na babban malamin hadisi Allah ya ji qansa  Sheikh Muhammad Nasiruddenil Albani.
[44] A wani qauyen har ginsami suke yi suna yanka shanu wasu matayen ma a qauye har yaji suke yi in ba a yanka mata kaza ba a ranar cika–ciki.  Wannan duk bidi’a ne kuma koyi ne da maqiya Ahlul Baiti, Nawasiba, abin da yake daidai yin Azumi a wannan ranar ba cika-ciki ba. Allah ya shiryi masu yin cika- ciki su gane cewa cika- ciki bidi’a ce.
[45] Majmu’ul Fatawa  25/308).
[46] Ma sahha wa ma lam yasihu Min YaumulAshura wa Tasua 10-17.
[47] muslim
[48]  Koda yaushe shi Ahlussunnah yana yalwata ma iyalinsa suna shagalinsu, su sha raga-dada da tagomashi, musulunci ya koyar  da mu koda yaushe ka ba iyalinka abincin da zai ishesu, shari,a ma ta yarda matarka ta xauki abincin da zai isheta  ta ci in ba ka ba ta abin da zai ishe ta ba,  kuma manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ma ya ce ya isa zunubi mutum ya quntata wa wanda yake dole ne ciyar da shi, akwai wasu azzaluman magidanta masu zuwa waje su ci tsire da shayi su bar iyali. da lami, mai yin haka yaji tsoron Allah,ya riqa ciyar da iyalinsa abinci mai daxi domin haka shara,a ta ce. Indama ba ta samu ba sai ayi haquri.
[49] Firaq Shi’a 23-44 da Maqalatu Shi’a 2 da Tarikhul maqal fi ilmi Rijal 2/174-183
[50] Duk wanda  ya ce Nana A’ishatu ta yi zina, to wannan ya qaryata  Qur’ani kuma ya na tuhumar Allah ne, domin Allah ya tsarkake ta a cikin Suratun Nur, mai cewa tayi zina ya bar musulinci. Amma  su ‘YanShi’a  la’antar  Nana A’ishatu a wajen su  addini ne, Allah ya shirye su amin.
[51] Wannan musibar ta shiga cikin makarantun gaba da sakandire yadda za ka ga mata suna yin wannan xanyen hukunci na Mutua, yaxuwar Mutu’a ya faru ne ta sanadiyar tsadar  da aure ya ke yi da kuma qin ma mata aure a ce ana jira sai ta gama makaranta, kuma ga shi sun balaga. Iyaye su kula in ko ba haka ba za su ga yaransu mata da cikin xan Shia ya yi Zina da ita da sunan Mutu’a, kuma ai ma yara aure da wuri shine tsira masamman mata.
[52] Hukumatul Isalamiyyah na Ayatul Lahi Khomen 52 da Manshurat 41 da www.khomeni.com
[53] Hukumatul Isalamiyyah na Ayatul Lahi Khomen 52 da Manshurat 41 da www.khomeni.com
[54] Amma abin ban mamaki ‘YanShi’a basa baqin ciki sauran yaran, sai sahabi Hussaini kawai, Allah sarki mai karatu  za ka qara fahitar cewa tsakanin sahabi Aliyu da sauranan sahabai duk xaya ne, tun da ga shi har yasa sunanayen  sahabai Abubakar da Umar da Usman, kuma tarihi ya tabbatar da cewa su ‘yan Shia da kansu su ka kashe sahabi Hussain duba littafin Shi’a Muntahal A’amal1-450 da I’ilamul wara na Xabaris 203 da Maqtalu Hussain 147da Ma’alimi Madaratina 62  kitabulRaudha na ‘yanShia dukkanin waxannan littafan na masu bi addini Shia ne da kansu su ka faxa cewa 'Yan Shia ne su kashe Hussain bayan sun aika ma shi da wasiqu ya zo suyi masa mubaya’a,  amma kuma suke baqin ciki na yaudara Allah, ya shirye su amin.
[55] majmiol Fatawa 25/165-166.
[56] Critical Revision of Shi’a shafi na 123-130 na  Professor Imam Musa Musawi.
[57] Nemi kaset din janazar da suka yi a Zariya zaka ga ban mamaki da jahilci da kuma kwaikwayon Kiristoci da xaukan gawa ana buga Badujala da ganga da saka gawa a akwati da sanya hure yadda de Arna suke yi Allah ya shiryi masu bin addinin Shia su gane Shia ba addini ba ne.
[58] AhlulsSunnah suna da siffofi ga siffofin na su kamar haka:(1) Tsaka-tsaki a aqida da Ibada da gudun duniya (2) Taqaituwa ga Qur’ani da Sunnah (3) Rashin ta’assubanci ga shugaba ko tsari (4) Girmama magabata na qarai (salaf) (5) Rashin dangantuwa ga wani abu, face Musulinci (6) Qwaxayin yaxa sahihiyar aqida (7) Rashin husuma (8) Son juna da qaunan juna (9) Rufa ma juna asiri (10) Biyayya ga shugaba. Ginin AhlusSunnah (1)Tsantsar tauhidi (2) Tsantsar biyayya ga manzon Allah sallalLahu alay wa alihi wasallam da riqo da Alqur’ani da sunnah bisa fahintar magabata (3) Barin bidia da nesantarta (4) Neman ilimi mai amfani da aiki da karanta da shi (5) Attasfiyah wat-tarbiyah (6) watsi da qungiyanci da ta’assubanci ga mazahaba (7) bayyanar da sharri da ke cikin dokokin da suka sava ma qur’ani da hadisi (8) kira zuwa ga jihadi.  AhlusSunnah na da sunaye ga Sunayen AhlusSunnah: (1) ‘Yan salafiyyah (2) Ahlul hadisi (3) Ahlul athar (4) Firqatun naajiyah (5) Ahlul ittiba (6) Xa’ifatul mansurah
[59] Muslim.
[60] Zadul mustaqani.
[61] Nasa,i
[62] Muslim 1162
[63] Sahihu Tirmizi
[64] Majmuol Fatawa 25/310-311
[65] Fathul Bari 4/291
[66]  Muslim 1134
[67] Fathul Bari 4/291
[68]  Sharhu muslim 4/267-268
[69]  Majmuol Fatawa 25/312
[70]Sharhu Muntani’I 6/471-469
[71] Irwa’ul ghalil 4/111
[72] Haka bikin samun ‘yanci kai a Najeriya (Independace Day) da ake yi duk xaya ga watan October na ko wace shekara, wannan bikin a shariar musulinci bai halasta musulmi ya yi ba. Bikin samun ‘yanci Najeriya ba musulinci ba ne koyi ne da Kafirai ya zama dole musulmi ya kiyaye ya kuma qaurace ma wannan tunvelen.

[73] Kamar yadda zaka ga musulmi ya sayi Greeting card  ya ba budurwansa wannan abin ban mamaki ne da dariya  musulmi ya sayi greeting card  wanda ya san asalinsa daga Kiristoci ya ke Allah ya kyauta.
[74] Shi ne yaran musulmai suke yin nock out  yadda Kiristoci suke yi in Kirsimeti yazo ko sabuwar shekara ta shiga(January)  buga Nock out, wannan Nock out asalinsa daga Arna yake don haka iyaye su hana yaransu buga Nock out domin haramun ne.
[75] Majmuol Fatawa  923/59
[76] Ahkamu AhlilZimmah 144-244
[77] Allami’u fil hawadis wal bidi’u 1/492 wannan ayar ta isa dalili akan musulmi kar ya zave Kafirine a matsayin shugabansa,’yan siyasa su kulla da wannan ayar dakyau.
[78] FathulBari 2/315
[79] Iqtida u Siradil Mustaqim 2/425 da Ahkamu Ahli Zimma na ibn Qaym 227-527/2
[80] Allami’u fil hawadis wal bidi’u 1/492 da Iqtida u Siradil Mustaqim 2/625 wannan ya haxa da motar da aka tanaza don kai Arna garinsu su yi Kirsimeti kai musulmi bai halasta ka hau ba balle ka tuqa su kai a matsayinka na direba.
[81] Majmuol Fatawa li Usaymin 3/44 da Lajnatul Da’ima 3/435
[82] Ahkamul Qur’an na Alqadhi Abukar ibn Arabiy alAndalusiy alMaliki suratul Ma’idah
[83] Lajnatul Da’ima 398/22 da Majmuol Fatawa Usaymin 105/3 da Iqtida u Siradil Mustaqim da Naha ahlil Islam an Tahniatu Kuffari bia’ayadihim 3-19
[84] The Story of Civilization by Will Durant, 15/23
[85] www.Catholic forum.com
[86]  Amma ya halasta sanya kaya mai ratsin ja kamar yadda ya zo cikin Bukhari Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya sanya kaya mai ratsin ja. Amma jan kaya haramun ne kayan kafirai ne, ya kamata duk musulmin kirki ya nisanci jan kaya. Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya tava umurtan wani sahabinsa ya je ya qona jan kayan da ya sanya ya ce ma shi wannan kayan   Arna ne.
[87] www.qa.com da  Fatwa na Shaykh Muhammad ibn Saalih al-‘Uthaymeen
[88] Akwai bikin Ranar Dariya ta duniya wannan bikin a qasar Indiya ake yin sa duk xan wannan qungiyar zai zo qasar Indiya su haxu su yi ta dariya na awa ashirin da huxu, wai suma rana ce ta masu dariya har suna cewa dariya tana maganin cututtuka masu yawa don haka ya sa suke dariya, Allah ya tsare musulmi da wannan tunvelen da wannan haukan, yawan dariya yana da illa a musulinci.