Wednesday, November 27, 2013

HUKUNCE HUKUNCIN JANAZA A MUSULINCI



GABATARWA
بـسـم اللـه الـرحـمـن الـرحـيـم
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره  ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادى له، وأشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله.     أما بعد: فإن خير الحديث كتاب الله، وخير الهدي هدي محمد، وشر الأمور محدثاتها، وكل محدثة بدعة، وكل بدعة ضلالة، وكل ضلالة في النار أما بعد:
Ina godiya ga Allah da ya bani ikon rubuta wannan littafi taqaitacce wanda yake magana akan hukunce hukunce janaza wanda ya shafi tun daga rashin lafiya jinya zuwa qabari.
 Wannan littafi ya zo ne sakamakon shawarar da Malamina  Malam Ahmad Bello Dogarawa ya bani na in rubuta littafin da yake bayani akan yadda shara’a ta koyar  da mu game da Janaza, ya bani wannan shawarar ne bayan munta shi karatu ya xauko ni a motarsa ya kawo ni inda zan shiga mota in dawo gida, bayan na dawo gida naba Allah zavi akan shawar da ya bani sai na same natsuwa akan rubuta wannan littafi taqaitatce akan hukunce-hukuncen janaza daga Qur’ani da Hadisai bisa fahintar magabata na qware. Don haka lalle malamina yana da falala mai yawa akaina Allah ya sakamasa da Aljannatil Firdausi amin.
 Gaskiya duniyar musulincin qasar Hausa ta na buqatuwa ya zuwa ga wannan littafi kusa kana iya cewa dukkan wani musulmi yana da buqatuwa ya zuwa ga wannan littafin masammam waxanda suke iya karatan Hausa domin yau an wayi gari an maida sha’ani janaza ya zama al’ada an jivinta janaza ya zuwa ga waxanda ba su san me shara’a ta ce ba, na ga mahimmanci fitar da wannan littafin cikin gaggawa saboda duka ranar da naje na halarci janaza nakan dawo gida cikin damuwa ganin yadda ake yin aiki da ka ba tare da la’akari akan me shara’a ta ce game da gawa ba.
Na fara littafin nawa tun daga rashin lafiya da neman magani da hukuncin shan magani da yadda ake jinya da ladubban zuwa ziyarar   mara lafiya da yadda ake so likita ya kula da mara lafiya da mutuwa da alamomin mutuwa da alamomin kyawawan cikawa da alamomin munanan cikawa da me ya kamata ayi ma mutum da zaran ya rasu da yadda ake wankan gawa da likafani da yadda ake sanya sa da dai sauran su za a gani insha Allah.
Kamar yadda yake al’adata ce littafina yana taqaituwa ne qarqashen Qur’ani da hadisi bisa fahintar magabata na qwarai (SalafusSalih) ina roqon duk wanda ya ga kuskure ko shawara qofa a buxe take kuma ina lale maraba da gyransa ko shawaransa
Addua wadda bata da iyaka da fatan alheri ya zuwa ga mahaifana Malam Abubakar Ibrahim da Malama Fatimatu Dalhatu Zaria Allah ya jiqansu ya sakama su da Aljannatil Firdausi amin Allah ya albarkaci zuri’ar su  ya yafe masu zunubansu amin.
Godiya zavavviya ga Malam Musa Sahabi Zaria Allah ya saka masa da alheri gaskiya yana taimaka man sosai wajen ganin naci gaba da talifi haka shima Malam Kidir Ibrahim Zaria alherin Allah ya je ya zuwa gare shi yana zaburar da ni akan cigaba da rubutu. Malam Abubakar Jumare Allah ya saka masa da Aljannah ya yi iya bakin qoqarinsa na ya duba wannan littafin amma Allah bai yarda ba saboda yanayin jikinsa Allah ya bashi sauqi amin kuma Allah ya sa kaffara ne. Babu shina yiwuwa in manta da Malamina Sheikh Muhammad Aminu Jumare Alqali Allah ya yi mai sakamako da Aljannah haka shima  Malam Haruna Ishaq Shika shima Alla ya saka masa da Aljanna amin. Allah ya jiqan Malamina Imam Malam Mika’il Isah Shika Allah ya bashi Aljannah amin.
      B azan manta da Dr Ahmad Bello Sardauna ba shugaban tsangayar qidaya da lissafin kuxi na Jami’ar Ahmad Bello Zaria (H.O.D Accounting) ya bayar da gudun muwa mai girma wajen ganin wannan littafi anfitar da shi Allah ya yi mai sakayya da gidan Aljanna shi da mahaifansa Allah ya albarkaci zuriarsa amin. Za a iya samun sauran littattafan dana rubuta a mudawwanata ta yanar giza-giza       http://harunaabubakarshika.blogspot.com ina roqon addua ta alheri ga duk wanda ya karanta littafi na nagode.
Wassalamu alaykum warahamatulLahi wa barakatuhu
25 Ramadan 429
Harun Abubakar Shika
08030582333-08054533361-   08020900001






























                                     RASHIN LAFIYA (CIWO)
Ciwo daga Allah ya ke babu bb  wanda ya fi qarfin Allah ya jarrabe shi da ciwo ko wane iri ne, in muka bibiyi tarihi za mu ga  bayin Allah da dama sun yi  fama da rashin lafiya ba don kome ba sai dai don Allah ya xaukaka darajarsu da kuma kankare  ma su zunubansu. Gwargwadon imanin mutum gwargwadon yadda Allah zai jarraba shi.  Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya gaya mana cewa girman lada na tare da girman jarrabawar da Allah ya jarrabe ka da ita, haqiqa idan Allah ya so wasu mutane sai ya jarraba su (da wata cuta), wanda ya yarda da hukuncin Allah to yana da yarda, wanda ya yi hushi to yana da sakamakon fushinsa.[1]
Don haka ciwo ba abin zargi ba ne domin akwai wani   sakamako   wanda Allah ya ke bai wa wanda ya yi ciwo,   haka ma’aiki sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya faxa  mana a  wani hadisi da aka   samo daga Anas Allah ya qara masa yarda ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘Idan Allah ya so bawansa da alheri sai ya sa masa wata cuta (uquba) a nan duniya, amma idan Allah ya nufi bawansa da sharri sai ya qyale shi da zunubinsa har ya cika masa da shi ranar qiyama.’”[2]
Wannan magana ta manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ta nuna mana  ashe duk wanda ciwo ya same shi ya yi haquri ba kansa ne farau ba, manyan mutane su ma sun yi  ciwo na tsawon lokaci  mai tsawo, misali kamar Annabi  Ayyub da Allah ya gaya mana ya yi ciwo na tsawon lokaci wanda har ya kai na shekara 18   ba ya fita saboda ciwo, wanda har ya kai ga gaba xayan dukiyarsa ta qare ‘ya’yansa duk suka mutu baki xayansu saboda tsananin ciwo, sai da ta kai  gaba xayan jikinsa ba ya amfani sai  zuciyarsa kawai,  wasu malaman tafsirin ma cewa suka yi sai da ya kai jikinsa ya kasance yana yankewa yana faxuwa  qasa. Wata rana matarsa[3] ta ce masa ya roqi Allah ya ba shi lafiya mana, sai ya ce shekarata saba’in lafiyata lau amma in kasa haquri da rashin lafiya ta shekara sha bakwai?[4]
   الله أَكْبَرُbayin Allah ke nan shekara da shekaru suna fama da rashin lafiya amma suka yi haquri, haka aka san bayin Allah  cikin haquri ko da yaushe.[5]
Kusan idan muka bibiyi tarihi zamu ga yadda Allah Ya ke jarraba bayinsa da cututtuka ba don komai ba sai don Ya qara masu daraja da xaukaka. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa salam ya yi ciwo, haka shi ma  babban sahabinsa Abubakar  shi ma haka, haka shi ma Imam Malik ya yi rashin lafiya har ya kai ba ya zuwa masallaci sai a gidansa yake yin sallah,haka ya mutu cikin wannan rashin lafiya. AllahYa rahamshe shi amin.  Shi ma xalibinsa Imamu Shafi’i  ya yi rashin lafiyar da ta kai in ya hau doki jini na zuba a duburarsa, har  ya cika masa huffinsa (takalminsa). A qarshe dai  ina mai cewa ciwo ko rashin lafiya daga Allah ne kuma ba  abin zargi ba (ba aibu ba ne) ne domin jarrabawa ce daga Allah, kuma akwai  sakamako mai yawa  ga wanda ya yi haquri kuma ya miqa al’amarinsa ga Allah. Imam Ahmad shi ma ya yi ciwo mai tsanani har ta kai ga yana nishi da qyar, kuma a cikin wannan ciwon ya rasu Allah, Ya rahamshe shi amin. 
Ana so mara lafiya ya yi haquri da cutar da ta same shi ya miqa lamarinsa ga Allah kuma ya yi haquri, babu abu mafi tsada fiye da Allah Ya ba ka haquri, kuma Allah Ya yabi masu haquri a cikin littafinsa kuma Ya yi ma su bushara da lada mai yawa kuma Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya faxi irin falalar haquri,  shi mumini duk abin da ya same shi lada ne.
 Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya  ce, “Abin sha’awa ga al’amarin mumini komai nashi lada ne. Idan abin farin ciki ya same shi ya gode wa Allah alkhairi ne a gare shi, in kuma abin baqin ciki ko damuwa ya same shi ko ciwo ne ya yi haquri alkhairi ne a gare shi.”[6]
Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce wanda Allah ya nufe shi da alkhairi sai ya sanya ma shi wata cuta.[7]  Babu wata damuwa ko baqin ciki ko ciwo ko wani abu mai cuta da zai sami mumini face lada ne a gare shi. Har qaya idan ya taka face Allah Ya kankare masa kurakuransa.[8]
Ibn Mas’ud ya shiga wajen Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya taras da shi yana zazzavi, sai ya ce ma shi, “ Ashe  kai ma kana zazzavi  zazzavi mai tsanani haka?” Sai Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Haka ne abin yake, ni  ciwon mutane biyu nake yi.” Sai Ibn Mas’ud ya ce, “Kana nufin kana da lada biyu ke nan?” Sai Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Na’am.”  Sannan  sai ya ce, “Babu wani ciwo ko qaya da zai sami musulmi face Allah ya kankare masa munanan  ayyukansa kamar yadda itaciya take kakkave ganyayen ta,[9]

           NEMAN MAGANI.
Haqiqa Allah Ya halasta shan magani ta harshen Manzon Allah Sallal Lahu alayhi  wa alihi wa sallam.  Malamai sun kasu gida biyu: Wasu na ganin  halascin shan magani,  wa su kuma suka ce rashin shan magani shi ne mafi alheri. Ga dai hujjojin masu  ganin halascin  shan magani kamar haka:

         HUJJOJIN MASU SHAN MAGANI.
Ya zo cikin musnad na Ahmad Ibn Hanbal Hadisi daga Usamatu ibn Sharik ya ce, “Na kasance wajen Manzon Allah Sallal Lahu alayhi  wa alihi wa sallam sai wani baqauye ya zo wajen Annabi Salla Llahu alayhi wa alhi  wa sallam  ya ce  wa  Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, ‘Wani mutum ne  mafi alheri,’ sai ya ce, ‘wanda ya fi su kyawawan xabi’u,’ sai ya qara tambayarsa, ‘Shin   za mu shan magani,’ sai ya ce, ‘Na,am ku yi magani ya ku bayin Allah domin Allah bai saukar da cuta ba face ya saukar da maganinta, ban da ciwon guda xaya.’ Sai  suka tambayi ciwon da ba shi da magani, sai ya ce, ‘Ciwon tsufa.”[10]  Wata ruwayar  sai ya ce, “Allah bai saukar da cuta ba face ya saukar da maganinta, wanda ya sani ya sani wanda bai sani ba bai sani ba.[11]
عن أسامة بن شريك قال: جَاءَ أَعْرَابِيٌ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم – فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ أَيُّ النَّاسِ خَيْرٌ؟ قَالَ: "أَحْسَنُهُمْ خُلُقاً". ثُمَّ قَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ أَنَتَدَاوَى؟ قَالَ: "تَدَاوَوْا؛ فَإِنَّ اللَّهَ لَمْ يُنَزِّلْ دَاءً إِلاَّ أَنْزَلَ لَهُ شِفَاءً, عَلِمَهُ مَنْ عَلِمَهُ, وَجَهِلَهُ مَنْ جَهِلَهُ". رواه أحمد
Wata ruwayar: Manzon Allah Sallal Lahu alayhi Wa alihi wa sallam cewa ya yi,  “Allah Ya halicci cuta da maganinta,  ku yi magani amma kar ku yi maganin da haramun.[12]
Cikin Tirmidhi ya ambaci    amfanin Tozalin Ismad a matsayin maganin ciwon ido.
 Wata Sahabiya Allah ya qara ma ta yarda ta ce, “Manzon Allah Sallal Lahu alaihi Wa alihi wa sallam ya ga wata yarinya a gidansa, a fuskarta akwai wata cuta sai Annabi ya ce, ‘Ku yi ma ta ruqquya tana da kambun baka.’”
 An samu wani sahabi ya faxa wa Annabi sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam cewa xan’uwansa yana ciwon ciki, Annabi sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam  ya ce ma shi   ya je a bashi zuma zai warke.[13]   
Wata ruwayar  Manzon ya ce, “Mafi alherin abin da za ku yi magani da shi, shi ne Qaho.”[14] 
Ya  tabbata cewa tokar keson tabarma tana maganin quna. 
Mun ga Masu ciwon gyambon ciki (ulsa) ya  ce su sha fitsarin raqumi.
Wata ruwayar daga Usama xan Harik ya ce, “Manzon Allah Sallal Lahu alayhi Wa alihi wa sallam ya ce Habbatus Sauda’a tana maganin komai amma ban da Rasuwa da tsufa.”[15]
 Wata rana kunama ta harbi Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  a masallaci  sai  ya ce, “Yanzun nan har Annabin Allah Kunama ba ta qyale shi ba! sai ya ce a kawo masa  ruwa. Sai  ya karanta QUL YA  AYYUHAL  KAFIRUN   ya zuba  gishiri ya zuba a qafarsa.[16]
Hadisi ya inganta daga  Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yake cewa, “Idan xayanku yana zazzavi mai tsanani, ya sanyaya shi da ruwan sanyi.”[17] Wato in kana zazzavi  matsananci sai ka yi wanka da ruwan sanyi. Za mu iya fahimtar haka a hadisin da ke  Bukhari a lokacin da ciwo ya tsananta ga manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  sai ya sa aka  zuba masa  ruwan sanyi  a kwatanniya  ya je ya yi wanka har sau biyu.[18]
 Waxannan su ne hujjojin masu ganin nema da kuma shan magani dole ne, har Ibn Qaym ya yi raddi a kan waxanda suke ganin ba za a sha magani ba a littafinsa,[19] da dai waxansu hujjojin da suke nuna halascin shan magani.
Wasu malaman na cewa rashin shan magain shi ne mafi alheri suka ce in mutum na da qarfin imani to ya qi shan  magani shi ne martaba ta qoli kuma  qin shan maganin shi ne mafifici  ga hujjojinsu kamar haka
1.       Wata rana Ibn Abbas yana zaune  sai ya ce wa xalinbansa, “Kuna so ku ga ‘yar Aljanna?”  Sai ya ce, “Wata rana  wata baqar mace ta zo wajen Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ta  ce ya Manzon Allah ina fama da ciwon farfaxiya, ka roqa min Allah in warke. Sai ya ce  “In kin so in yi ma ki addu’a ki warke, in kuma kin so ki yi haquri ki  mutu da ciwonki makomarki Aljanna. Sai ta ce a bar ta da cutarta ta  mutu ta shiga Aljanna. Amma sai ta ce wa Manzon Allah   sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi ma ta addu’a  in tana farfaxiyar ta daina yin tsirara,  sai Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya yi ma ta  addu’a ta daina yin tsirara  in ciwon ya tashi ma ta.   Don haka suka ce qarfin Imaninta ya kai na ta qi shan magani.
2.      Sahabi Amru bn Asimim ya kasance ba ya shan magani, in yana tafiya sai ya ji ana ma sa sallama sai ya tambayi Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  cewa bai san ma su yi ma shi sallama ba. A nan ne Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Mala’iku ne suke yi ma ka sallama saboda qarfin Imaninka.” Amma wata rana da ya yi rashin lafiya ya yi magani sai  mala’ikun suka daina yi masa Sallama, da kuma ya sake  daina shan maganin  sai suka dawo da yi masa Sallamar.
3.      Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ambaci wasu mutane dubu saba’in da za su shiga Aljanna babu hisabi, cikin Siffofinsu ba sa shan magani.[20]
4.      Wani sahabi an sare shi a fuskarsa  ranar uhudu har idonsa ya yi qasa zai faxi, sai ya zo wajen Annabi Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya ce a yi masa addu’a. Sai Annabi ya  ce masa  ya yi haquri da ciwonsa ya samu Aljanna,  sai  ya ce yana son Aljanna amma a yi masa addu’a domin yana neman aure.[21]
5.       Lokacin da sayyidina Abubakar Sadiq bai da lafiya an ce ma shi, “A kira ma ka likita? Sai ya ce haqiqa likita (Allah) yana ganina, ni kuma zan yi abin da yake so ne”.[22] Abubakar shi ne mafificin mutane a cikin wannan al,umma bayan Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam sannan kuma shi shugaba ne kuma  abin koyi ne. Wata ruwaya Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam   ya ce, “Likita shi ne Allah”.
Malamai dai sun haxa dalilai wuri xaya suka ce babu laifi shan magani. Shi kuma al-Usaineen ya ce akwai inda shan magani zai iya zama dole amma idan mutum yana da qarfin imanin da zai iya qin shan maganin, to ya qi shan maganin shi ya fi. Sai dai a lura cewa babu wanda ya hana shan magani, kuma ko ka sha magani kada ka xauka cewa magani ne ya warkar da kai, Allah ne ke warkarwa ba magani ba.
A mazhabar Ahmad ibn Hanbal Shan magani halas ne babu laifi in mutum ba shi da lafiya ya sha magani, amma kuma a mazahabarsa barin magani shi ne ya fi daraja kuma ya fi fifiko. Su kuma Shafi’iyya barin shan magani shi ne mafi alheri, har ma Imamun Nawawi ya ce   mazhabarsu wato Shafi’iyya  da Salaf baki xaya da Kalaf barin shan magani shi ne mafi alheri in dai mutum zai iya. Abu Hanifa shi yana ganin shan magani dole ne, amma kuma ita mazahabar Malikiyya tana ganin kana iya shan magani kana kuma iya barinsa.[23]
Shi kuwa babban Malami Ibn Taymiyyah cewa ya yi shan magani ba dole ba ne wannan ita ce maganar jumhurun jagororin malamai. Ya ce waxansu ‘yan kaxan daga yankin Hambali da Shafi’iyya ne suka wajabta shan magani.[24]

HUKUNCIN MAGANI DA ABIN DA AKA HARAMTA.
 Kamar yadda muka gani cewa Allah bai hana mu shan magani ba, to amma kuma haramun ne yin magani da duk abin da aka haramta mana. Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa  alihi wa sallam ya ce, “Kada ku fara ku yi magani da abin da aka haramta ma ku”.[25] Ka yi qiyasi a kan duk wani magani da ka san an haxa shi da abin da yake haramun, to amfani da shi haramun ne. Misali kamar giya, wiwi, kashi, mushe, jini, fitsari, da duk abin da ke sa maye ko abin da yake haramun ne babu ko shakka haramun ne amfani da shi a matsayin magani. Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam  ya ce, “Allah bai sa mana maganinmu a cikin abin da ya haramta mana ba,  kuma Allah bai sa mana waraka  a cikin abin da ya haramta ba.”[26]
Sahabi Xariq ibn Suwaydi ya tambayi manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam game da giya da suke amfani da ita a matsayin magani. Sai Annabi sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce masa giya ba magani ba ce cuta ce.[27]
 Ka na iya cewa duk maganin da yake bugarwa shi ma ya haramta a gareka.  

HUKUNCIN SHAN MAGANIN DA KAFIRI YA BA KA.
Bayan mun fahimci halascin shan magani da kuma zuwa neman sa, to yanzu abin tambaya a nan shi ne shin ya halasta shan maganin da arne ya ba ka? Sheikh Usaymin ya ce abin qyama ne kuma bai dace ba musulmi ya je wajen kafiri neman magani. Ya cigaba da cewa domin shi kafiri ba abin amincewa  ba ne, ya ce sai dai in lalura wato idan ya kasance duk gari babu asibitin musulmi ko babu kyamis xin Musulmi sai ka je wajen kafirin amana a matsayin lalura, a qarshe ya ce kafiri dai ba abin amincewa ba ne, ya qara da cewa musamman wajen haihuwa bai dace kafiri ko kafira ya ko ta  amshi haihuwar musulma ba.[28] Shi ibn Muflihi ya ce, “Taqiyudeen ya ce, ‘Idan Bayahude ko Kirista masani ne ga likitanci sosai kuma amintattace ne al’umma sun yarda da shi, to babu laifi musulmi ya je wajensa ya nemi magani tun da dai an amince masa.[29]      
Faxakarwa: Babu laifi mace ta duba namiji a matsayin lalura haka ya faru zamanin Manzon Allah salla Llahu alayhi wa aihi wa sallam lokacin yaqi mata na sanya wa sahabbai bandeji a raunukansu,  kuma ya tabbata wata Sahabiya mai suna Asshifa tana bayar da magani.  Yana da kyau mata su karanta likitanci domin taimaka wa addini domin akwai baqin ciki halin da muke ciki yadda maza arna ke duba mata musulmai, wannan abin takaici ne, ya kamata mata su share mana hawaye su yi qoqari su karanta wannan farni. 
   LADDUBAN ZIYARAR MARA LAFIYA DA ABIN  DA KE  KAN MAI JINYA  DA  LIKITA DA AN GUWAR ZOMA.
Kamar yadda muka gani a baya cewa ciwo daga Allah yake kuma ciwo kaffara ne na zunubai, kuma mun ga cewa hatta  manya-manya daga cikin  bayin Allah  sun yi ciwo.   Musulunci ya koyar da komai domin hatta yadda a ke zuwa ziyarar/gaida mara lafiya manzon sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya koyar da mu ladubban zuwa ziyarar/gaida da mara lafiya. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa aihi wa sallam ya kasance yakan je gaida mara lafiya kuma hadisi ya tabbata daga manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam da ya ke nuna mana idan mutun ba shi da lafiya yana da haqqi a kanka na ka je ka gaishe shi, muddin ba ka je ba ka tauye masa haqqinsa.[30]   Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya ce, “Ku gaishe da mara lafiya Musulmi, ku ciyar da abinci,ku ‘yanta wuyaye.” [31]
Hakqin Musulmi ga Musulmi guda shida ne: Idan ya  haxu da shi ya yi  masa Sallama, idan ya kira ka ka amsa ma shi, in ya nemi ka yi masa nasiha ka yi ma shi, in ya yi atishawa ya  kuma ce Alhamdu lil Lah, ka gasshe shi, in ya yi rashin lafiya ka je ka gasshe shi. Ya ce mai gaida Mara lafiya yana tafiya a gavar  Aljanna ne har ya je ya dawo.[32]
Ga ladubban kamar haka;
1.      NIYYA  KYAKKYAWA:
  Domin dukkan ayukka ba sa ingantuwa sai da niyya. Ana so niyyar ta zamanto kyakkyawa koda yaushe, mai zuwa ziyarar mara lafiya ana so ya yi niyyar zuwa gasshe da mara lafiya domin Allah ba wai don wani abu ba, a’a ya je ne domin samun lada wajen Allah, haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ambaci lada mai yawa ga wanda ya je gasshe da mara lafiya domin Allah.[33]

2.      NEMAN IZINI:  Ana so ka nemi izinin mara lafiyan kafin ka shiga wajensa kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhari Ibn Abbas ya nemi izinin shiga wajen Nana A’isha Allah ya qara mata yarda lokacin  da ba ta da lafiya  kafin ya shiga.[34] Kai ma ana so ka nemi izinin mara lafiya kafin ka shiga  wajensa ko da kuwa  a asibiti, yayin da Ibn Abbas ya je gaishe  da Nana A’ishatu Allah ya qara mata yarda, da ya je ya nemi izinin shiga  sai ta ce kada ya shigo, sai aka gaya mata Ibn Abbas ne fa xan baffan Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, sai ta ce kada dai ya shigo, da aka matsa mata sai ta ce, “Ina tsoron in ya shigo zai yabe ni, amma ya shigo. Da ya shigo  sai ya ce mata, “yaya jiki?”  kamar dai yadda a ka koyar da su, sai ta amsa da cewa, “Muna fatar rahamar Allah  kuma muna tsoron azabarsa.” Sai Ibn Abbas ya ce, Haba ke da kike matar Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam! Ke ce fa wadda Annabi ya fi so, kuma ke ce wadda aka saukar da aya kaza da kaza saboda ita.” Ya yi ta gaya mata kyawawan ayyukanta. sai ta ce, “Da ma abin da na ke tsoro ke nan na ce  kada ka shigo,  da ma na san sai ka yabe ni sai ka yi ma ni Kirari.”[35]     
  Shi Ibn Abbas  ya yi abin da Annabi  sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi umurni ne da a yi wa mara lafiya, ita kuma ta yi tawali’u  ne kuma da ma tawali’u  hali ne na  mutanen kirki, don haka babu kyau a rinqa tuna wa mara lafiya munanan ayyukansa, haramun ne a je ziyarar mara lafiya kana a riqa tuna masa munanan ayyukansa.
 Abdullahi ibn Umar lokacin da ya ke ciwon ajali Hajjaj ibn Yusuf As Saqafi  ya nemi izinin ya  shiga ya gasshe  shi,  sai  Abdullahi ibn Umar  ya ce a ce masa ba ya so, ya taqura sai ya shiga,  da ya shiga ya yi sallama Abdullahi bn Umar ya yi banza  da shi.[36]
 Bukhari ma ya kawo magana mai kama da wannan da ke nuna ladabin zuwa   ziyarar mara lafiya.[37] 
 Dattijon arziqi mafifici mai daraja a bayan qasa bayan manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  Abubakar Siddiq, shi ma ya nemi izinin shiga ya gasshe da Nana Fatimatu Allah ya qara ma ta yarda  lokacin da ba ta da lafiya, ya yi sallama  Sayyina Ali xan Abi Xalib Allah ya qara ma sa yarda  ya fito sai ya ce masa ya nema ma sa izinin shiga ya gasshe da Nana Fatimah,  sai Ali ya shiga ya gaya ma ta Abubakar yana neman izinin  ya shigo ya gasshe ta, sai ta ce ya shigo, shi kuma  ya shiga ya gasshe ta.
Ana so mai zuwa ziyarar  mara lafiya ya nemi izinin shiga kafin ya shiga wajen mara lafiya.
3.  Yin sallama:Yin sallama kafin shiga wajibi ne kuma haqqinsa ne.[38]
4.  Yi masa Addu’a:    Ana so in an je gasshe da mara lafiya a yi ma shi addu’a, a ce  masa Allah ya kawo  sauqi. Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya kasance in ya je gasshe da mara lafiya yakan yi ma shi Addu’a sau uku.
 5.     A yi ma shi wasiya da haquri.[39]
 6       A tsaya wajen kansa a tambayeshi ya ya halin da ya ke kuma yaya jiki?[40]
 7.   A tambaye shi me yake so ya ci? Idan har  ba zai cutar dashi ba, to sai a ba shi ya ci.[41]                                                              
 8.      A tava kansa (Goshinsa) ko hannunsa ko cikinsa sai a ce   ya ya jiki?[42]
9.    A nuna ma shi cewa wannan ciwon mai sauqi ne komai tsananinsa, kuma a nuna masa cewa zai warke in sha Allah haka Annabi Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya ke yi wa duk wanda ya je gaidawa. Yana cewa da sauqi, to kaffara ne a gare ka in sha Allah.”[43]
10. Ana so a tuna masa ayyukansa na alheri, babu kyau a tuna masa wasu munanan ayyukansa, alherinsa ake so a tuna masa, hadisi ya zo a Bukhari. 
11. Za a iya yi masa tofi a wurin ciwon nasa, domin ya tabbata Annabi Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam yana yi in ya je ziyarar mara lafiya.  Ana iya karanta wata addu’a kana a tofa masa wadda ta tabbata.
12.     Ana so a kira sunan mara lafiyan, kana a ce, “Ya Allah ka warkar da wane.” har sau uku. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam  ya je gasshe da Sa’ad lokacin yana cikin rashin lafiya, da Annabi sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya je sai ya ce, “Ya Allah ka warkar da Sa’ad.”[44] ya faxi haka har sau uku. Kai ma ana so ka kira sunansa sau uku kana ka ce Allah ya warkar da shi har sau uku.
                        ً، اللهم اشف سعداً اللهم اشف سعداً، اللهم اشف سعداً
13   Ba a so a daxe a wajen mara lafiya domin kada ya qosa da kai, sai dai idan shi ne ya so da ka daxe saboda ka ga alamar ya samu sauqi sosai.  Xawus ibn Kaysan ya ce, “Mafificiyar ziyarar mara lafiya ita ce wadda ba a daxe ba.”[45]
 Imamul Awza’i ya ziyarci Ibn Sirin lokacin da ba shi da lafiya, a tsaye ya tsaya bai zauna ba.  Amma idan mara  lafiyan ya nemi da ka daxe to ba bu laifi   idan ka daxen.
13. Ka ce wa mara lafiya ya yi maka addu’a.   Hadisi ya zo da yake nuna mana Addu’ar mara lafiya kamar addu’ar mala’iku ce wajen amsawa, har ila yau yana da mahimmanci in ka je gasshe da mara lafiya ka roqe shi ya yi maka addu’a.
14.    Ana so ka tunatar da shi tuba wato ka ce ma shi ya yi ta tuba ga Allah domin ana so Musulmi ya kasance mai tuba ga Allah koda yaushe, domin an so Musulmi ya riqa yin tuba ga Allah.[46]
15.   Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam  bai keve wani lokaci na daban ba wanda  a wannan lokacin  ne kawai za a je gasshe da mara lafiya ba, ya kasance yakan je da rana yakan kuma je da daddare bai kuma keve wata rana ba ya ce sai wannan ranar za a je ziyarar  mara lafiya ba, kai ko da wane lokaci za ka iya zuwa.Amma idan shi mara lafiyan ne ya keve wani lokaci da za a je gasshe  shi, to shi ya san dalilin da ya sa ya keve wannan lokaci.
16.  Wasiyya:  Ana so a tunatar da shi wasiyya in bai rubuta ba, ka tuna masa ya tabbatar ya rubuta.  Rubuta wasiyya ya tabbata mai lafiya ma an so ya rubuta wasiyya.  Abdullah ibn Umar  Allah ya  qara masa yarda  ya ce  Mazon Allah sallal Lahu alayhi  wa alihi wa sallam ya ce,  “Babu wani haqqi da mutum yake da shi da yake so ya yi wasiyya da shi ya kwana biyu face wasiyyarsa tana qarqashin matashinsa.” A wata ruwayar Mazon Allah sallal Lahu alayhi  wa alihi wa sallam  cewa ya yi, “Ba siffar Musulmin kirki ba ce a ce ya kwana dare biyu ba tare da wasiyya ba.”
17.    Babu laifi  namiji ya je  gasshe da  mace mara lafiya amma ba  zai tava  jikinta ba.
18.  A yi masa bushara da fatar samun lada. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya je gasshe da wata mata  sai ya ce ma ta, “Albishir a gare ki ya ke  Ummu Ala’I, haqiqa rashin lafiyar  musulmi tana tafiyar da  kurakuransa kamar yadda wuta take tafiyar da dattin da ke jikin zinariya da azurfa.”[47]
19.    YAWAITA ZUWA ZIYARAR SA:  kamar yadda Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya kasance  ya sa a yi wa Sa,ad bn Ma,az  bukka a masallaci lokacin da aka ji masa rauni a yaqin Kandaq,  ya sanya  akai masa  bukka domin ya sami halin duba shi lokaci bayan lokaci,[48]
20.  Yi wa dangin mara lafiyan wasiyya da haquri musamman ma idan rashin lafiyar ya tsananta.[49]
21.   Zuwa gasshe shi lokacin da ba zai zama mai qunci a gare shi ba: Ahmad bn Hambal ya kasance da azumi yana  zuwa gasshe da mara lafiya da daddare. Bai kamata mutum ya je ziyarar  mara lafiya da asubahi ba, Ahmad bn Hambal ya kasance  ba ya son zuwa gasshe da mutum da tsakiyar rana ya ce wannan ba shi ne lokacin gasshe da mara lafiya ba.[50]
22.   Zuwa gasshe shi da qafa ba a kan abin hawa ba idan wajen babu nisa. Jabir bn Abdullahi ya ce, Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya zo gasshe ni  da qafarsa ba a kan doki ba, ba kuma a kan Alfadari ba.”[51]
23.   A  karanta masa wannan adduar sau uku (3):
                        [52] أسال الله العظيم رب العرش العظيم أن يشفيك"
24.    Ka ce masa ya karanta wannan adduar a wurin ciwon nasa ko wajen da ya ke masa raxaxi zai karanta sau bakwai Bismillahin farko sau uku 3.[53]
           باسم الله باسم الله باسم الله، : أعوذ بعزة الله وقدرته من شر ماأجد وأحاذر"
15. Ana so a tuna wa mara lafiya cewa makaruhi ne yin nishi  irin nishin mara lafiya wanda aka san mara lafiya ke yi, an karanta wa Imam Ahmad ibn Hambal cewa Dawus bn Kaysar al Yamani  yana karhanta nishin mara lafiya  ya ce wannan nishin kai kuka ga wanin Allah ne. Da Imam Ahmad ya ji wannan maganar Dawus bai qara nishi ba har ya mutu.[54]
Waxannan su ne ladubban zuwa ziyarar mara lafiya. Babu laifi don mace ta je ta ziyarci mara lafiya kamar yadda Nana Aishatu ta je gasshe da Sahabi Bilal Allah ya qara masa yarda, da ta je ta ce, “Ya ya jiki? Allah ya kawo sauqi.”[55]
 Ummu Darda ta je ta gasshe da wani mutum mara lafiya a masallacin Annabi sallal Lahu alayhi wa alih wa sallam shi ya sa Bukhari ya yi babi a kan halascin mace ta  ziyarci namiji idan ba shi da lafiya. Ya zo cikin  Muwaxxa cewa Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya je ya gasshe da wata mata da ba ta da lafiya.[56]
Amma idan ba’a  aminci ma fitina ba wato babu mamaki idan namiji ya je ziyarar mace ya iya ya fitinu to yana iya bari, ko kuma ita in ta ziyarci namiji mara lafiya tana iya fitinuwa to tana iya bari, kuma babu kevewa idan xayansu ya ziyarci xan’uwansa mara lafiya, babu kuma magana mai tsawo domin gudun kada wani abu mummuna ya faru.[57]
       SHIN YA HALASTA ZUWA GAISHE DA KAFIRI?
Lalle musulunci ya bai wa kowa haqqinsa kuma ya koyar da mu yadda za mu yi mu’ammula tsakaninmu da wanda ba musulmi ba.  Babu  laifi idan ka je gasshe da arne a yayin rashin  lafiyarsa, amma da sharaxin za ka jawo hankalinsa zuwa musulunci.  Kamar yadda ya zo Manzon Allah   sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya je gasshe da wani Bayahude da ba shi da lafiya, sai wanda ya ke masa hidima ya bijiro masa da cewa ya musulunta. Sai yaron ya kalli babansa, sai babansa  ya ce masa, “Ka amsa kiran Abulqasim!” Sai yaron ya musulunta. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya yi godiya ga Allah da ya tserar da shi  daga wuta.  Kuma ya tabbata cewa ya je gasshe da Baffansa Abu Xalib amma da yake Allah bai nufe shi da musulinta ba,  miyagun da ke kusa da shi suka hana shi musulunta, ya mutu ba musulmi ba. Imamul Bukhari ya yi babi da yake ce wa ‘Babin gasshe da Mushiriki’. Ibn Qaymul Jauziyya ya nuna halascin zuwa ziyarar kafiri in ba shi da lafiya amma da sharaxin za ka ce ma sa ya musulunta: Duba littafin nasa,[58] Ya kawo hadisin Anas da ya ke bayar da labarin yaron da yake wa Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam hidima ya yi fama da ciwo Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya je gasshe shi ya ce ma shi ya musulunta.[59]
        ABUBUWAN DA KE KAN MARA LAFIYA.
1.     Haquri: Duk   wanda ciwo ya same shi ana son ya yi haquri ya yarda da hukuncin da Allah  qaddara  a gare ka. Allah ya yabi masu haquri idan ciwo ya same su. Duba fassarar wannan ayar a cikin baqara.[60]
ولنبلونكم بشئ من الخوف والجوع ونقص من الا موال والانفس والثمرات وبشر الصابرين . الذين إذا أصابتهم مصيبة قالوا : إنا لله وإنا إليه راجعو ن. أولئك عليهم صلوات من ربهم ورحمة , وأولئك هم المهتدون
 Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya faxa mana duk wanda ciwo ya same shi ya yi haquri to Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce Allah zai ba shi Aljanna.[61]
2.      Babu laifi mara lafiya ya faxa wa waxansu ciwonsa da nufin ya sami maganin  ciwon, ba laifi ne ba ya faxa wa likita ko abokinsa rashin lafiyarsa. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya faxa wa Ibn Mas’ud cewa shi yana ciwon mutune biyu ne.
3.      Ya nemi maganin ciwonsa babu laifi, kamar yadda Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku yi magani! Allah bai tava saukar da wata cuta ba face ya saukar da maganinta sai dai ciwo xaya kawai shi ne tsufa.”[62]
4.      Ya rubuta wasiyya, Babu makawa ana so mara lafiya ya yi gaggawar rubuta wasiyya. Kamar  yadda adddini ya yi umurni da rubuta wasiyya kuma wasiyyar nan ba a yin ta ga waxanda za su gaje ka. Idan mutum ya yi wasiyya ga magada ya ce a ba su wani sashi  na dukiyarsa, to ba za a cika ta ba. Ko ya ce idan ya mutu a rufe shi a gida, to ba za a rufe shi a gidan  ba, domin yin hakan sava wa shari’a ne. Muddun dai ya yi wasiyya da savon Allah to ba za a yi ba, ana so ya rubuta wasiyyarsa da alheri kamar ya yi wasiyya da cewa duk wanda ya yi masa abin da ya sava wa shari’a bai yafe ba, ya hana  a yi masa kuka, ya rubuta sunayen waxanda yake bi bashi da masu bin shi, da kayan da aka bashi na ajiya,  da kuma wanda ya ke so ya yi masa sallah in ya rasu, kamar dai yadda ta tabbata wasu sahabbai sun yi haka.
5.      Kyautata zato ga Allah.
ALAMOMIN RASUWA.
 Allah maxaukakin Sarki mai tausayi ne ga bayinsa  kuma  mai son bayinsa ne  da rahama, yana daga cikin rahamarsa Ya sanya ma bayinsa alamar Rasuwa idan ba su da lafiya, ko kuma Rasuwa ta zo masu za su ga alamomi.
Idan mutum ya zo Rasuwa kuma a ka dace na kirki ne, to zai ga mala’ikan Rasuwa,  idan mutumin kirki ne zai ga mala’ikun Rasuwa cikin siffa mai kyau  yana riqe da likkafani na Aljanna da turare shi ma na Aljanna, za su zauna wajen kansa iya ganin idon daga nan sai mala’ikan Rasuwa ya zo ya zauna wajen kansa sai ya ce masa, “Ya wane! Ana maka bushara da yardar Allah a gare ka (Allah ya sa mu cikin waxanda za a yi wa wannan bushara). Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce zai ga masaukinsa a Aljanna, sannan sai mala’ikan Rasuwan  ya ce masa, “Ya ke wannan rai tsarkakakiya fito ya zuwa rahamar Allah da yardarsa.”
Amma idan wannan bawan Allah yana cikin mutanen banza ne wato xan-wuta, to zai ga  mala’ikan azaba cikin baqar fuska zai zauna wajen kansa, kuma nan take zai ga  mazauninsa a gidan wuta. Sai  Mala,ikan Rasuwa ya ce ma shi, “Ya ke wannan rai mummuna! fito ana ma ki bushara da fushin Allah da a zabarsa.”
Cikin waxannan halayen ne wanda ya zo Rasuwa zai gani.[63]
ALAMOMIN  DA  MAI  JINYA ZAI GANI NA ALAMAR RASUWAR XAN’UWANSA .
Mutane sun sha  bamban wajen Rasuwa, wani sa a xaya ya bar duniya  wani kuma yakan iya sa’a biyu wani kuma yakan kai kwana biyu yana cikin gargara kafin ransa ya fita, wasu kuwa sukan wuce kwana biyu. mafi rinjaye kuma  abin da ya ke mabayyani shi ne mafi  yawan waxanda suke cikin gargarar Rasuwa  waxannan alamomin  masu zuwa za su bayyana a gare su wanda yake jinya in ya gansu to wannan bawan Allah shi ke nan
1.      Gefen diddigensa zai yi sanyi saboda rai ta diddige yake fara fita. Idan mutum yana cikin gargara in ka tava diddigensa za ka ji sanyi, in ka tava qwaurinsa za ka ji zafi, bayan wani lokaci diddigen da qwaurin za su yi sanyi mai tsanani, daga baya cinya ta yi zafi.
2.      Hannunsa zai yi taushi sosai kai ka ce auduga ce.
3.      Zufa za ta fara fita ta goshin in na kirki ne.[64]
4.      Maganar da ba a fahimta saboda harshensa ya karye.
5.      Wani sauti zai riqa fita ta qirjinsa.
6.      za a ga wani qulu ya zo maqogwaro.
7.      Gargara wato  zuwan rai ya zuwa maqogoro.[65]

ABIN DA ZA KA YI, KAI MAI JINYA  GA MARA LAFIYA.
1.      Kyautata masa zato ta hanyar ambatonsa da kyakkyawan zato.
2.      Kar a faxi komai a gaban mara lafiya sai alheri, Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Idan kun je wajen mara lafiya ko matacce kada ku faxi komai sai alheri domin mala’iku suna cewa amin a kan abin da kuke faxa.”[66]
3.      Kiran sunansa a ce masa ya faxi kalmar shahada haka, sunna ta koyar. Za a yi ta umartarsa har  ya faxa, idan ya faxa a qyale shi kada ya faxi wata maganar daban.
4.      Share masa fuskarsa da qyalle jiqaqqe da ruwa.[67]
5.      Ba  a so a aje  akwatin rediyo mai hoto Talabijin [TV] a wajen mara lafiya.
6.      Haka nan ba’a kunna rediyo kana a bar shi, a yi ta tuna masa Allah dai.
                      ALAMOMIN  KYAWAWAN  CIKAWA.
Allahu Akbar, Allah mai tausayi ne da rahama ga bayinsa, saboda tausayinsa da yake da shi ga bayin ya sanya waxansu alamomi da wanda duk  ya cika da xaya daga cikinsu to ana masa fatar ya yi Rasuwa mai kyau kuma ana masa fatar samun Aljanna.  Allah Sarki,  ya kai bawan  Allah ka yi murna da wannan bushara kuma ka yi  fatar Allah ya ba ka xaya daga cikin waxannan alamomi, ga su kamar haka;
1.      Faxar kalmar shahada: لا إله إلا الله yayin Rasuwa, akwai hadisai masu yawa da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya ce wanda ya kasance kalmarsa ta qarshe لا إله إلا الله “La ilaha illal Lahu” xan Aljanna ne.[68]
2.      Rasuwa goshin mutum na zufa: Bureda ya ruwaito hadisi  ya kasance yana garin Khurasan sai ya je gasshe da xan wansa yana fama da rashin lafiya. Da ya je sai ya ga zufa na keto masa, sai ya ce, “Allah Sarki! Na ji Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam yana cewa, “Mumini yana Rasuwa ne da zufa a goshinsa.”[69]
3.      Rasuwa Ranar Juma’a ko kuma daren Juma’a.[70]
4.      Rasuwa a fagen fama, wato wajen yaqi kamar yadda ya faru da sahabbai a Badr da Uhudu da dai sauran yaqoqi waxanda sahabbai suka yi, Allah ma ya ambaci haka a cikin suratul Baqara da Ali Imrana.[71]
5.      Rasuwa a sanadiyyar ciwon ciki: Wanda ya mutu sanadiyar ciwon ciki  shi ma ana yi masa fatar shahada ne.[72]
6.      Rasuwa  ta sanadiyar  Annoba da ta faxo wa qasa(kamar amai da gudawa, da sanqarau, ko qyanda da sauran su) Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya ce, “Annoba shahada ce ga kowane  musulmi.”[73]
7.      Rasuwa ta sanadiyyar gobara ko mota ta kama da wuta mutane su mutu.[74]  
8.      Rasuwa ta sanadiyyar ruwa, wato  ambaliyar ruwa ko ruwa ya cinye mutum  a rafi. Ko kuma ruwa ne  aka yi ya zama sanadiyyar Rasuwarsa.[75]
9.      Wanda kago (gini) ya faxo masa. (wato yana xaki rufin xakin ya faxo masa, ko katanga ta faxo masa ya rasu)[76]
10. Matar da ta mutu a sanadiyar  haihuwa, ko wajen haihuwa ta rasu.[77].
11. Rasuwa sanadiyyar ciwon tarin fuka (TB)[78]
12. Rasuwa wajen kare dukiyarka, xan fashi ya zo maka fashi ka mutu. Sanadiyyar kare dukiyarka.[79]
13. Rasuwa wajen kare iyalinka.[80]
14. Rasuwa ta sanadiyyar ciwon dorina(bulala)[81]
15. Rasuwa wajen kare kanka.
16. Wanda ya mutu wajen kare addinin Allah.
17. Rasuwa wajen dako (Ribaxi).[82]
Rasuwa a kan aikin alheri.[83] Misali Ana gama sallah sai mutum ya mutu ko kuma ana cikin yin Sallah, ko bayan karatun qur’ani , ko bayan ladan  ya gama kiran sallah sai ya rasu
18. Wanda wani shugaba azzalumi ya kashe shi.
19. Wanda ya rasu mutanen kirki suka yi ma shi yabo na kirki.
20. Alamar da za a gani wajen yi wa gawar wanka: Wato kamar a ga xan yatsansa yana ishara da kalmar shahada,  ko hasken fuska ko murmushi fuskanrshin na yardar Allah da Aljanna , za ka ga mamaci yana murmushi wanda bata buxe fuska lokacin wanka ko lokacin sanya masa likafani, wani lokaci masu yi ma gawa wanka zasu sami sauqin wanke ta, ita ma ana sa ran ta sami kyakkyawar cikawa.[84]
21. Matar da ta mutu da ciki  ana mata fatar shahada, wasu malaman kuma suka ce budurwar da ta mutu tana son aure amma Allah bai ba ta ikon  yi ba  ita ma ana mata fatar ta yi shahada[85]المرأة تموت بُجمع شهيدة، ويقال بضم الجيم وكسرها وهي المرأة تموت حاملاً، وقد جمعت ولدها في بطنها، وقيل: هي البكر، وصحح القرطبي والنووي                                            
Waxannan su ne alamomi na kyakkyawar cikawa. Duk wanda ya sami xaya daga cikin waxannan ana yi ma sa fata ya yi Rasuwa mai kyau kuma ana masa fatar samun Ajanna.  Allah  ya ba mu Ajannatu Firdausi Amin.

 ALAMUN MUMMUNAR CIKAWA.
1.      Mutum ya mutu kan shirka ko cikin Shirka ko rashin sallah ko mutum ya mutu yana zina. Allah ya kare mu, ko mutum ya mutu yana shan giya ko mutum ya mutu a mashayar  giya ko Silma ko yana jin kaxe-kaxe, Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce kowane bawa za’a tayar da shi a kan abin da ya rasu (Yake yi).
2.      Mummunar sheda da mutanen kirki za su yi wa gawar kamar yadda sahabai suka yi wa wata gawa, daga nan ne sai Manzon Allah  sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya ce wuta ta tabbata a gare ta.
3.      Mumin abin da masu wanka zasu gani wajen yi wa gawa wanka.[86]
ABUBUWAN  DA SUKE WAJIBI GA WANDA AKA YI MASA RASUWA.
            Ya zama dole ga dangin mamaci su riqi waxannan abubuwa;
1.      Haquri da yarda da qaddarar Allah, haka Allah ya faxa. [87]
Haquri a kan Rasuwar yaran ka/ki akwai lada mai yawa, musamman ma ga mata, ladar ta fi yawa kuma a kan su ne hadisi  ya zo qarara, Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Duk matar da yaranta guda uku suka mutu, za su kasance a gare ta garkuwa daga shiga wuta, sai wata mata ta ce ko da yara biyu  ne? Sai Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa aihi wa salam ya ce ko da yara biyu ne za su zama hijabi ne a gare ki daga shiga wuta.[88]
             Wannan kariyar daga shiga wuta za ta samu ne da                                         sharaxin kin yi haquri, amma in kika kasa yin haquri  kika faxi maganganu na rashin kirki da fitsara da surkulle da  shiga wajen bokaye, to ba ta cikin wadanda Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ambata.Kuma duk mai yin  haka tana cikin fushin Allah da bala’i.
2.      Abin da yake wajibi ga dangin da aka yi wa rasuwa shi ne fadar
إنا لله وإنا إليه راجعون  اللهم اجرني في معيبتي وأخلف لي خيرا منه
3.      Sai a kira sunan mamaci sannan a yi masa addu’a kamar yadda A Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya yi a lokacin da Abu Salma ya rasu.Sai ka  ambaci sunansa a inda aka bar alama. [89]
: اللهم اغفر **********، وارفع درجته في المهديين، واخلفه في عقبه في الغابرين،واغفر لنا وله يا رب العالمين،وافسح له في قبره ،ونور له فيه                                                      
Babu laifi a buxe fuskar  wanda ya rasu   a sunbance shi a kira sunansa a yi masa addu’a. [90]

TAKABA.
Mata suna yin takaba idan xaya daga cikin waxannan nata suka rasu;
1.      Mijinta.
2.       Babanta.       
3.      Xanta.
Na farko shi ne wajibi  idan mijinta ya rasu za ta yi takaba na wata huxu da kwana goma  kamar yadda Allah ya faxa a cikin suratul Baqara, mace  mai takaba ba za ta yi waxannan abubuwan masu zuwa ba.
1.       Babu sanya tufa mai  kala/launi.
2.      Babu sanya ko shafa turare ko da turaren wuta ne ba zata kunna shi a xakinta ba.
3.      Babu sa tozali. (sai dai in magani ne ko lalura)
4.      Babu qunshi.
5.      Babu sanya gazar.
6.      Babu sanya jan-baki.
7.      Babu sanya hoda.
8.      Ba za ta shafa man shafawa mai qamshi   ba sai lakuci sharva.
9.      Ba za ta yi kitso ba.
10.  Babu sanya sarqa ko zobe, dukkansu haramun ne a gare ta.
Za ta bar waxanan   abubuwan ne na tsawon wata huxu da kwana goma, amma ga mijin ne kawai za ta yi na tsawon wata huxu da kwana goma, amma idan xanta ne ko babanta na kwana uku ne kawai za ta yi, amma ba dole ba ne,  idan ma da za ta bar yin takabar ga xanta da babanta hakan ya fi dacewa kuma an fi son haka duk da cewa ya halasta ta yi takabar. [91]
Babu wani abu wai shiga takaba da mata suke yi ko bikin fita takaba ko karatun takaba wannan duk aikin jahiliyya ne ta maguzawa kuma bidi’a ce da za ta iya kai mata ya zuwa ga shirka. Akwai kuma wata shirka da ake sa mata na kwanciya da wuqa ko takobi, wai kada mijinta ya yi mata fatalwa, kai wannan da ji ka san surkulle ne kuma shirka ne, da yawo da buta wai mijin yana bin sanyin butar, wannan duk surkulle ne da zai kai mutum ya zuwa ga shirka. Mata a gidajen mazajensu suke yin takaba musulunci ne ya ce mace ta yi takaba a xakin aurenta idan mijinta ya rasu.  

ABUBUWAN  DA SUKA KAMATA  GA  MACE  IDAN  XANTA KO BABANTA YA RASU.
1.      Saduwa ya halasta idan xanku ya rasu ku sadu saduwa ta aure babu laifi, yin haka ma shi ne abin da ya fi dacewa in buqatan haka ta taso, haka ya faru lokacin Manzo Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ga Ummu Sulayman da mijinta Abu Xalhatul Ansari, xanta ya rasu kuma suka yi saduwar aure har Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi ma su addu’a   Allah Ya sa albarka ga saduwarsu. Kuma Allah Ya amshi addu’ar  Ya sa albarka a wannan saduwar.[92]
2.      Yin kwalliya in da buqata.

ABUBUWAN  DA SUKE  HARAMUN NE AIKATA SU IDAN AKA YI WA MUTUM RASUWA.
Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya haramta waxannan abubuwan ga duk wanda aka yi ma sa rasuwa ya zama haramun ne a gare shi   ya aikata su, idan ya aikata xaya daga cikin su to mutum ya sava wa Allah da Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam kuma yana janyo wa mamacin musiba ne da bala’I, ‘yan’uwa ya kamata a kiyaye.
1.      Kuka wanda ke jin muryar mutum tana xagawa yana kuka da qarfi. Babu kyau idan an yi wa mutum Rasuwa ya yi kuka yana xaga murya, wannan haramun ne. Amma kuma wanda babu xaga murya ya halasta. Shi ne wanda hawaye yake fitowa, ana kiran irin wannan kukan “Yavune” wannan babu laifi yin haka, yin haka ma alama ce ta tausayi. Wani Hadisin Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce ana yi wa matacce azaba a cikin qabarinsa sakamakon kukan da aka yi masa.
2.      Dukan kumatu da yayyaga riga shi ma Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya hana. Ya ce ba shi tare da ni wanda aka yi masa Rasuwa ya rika dukan kumatunsa ya kuma yaga tufarsa yana maganganu irin na jahilan farko.
3.      Aske gashin kai (qwal-kwabo[93]). Wani idan aka yi ma sa Rasuwa sai ya aske gashin kansa domin baqin ciki, wani kuma aske gemunsa yake yi, shi ma yin haka haramun ne[94].
4.      Barin gashin kai na wasu kwanaki saboda baqin ciki.
5.      Barin gemu na wasu kwanaki saboda an yi ma sa Rasuwa. Daga baya ya aske.
6.      Sanar da Rasuwa a cikin amsa-kuwwa ta masalaci “Loud speaker”.
7.      Faxin Rasuwa a gidan radiyo, tare da ambatar irin xaukaka ko darajar da Allah Ya yi wa wanda ya rasu da faxin yawan yaransa, ko a shiga kasuwa ana faxi, “Wane xan wane mai yara kaza da kaza ya rasu.”
MATASHIYA.
Ya halasta a faxi Rasuwar mutum domin a samu waxanda za su zo su yi mashi sallah kamar yadda Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya sanar da Rasuwar Najashi[95] Sarkin Habasha,  ya ce a fito a yi ma sa sallah. Haka nan ma ya sanar da rasuwar Sayyidina Ja’afar yayin da ya yi shahada a yaqin Mu’uta ya ce a roqa ma sa Allah, kuma a duk sa’ilin da ka faxa wa wani Rasuwar xan’uwanka ka ce ma shi ya yi ma sa addu’a kamar yadda Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yake yi wa sahabbansa.
ABUBUWAN  DA AKE YI WA MUTUM MUSULMI DA ZARAR YA RASU.
Da zarar xan’uwanka/ki ya rasu ana  so a yi ma sa waxannan abubuwan masu zuwa:
1.      Rufe masa idanuwansa kamar yanda Manzon Allah Sallal Lahu alyhi wa alihi wa salam ya yi wa Abi Salamah.[96]
2.     Yi ma sa addu’a tare da kiran sunnansa a yi ma sa addu’a.[97]
3.      Rufe masa gaba xayan  jikinsa kamar yadda Nana Aisha ta faxa mana cewa haka aka yi wa Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam da  ya rasu aka rufe gaba xayan jikinsa, babu kyau a bar gawa a buxe.[98]
4.      Gaggawar shirya shi na yi ma sa wanka da yi ma sa likkafani.[99]
5.      Cire ma sa kayan jikinsa  da gaggawa.
6.      Xora shi a kan karan-gado ko gadon katako ko dai wani abu mai bisa, kada a bar shi a qasa. Ga misalin gawa kafin wanka kamar haka:
                   
7.      Miqar da gavovinsa da yatsunsa na hannunsa.
8.      Xaure gemunsa da qyalle kafin a je yi ma sa wanka, ana yin haka ne don gudun kada ya kunbura.
9.      Xaura wani abu mai nauyi a cikinsa don gudun kada ya kumbura.[100]
10. Gaggawar biya ma sa bashi.[101]
11. Istirja’i wato faxan إنا لله وإنا إليه راجعون اللهم اجرني في مصيبتي وأخلف لي خيرا منها                                                                          
12. Ambatar alherinsa.
13. Faxa wa dangi rasuwarsa babu laifi.
14. Babu laifi a jira har danginsa su haxu domin samun yawan Jama’a.
15. A yi saurin zartar da wasiyyarsa.

LADUBBAN WANKAN GAWA.
Musulmi yana da tsari, hatta yi wa gawa wanka  sai da aka nuna mana yadda za a yi,  da sharuxxan ta. Ga sharuxxan wankan gawa  kamar haka:
1.      Ya kasance Musulmi, kafiri haramun ne ya yi wa Musulmi wanka.
2.      Mai hankali banda yaro.
3.      Mai sirri kuma amintacce, banda mai surutu mara sirri.
4.      Masani game da hukunce hukuncen wankan gawa.
5.      Ya kasance yana  yi  ne domin neman yardar Allah.
6.      Namiji ya wanke namiji, bai halatta namiji ya wanke mace ba sai dai in matarsa ce ko mahaifiyarsa ko ‘yarsa.
7.      Mace ta wanke mace, bai halatta mace ta yi wa namiji wanka ba sai dai in mijinta ne ko babanta, ko xanta ko dai wani muharraminta. Idan kuwa ba haka ba sai dai a yi masa taimama.[102]
Waxannan su ne sharuxxan wankan gawa kuma haka sunna  ta koyar: Miji ya wanke matarsa mata ta wanke mijinta ko ‘ya‘yanta ba wani  ba, haka bai halatta wani ya yi wa mace wanka ba in dai ta kai shekara bakwai haka Usaymin ya ammbata.[103]
Kuma wannan ya nuna mana rashin asalin qeve wasu tsofaffi domin yi wa gawa wanka waxanda ba su san komai na yadda ake wanka ba sai shirme da surkulle da shirka, ya kamata a kula da kyau don Allah, yana da kyau a riqa sanya  waxanda suke da hakqin yin waka kuma suka san yadda sunna ta koyar.

       WAJEN  DA AKE YIN WANKAN GAWA.
1.      Wajen ya kasance mai tsarki mai tsafta, bai halatta a yi wa matacce wanka a bayi ba, Yi masa wanka a bayi Wulaqanta gawar ne da kuma cutar da mala’iku Allah.
2.      Wurin ya kasance sitirtacce kuma ya kasance rufaffe. ana  so wurin ya kasance mai  sirri. Babban tabi’i  ibn Sirin ya ce mustahabbi ne xakin da za’a yi wa gawa wanka ya kasance rufaffe, mai duhu yadda ba za a ga al’aurar gawar ba.  Ya kasance dai xakin rufaffe ba mara rufi ba, ba kuma fili ba, ba a yi a tsakar gida.
3.      Ya zamanto xakin babu hoton duk wani abu mai rai domin mala’ikun rahama ba sa shiga xakin dake da hoto ko kare.[104]
4.      Sannan wurin ya kasance ba kowa zai iya zuwa ba sai dai wanda ake da buqatarsa.[105]
   ABUBUWAN DA AKE BUQATA DOMIN  YI WA GAWA WANKA.
1.      Ruwa ya   kasance mai tsarki kuma na halas.
2.      Ruwan ya kasance matsakaici tsakanin sanyi da zafi.
3.      Magarya dakakkiya (garin magarya)da shi za a yi wanka na biyu.
4.      Kafur shi ma ya zama dakakke (gari) da shi za a yi masa wanka na uku.
5.      Miski (Turare).
6.      Sabulu.

ABIN LURA KAFIN YIN WANKA.
1.      A tabbatar da Rasuwar gawar.
2.      A xaura gawar a wani abu mai tudu kamar gadon qasa ko karan-gado (Gadon Kara) ko gadon katako ko gadon da aka cire katifa. Ya kasance dai a sama ba a tandarqin qasa ba ko tabarma.
3.      A kunna turaren wuta wato turaren qanshi a xakin wankan gawar.
4.      Suturta gawa (wato a sami wani qyalle a rufe gabanta (ala’urarta) ba a so a bar ta tsirara, ya kasance tun daga cibiya har gwiwarta  a suturce.
5.      Ya kasance sun kai  su biyu zuwa uku: Wato mai wankan daban mai zuba ruwa daban da kuma mai juya ta.
6.      Mai wankan ya sanya wani kyalle a hannunsa kamar safar  hannu ko wani abu mai kama da shi kamar irin safar da likitoci suke amfani da ita.
7.      Mai wankan ya yi a hankali cikin tausasawa da jinqai
8.      A tabbatar an cire kayanta (gawa) da zarar ta rasu, idan ya qi ciruwa babu laifi in an yanke kayan jikinta da reza ko almakashi.
9.      A yi qoqarin miqar da gavovin gawar cikin gaggawa.[106]
10. Ba’a tava farji mace idan dai ta kai shekara bakwai, sai dai in matarka ce.[107]
Idan gawar ta daxe da rasuwa gavovinta sukan sassandare misali kamar qafarta ko hannunta,  za’a miqar da su,  yadda, ake miqar da su kuwa shi ne a samu ruwan xumi ana mammatsa gavarta da  tattanqwara  su (gavovin) a hankali ana yi a hankali har su mimmiqe.
WAXAN DA  SHARI’A  TA  YARDA  A  YI MASU  WANKA  IDAN SUN RASU.
1.      Muslumi: Idan Kafiri ya mutu ba’a yi masa wanka.
2.      Yaro.
3.      Jariri.
4.      Vari in dai ya kai wata huxu zuwa Sama da haka.
5.      Mahaukaci in dai musulmi ne.
6.      Karuwa.[108]
7.      Wanda ya mutu wajen aikin haji.
8.      Mashayin giya.
9.      Wanda ya kashe kansa amma liman da mutanen kirki ba za su yi ma  shi wanka ba, ba kuma za su je wajen sallarsa ba.[109]

WAXANDA BA A YIN MASU WANKA.
1.      Shahidi ko da ya mutu da janaba.[110]
2.      Varin da bai kai wata huxu ba.
3.      Wanda ya qone quna mai tsanani ko haxari ya radaddage. Waxannan ba a  yi ma su wanka.[111] 
FAXAKARWA.
Idan mutum ya rasu da zobe ko haqorin Hajji a bakinsa za’a cire shi. 
Sheik Usaymin yana ganin babu laifi idan mutum ya rasu a yanke masa qumbarsa, a kuma  yanke masa gashin hammata da na mara da kuma rage ma shi gashin baki. [112]
An samo hadisi daga Abu Ka’ab ya wanke gawa sannan ya ce a kawo ma shi aska ya aske ma gawar gashin hammatarta.[113]
 Amma banda gemu domin aske gemu haramun ne.
 Sahabi Khubab ya aske gashin hammatarsa kafin a kasha shi.[114]
KWANCE  KITSON MACE KAFIN WANKA.
Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa aihi wa sallam ya yi umurni da a kwance gashin kan ‘yarsa Zainab,Ummu Adiyah ta ce mun kwance gashin kanta sannan muka yi mata kitso guda uku a kanta.[115]
Don haka idan mace ta rasu, to gabanin  a yi mata wanka sai an kwance gashin kanta an  tsefe shi wato an  taje shi sannan  a yi  mata kitso guda uku, kamar yadda hadisin Ummu Adiyah ya nuna, za a yi guda xaya ya nufi bayanta.
SAMFURIN WANKAN GAWA.
Kamar yadda muka gani wajibi ne idan mutum ya rasu a yi masa wanka, ana iya yi kamar haka duk wanda ka yi a cikin waxannan nau’o’in ya yi;
1.      Sau Uku.
2.      Sau biyar.
3.      Sau bakwai.
4.      Ya kasance dai mara kamar yadda Manzon Allah Sallal Lahu alaihi wa alaihi wa sallam ya ce ma masu yi wa Nana Zainab wanka, ya ce,  “Ku wanke ta sau 3 ko 7 ko fiye da haka in an ga buqatar yin haka.”[116]
YADDA AKE WANKAN GAWA.
1.      Za a kawo bokitin ruwa guda uku a aje in mun zavi guda uku. Kamar yadda yake cikin ladubban wankan gawa a xora shi a kan wani abu mai tudu bayan an sa ta a kan gadon katako ko wani abu mai tudu sai a kwantar da gawar a rigingine wato fuskarta na kallon sama bayan an tuve ta. Sai dai kada a manta da rufe al‘aurarta daga cibiya zuwa guiwa, kuma mai wankan kar ya manta da safar hannu ko wani kyalle da zai rufe hannunsa da shi .
2.       Daga nana sai a xan xaga kanta kaxan kamar za a zaunar da ita sai  a mammatsa cikinta a hankali har sau uku, daga cibiya zuwa kirji, za a matsa ana yin haka ne idan akwai wata najasa a cikinta to za ta fito. Daga nan sai mai wankan ya sanya qyale a hannunsa  na hagu ya wanke wannan najasar, bayan ya wanke najasar sai ya yi mata tsarki. Ga yadda za ka yi kamar  haka:
          
3.      Sai a yi mata alwala ta sallah, za a fara da faxar  بسم الله Bismillah”  yadda dai a ke alwala ta sallah, sai dai wajen wanke bakin da shaqa ruwa za a sanya tsumman nan  jiqaqqe da ruwa ya goge haqoranta da shafa hancin ana  goge cikin hancin.[117]
4.      Bayan Alwala sai a wanke kan gawar zuwa wuyanta sau uku, sai dai a tabbatar  an sa ruwa a kanta sosai.
5.      Sai vangaren jikinta na dama wato a kasa jikinta gida biyu a fara wanke vangaren dama daga nan sai na hagu, za a fara ne tun daga qafar gawar har zuwa qafafuwanta baki xaya.  Ita ma qafar hagu kamar yadda aka yi wa  na dama, wannan an gama da bukiti na farko ke nan.
6.      A bokiti na biyu wato wanka na biyu sai a kawo dakakkiyar magarya wadda aka daka tun daga farko a sanya a cikin ruwan a kaxa sosai sai ya yi kumfa sannan sai a xebi kumfar da ruwan a wanke kan gawar da wuyanta sau uku. Daga nan sai a wanke sauran jikin, kada a manta za a fara daga vangaren dama ne daganan sai na hagu.
Idan ba a samu magarya ba babu laifi a yi amfani da sabulu mai qanshi a yi mata wanka da shi (gawar).[118] .
7.      A bokiti na uku za a sanya kafur bayan an mayar da shi gari, sai a zuba a cikin ruwan wankan  sai a yi mata wanka da  shi kamar yadda aka yi bokiti na biyu. Idan kuma ba a samu kafur ba sai a yi amfani da turare mai qamshin gaske. Bayan kuma an gama mata sai a fesa mata turare.[119]
Anfanin kafur shi ne domin ya na sanya jikin gawa ya yi tsabta da qamshi.
Idan kuma aka zavi a yi mata (gawar) wanka biyar ne to haka za a yi yadda aka yi wa mai guda uku, idan ma bakwai ne to duk dai haka za a yi. (wato a na huxu sai a sa magarya, na biyar a sa kafur ko kuma a jinkirta sanya  kafur sai a qarshe (wallahu a alam).
8.      Kada a manta idan mace ce gawar za a kwance kitsonta a fece shi, bayan kuma an gama wankan sai ai yi mata kitso guda 3 a jefa kitson bayanta (qeyarta). Wasu Malaman sun ce ana iya yanke qumbar gawar da rage gashin baki amma banda gemu domin aske gemu haramun ne, kana raye ko bayan ka mutu. bayan askin sai a sanya abin da aka  yanke cikin likafanin. [120]
Ibn Abi Shaybah ya kawo  abin da ke nuna halascin yanke wa gawa qumba da rage mata gashin baki da haxasu a cikin likafani a rufe  shi da ita.[121]
Matar da ta rasu tana cikin al‘ada wanka xaya za a yi mata.[122]

FAXAKARWA.
·        Idan gawar kuturwa ce kuma kuturtar ta yi muni, toba sai an yi mata wanka ba. A maimakon haka sai a yi mata taimama a maimakon wanka. Taimama kuwa hannu da fuska kawai ake shafawa. Haka hadisai suka nuna musamman  hadisin Ammar  ibn Yasir.[123]
·        Idan ba ruwa sai a yi wa gawar Taimama.[124]
·        Babu laifi mai janaba ya yi wa gawa wanka.
·        Idan  gawa ta kumbura ko wani sashi a jikinta ya fara yagewa, sai a yi mata taimama. Ko kuma quna ce mai muni gawar ta yi, ita ma ba sai an yi mata wanka ba, sai a yi mata taimama kawai ya wadatar.
·        Wanda ya rasu jini na zuba a jikinsa babu laifi a sa magani  domin jinin ya tsaya, ko a sa bandeji ko kuma wani tsumma.
·        Idan mace ta rasu alhali kuwa babu mata sai maza, to bai halasta mazan nan su yi mata wanka ba. Haka nan   ita ma da namiji zai rasu kuma babu maza, alhali kuma su matan ba muharraman sa ba ne, to su ma ba za su yi masa wanka ba sai dai su yi masa taimama. An samo Hadisi, “Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘Idan namiji ya rasu cikin mata babu maza, ko mace ta rasu babu mata, taimama za a yi masu a je a rufe su  suna matsayi wanda bai samu ruwa ba ne.’” [125]
·        Idan mutum ya rasu a ka je  aka rufe shi ba a yi masa wanka ba, jumhurun malamai da mazahabar Malikiyya da Hannafiyya da Hamabaliyya da Daud da ibn Hazam sun ce a je a tono shi  a yi masa wanka matuqar dai bai canza ba (Wato bai yi wari ba).[126]

 MACEN DA TA RASU  TANA DA CIKI.
Idan mace ta rasu da ciki kuma cikin ya wuce wata biyar, to ana sa ran abin da ke cikin ya na da rai. Don haka ya halasta a fexe cikin a xauko jaririn kafin a yi mata wanka. Amma idan an tabbatar ba shi da rai, to ba za a fexe ta ba. Sai dai kuma idan yana da rai za a fexe ta a xauko jinjirin domin tsirar da rai.[127] Wannan kuma ita ce mazahabar Abu Hanifa da shafi’i da Ahmad ibn Hambal da wani vangaren malikiyya.
WANDA YA YI  WA GAWA WANKA  SHIN SAI YA YI WANKA?
An so wanda ya yi wa gawa wanka shi ma ya yi wanka amma fa wannan wankan ba dole ba ne mustahabbi ne. Hadisi ya zo daga ibn Abbas ya ce, “Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘Ba dole ba ne a kan ku don kun yi wa gawa wanka a ce sai kun yi wanka, domin matacce ba najasa ba ne. Ya isar maku idan kuka wanke hannunwanku’. [128]
Saboda haka mustahabbi ne in an yi wa gawa wanka a kuma yi wanka, amma ba dole ba ne.  Wani hadisin cewa ya yi  wanda ya yi wa gawa wanka shi ma ya yi wanka, wanda kuma ya xauki gawa to shi ma ya yi alwala.[129]
Shi ma wannan hadisin bai nuna wajabci ba kamar yadda malamai suka yi bayani. Abu Ammar ma haka ya ce: Ba dole ba ne   mustahabi ne. Wajabcin da ke cikin hadisin shi ne wanda malaman Usul fiqhu suke ce masa Wujubul Istihibab.

BIDI’O’IN WANKAN GAWA.
1.      Keve waxansu tsofaffi da sunan wai su ne kawai za su yi wa gawa wanka kuma ba su san yadda ake yin wankan a shar’ance ba, sai surkulle da maganganu waxanda suka sava wa shari’a. Ya kamata ‘yan’uwa mu kiyaye idan an yi  rasuwa mu hana irin wanxannan tsofaffi yin wanka tunda ba  su iya ba,   kuma  ba su ke da alhalkin yin wankan ba. Mu tabbatar an yi wa mamaci  wanka yadda shari’a ta nuna.
2.       Sanya kanwa wajen yi wa gawa wanka wannan kuskure ne babba kuma sava wa sunna ne.
3.      Yi wa gawa wanka a bayi haramu ne.
4.      Kunna fitilla a xakin da aka yi wa gawa wanka na kwana xaya ko biyu ko uku shi ma bidi’a ne.
5.      Yin zikiri yayin yi wa gawa wanka.
6.      Barin gashi ba a kwance ba da qin yi wa gawa kitso guda uku idan mace ce.kuma laifi ne mai girma.
7.      Shan ruwan da aka yi wa gawa wanka wannan yana iya zama shirka.
8.      Shafar kwano ko kwatanniyar da aka yi wankan gawa da sunan wai neman tubarraki wannan shirka ce, Allah ya kyauta.
Waxannan dukkan su haramun ne a yi su lokacin yi wa gawa wanka ko bayan an gama yi mata wanka. Sannan bayan an gama wankan sai kuma sanya wa gawa likkafani, to shi ma manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya koyar da yadda ake yi. Ga yadda ake sa likafani kamar haka:

LIKAFANI.
Likafani shi ne suturar da ake wa mamaci bayan an gama yi masa wanka. Wajibi ne a sanya ma gawa likafani, Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya faxa ga wanda ya faxo a wajen aikin Hajji ya rasu. Ya ce ku yi masa likafani da kayan jikinsa domin zai tashi yana mai talbiyya ranar Qiyama.[130]
Musad bn Usman shi ma an yi masa likafani da kayan jikinsa bayan ya yi shahada a yaqin Uhudu.
A wata ruwayar Manzon sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku riqa sanya fararen tufafi kuma  ku yi likafani da shi (farin tufafi)”.A taqaice muna iya cewa likafani wajibi ne a kan Musulmi namiji ko mace idan xan uwansu ya rasu su yi masa likafani, haka maganar Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ta nuna.[131]
Ana so likafani  ya kasance ya cika waxannan sharuxxan masu zuwa;
1.      Ya kasance fari, haka Annabi Sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku rinqa sanya fararen tufafi domin farin tufa shi ne mafi alherin tufa. Kuma ku yi wa matattunku likafani da farin tufafi ’’.[132]
2.      Likafani ya kasance guda uku.  Haka aka yi wa Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam.[133]
3.      Ya kasance na auduga.
4.      Ba a yi wa gawa hula da riga da rawani. Haka hadisin Nana  A’isha Allah ya qara mata yarda ya nuna, kuma ba a yi wa Manzo Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam  hula da riga ba da ya rasu. Su ma sahabbansa ba a yi masu ba, don haka yin hula da rawani da riga ba karantarwar Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ba ce.[134]
5.      Ya kasance mai tsabta kuma kyakkyawa.[135]
6.      A sanya ma likafanin turare bayan an gama sanya likafanin, kamar yadda sahabi ibn Umar da ibn Abbas suka yi wasiya da a sanya ma likafaninsu turare.[136]
7.      Kada yadin ya kasance na alfahari domin Allah ya hana alfahari.
8.      Idan da hali xaya daga cikin likafanin ya zama Saqaqqe.
Idan ba’a sami sabo ba sai a wanke tsoho a yi amfani da shi babu komai lalura ce. Ana amfani da tsohone a matsayin lalura. Kuma idan ba a samu wanda zai rufe masa jikinsa baki xaya ba sai a rufe fuskarsa, a sa ciyawa ko ganye a qafarsa, haka Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi umurni da  a yi wa Mus’ab ibn Umair a lokacin da ba a samu likafanin da zai rufe masa  jikinsa baki xaya ba.[137]
Wanda ya rasu a wurin aikin Hajji za a yi masa likafani ne da kayan jikinsa.[138]



TANADIN LIKAFANI TUN GABANIN RASUWA
Mun san ba a yin likafani sai bayan rasuwa, to amma bai zama laifi ba in aka tanaji likafanin tun ana raye. Irin haka ta faru  a zamanin Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, bai kuma hana ba. Wato  a lokacin da wani sahabi yake zaune a gaban Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, sai wata mata ta kawo masa wata  riga saqaqqiya ta ce, “Na saqa ta ne domin in tufatar da kai ita.” Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, ya karve ta yana mai buqatar ta, ya shiga gida ya sanyo ta. Dagan an sai wani sahabi ya nuna buqatarsa. Sai Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ba shi  ita. Sai Sahabbai suka nuna abin da wannan sahabi ya yi bai  kyautu ba. Sai shi kuma ya ce yana so  ne ta zama likafaninsa. Sahal ya ce  ita ce kuma ta zama likafanin nasa. [139]   Shi ma Sa’ad ibn Abi wakkas ya aje bargon da ya je yaqin Badar da shi ya ce shi ne yake so ya zama likafaninsa.
Bai zama laifi ba in ka tanaji likafaninka tun kana raye. Imamul Bukhari ya yi babi musammam a kan halascin ajiye likafani tun ana raye.

A KAN WA SAYEN LIKAFANI YAKE?
Sayen likafani yana kan dukiyar wanda ya rasu ne ko da kuwa matarsa ce. Wannan ita ce magana tabbatacciya. Haka nan ma da mace mai aure za ta mutu, to sayen likafaninta za a yi shi ne a cikin dukiyarta ba a cikin dukiyar mijinta ba. Haka nan ma qabari shi ma cikin dukiyarta za a biya kuxin gini.[140]
 Amma da za a samu waxansu jama’a su sayi likafani su bayar don Allah, to shi babu laifi. Kuma muna yi masu fatan alheri shi ma mijin idan ya saya a cikin dukiyarsa duk babu laifi, amma ba dole ba ne a ce sai ya saya, don ba haqqinsa ba ne.
Haka nan da mace za ta rasu a wajen aikin Hajji, to da kayan jikinta za a yi mata likafani kamar yadda aka yi wa wanda ya faxo wajen aikin Hajji a zamanin Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam. Usaymin yana da fahimtar cikin dukiyar mamaci za a xauka a saya masa likafani ba cikin dukiyar wani ba.[141]

YADDA AKE SANYA LIKAFANI
Babu bambanci tsakanin mace da namiji wajen likafani. An yi wa Manzon Allah Sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam likafani guda uku (3) ne, sahabbansa sun zavi yin uku ne saboda sun san shi ne karantarwar sa  tun yana raye.[142]  Ga yadda za a sanya likafanin kamar haka. Za a kawo likafani guda uku.
1.      Za a shinfixa na farko mai faxi yadda zai rufe daga qirji zuwa qafa ya kuma zova. Misali idan mamacin zai ci yadi biyar ne idan yana raye, to sai a ninka.
2.      Likafani na biyu ya ninka na farko yadda zai rufe tun daga  kai har ya  zova qafarsa.
3.      Iikafani na qarshe ya fi na biyu faxi da tsawo sai a  rufe gaba xanyan jikin gawa har ya zova, sai a xaure qarshen kan da qafar gawar da ragowan qyallen da ya zova ko kuma wani zare fari. Kar a manta an riga an shinfixa likafanin nan guda ukun tun farko. Idan kuma Allah ya sa ba a sami likafanin ba sai guda xaya, to sai a yi amfani da guda xayan a matsayin lalura. Shi guda xaya za a rufe shi ne baki xaya.
 Ba a yin hula ko rawani domin bai tabbata ba. Da ya tabbata da an yi  wa  manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ko sahabbansa tsira da amincin Allah su tabbata a gare su baki xayan su.     
Ba wata hujja tabbatacciya da ta ce a yi wa mace likafani guda biyar, don haka ita ma likafani uku (3) za a yi mata kamar yadda  ya zo a karantarwar Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ta nuna.[143] 
Fauzan a cikin littafinsa na gawa ya nuna za a iya shimfixa likafanin guda uku a lokaci xaya watoxaya bisa kan xaya sannan sai a kawo gawar a xora ta a kan su, sai ka aikata yadda bayani ya gabata a sama.[144]
Wasu kuma suna ganin za a sa auduga da turare a toshe hancin gawar da kunni da kuma hammata, ragowar kuma a sa a idonta. Albany a cikin Ahkamul Jana’iz ya ce yin haka bidi’a ce don  manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  bai koyar da haka ba kuma su ma sahabbai ba su yi haka ba. Don haka bai halasta ba.
Idan gawawwaki sun yawaita kuma likafani ya yi qaranci ya halasta a haxa mutane biyu ko fiye da haka a likafani xaya sai a gabatar da wanda ya fi su qur’ani ya fuskanci liman.[145]
Bayan an gama sanya wa gawa likafani sai a fesa mata turare mai qamshi sannan a saka ta cikin makara,da ga nan a fita da ita filin sallar gawa.

  SALLAR GAWA
Hukuncin wannan sallar ba dole ba ne a ce kowa sai ya yi ta, faradul kifaya ce wato wani ya iya xauke wa wani ko wasu suna iya xauke wa wasu. Idan wasu suka yi to sun xauke wa waxanda ba su yi ba. Ma’ana idan wasu suka yi zunubi ya faxi a kan wanda bai samu halin zuwa wajen salla ba  amma waxanda suka yi su kaxai ne zasu samu ladar sallar.

 SHARUXXAN SALLAR GAWA
Wannan sallah tana da sharuxxa kamar haka:
Niyya: Ita niyya wajiba ce a kowace ibada kuma ita wannan niyyar a zuciya ake yin ta. Furuci da niyya bidi’a ce bai halasta ba, yin furuci da niyya a wajen sallar gawa ko sallar farilla ba.
 Fuskantar  Alqibla:  kamar yadda ake fuskantar  alqibla wajen sallar farilla to ita ma sallar gawa ana fuskantar alqibla.
 Suturce Al’aura: suturce al’aura wajibi ne, ba a yin sallah tsirara sai dai da lalura mai qarfi idan ya zama lalura mai qarfi sai a yi sallar tsirarar kamar yadda Askari ya koyar da mu sai a yi idon mamu a rufe.
Tsarki:  Masu sallar da wurin da za’ayi sallah ya  kasance mai tsarki.
Alwala: Alwala a kowace sallah wajibi ne manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ya ce ba a amsrar  sallah sai da alwala.   لا تُقبل صلاة بغير طهور  [146]
RUKUNNAN SALLAR GAWA
Wannan sallah tana da rukunai kamar haka:-
1.      Tsayuwa: Ana yin sallar ne a  tsaye, ba a yin ruku’u babu kuma sujuda babu tahiya.
2.      Kabbara huxu a qalla, zuwa  tara.
3.      Karatun Fatiha: Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa aihi wa salam ya ce, “Babu sallah ga wanda bai karanta fatiha ba.”[147]Sahabi Abu Umama ya ce sunnah a sallar gawa ita ce karatun fatiha a asirce[148] .
4.      Salati ga manzon Allah (SAW).
5.      Yin addu’a ga mamacin.
6.      Jerantawa.
7.      Sallama.


SUNNONIN SALLAR GAWA
Wannan sallah  tana da sunnoni kamar haka:
1. Xaga hannu yayin kabbara ta farko.
2 Yin karatu a voye.
3 Xora hannun dama a kan na hagu (qablu), haka manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa aihi wa sallam ya koyar kuma haka ya umurta da a sa hannun dama a kan na hagu a wajen sallah. Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam bai tava yin sallah hannunsa a sake ba kuma su ma sahabbai ba sa sakin hannuwansu a wajen sallah.
4.      Yin sahu miqaqqe mai faxi yadda ake yin sahun salloli. Ba a matsewa  mammatsewa wajen sallar gawa bidi’a ce. Ana yin sahu ne  mai kyau kamar yadda Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam   ke yi shi da sahabbansa. Jabir bn Abdullahi ya ce, “manzon sallal Lahu alayhi wa aihi wa sallam ya yi wa  Najashi sallah, muka yi sahu-sahu.” Sahabi Jabir ya ce, “Na kasance a sahu na biyu ko na uku[149].  
5.      Adadin sahun sallar  Gawa su kai uku. Komai qarancin masallatan.
Kuma ana yin sahu ne yadda ake yin sahun salloli, ba a matse sahu ana yin sahu  ne da faxi.
6.      Karatun surah: Karatun sura a sallar gawa Sunna ne.
7.       Yin sallah da takalmi: Ba a cire takalmi wajen  yin sallar gawa. Wasu malaman suna gani cire takalmi wajen sallar gawa bidi’a ce,  Albany ya kawo wannan maganar a cikin Ahkamul Jana’iz.
YADDA AKE YIN SALLAR GAWA[150]
 Liman zai tsaya a saitin kan gawar idan gawar ta namiji ce. Ga misali:          
 Amma idan mace ce liman zai tsaya a tsakiyar ta, su kuwa mamu zasu yi sahu a bayan liman kuma su daidaita sahun kamar dai sahun kowance sallah. Babu matsewa, kuskure ne babba mammatsewar da ake yi wajen sallar gawa. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya koyar da a yi sahu yadda ake sahun salloli. Yin haka shi ne sunnah savanin haka bidi’a ce. Sannan sai ka xaga hannunka wajen kabbarar harama. Bayan ka yi kabbarar haraman sai ka sa hannunka a qirjinka, ba a sakin hannu a kowace sallah haka sunnah ta tabbatar.[151]
 Da zarar an yi kabbarar harama sai a yi a’uziyya da basmala                                                           
 أعوذ بالله من الشيطان الرجيم من همزه ونفخه ونفثه  بسم الله الرحمن الرحيم
Basmalah wato a karanta Auzu billahi da Bismillah a asirce, daga nan kuma sai a karanta suratul fatiha, ba a karanta addua’r istifta’i kamar yadda Imam Nawawi ya ce a cikin RiyadusSalihin.
Kabbara ta biyu: bayan ka yi kabbara ta biyu sai ka yi salati ga manzon Allah (SAW) wato ka ce:
اللهم صل على محمد وعلى آل محمد كما صليت على  إبراهيم وعلى آل إبراهيم إنك حميد مجيد اللهم بارك على محمد وعلى آل محمدكما باركت على إبراهيم وعلىآل إبراهيم إنك حميد مجيد
Allahumma salli ala Muhhammad wa ala ali  Muhammad kama sallaita ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim innaka hamidun majid, Allahumma barik ala muhhammad wa ala ali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim innaka hamidun majid.
KABBARA TA UKU : Bayan ka yi kabbara ta uku sai ka yi addu’a ga mamacin wato sai ka ce:
اللهم اغفرله وارحمه وعافه واعف عنه وأكرم نزله ووسع مدخله واغسله بالماء والثلج والبرد ونقه من الخطايا كما ينقى الثوب الأبيض من الدنس وابدله دارا خيرا من داره وأهلا خيرا من أهله وزوجا خيرا من زوجه وادخله الجنة واعذه من عذاب القبر ومن عذاب النار  
  Allahumma agfir lahu warhamhu wa afihi wa afu anhu wa akrim nuzulahu, wa wassi’i mudkalahu wagsilhu bil ma’i was salji, wal baradi wanakkihi minazzunibi walkhadaya kama nakkaita saubi-abyad mina ddanasi, wa ab dilhu da’ran khairan mindarihi wa ahlan khairun min ahlihi, wa zaujan khairan min zaujihi, wa adkhilhul Jannata wa aizhu min azabil kabar.
KABBARA TA HUXU: Bayan kabbara ta huxu sai ka sake yin addu’a  sai ka/ki ce:
اللهم اغفر لحينا وميتنا، وحاضرنا وغائبنا، وصغيرنا وكبيرنا، وذكرنا وأُنثانا، اللهم من أحييته منا فأحيه على الإسلام، ومن توفيته منا فتوفه على الإيمان، اللهم لا تحرمنا أجره ولا تضلنا بعده
((اللهم أعذه من عذاب القبر))
Allahumma agfir lihayyina wa miyyitina wa shahiduna wa ga’ibina wa sagirina wa kabirina wazakarina wa unsana Allahumma man ahyaytuhu minna fa ahyihi alal islami waman tawaffaitahu minna fatawafahu alal imani, allahumma la tuharrimna ajarahu, wa taftina ba’adahu. Da zazar an gama wanna addu’a sai ayi sallama daga nan kuma sai a xauki gawan zuwa makabarta
Ko ka karanta wannan adduar:
اللهم اغفر لحيِّنا وميِّتنا، وشاهدنا وغائبنا، وصغيرنا وكبيرنا، وذكرنا وأنثانا، اللهم من أحييته منا فأحيه على الإسلام، ومن توفيته منا فتوفَّه على الإيمان، اللهم لا تحرمنا أجره ولا تُضلَّنا بعده
IDAN GAWAR  MACE CE
Idan gawar da za a yi wa sallar ta mace ce, to sai a yi amfani da lamirin mace wajen yin addu’ar, wato idan ka yi  kabbara ta uku misali, sai ka ce:-
            Allahumma agfir laha warham ha har zuwa qarshe wato duk wurin da hu yake sai amayar dashi ha.
SALLAMA: Sallama a sallar   gawa ya halasta, ka taqaita  a kan sallama xaya. Ya tabbata a hadisi ingattace  daga Abu Hurairah Allah ya qara masa yarda, ya ce “Haqiqa manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi ma gawa salla, ya yi kabbara guda huxu, sannan ya yi sallama xaya.[152]
أبي هريرة رضي الله تعالى عنه : " أن رسول الله صلى الله عليه وسلم صلى على جنازة ، فكبر عليها أربعا ، وسلم تسليمة واحدة
Amma sallama biyu ma ta inganta. Ana iya yin sallama biyu wajen sallar gawa, kai ko ba sallar gawa ba ya halasta ka yi sallama xaya amma kar a manta sallama biyu ta fi inganci. Kuma kar a manta sallamar a hankali ake yi ba a yi  da qarfi kamar a sauran salloli.

 IDAN GAWAR TA YARO CE KO YARINYA
Idan gawar da za a yi sallar yaro ne ko yarinya waxanda ba su balaga ba. Za a yi addu’a ne kamar haka:-
Allahumma ij’alhu faraxan wa zukharan li walidaihi wa shafi’an mujiban allahumma sakkil bihi mawazinahuma wa a’azzim bihi ujurahuma wa alhikhu bi salihil mu’uminina waja’alhu fi kafalati ibrahima wakihi birahmatika min azabil jahim.
Ko kuma ka ce:
((اللهم اغفر لحينا وميتنا، وحاضرنا وغائبنا، وصغيرنا وكبيرنا، وذكرنا وأُنثانا، اللهم من أحييته منا فأحيه على الإسلام، ومن توفيته منا فتوفه على الإيمان، اللهم لا تحرمنا أجره ولا تضلنا بعده.

Sannan ka karanta wannan adduar:
 (اللهم اجعله لنا فرطاً وسلفاً وأجراً.
((اللهم اغفر لوالديه وارحمهما
Wato za a yi wannan a madadin wancan addu’ar da ake yi bayan kabbara ta uku.

WANDA YA ZO A MAKARE
Wanda ya zo ya tarar da an fara sallar gawa, to daga zuwan sa  zai yi kabbara  ya dasa daga inda ya same su, idan liman ya yi sallama sai ya yi sauri ya rama kabbarorin da suka kubce masa. Idan zai yiwu ya rama ba tare da an xauke gawar ba to sai ya yi addu’ar a bayan kowace kabbara. Amma in har za a xauke gawar ba tare da ya gama ba to zai gaggauta yin kabbarorin ba tare da ya yi wata addu’a ba.
MATASHIYA
ü  Ana so idan mutum ya rasu a yi gaggawar sanar da mutane domin su zo su halarci sallarsa. Sannan kuma ya kamata a jira mutane su taru sa’annan a yi sallar  idai jiran ba zai tsananta ba. Saboda Annabi ya ce babu wani mutun da zai rasu a sami al’umma cikin musulmi waxanda zasu kai su xari (100) dukkanin su suna riqo da sunnah face Allah ya ba su ceton sa.
ü  Sannan kuma ya halasta mata su yi sallar gawa wato su yi sahun su a bayan sahun maza kamar yadda ya tabbata cewa mata sun halarci janazar Ummukulsum Bintu Aliyu matar sayyidina Umar[153] Allah ya qara masu yarda amin.[154]
ü  Sannan kuma sun samu su yi sallar su kaxai ba tare da maza ba, wato a kai masu gawar cikin gida ko masallaci su yi wa gawar salla su kaxai. Bayan sun gama sai a fito da gawar waje maza su yi mata salla, kamar yadda Nana Aisha ta yi wa  sahabi Sa’ad ibin Abi Waqqas.[155]
ü  Ya halasta a yi wa jariri salla matuqar ya fito duniya da ransa.
ü  Hakanan ma varin da ya kai wata biyar ko huxu shi ma ya halasta a yi masa salla, sai a yi wa mahaifiyar addu’a ta alhari. 
ü  Limamin da zai ma gawa sallah kar ya manta  ya gaya ma jama’a abin da ake karantawa,kabbaran farko akarata fatiha da sura kabbara ta biyu akaranta salati Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam kabbara ta uku ayi ma gawar addua ta alheri da fatan tsira kabbara ta huxu a yi gava xayan musulmai addua.
                                        

 XAUKAR GAWA
Imam Musulmi ya fitar da  hadisi daga Abu-Huraira  Allah ya qara masa yarda ya ce, “Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘wanda ya fita tare da gawa daga gidanta har aka yi mata salla sannan ya raka ta ya zuwa maqabarta, har aka rufe ta yana  da yankin lada guda biyu ko wani yankin lada guda xaya,  girmansa kamar girman dutsen Uhudu. Wanda  aka yi mata (gawa) salla ya koma gida bai je aka rufe ta ba, yana da yankin lada guda xaya girmansa kamar dutsen uhudu.[156]
Hakqi ne na xan uwa Musulmi idan ya rasu a raka shi ya zuwa maqabarta. Wasu Malamai suna ganin dole ne gaba xayan Musulmi su raka shi kamar dai yadda hadisin Muslim ya nuna haqqin Musulmi ga xan’uwansa guda shida ne. A cikin haqqin; in ya rasu ka raka gawarsa.[157]
Wani hadisin Manzon Sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam cewa ya yi, “Ku raka gawa, rakata  yana tuna maku lahira.”[158]
Malamai dai ma’abota ilimi  sun ce raka gawa zuwa Maqabarta Faradhul kifaya ne ba dole ba ne, ba sai kowa ya rakata ba. Amma da za a je baki xaya to ya fi dacewa da alheri, kuma shi ne abin da aka fi so. Xaukar ta da raka ta ba dole ba ne kowa ya yi,  sai dai sunna ce mai qarfi.[159]

SIFFAR YADDA AKE XAUKAR GAWA
1.      Bayan an gama yi wa gawa wanka sai a  naxe ta a likafani kamar yadda bayani ya gabata, a sa ta a cikin makara fuskanta na kallon sama, sannan a rufe gawar idan gawar ta mace ce a rufe makarar baki xaya. Haka  aka yi  ga Fatimatu Zahara’u ‘yar Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam da Zainab bintu Jahashi Ummul Mumin.[160] amma namiji ba za a yi masa yadda aka yi wa mace ba.
2.      Ana so masu xaukar gawa  su zama mutane huxu mustahabbi ne ko kuma su kai shida amma huxun dai shi ya fi. Yin hakan sunna ce ya zama mutane huxu, hadisin ibn Masud  ya nuna mana haka [161].
3.      Mutane huxu za su xauki gawar biyu a gaba biyu a baya. Yin haka  ita ce sunna.[162]
4.       Umurni ne in an xauki gawa a yi sauri da ita. Manzon Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya yi umurni da a riqa sauri da gawa idan an xauke ta.[163]
5.      Ba a zama har sai an saka ta cikin qabari.[164]
6.      Ana son waxanda suke raka gawa su raka ta suna masu qasqantar da kansu ga Allah suna  masu tunananin Rasuwa.
7.      Ba a Zama idan an xauki gawa har sai an saka ta a qabari.[165]
8.      A wuya ake sa gawa idan an xauke ta. Wannan ita ce sunna kamar  yadda Abi-Sa’idu Kudiri ya kawo hadisin da ke nuna haka.[166]
Mata ba sa raka gawa ya zuwa maqabarta sai dai ya halasta su raka ta ya zuwa waje  a yi  mata salla amma zuwa maqabarta bai halasta a gare su ba.[167]
Ya halasta mai raka gawa ya wuce gabanta ko bayanta duk sun tabbata ga Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam sai dai biyo bayanta shi ne mafifici   wato a sa gawa a gaba  masu rakata suna biye.  Wato tana gaba kuna biye. Domin ladar bin baya wajen raka gawa  kamar  kun yi salla ne a cikin jam’i. Idan kuwa kuka shiga gabanta, ladarku ladar wanda ya yi salla shi kaxai ne.[168] Zamu iya  fahimtar  bin bayan gawa shi ya fi da a shiga gabanta.
Ya halasta a hau keke ko mashin ko doki ko jaki wajen raka gawa amma dole ka jira mutane  su yi  gaba sannan ka biyo baya  kar  ka hau abin hawanka,  haka ya faru zamanin Annabi Sallal Lahu alayhi  wa alihi wa sallam an kawo masa abin hawa sai ya qi hawa. Bayan da jama’a suka wuce sai ya biyo bayansu  a kan abin hawansa sai aka tambaye shi sai ya ce bai dace ba in hau abin hawa alhali malai’ku na qasa (Wato su ma suna raka ta kuma bayanta suke bi).  Bayan da suka wuce sai ya biyo bayansu.[169]

SHIN XAUKAR GAWA A KAN ABIN HAWA YA HALASTA?
Xaukar gawa a kan abin hawa, wato a keve mota ta musamman domin xaukar gawa ya zuwa maqabarta kamar yadda waxansu garuruwa suke yi, babu ko shakka yin haka ba shari’a ba ne kuma kuskure ne babba ya sava wa abinda shari’a ta koyar kamar ta hanyoyi kamar haka:
1.      Al’ada ce ta kafirai xaukar gawa a mota. Kuma Musulunci ya umurce mu da mu sava wa kafirai. Kuma bai halasta koyi da su ba, ko ta ko’ina. Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce wanda ya kamanta kansa da wasu mutane yana  tare da su.[170]
2.      Kuma xaukar gawa a mota bidi’a ce cikin ibada ta sava wa sunnar da ta ce a xauke ta a wuya/kafaxa haka hadisi ya ce. Amma sanya ta a cikin mota bidi’a ce kuma hadisi ya nuna mana dukkan bidi’a  vata ce. Sai dai lalura.
3.      Tanasa a samu qarancin masu raka ta wanda sunna ta umurci  da a raka ta.
4.      Ta kore ma mutane tuna lahira na wajen rashin xaukar ta a kafaxa kamar yadda hadisi ya nuna.
Ibn Abidin ya ce xaukar gawa a dabba makaruhi ne in ba da uzuri mai qarfi ba, kamar nisan maqabarta ya ce babu laifi a sanya ta a jaki a kai ta mutane na bin ta a qasa amma banda mota.[171]
Ibn Taymiyya shi ma ya ce bai dace xaukar gawa ba a dabba ba. Xaukar ta a wuya ita ce Sunna. [172]

ABUBUWAN  DA SUKA HARAMTA A RAKA GAWA DA SU
A kwai abubuwan da suke haramun ne raka gawa da su ko kuma ana tafiya ana yin su, duk ba su halasta a yi su ba. Yana da kyau ‘yan’uwa mu kiyaye domin dacewa da koyarwar Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam da kuma nema wa mamaci alheri. Duk lokacin da aka yi sunna wajen sha’anin gawa, yana shafar gawar, haka ita ma bidi’a in aka aikata ta sharrin ta zai iya shafar mamacin. Don  haka ya dace  a kula. Ga abubuwan da shari’a ta hana a raka gawa da su kamar haka:
·        Raka gawa da wuta ko garwashin wuta.[173] Kamar yadda Indiyawa suke yi. Wannan babu savani cewa haramun ne raka gawa da wuta ko bakin wuta. Haka ita ma fitillar qwai ta shiga cikin wannan hukunci da kyandir da duk abin da zai xauki sunan wuta.[174]
·        Raka gawa ana zikiri shi ma haramun ne.[175]
·        Raka gawa ana karatun qur’ani shi ma haramun ne.[176]
·        Raka gawa ana Allahu Akbar shi ma haramun ne.
·        Raka ta ana waqa da kixa da sarewa irin yadda Kiristoci da masu bin addinin Shi’a suke yi da Sodoji suke yi shi ma bai halasta ba. Wannan shi ne mafi muni da sharri, a raka gawa ana waqa da kixa wannan a fii yake koyi ne da kafirai maqiya Musulunci.[177]
·        Raka ta ana surutu shi ma bai halasta ba, abin da yake daidai raka ta ana yin shiru.[178]
·        Bai halasta Musulmi ya raka gawar Kafiri ba.[179]
·        Kuma shi ma Arne bai Halasta ya raka Musulmai ba.
·        Babu kyau shiga maqabarta da takalmi ko tsakanin qabari.[180]
QABARI
Wajibi ne rufe gawa ko da kuwa ta Kafiri ce shi ma za’a rufe shi saboda xan Adam yana da daraja ko da Arne ne, Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya sa an rufe manyan kafirai da aka kashe a yaqin Badar.[181]
Dole ne rufe mutum idan ya rasu bai dace a bar shi a fili ba tare da an yi masa qabari ba. Sannan ba a rufe Musulmi a Maqabartar Arna ko kafirai a maqabartar Musulmai ba kafirai za’a rufe su a Maqabartar su ta Arna Musulmai a tasu ta Musulmai.
LOKUTAN DA BABU KYAU A BISNE GAWA
Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya hana rufe matattu a waxannan lokutan:
ü  Lokacin da rana ta ke fitowa.
ü  Lokacin da rana ta ke tsakiya.
ü  Lokacin da rana zata faxi ta yi ja-jawur.
ü  Babu kyau rufe gawa da daddare sai dai larura mai qarfi.[182]
Ba a rufe mutum a gida, abinda sunna ta nuna shi ne rufe mutum a maqabarta kamar yadda Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya riqa yi wa sahaban sa. Ba a sami wani sahabi da ya ce a rufe shi a gida ba. Don haka rufe mutum a gida bai halasta ba.
·        Babu kyau rufe mutum a masallaci, haramun ne.[183]
Kuma duk inda mutum ya rasu anan ake rufe shi haka shari’a ta nuna. Manzon Allah ya ce qasa ta tsarkake kowa, duk inda mutum ya rasu a nan a ke rufe shi ba za a ce sai an dawo da shi gida ba. Duk garin da ka rasu a nan za a rufe ka,  hadisin Huzaifatu Yaman ne ya faxe shi.[184]

IDAN MACE KIRISTA TA MUTU DA CIKIN MUSULMI[185]
Idan mutum musulmi ya auri kirista sai ta mutu da cikin Musulmi, to ba za a kai ta maqabartar Arna ba ba kuma za a kai ta ta Musulmai ba, za a rufe ta tsakanin Maqabartan Musulmai da ta Arna. Sannan kuma bayanta yana kallon  Ka’aba(gabas), yadda shi kuma jaririn ko jaririyar da ke cikin nata   zai  fuskanci  alqibla.[186] (idan da ciki)

YADDA AKE YIN QABARI
Ana so a yi qabari da zurfi da kuma faxi a kuma kyautata shi ba a so a yi qabari mara zurfi kuma mai qunci Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi umurni da a yi qabari mai zurfi wajibi ne. An Samo hadisi daga Hisham wanda yake nuni a kan wajabcin gina qabari da zurfi da kuma faxi.[187]
 wata ruwayar  a gaban manzon Allah sal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ake gina qabari, sai ya ke umurtar masu gina qabarin da su faxaxa shi kuma su kyautata shi.[188]
   Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku faxaxa wajen kansa (gawa) kuma ku yalwata wajen qafafuwansa.[189]
Zamu fahimci kuskuren masu gina qabari a yau yadda suke daidaita qabari wajen qafa da kai da ciki duk suna yin su dai-dai. Yin haka kuskure ne ya kamata mu gyara, da kai da qafafuwa su fi faxi kamar yadda Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi umurni da a yi. Kuma yana da kyau a ce masana addini su ne suke ginin qabari, yin qabari da zurfi da faxi shi ne sunna, sai mu gyara. Allah ya ba mu ikon gyarawa. A qalla ana so zurfin qabari ya kai kamar qirji ko cibiya kuma ana yin qabari a jere wato a yi a layi..
Bayan mun ga  ana so a yi qabari da zurfi da kuma faxi, qin yin qabari da zurfi da faxi sava wa addini ne. To sannan kuma yana da kyau mu gane qabari  ya kasu kashi biyu, akwai:
1.      Lahadu
2.      Shuqqu
·        Lahadu shi ne qabarin da za a gina shi da faxi da zurfi sannan a qwaqule bangon gabas (Qibla). A bangon qibla za a sanya mutum, wannan shi ne lahadu.
·        Shuqqu shi ne qabarin da za a gina   tsakiyarsa ko kuma mu ce wanda ake ce ma uwa da ’ya (Shi ne qabarin da aka saba yi a qasar Hausa suna ce masa uwa xiya).

WANNE NE MAFIFICI?
Ba shakka Lahadu shi ne mafifici, kuma shi Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi umurni da Musulmi su yi wa matattun musulmai  idan sun rasu.
Lahadun shi ne  aka yi wa Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam.
Sahabi Sa’ad bn Abi Waqqas ya faxa a yayin rashin lafiyarsa ya ce, “Idan na mutu ku yi mani Lahadu, kuma ku sanya mani bulo (Tubali) kamar yadda aka yi wa Manzon Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam[190].
Babu shakka Allah yana zava wa Annabinsa sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam abinda ya ke mafifici, don haka  da ya rasu aka gina masa qabarin  Lahadu kamar yadda Sahabi Annas ya labarta mana. Ya ce da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya rasu akwai masu sana’ar ginin qabari a Madina, xaya yana Lahadu xaya kuwa yana Shuqqu. Sai suka yi istikara a kan Allah ya zava masu wadda ya fi. Sai suka aika, sai kuwa Allah ya sa saqo ya ishe mai yin Lahadu, sai aka yi wa Ma’aiki Sallal Lahu layhi wa alihi wa sallam Lahadu.[191]
A wata ruwayar Manzon sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Lahadu ne namu mu  Shuqqu kuwa na wanxanda ba mu ba”[192].
Babu savani kan qabarin Lahadu shi ne mafifici shi ne kuma ya kamata duk Musulmi ya yi wasiyya da in ya mutu a yi masa.  Amma  in babu halin yin lahadu babu laifi in aka yi Shuqqu.

MATASHIYA
Babu laifi ba ne sai dai ba haka aka so ba, a yi wa mutum Shuqqu. Yana da kyau mai karatu ya duba littafin Imamun Nawawi ya yi bayani mai daxi mai kuma gamsarwa.[193]
·        Yayin da za a saka gawa a qabari ana karanta wannan addu’ar:
بسم الله ، وعلى سنة رسول الله،أو :ملة رسول الله صلى الله عليه وسلم
Ko kuma ka ce:
باسم الله ، وبالله على ملة رسول الله صلى الله عليه وسلم
Sunna ce a shigar da gawa qabarin ta ta qafa (ta fuskar qafar kabarin ba ta kai ba). Babu kyau a ajiye gawa a yamma sannan a xauko ta a sanya ta qabari, yin haka sava wa koyarwar Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ce.[194]
 Ana saka gawa ta vangaren dama jikinta  na fuskantar qibla.[195]
·        Ana saka gawa  a hankali ne ta tsagin dama tana mai kallon qibla.[196]
·        Dangin mamacin (gawa) ke saka ta a qabari, idan mace ce kuma mijinta  ya nemi taimakon babanta ko yaranta. Amma bai kamata wani ya saka gawa qabari ba in dai ba dangin gawar ba ne sai dai in babu kowa daga cikin dangin.
·        Wanda ya sadu da iyalinsa a daren da ya gabata bai halasta ya saka gawa qabarin ta ba, ko da kuwa matarsa ce.[197]
·        Amma in ba su kiyaye qa’ida ta sunna ba gara a sami waxanda suka san yadda ake yi a sunna su saka ta a qabarin.

      ME   AKE RUFE QAVARI DA SHI?
Yana da kyau koda yaushe mu yi aiki da koyarwar Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, yin haka shi ne tsira kuma shi ne zai kai mu ga nasara.
Zamanin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam abinda ake rufe qabari da shi shi ne tubali ko bulo, haka hadisin Sa’ad ibn Abi Waqqas ya nuna da wasu ruwayoyi ingantattu, amma banda tukunya. Kuma ya tabbata za a iya sa ganye a rufe qabari da shi ko itace banda tukunya. Sanya tukunya ba shari’a ba ne al’ada ce.
Kuma ya tabbata za a iya sanya ciyawa, domin lokacin Fathu Makka Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam bayan an ci Makka da yaqi wato bayan Fathu Makka ya hana sare itatuwa saboda Makka harami ce. Sai Abbas ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam banda Iywa (wata irin ciyawa ce wadda ake Asabari da ita)?” Sai Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce banda ita(Iywa). Abbas ya ce, “Domin muna rufe mattattun mu da ita kuma muna rufin xaki da ita.”[198] Ishara, ashe da ita a ke rufe qabari. Ya kamata mu gyara, mu koyi yadda sunna ta koyar ba tukunya ba. Allah ya bamu ikon gyarawa.
Bayan an sa bulo ko tubali ko itace ko ciyawa, sai a tura qasa sau uku ta vangaren kansa (gawar), haka Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yake yi.[199]
ü  Haramun ne saka mutum cikin akwati a rufe shi cikinsa, wannan koyi ne da kafirai.[200]
ü  Kana iya sa dutse a qabarin xan’uwanka don ka gane qabarinsa saboda zuwa ziyara a gare shi, amma ba zaka sa sunansa ba, wannan haramun ne rubutu a qabari.[201]
ü  Xaga qabari misalin tiqa xaya kar ya wuce tiqa xaya, haka hadisin Jabir ya yi mana bayani.[202]Manzon Allah  sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya hana xaga qabari ya wuce tiqa xaya tsakanin sa da qasa. Ya umurci sahabi Aliyu Allah ya qara masa yarda da ya je ya daidaita  duk qabarin da  bisan sa ya wuce tiqa xaya.[203]
Idan ka kalli qaburburan mu za a ga sun sava wa koyarwar Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Yadda ake xaga shi ya yi bisa wannan kuskure ne, yana da kyau mu gyara. Ba dole ba ne duk qasar da aka gino sai an mayar da ita.
Imamul Qurxubi ya yi magana mai gamsarwa kuma mai kyau kan rashin halascin qabari ya wuce tiqa xaya tsakaninsa da qasa. Ya ce duk qabarin da ya wuce tiqa xaya tsakaninsa da qasa a baje shi ya koma tiqa xaya tsakaninsa da qasa. Yana da kyau mai karatu ya duba suratul Kahafi a Tafsirinsa.

RABA QASA
Akwai wani abu da aka saba da shi a qasar Hausa wajen ginin qabari. Idan aka zo ginin qabari zaka ga ana raba qasa, Jar qasa da Baqa wato qasar sama daban na sama da ban wannan aiki ba dai-dai ba ne bidi’a ce. Ya kamata  mu gyara domin bidi’a komin qanqantar ta sharri ne, kuma sava wa Annabi Sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ne. Shi ya koyar da mu yadda ake yin qabari bai kuma ce a raba qasa ba.
Haka nan babu kyau yin ma qabarin siminti ko gini,  koyi ne da kafirai.

RUFE MUTANE BIYU A QABARI XAYA
Babu laifi in an haxa mutane biyu ko fiye da haka a qabari xaya, an samo ruwaya daga Jabiri ibn Abdullahi ya ce Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya kasance yana haxa mutane biyu a cikin likafani xaya. Sai ya tambayi wanda ya fi karatun qur’ani, sai ya fara sa shi a lahadu sauran kuma su biyo bayansa.[204]
Babu laifi  haxa mutum biyu ko fiye da haka a qabari xaya in buqatar haka ta taso.

HAXA MACE DA NAMIJI A QABARI XAYA
Babu laifi idan aka haxa namiji da mace a qabari xaya saboda lalura. An samo Asari daga Wasilatu ibn Asqa’i Allah ya yarda da shi ya kasance idan zai rufe mace da namiji a qabari xaya yana sanya namiji a bangon qilba (Gabas), sai kuma ya sanya mace a bayan namijin.[205]
Shi kuma Imam shafi’i ya ce  haxa namiji da mace a cikin qabari xaya  bai kamata ba, sai dai in lalura. ya ce in dai lalura ce to babu laifi sai a  haxa  amma namiji ya kasance a gaba ita kuma a baya. Sai a sanya turvaya wadda zata raba tsakanin shi da ita.[206]
ME AKE YI BAYAN AN GAMA RUFE GAWA?
Addu’a bayan an gama rufe mamaci,  ana tsayawa a yi masa addu’a. Yin addu’a sunna ce kuma wannan addu’a a tsaye ake yi ba a zaune ba. Ana so gaba xayan jama’a su kalli gabas, kuma duk wanda ya je maqabarta ake so ya yi masa addu’a, ba wai  a keve waxansu mutane daban ba a ce su ne wai zasu yi masa addu’a ba. Yin haka bidi’a ce a zavi waxansu daban da za su yi addu’a. Manzo Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya kasance idan an gama rufe gawa yana tsayawa yana yi mata addu’a, kuma ya kasance yana umurtar sahabbansa da su tsaya su yi mata addu’a. Sai dai kuma kowa yana yin ta ce ne daban ba a yi cikin jam’i ba, yin addu’a cikin jam’i babu kyau  bidi’a ce.
Abin baqin ciki yau zaka ga masu da’awar cewa su Ahlussuna ne zaka ga in an gama  rufe gawa suna yin addu’a cikin jam’i. Wannan gaskiya  abin kunya ne a ce mai  danganta kansa da sunna yana addu’a a jam’i bayan rufe gawa, alhali kuma ba  ya yin haka a masalaci bayan gama Sala. Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yana cewa ku riqa roqa wa xan’uwanku gafara ku roqa masa sabati yanzu za’a tambaye shi.[207]
Sahabi Sa’ad bn Abi Waqqas ya ce wa yaransa idan na  rasu ku tsaya a qabarin kuna yi masa addu’a  kwatankwacin  yadda za a yanka raqumi a fexe shi a raba namansa. Ya ce ku yi haka kuna yi ma ni  addu’a.
Allah kaxai ya san bakin da yake na kirki, don haka keve waxanusu wajen addu’a ga gawa bidi’a ce. Ana so kowa ya yi      tasa addu’ar haka sunna ta tabbatar. Ba a samu Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi addu’a a jam’i bayan rufe gawa ba, su ma sahabbai ba a samu ba, to ina muka ga mu mu yi a jam’I, kuma muna da’awar sunna? Allah ya ba mu ikon gyarawa.[208]

DAFA ABINCI GA DANGIN MAMACI
Musulunci ya koyar da tausayawa hatta ga dabbobi. Har ila yau kuma yana daga cikin tsausayawa da kyautatawa a dafa abinci a aika da shi gidan da aka yi rasuwa. Yin haka sunna ce kuma kyautatawa ne kuma akwai lada mai yawa. An samo hadisi daga AbdulLahi ibn Ja’afar ya ce Manzon Sallal Lahu alyihi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku dafa wa iyalan gidan Ja’afar abinci domin haqiqa abin  al’amari ya same su  mai shagaltar da su  ya zo masu.[209]
   Haka nan ma an samo daga Nana A’isha Allah ya qara mata yarda, ita ma ta kasance tana dafa abinci ga gidan da aka yi rasuwa. Ta ce na  kasance na ji Manzon Sallal Lahu alyihi wa alihi wa sallam yana umurta ta da yin  haka (wato dafa abinci ga gidan da aka yi rasuwa).[210]
Wannan sunnar ta xan yi rauni. Ya kamata a raya ta, ko ma don samun lada. Ga kuma qara soyayya ga juna da qara danqon zumunci ga kuma raya umurnin Manzon Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam.
Amma banda masu zaman amsar gaisuwa, su ba za  a ba su wannan abincin ba. Domin su zaman bidi’a suke yi. Mun sani cewa zaman amsar gaisuwa bidi’a ce,  zaman amsar gaisuwa harmun  ne. Za mu ga bayani a gaba in sha Allah.

YIN WA’AZI A MAQABARTA
Ya tabbata yin wa’azi a maqabarta yayin rufe gawa ko bayan rufe ta domin a tunatar da mutane Rasuwa, kuma su gane su ma zasu zo wannan gida, kuma aikin su ne kawai zai bi su. Haka kuma a tunatar da su abinda zai biyo bayan Rasuwa. Babu laifi a wannan lokacin ko da an zauna, amma a kiyaye kar  a zauna a qabari. Kuma ana so mai wa’azin ya kalli gabas.  Hadisi ya zo da ga  Manzon Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya yi wa’azi wajen rufe gawa a maqabarta, ya kuma tsoratar game da a azabar qabari. Ya ce mu nemi tsari daga  azabar qabari[211].
Gaskiya a halin yanzu muna tsananin buqatar tunatarwa a maqabarta kuma ga shi Sunna ce yin haka. Don Allah muna roqon duk wanda zai iya tunatarwa to ya tunatar da mu, musamman game da yadda mutane suka manta da Rasuwa, Yana da kyau mai karatu ya duba hadisin da Annabi Sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ya tunatar a maqabarta.

ABUBUWAN DA SUKA HARAMTA BAYAN AN RUFE GAWA
1.      Fidda’u shirka ce kuma faxa ne da koyarwar Annabi sallal Lahu alaihi wa alihi wa salam.
2.      Addu’a a cikin taro a maqabarta.
3.      Yin gini a qabari.
4.      Yi wa qabari siminti.
5.      Kunna fitila a qabari.
6.      Karatun qur’ni ga gawa a maqabarta ko a gida bidi’a ce kuma jawo wa wannan mamacin bala’I ne.[212] Haka nan ma yin haka sava wa Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ne, domin ya hana karatu a maqabarta wani hadisin cewa ya yi, “Ku karanta suratul Baqara a gidajenku. Kada ku maida gidanku Maqabarta”[213].
ishara a fili ba a karanta qur’ani a maqabarta domin ya ce kada ku maida gidanku maqabarta. Ashe a fili yake ba a karatun qur’ani a maqabarta.
Wata  ruwayar cewa  ta yi, “Ku yi sallar (Nafila) a gidanku kada ku maysr da gidajenku  maqbarta”.[214]
Sheikh Ibn Abiy Hamzah ya ce, “Karatun qur’ani a maqabarta bidi’a ce ba sunna ba ce.[215]
Sheikh Dardin Ya faxa yake cewa a cikin littafin sharhus sagir ya ce abin qyama ne karatun qur’ani  ga matattace ko a maqabarta domin ba shi cikin aikin salaf abinda yake aikin magabata yi wa gawa addu’a ba karatun qur’ani ba[216].
 Haka nan ma ya zo a cikin Hashiyatil Adawi da ke nuna haramcin karatun qur’ani a maqabarta ga gawa.
Imam Ahmad ibn Hambal ya ce karatun qur’ani a maqabarta bidi’a ce. Wannan ita ce maganar baki xayan Sahabban Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Ya cigaba da  cewa  haka nan ma karatun qur’ani ga gawa shi ma bidi’a ce.[217]
Sheikh Istanbuli shi ma ya ambata cewa karatun qur’ani a maqabarta bidi’a ce. Yana da kyau mai karatu ya nemi litattafin Sheikh Ahmad Abdussalam Asshaqiriyu wanda Istanbu’i ya yi ma ta’aliqi.[218]
Imamu Shaxibi ya faxa cewa karanta qur’ani a gaban gawa ko a maqabarta bidi’a ne.[219]
7.      Yanka  a wajen qabari shirka ce duk wanda ya yanka kaza ko rago ko sa a maqarbarta ya yi shirka Allah ya shiryi masu yin wannan mummunan aikin.
8.      Kiran Sunan wanda ya rasu a ce ma shi ya faxi  kalmar shahada, yin haka bidi’a ce.
9.      Rubuta sunan matacce a jikin qabari bidi’a ce kuma koyi da kafirai ne.
10. Xibar qasar qabari domin neman tuburraki shirka ne.
11. Bayar da sadaka a maqabarta bidi’a ce.
12. Yin ta’aziyya a maqabarta bidi’a ce.

ME KE AMFANAR MUTUM BAYAN RASUWARSA?
A kwai abubuwan da shari’a ta bayyana mana ko bayan  mutum  ya rasu  suna amfanar sa yana qabarinsa, ana rubuta masa lada ga wasu daga cikin su kamar haka:
1.      Addu’a: Wannan addu’ar ta iyalinsa ce ko abokansa ce ko yaransa.[220]  wani hadisin kuma Manzon Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Addu’ar da mutum ya yi ga xan’uwansa   bai sani ba, karvavviya ce.[221]
2.      Biya  masa bashin da a ke bin sa.
3.      Biya masa azumin da a ke bin sa.[222]
4.      Aikin alherin da mamaci ya yi yana amfanar mamaci.[223]
5.      Sadaqatul Jariya (Wadda ya gina masallaci ko islamiya ko ya gina rijiya ko ya shuka itacen da ake shan ‘ya’yansa).[224]
6.      Ilimin da wani ya koyar mai amfani.
7.      Wanda ya bar Qur’ani ko ya bayar da kyautar sa.[225]
8.      Yin ma mahaifa ko mamaci aikin Hajji, ladan na zuwa gare su.
9.      Yin layya ga mahaifa bayan mutuwar su lada na zuwa gare su.
Waxannan su ne abubuwan da idan mutum ya same su yana qabari, to ana rubuta masa lada. Muna roqon Allah ya ba mu samun su.

TA’AZIYYA
Ya tabbata  a shar’ance idan mutum ya rasu a yi wa dangin mamacin ta’aziyya, ana yin ta’aziyyar ne da kalmomi masu daxi da za su faranta wa wanda aka yi masa rasuwar rai. Ba ma sai rasuwa  ba, duk abinda ya faru da wani xan’uwa musulmi na musiba duk ya tabbata ana yi masa ta’aziyya da kalmomi masu daxi da zasu faranta masa zuciyarsa da  kuma lallashin sa da ya yi haquri ya qara yarda da  qaddara.
Manzon Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam idan zai yi wa wani ta’aziyya  yana cewa;[226]
إن لله ما أخذ ، و  لله  ما أعطي ، وكل شئ عنده إلى أجل مسمى
Kuma ka kira sunan mamacin ka ce Allah ya rahamshe shi Allah ya ba shi aljanna. Ka dai faxi kalmomi masu daxi waxanda suka dace, kuma ba a qayyade ta’aziyya ba a ce kwana uku ko sati xaya. Duk  lokacin da a ka yi rasuwa har shekara, ya tabbata in ka haxu da wanda a ka yi wa rasuwar to kana iya yi masa ta’aziyya. Maganar iyakance ta’aziyya da kwana 3 wannan magana ba gaskiya ba ce ba kuma koyarwar Manzon Allah salla Lahu alayhi wa alihi wa sallam ba ce.

ZAMAN AMSAR GAISUWA
Yana daga cikin abin ban takaici da baqin ciki zaka ga jama’a sun shimfixa tabarma a kofar gida suna amsar gaisuwa. Kuma abin ban mamaki har da waxanda suke danganta kansu da sunna, sai ka rasa ina suka samo irin wannan aiki na zaman amsar gaisuwa. Yanzu abin ya koma har da shimfixa rumfa ( canoe fee) mutane suna zaune suna gulma da hirar siyasa, ka rasa inda suka samo wannan xanyen hukunci.
An tambayi Imamu Ahmad Ibn Hambal me zai ce game da masu zaman amsar ta’aziyya idan an yi rasuwa, sai ya ce, Wannan aikin maguzanci ne.” Ya yi  inkari mai tsanani.
Imamu Shafi’i shi ma ya ce wannan abin qyama ne. haka shi ma Auza’i ya ce  Sahabi Abduahi Bajali ya ce, “Mun kasance mu na qirga zaman amsar gaisuwa in an yi rasuwa,  xaya daga cikin abubuwan da Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya hana. [227]
Imamun Nawawi ya ce a cikin majmu’u, “Zaman da mutanen suke yi domin amsar gaisuwa  idan aka yi rasuwa a gida ko masallaci ko wani waje daban, ya ce yin  haka abin qyama ne.[228]
 Imamu Shafi’i :  ya faxi rashin asalin zaman amsar gaisuwa.[229]
Sheikh   Abubakar Jabir aljaza’iri ya faxa cewa zama a gida domin amsar gaisuwa bidi’a ce, ya nuna yin haka jahilci ne.[230]
Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Allah ya ji kansa da gafara  amin ya faxi acikin Tafsirin sa a cikin suratu Ahzab cewa zaman ansar gaisuwa ba addini bane  al’adace kuma ta sava ma koyarwar Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam, ya qara da cewa bidia ne kuma  ba daidai ba ne ya kamata duk musulmin kirki ya nisanci zaman ansar gaisuwa, har ya kawo misalin lokacin da aka kashe sayyina Hamza  Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam bai zauna ya anshi gaisuwa ba haka lokacin da Nana Khadijah Allah ya qara mata yarda ta rasu manzon Allah  sallalLahu alayhi wa alihi wasallam bai zauna amsar gaisuwa ba, Sahabbansa ba su zauna ansar gaisuwa ba  bayan ya rasuwar Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ba. Nemi kaset karatunsa na suratul Ahzab Allah ya jiqan Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Allah ya gafarta masa.
 zaman amsar gaisuwa ba addini ba ne, kuma yanzu  zaka ga an mayar da shi wajen cin  mutuncin jama’a  da hirar banza da gulma da hirar siyasa. Mutane ba sa tunanin maganganun da suke yi sun manta da Allah zai tambaye su maganganun da suke yi.  Allah ya ba mu ikon gyarawa amin.
Sheikh Hamidi Fakqi ya ambata a ta’aliqin da ya yi wa Bulugulmaram, ya ce zaman amsar gaisuwa kwana 3 ko fiye da haka ba addini ba ne bidi’a ce ta jahiliyya (Maguzanci ne), bidi’a ce da alfahari da riya da qarya.
Ibn Qaym  shi ma ya nuna babu kyau zaman amsar ta’aziyya idan an yi maka rasuwa, ya kuma nuna yin haka bidi’a ce.[231]
Sheikh Usaymin  yana ganin bai kamata mutum ya je inda aka shimfixa tabarma ana amsar gaisuwa  ba. Ya ce, “Kada ka je ka,  bari  in ka haxu da shi, sai ka yi masa ta’aziyya domin kada ka taimaka wa bidi’a. 
Sheikh Usaymin ya yi Magana mai gamsarwa da take nuni da haramcin zama a kofar gida ko masllaci ko wani waje domin ansar ta’aziyya a duba fatawar sa za a qaru sosai.
Kuma in ka tambayi Malamai za su gaya ma cewa ba inda aka ce a zauna akofar gida a karve gaisuwa tun daga  Qawa’idi har Muktas haka kuma littafan Hadisai ba inda aka yarda mutum ya zauna yana ansar gaisuwa in aikai masa rasuwa.
                                          وأحسن الهدي هدي محمد
ADDU’A
Addu’ar uku da bakwai da ta arba’in  da ta shekara duk ba  addini ba ne bidi’a ce, ko  ka ce asalin wannan addu’o’in  daga maguzawa yake, mu tambayi tarihin. ‘Yan bidi’a suna yin addu’ar 3 da 7 da ta  arba’in don neman abinci  ne su ma sun san cewa ba shi da asali. Abin da yake daidai ko da wani lokaci yaran kirki yana ma mahaifansa addua.




KAMMALAWA
Wannan shine   xan abin da Allah Ya hore man in yi magana akansa wanda ya shafi hukunce-hukuncen Janaza ina roqon Allah ya amfar dani da ‘yan uwa na musulmai baki xaya, kuma ina roqon ‘yan uwa da muji tsoron Allah mu gyra aiyukan mu, mutuwa ko da wani lokaci tana iya zuwa wa xaya daga cikin mu. Duk yayin da xan uwan mu ko ‘yar uwar mu suka rasu mu dage muyi masu janaza yadda Musulinci ya koyar mu daina barin waxanda ba su san shari’a ba su riqa yni ma gawa surkulle. In muka yi janaza yadda musulinci ya tsara, shi mamacin yana samun lada kuma muma muna samun lada amma in muka sava   muka yi bidia zamu haifar ma xan uwan mu da matsala Allah ya kyauta amin.  Aqarshe ina roqon duk wanda yaga kuskure ko gyara qofa a buxe take kuma ina mai farin ciki da gyaransa, har ila yau ina roqon ‘yan uwa da su yi man addua ta alheri ni da mahaifana Allah ya ji qansu baki xaya Allah ya albarkaci zuri’ar su amin.  Na gama rubuta wannan littafin cikin daren 25 Ramadan 14329.
Za a iya samun sauran littattafan dana rubuta a mudawwanata ta yanar giza-giza       http://harunaabubakarshika.blogspot.com ina roqon addua ta alheri ga duk wanda ya karanta littafi na nagode.

‍ والله تعالى أسأل أن يجعل هذا العمل مقبولاً، مباركاً، خالصاُ لوجهه الكريم، وأن ينفعني به في حياتي وبعد مماتي، وأن ينفع به كل من انتهى إليه؛ فإنه سبحانه خير مسؤول، وأكرم مأمول، وهو حسبنا ونعم الوكيل، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم،  وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لاإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك
                                         Harun Abubakar Shika
                             08030582333-08054533361-   08020900001
                                     harunaabubakar99@yahoo.com




[1] Tirmidhi.
[2] Tirmidhi.
[3] Matarsa ce ta ke zuwa ta nemo ma su abinci na tsawon ciwon da ya yi ita ta yi ta wahala da shi tsawon shekara goma sha bakwai. Wannan yana nuna mana yadda matayen qwarai suke haquri da mazajensu su ma mazajen suke haquri da su wannan yana daga cikin siffar mataye na qwarai, haquri, shi ma miji ana so ya fi matarsa haquri haka ake so. Matayen magabata suna taimaka wa mazajensu ba tare da sun yi masu gori ba.  Wannan shi ne abin da ya kamaci  dukkan matayen Musulmi. Yana da kyau wanda zai yi aure ya nemi mai addini ba mai karatu ba, domin manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam cewa ya yi a nemi mai addini yana da matukar mahimmanci. ‘Yan’uwa a lura da wannan wajen neman aure a duba mai addini shi zai sa ka sami mai bin Allah wadda ta san mutunci mai girmama na gaba da sanin ya kamata mai  biyayya mai godiya ba rainuwa da kuma jin maganarka. Allah Ya sa mu dace amin. Wasu da dama suna ruxuwa idan sun ji mace ta iya karatun Qur’ani sai su xauka ita ce siffar da ake nufi, wannan kuskure ne. Ya dai kamata ‘yan’uwa su tambayi malamai siffar matar da Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya ce a aura, haka kuma da shi ma irin namijin da ya kamata mace ta aura, domin a na samun matsala wajen aure. Ya kamata malamai su yi bayani sosai a kan wannan nuxuqan duba littafi na haqqoqin ‘ya’ya a Musulinci da kuma dalilan da kan kawo lalacewar tarbiyya.   duba suratul Anbiya’i  za ka ga qissar  ciwon Annabi Ayyub.
[4] Ibn Kasir.
[5] Daga baya Allah Ya ba shi lafiya sannan kuma Ya mayar ma sa da yaransa waxanda suka rasu Allah Ya ba shi waxansu, kuma Ya ba shi dukiya mai yawa. Wannan duk sakamakon haquri ne. Wata rana ya je rafi yana wanka sai Allah Ya sa sama ta kama yin ruwan Zinariya (wato ruwan kuxi) sai ya riqa Tarawa, sai Allah Ya ce ma shi bai wadatu da ni’imarsa ba? Sai ya ce masa babu mai wadatuwa da rahamarKa   Ya   Allah.  duba Bukhari zaka ga Qissar. 
[6] musulim
[7] Bukhari da Mulim
[8] Bukhari da Muslim
[9] Bukari da Muslim.
[10] Ahmad.
[11] Abu Dauda da Tirmizi.
[12] Siilatus sahiha 1633.
[13] Muslim. Wannan mutumin da ya sha zuman a karan farko ya warke amma ya qi faxi,  xan uwansa ya gayama Annabi  sai Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce a qara ba shi aka qara bashi ana uku Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce Allah ya faxi gaskiya cikin xan uwanka ya yi qarya.
[14] Silsilah 1053.
[15] Muslim.
[16] Tufatun zaqarin na Shawkani.
[17] Bukhari.
[18] Bukhari. Wannan yana xaya daga cikin dalilin da ya sa likitoci suke wa mutum qarin ruwa idan an kai mutum ranga-ranga, kai ma idan kana fama da zazzavi mai tsanani kana iya wanka da ruwan sanyi zaka warke da yardar Allah.   
[19]  Zadul Ma’ad da Dibbun Nabawi
[20] Muslim.
[21] Bukhari.
[22]  Sifatus safawa 264.
[23] Minhaj Sharhin Sahih Muslim 191/14 da Attamhid na ibn AbdulBar 65/24.
[24] Majmu’ul Fatawa 269/24.
[25] Abu Daud.
[26] Bukhari.
[27] Muslim da Abu Dauda.
[28] Zadu Mustaqni’i Ilimin likintanci wani ilimi ne na musulmai ba na Arna ba ne,  kafirai ba su fara karatun likitanci ba sai  da suka je qasar Andulus (Spain) daular musulunci a wancan zamani suka koya, musulmai suka koya wa Arna likitanci haka nan ma ilimin Andasa wato ilimin Qere-qere dukkan waxannan nau’o’in ilimin kafirai a Andulus suka koya. Amma abin baqin ciki yau Kafirai sun mamaye wannan ilimin har wasu ‘yanbana bakwai suna ganin ilimin Boko  kafirci ne wannan kuskure ne Allah ya shiryi waxan nan yaran  su gane cewa ilimin Boko ba na Arna banne.
[29] Adabul Shariah na ibn Muflihi
[30] muslim
[31] Bukhari.
[32] Bukhari.
[33] Muslim268 da AbuDauda 3569.
[34] Yana  da kyau ‘yan‘uwa su kiyaye shiga gidajen jama’a, wannan bala’i ne kuma laifi ne shiga gidajen jama’a ba tare da izini ba, ko da ka yi sallama sai ka jira an ba ka izini kafin ka shiga, haka   Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya koyar da mu. Haka nan ma haramun ne qanin miji ya shiga xakin matar wansa sai da izinin yayan nasa, idan kuma baya nan to haramun ne  kai qaninsa  ka shiga xakin matar. Allah ya ba mu ikon gyarawa amin.
[35]  Bukhari.
[36] Hajjaj bn Yusuf saqafi shi ne ya sa aka soki  Sahabi mai daraja Abdullahi bn Umar Allah ya qara masa yarda da wani masoki mai dafi, ba don komai ba sai don  zalunci da mugunta, Abdullahi bn Umar ya yi wa  Hajjaj magana ne  ranar juma’a a kan ya tsananta wa jamá’a  wajen huxuba har la’asar,  sai ya sa aka soke shi.  Wannan sukar ce  ta zama sanadiyyar Rasuwarsa. Bayan an soke shi ne  daga baya ya zo gasshe shi don yaudara, sai shi kuma Abdullahi bn Umar ya ce ba ya so, shi ya sanya Shamsudden Zahabi  a cikin  littafinsa Siyar ya faxi miyagun maganganu a  kansa ba don komai ba sai don ya kashe sahabai da bayin  Allah nagargari har a qarshe yake cewa, “Muna qin sa ne saboda Allah ya ce ’’ mugu xan ta’adda azzalumi xankama karya  jabberi’’ ya dai sossoke shi. Mai karatu yana da kyau ya karanta tarihinsa a cikin SIYAR A’ALAMUN NUBALA  shafi  343/4.
[37] Siyar na ZAhabi 230/3.
[38] Muslim.
[39] AbuDauda 309 da Ahmad 21833.
[40] Bukhari 1356 ba a tsayawa  a tsakiyar mara lafiya sai dai wajen kansa.
[41] Abu Ya’ala fi Musnadihi 83/7  yana da kyau idan mutum zai je gasshe da mara lafiya ya je masa da wani abin sha ko ci wannan ta’ada ce ta musulunci.
      [42] Bukhari 5659 da Mulim 1628  amma  a kiyaye  banda mata sai dai in matarka ce in kuwa ba matarka ce ba kada ka fara ka tava ta, haramun ne ka tava jikin mace sai dai in matarka ce ko muharramarka.
[43] Muslim da  Zadul Ma’ad: Wannan ya na nuna wa likitoci yadda ake  so su yi wa mara lafiya, ba a ba shi tsoro da ciwonsa komai tsananinsa, haka musulunci ya koyar. Idan  ka tsorata mara lafiya ko wane irin magani ka ba shi ba zai yi masa tasiri ba, domin kai ma ka sa masa wani ciwon na damuwa a sakamakon tsorata shi da ka yi. Manzon Allah salla Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya kasance yana ce wa mara lafiya, “Za ka warke kuma za ka yi rayuwa mai tsawo nan gaba.” Don Allah likitoci da masu jinya su kasance masu faranta wa marasa lafiya, su kasance suna ba su labarin waxanda suka warke ba tsoratar da su ba  da cewa wannan ciwon ba a warkewa ba, yin haka babu kyau, shi ya sa ake so masu addini su karanta wannan farnin. 
[44] Bkhara 5659 da  Muslim 1628 da Abu Dauda 3104.
[45] Attamhid 277/24.
[46] Kitabul  Jana’iza na Usaymin Zadul Mustaqari).
[47] Abu Dauda 3072 da Silsilatu Sahiha 714.
[48] Bukhari Kitabul Magazi  4122 da Muslim Kitabul Jihad 1769.
[49] Haqqul  Ikwa na Abu Ammar Mahmud almisri.

[50] AdabulShariah 190/2 da Haqqul Ikwa na Abu Ammar Mahmud almisri 68
[51] Bukhari 5664.
[52] Abu Dauda.
[53] Muslim.
[54] Al ,Ubudiyya na ibn Taymiyya.
[55] Bukhari 3926.
[56] Muwadxa 531.
[57] Haqqul Ikwa na Abu Ammar Mahmud alMisri.
[58]  Zadul Ma’ad.
[59] Bukhari.
[60]  Suratl baqara 155-157.
[61] Bukhari.

[62] Ahmad.
[63] Sahihu Jami’u 1676 da Ahmad 1063 da Abu Dauda 4753.
[64] Nasa’i 1828.
[65] Kitabul Jana’iz na Nabil Muhammad 34-35.
[66] Muslim 919.
[67] Bukhari 651.
[68] Muslim da Ahmad 1384. " من كان آخر كلامه لا إله إلا الله دخل الجنة ".
[69] Ahmad 357 da Nasa’i.
[70]Ahmad (6582-6646) Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya ce, “Babu wani  mutum musulmi da zai mutu ranar juma,a ko yini Juma,a face Allah ya kare shi daga fitinar qabari.”
[71] ولا تحسبن الذين قتلوا في سبيل الله أمواتا ، بل أحياء عند ربهم يرزقون . فرحين بما آتاهم الله من فضله ، ويستبشرون بالذين لم يلحقوا بهم من خلفهم ألا خوف عليهم ولا هم يحزنون . يستبشرون بنعمة من الله وفضل ، وأن الله لا يضيع أجر المؤمنين

[72] Muslim 7/51.
[73] Bukhari 10/156-157.
[74] Muwadxa 232-233/1 da Abu Dauda 26/2.
[75] Bukhari 33/6.
[76] Muslim 51/6.
[77] Ahmad 201/3.
[78] Xabarani.
[79] Bukhari 93/5.  
[80] Abu Dauda 2/275.
[81]  Da 15, 16Xabarani da Abu Dauda274/2 da Nasa,i da Tirmidhi 316/2.
[82] Muslim 51/6 da Nasa’i 63/2.
[83] Ahmad 391/5.
[84]Ahkamu Jana’iz na Nabil Muhammad Mahmud 76.
[85] Kitabu Muslim liQurxubi 756-758/3 da Sharhu Nawawi ala Sahih Muslim. 66-67/13 da FathulBari 43/6.
[86] Kitabul Jana,iz na  Muhammad Mahmud Nabil  78.
[87] suratul Baqara 155-156.
[88] Bukhari da Muslim.
[89] Baihaqi 334/3 da Ahmad 297/6.
[90] Baihaqi 298/3.
[91] Ahkamu Jana’iz Abu Ammar 15-16.
[92] Bukhari da Muslim.
[93] Wasu malaman suna ganin qwal-kwabo bai halatta ba in ba wajen aikin hajji ba, domin manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ba ya yin qwal-kwabo kuma bai  tava yi ba. Shi ne ya sanya ma Sheikh Usman ibn Fodiyo a cikin IhyausSunnah ya ce qwal-kwabo bidi’a ce abar zargi.
[94]  Aske gemu haramun ne a Qur’ani, da Hadisi, da maganganun Sahabbai, da gaba xayan mazhabobinmu guda huxu, da malam Fiqihu,  duk sun bayyana cewa aske gemu haramun ne. Don haka masu aske gemu su ji tsoron Allah su bari, Ibnil Jauzi a littafinsa “Talbisul Iblis” ya ce duk laifi idan ka yi barci ba a rubuta maka zunubi, ya ce amma banda mai aske gemu. Mai aske gemu yana barci ne kuma ana rubuta ma shi zunubi. 
[95]   Najashi Sarkin Habasha ne ya musulunta ne a wajen sahabin manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  “Jaafar  ibn Abi Xalib.” Ya zauna a Habasha har ya rasu bai ga manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ba amma ya yi imani da shi, da ya rasu Mala’ika Jibril ya zo ya gaya ma sa ya rasu , sai ya gaya wa Sahabbai Najashi ya rasu suka fito suka yi ma sa sallah saboda ba a yi masa sallah ba a can Habashar.
[96] Muslim 920 Abu Dauda 3102.
[97] Musim 920.
[98]  Bukhari 1241 da Musim 942.
[99] Tirmizi 1078.
[100]  Na 5,6,7,8,9  ka  duba Muguni Nabidin 2/451 da Furua 2/192 da 21194.
[101] Bukhari 2291 da Nasa’I 1961.
[102]  Ahkamul Jana’iz na Abduahi bn Jaruallah bn Ibahim  13-15.
[103] Zadul mustaqani,i.
[104] Muslim 919 Aljanu suna son xaki  ko gidan  da ya ke akwai hoto ko kare shi ya sa in za a cire Aljanu a jikin namiji ko mace sai an cire hoto kafin yin ruquya. Ana cire  hoto domin in akwai hoto mala’ikun rahama ba za su zo ba  kuma ko bayan an cire aljanu  a jikin mace suna dawowa jikin wanda aka cire  wa in dai akwai hoto a xakin, ya dai tabbata xaukar hoto da liqa shi a gida ko xaki haramun ne. Ba a fara shirka a bayan qasa ba sai ta sanadiyar hoto wannan sananniyar magana ce a wajen malaman tauhidi ruwaya da ga ibn Abbas,  duba littafina Sharuxxan Hijabi a Muslinci.
[105] Kitabul Jana’iz  na Nabil ibn Muhammad Mas’uds.
[106] Kitabul Janaiz na Nabi bn Muh’d Mahmud.
[107] Usaymin Jana’iz 4.
[108] Karuwanci masifa ce, duk  matar da ta mutu tana zina ba ta  tuba ba Allah sai ya qona ta. Karuwanci shi ke kawo masifa da rashin albarka da cututtuka waxanda  ba a san su a baya ba, iyaye su ji tsoron Allah su kula da tarbiyar yaransu musamman mata, kuma abin da zai maganin karuwanci shine rage tsadar aure da aurar da yara da zarar sun balaga kada a jira a ce sai sun gama makaranta, barin su zuwa wani lokaci shi ke kawo lalacewarsu iyaye a ji tsoron Allah a gyara.
[109] Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce wanda ya sha guba ya kashe kansa zai tashi da wannan gubar da ya sha a hannunsa ranar tashin qiyama Allah zai azabtar da shi a cikin Jahannama, Allah ya kyauta. Masu shan fiya-fiya domin su kashe kansu sun ji sai su ji tsoron Allah su gyara, wasu malaman ma suna ganin duk wanda ya sha wata guba ya kashe kansa  ya mutu kafiri.

[111] Kitabul Janaiz na Jarullah bn Jarullah.
[112] Usaymin a Zadulmustaqani,i kitabul Jana’iz.
[113] Abiy Shaybah 3/247.
[114] Bukhari.
[115] Bukhari1254/Musim 939.
[116] Bukhari 99-104/3 da Muslim 47-48/3 da Abu Dauda 60/2.
[117] Usaymun fatawa

[118] Minhaju Muslim.
[119] AhkamuJana’iz na nabil bin Muhammad 81-120.
[120] Al’ummu  na Imamu Shafi’i 248/1 da Majmu’u 5/187  da Ahkamu Jana’iz na jarullah 16.
[121] Almusanaf Abiy-Shaybah 3/248.
[122] Mugmy 2/463.
[123]  Bukhari.
[124] Kitabul Jana’iz na Jarullah 17.
[125] Bayhaki 3/398 da ibn Abiy shaybah 3/413.
[126] Muhallah 5/122 da Majmu’u 5/178.
[127] Mukhtasar  da Gayatul Muntaha1/254 da BugayatusSalikin 1/232da fatawan Hindiyah 1/157.
[128] Bayhaqiy 3/398 da Hakim 1/386.
[129] Tirmizi 2/132 da Abu Daud 62-63).
[130] Bukari
[131] Ahkamu Jana’iz na Muh’d Hassan 121
[132] Ahkamu Jana’iz na Muh’d Hassan 121.
[133] Ahmad 40/6 da Bayhaki 399/3.
[134] Bukhari 1263 da Muslim 941. Maganar da ake cewa za a yi wa gawa hula da rawani da riga bai tabbata ba, magana ce mai rauni raunin kuma mai tsanani duba Fatawar Usaymin.
[135] Mulim 943.
[136] Ahmad 14131 da sahih Jami’u Albany.
[137] Bukhari 1276.
[138] Bukhari.
[139] Bukhari 1277 da ibn Majah 3555.
[140] Muhalla ibn Hazam 5/122) fikhussunna linnisa 45.
[141]  Tanbihu Afham 496
[142] Fatawa Usaymin
[143] Zadul mustaqani da Ahkamu Jana’iz na Nabi 151 da Ahkamul Jana’iz Usaymin.
[144] Ahkamul Jana’iz  na Jarullah 1.
[145] Qibla  Ahkamul Jana’iz na Abu Ammar.
[146] Muslim 224.
[147] Bukhari 756 da  Muslim 394.
[148]  Bukhari 1335Nasa’i 1998.
[149] Bukhari 1317 da Muslim 964.
[150] Limamin da zai ma gawa sallah ya gaya ma jama’a abin da ake karantawa tun daga kabbaran farko har zuwa na huxu
[151] Hadisai ingantattu sun tabbata da suke nuna duk sallolin manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam na nafila da farilla da ta gawa hannunsa a qirji yake sanya su, ba ya sakin hannunsa kuma haka ya koyar kuma ya umurci sahabbai da su  riqa sanya hannunsu  a qirji. Su ma shugabannin mazahabobin mu guda huxu su ma duk sallolinsu hannunsu a qirji suke sanyawa. Wasu jama’a marasa adalci suna cewa wai mazhabar  malikiyya ta  umurci da a saki hannu wajen sallar farilla ta nafila kana iya sanya hannunka a qirji. Wannan magana gaskiya rashin adalci ne da kuma qirqirar qarya ga Imam Malik domin shi dai Imam Malik baya sakin hannu wajen salla. Bil hasali ma ya ruwaito hadisai guda biyu a babban littafinsa Muwaxxa da suke nuna tabbatar da sa hannu a qirji wajen salla. Ibn Abdulbar ya yi magana mai  gamsarwa cikin littafinsa Attamhid  sharhin da ya yi wa Muwaxxa ya tabbatar da cewa Imam Malik ba ya sakin hannunsa a wajen sallah. Ya kawo wata qissa ta Imam  Malik da wani mugun sarki Walid  inda ya sa a ka yi wa Imam Malik  dukan tsiya, da ya zo salla sai ya saki hannunsa, da ya gama salla sai xalibansa suka ce masa mun ga ka yi abin da Annabi bai tava yi ba kuma kai ma ba ka tava yi ba. Sai ya amsa masu da cewa ba ya iya riqe hannunsa  ne saboda dukan da aka yi masa. Wannan ita  ce ranar da Imam Malik ya tava sakin hannunsa sabo da dukan da aka yi masa. Imam Assubki shi ma ya tabbatar da cewa Imam Malik ba ya sakin hannunsa  a wajen salla shi ma ya kawo qissar Walid da Imam Malik: Duba DINUL KHALIS,  shi ma mai littafin Irsalil Malik  ya  kawo hujjojin da suke nuna cewa  sakin hannu ba koyarwar Imam Malik ba ce domin shi ma ba ya sakin hannunsa. Kuma malaman  hadisi sun yi raddi ga masu danganta kansu da Imam Malik  da suke sakin hannu  a farilla amma a nafila  su yi qablu, wato su sanya hannunsu a qirjinsu. Sai malaman  hadisi suka ce mene ne dalilin da ya sa ba sa yi a farilla domin dukkan su ai salloli ne. Muna masu  addu’a ga masu  cewa wai suna bin Malikiyya  da su riqa sanya hannunsu a qirji  domin haka ne karantarwa Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam da Imam Malik. Masu bin addinin Shi’a ne suka ce sanya hannu a qirji yana vata salla, haka Ayatullahi Khomen ya ce a cikin littafinsa TAHRIRUL WASILA. Ya faxi haka ne don qiyayya da gaba ga AhulSunnah, shi ya sa duk xan Shi’a ba ya yin qablu. Wannan magana ce sananna a wajen masu bin addinin Shi’a, kuma bai kamata Ahlul Sunnah su riqa koyi da masu bin addinin Shi’a ba. An samu wani mugun xan bidi’a ya yi sharhin AHDHARI sunan sharhin HALLUL MASA’IL. A cikin littafin ya kawo hadisin qarya da wai ya ke nuna ana iya yin salla a saki hannu. Wannan kuskure ne Allah ya shirye shi. Wasu kuma suna cewa akwai hadisi a NAILUL AUDAR littafin Shaukani amma da zaka duba zaka ga shi Shaukani yana  ganin wajibi ne sanya hannu a kirji wajen salla. Maganar sakin hannu a sallar Farilla maganar mai    MUKTASAR   ce  ba maganar Annabi  sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ba ce, ba kuma maganar Imam Malik ba ce. Karantarwar Annabi da Imam Malik ita ce qabzu a cikin sallah kowace sallah. Wannan maganar ita ce mai Askari ya goyi bayan ta haka shi ma mai FATHUL JAWAD ya ce a sharhin Askari  ya kawo hadisin  ibn Kuzaima  da ya nuna sallar Annabi sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ita ce yin qabzu ba sakin hannu ba, Allah ka  ganar da mu amin.         
[152] Dari Qudini 191 da Hakim 360/1 da Bayhaqi 43/4.
[153] Tsakanin Sahabi Aliyu da Sahabi Umar Allah ya qara masu yarda babu matsala tsakaninsu abin da ya ke tabbatar da haka shine yadda Sahabi Aliyu ya aurar da ‘yarsa Ummu Khulsum ga Khalifa Umar Allah ya qara masa yarda kuma ta kasance matar Umar har ya bar duniya kuma ranar da aka kashe Sahabi Umar  Sahabi Aliyu Allah ya qara masa yarda ya girgiza girgiza mai tsanani kuma Sahabi Umar har addua yakeyi ya ke cewa ya Allah kar ka zaunar dani garin da babu Sahabi Ali, wannan ya nuna mana qaryar masu bin addinin Shia da suke sharri ga sahabi Umar,  Allah ya shirye su amin.
[154]  Nasa’i
[155]  Muslim
[156] Muslim 945.
[157] Muslim.
[158] Ahmad 3/27 da Bukari Fil Adabu/Mufrad518.
[159] Ibn Abidin 1/624 da Fahul Bari 3/113.
[160] Kitatul Jana’iz Nabi 226.
[161] Ibn majah 16.
[162] Zadusmustaqani’i.
[163] Bukhari 1315 da Muslim 944.
[164] Bukhari 1310 da Muslim 959.
[165] Bukhari 131.
[166] Bukhari 1/314 da Nasa’I 1/41.
[167] Majmo’ul Fatawa 5/270 da Jamiu ahkhmu Nisa’i na Mustafha Adawi1535.  Kiristoci da masu bin addinin Shi a su ne matayensu su ke raka gawa har maqabarta wannan ko aiki ne na kafirai, wannan kuma a bayyane ya ke domin musulmin Najeriya sun ga yadda masu bin addinin Shi’a suka yi wa wani xan uwansu da aka  kashe wajen zanga-zangar da suke yi a Zariya inda mata suka raka gawar wanda aka harbe har maqabarta, suna raka ta suna waqa suna buga ganga mazajen su kuma na rawa har maqabarta yadda dai Kiristoci da Yahudawa suke yi. Idan mutum bai san masu bin addinin Shi’a ba, idan ya ga wannan janazar zai rantse da Allah kiristoci ne ko wasu maguzawa ne. Wannan da ma ba sabon abu ba ne domin duk wanda yake kallon gidan talabijin na ALMANAR ya san yadda ‘yan Shi’an Hizbullah na Labanon suke yi yadda Kiristoci suke yin Janaza su ma haka suke yi. Muna roqon Allah ya shiryi masu bin Addinin Shi’a su gane cewa Shi’a ba addini ba ne.
[168] Bayhaqifi Kubra 3/25 da Ahkamul Jana’iz  na Albany 4).
[169] Abu-Dauda 3177 da ibn Majah 148.
[170] Muslim.
[171] Ibn ABidin 723.
[172] Majmu’u Fatawaa 5/270 abin da ya ke gaskiyan labari   shi ne bai halasta ba a sa gawa a mota a kai ta ba sai dai inda wata lalura mai qarfi.
[173] Ahmad 2/427 da Abu Dauda 3171.
[174] Muslim 121 da Ahmad 4/199 da ibn majah 1487 da Bayhaqi 3/395.
[175] Bayhaki 4/74.
[176] Azkar na Imam Nawawi 303.
·         [177] Azkar na Imam Nawawi 303. Mai karatu ya nemi faifan CD na Janazar da masu bin addinin Shi’a suka yi a Zariya zai ga koyi da Kiristoci a fili yadda shugabansu ya yi limanci salla. Duk wanda ya ga wannan janazar zai qara sakankancewa a kan masu bin addinin Shi’a ba su da banbanci da Kiristoci.

[178] Azkar na Imam nawawi da Ahkamu Jana’iz na Albany.
[179]  Koda wajen aikin ku xayane bai halasta ka raka wannan Kafirin ba domin addininka ya hanaka, in kuma ka rakata ka nuna addininsu daidai ne Allah yasa mufi karfin zuciyar mu amin.
[180] Abu Dauda.
[181] Bukhari 3/3979 da Muslim 4/294.
[182] Abu Dauda 3149 da Muslim 831 Ahmad 3/593.
[183] Ahkamul Janaiz na Muhammad Hassan, ba mamaki wani mara sani ya ce to ai ga gawar Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam a masallaci. To duk wanda ya faxi wannan maganar alama ce ta ba ya zuwa makaranta, domin asalin qabarin Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yana xakin Nana A’isha ne. Qabarin Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam bai shiga masallaci a sai bayan duk Sahabai sun rasu, Tabi’ai ma sun rasu, sai Sa’id bin Musayib kawai ya rage a cikin Tabi’ai shi ma ya yi suka mai tsanani a kan sanya qabari cikin masallaci. Amma  waxannan sarakunan su ka qi jin maganarsa saboda su ba malamai ba ne. Don haka haramun ne rufe mutum a masallaci.
[184] Muslim.
[185] Musulunci bai hana ka ka auri Kirista ba ko Bayahudiya wannan hukunci ne tabbatacce. Sayidina Umar ne ya so ya hana sahabbai ,su kuma su ka sava masa har sahabi Huzaifa ya auro Kirista. Ya ce ba wai ya na son ta ba ne sai dai don ya nuna wa Sayiddina Umar kar ya haramta wa  mutane abinda Allah  bai haramta masu  ba. Shi ma sahabi Usaman ya auri Kirista don ya nuna ma Sahabi Umar kar  ya haramta abin da Allah da Manzonsa ba  su hana ba. Shi Umar hujjarsa akwai mata musulmai da suke neman masu auren su, don haka su ya kamata  a gama da su kafin Kiristoci. Shi ma xansa yana cikin masu hana auren Kiristoci. Babu laifi don mutum musulmi ya auri Kirista sai  dai ba kowa  ba, sai wanda ake sa ran za su  iya musuluntar da ita  ba wai yanda mutanen banza suke yi ba, bayan sun gama fasiqanci da Kirista daga baya  su aure ta ba, ba  irin waxannan ake nufi ba. Kuma su ma matan Kiristocin sai masu kamewa ba ‘yan iska fasiqai ba. Yana da kyau mai karatu ya duba littafin ALQADHI ABUBAKAR IBN ARABIY ALMALIKI ALANDALUSI  AHKAMULKUR’AN Saratul Ma’idah zai ga bayanin da ke nuna halascin auren Kirista.  
[186] Mugni Ibn Qudama 2/563.
[187] Abu-Duda 3215 da Nasa’I 2011 da Tirmizi 1713 da ibn Majah 1570.
[188] Muskah 1703.
[189] Ahmad 22955 da Abu Dauda 3332.
[190] Muslim 966.
[191] Ibn Majah 1557 daAhmad 3/99.
[192] Abu-Dauda 3207 da Nasa’i 2009.
[193] Majamu’ul Sharhul Muhazab 5/287.
[194] Abu Dauda 3195).
[195] Muhallah 5/173.
[196] Muhallah 5/173.
[197] Bukhari.
[198] Bukhari.
[199] Ibn Majah 1565 da Irwa’u Ghalil 751.
[200]  Masu bin addinin Shia cikin akwati suke rufe wanda ya mutu.
[201] Abu Dauda  3207.
[202] Ibn Habban 2170 da vayhaqi 3/410.
[203] Musim.
[204] Bukhari 1343 da Nasa’I 2771 da ibn Majah 15141.
[205] Abdu Rak 7378 da Jamiu Ahkmun Nisan a Mutapha Adawi 1/556.
[206] Al’uMmu 1/245. 

[207] Abu Dauda.
[208] ‘Yan bidi’a ne ke yin addu’a cikin jam’i bayan sallolinsu   da kuma maqabarta. Koda yake a da ba sa yin addu’a a maqabarta, daga baya ne suka gane gaskiya sai kuma suka haxa da bidi’a ta yadda suke yi cikin taro su keve waxansu su ce wai su ne za su yi addu’a ga wannan mamacin. Abin da sunna ta koyar da mu kowa ya yi tasa. Kada mutum ya shiga tsakanin bawa  da ubangijinsa. Haka sahabi Umar ya ce. Muna fatar jama’a zasu gyara kowa ya yi wa gawa addu’a,  kuma  ana so a daxe ana yin addu’ar ga mamacin. Sannan kuma alqibla ake kallo wajen yin addu’ar.
[209] Ahmad 2/204.
[210] Bukhari 5417 da Muslim 2216.
[211] Abu Dauda)3753 da sahih Jami’u 1676.
[212] Kitabu Jana’iz na Nabi Muhammad 263.
[213] Muslim.
[214] Tirmidzi da Nasa’I da dhiyaul Maqadisi.
[215] Madakal.
[216](Sharhus sagir 1/180.
[217] Hukumul qiratu alall Amwatu 24.
[218] Hukumu Qiratu qur’an ala Amwatu.
[219] Fatawal Shaxibiy 210.
[220] Suratu Hahar 10.
[221] Musim 2733.
[222] Bukhari 1952 da Musim 1147.
[223] Abu Dauda 3511 da Nasa’I 7/341.

Bayhaqi fi shu’abu Imam 3174 da ibn Majah 242 da ibn Kuzaimah Fisahihi 4/121.
[226] Bukhari 1284 da Muslim 923.
[227] Ibn Majah 1612 da Ahmad 666.
[228] Almajahmu’u 5/306).
[229] Alummu 1/248).
[230] Mindaju Muslim 266).
[231] Zadul Ma’ad.