Wednesday, September 14, 2011

BAYANI KAN AZUMI

                            GODIYA
بـسـم اللـه الـرحـمـن الـرحـيـم                                                                              
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره  ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادى له، وأشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله.     أما بعد: فإن خير الحديث كتاب الله، وخير الهدي هدي محمد، وشر الأمور محدثاتها، وكل محدثة بدعة، وكل بدعة ضلالة، وكل ضلالة في النار أما بعد:
Haqiqa ina wa Allah godiya da ya bani ikon rubuta wannan littafi taqaitacce Wanda yake Magana kan “ Bayani kan Azumi  da hukunce-hukuncen Zakkatil Fitir da Iitikafi da               Tarawihi/Tuhajjui da hukuncin sallah da Amsakuwa (Speaker) cikin dare da sallar idi da hukuncinta da bayanin azumin nafila da nau’ikan su, Ina rokon Allah daya anfanar da shi.                             Wannan littafi shine bugu na uku kenan ya kuma taqaitune qarqashin Qur’an da Hadisi da maganganun sahabbai da kuma maganganun magabata na qwarai (salafusSalih) Ina roqon duk wanda ya karanta wannan littafin da ya yi man addua ta alheri, kuma duk wanda yaga kuskure to qofa a buxe take ya aiko da gyaransa in sha Allahu zan gyara kuma muna farinciki da gyaransa       Ba zan gushe ba ina mai godiya ga Malam Abubakar Jumare Gixaxo Zaria da ya duba littafin tundaga farko har qarshe ya gyara kurakuran da ke ciki da kuma ba da shawara duk da rashin lafiyarsa amma haka nan ya duba littafi Allah ya bashi lafiya Allah kuma yasanya ciwon nasa yaza kaffara a gareshi amin, Allah yasa ka ma shi da Aljanna amin. Ba kuma  zan manta da Malami na ba Malam Ahmad Bello Dogarawa   wanda  koda yaushe yakan qarfafaman muhimmanci  yin rubutu domin ‘’yanuwa su anfana shima Allah yasa ka ma shi da  Aljanna amin.                             
Da Malam Haruna Ishaq Shika Alqali da Malamina Imam Mikail Isah Shika da Malam Muhammad Amin Jumare Maqarfi Alqali da Malam Musa Sahabi Zaria shima Allah ya saka masa da alheri, shima yaba da nasa gudunmuwar wajen ganin wannan littafin ya kyautatu   Allah Yasa kamasu da Aljannah amin.  Da duk wanda ya taimaka wajen ganin wannan littafi ya fito Allah yasa kama shi da alheri amin kamar Dr Ahmad Bello Sardauna shugaban tsangayar qididdigan kuxi da lisafi na Jami’ar Ahmad Bello Zaria (H.O.D Accounting Department) ya taimaka sosai wajen ganin wannan littafi ya fito.   A qarshe ina wa mahaifiyata Malama Fatimatu Dalhatu Zaria da mahaifina Malam Abubakar Ibrahim   adduar Allah ya saka masu da alheri, dukkan alherin duniya da na lahira Allah ya tabbatar da shi ga mahaifana Allah ya albarkace zuri’ar da suka bari kuma Allah ya basu Aljannatil Firdaus amin.       A qarshe ina qara cewa   duk wanda ya ga gyara ko shawara kofa abuxe take kuma zanyi farin ciki da gyaransa ko shawaransa, za a iya samun sauran littattafan dana rubuta a Mudawwanata ta yanar giza-giza mai alamar  http://harunaabubakarshika.blogspot.com ina roqon addua ta alheri ga duk wanda ya karanta littafi na nagode.                                      
                                 Wassalamu alaykum warahamatulLah.
                                                 1/Sha’aban/1429  
                                       Harun Abubakar Shika
                          08030582333-08054533361-08020900001                                                                                                  harunaabubakar99@yahoo.com –harunshika@gmail.com    




















                                      TAQARIZI

بسم الله الرحمن الرحيم
الحمد لله رب العالمين ، وصلى الله وسلم على نبينا محمد وعلى آله وأصحابه ومن تبعهم بإحسان إلى يوم الدين ، أما بعد       
Cikin rahamar Allah da tausayinsa ya sanya  cikin kowace al’umma mai kira zuwa ga Allah ta hanyar tallata  shariarsa da yaxa  shiriyar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa’alihi wasallam, Allah subuhanahu wata’ala yana ce wa,
                          إِنَّمَا أَنْتَ مُنْذِرٌ وَلِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ           
Aqarqashin haka ne aka sami Xan uwa Harun Abubakar Shika ya wallafa littafi cikin harshen Hausa wanda ke xauke da bayanin shariar Allah da kuma sunnonin ma,aikinsa sallallahu alaihi wa,alihi wasallam dangane da Azumi da I,itikafi da Tahajuddi da Zakkatil Fitir.
Mawallafin yayi qoqarin matuqa wuri kusanto da shiriyar manzon Allah sallallahu alaihi wa,alihi wasallam ga al,umma, don gaskiya ya tattara mas’aloli da  dama waxan da Al’umma keda qishinsu kuma ya tabbatar da gaskiya acikinsa, cika daidai na ga Allah kawai, amma gaskiya yayi qoqari Allah yasa ka masa da alheri.
 Don haka Allah ya saka masa da alheri ya qaramasa lafiyar aiki don taimakon addini ya amfaneshi da wannan aiki ranar tashin Qiyama amin.

Abubakar Jumare Gixaxo
Zaria







                                              TAQARIZI
                                      بسم الله الرحمن الرحيم

إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره  ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادى له، وأشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله.     أما بعد
Na karanta wannan littafin na Xan uwa Malam Haruna Abubakar Shika (wato Malam Haruna Abubakar Izzah) wanda gaskiya nayi sha’awar yadda ya shirya littafin musammam yanda ya riqa koqarin kauce wa sanya ra’ayin shi sai dai ra’ayin Malamai musammam ma a kan matsalolin da ake da savani akansu.
Nayi sha’awa gaskiya yadda Malamin   ya gabatar da maganar ganin wata da matsalolin yin sallar Tahajuddi da amsakuwa (speaker) da kuma matsalar I’itikafi gaskiya lallai malamin yayi Nasiha ya kyautata Nasiha.
    A qarshe Allah Ya yi sakamako da alkhari ya qara basira da dauriya akan cigaba da irin wannan aiyyuka akan wannan harshe na Hausa kuma Allah Ya yawaita mana masu irin wannan aiki amin.       
                                                                     Xan uwa
                                                             Musa Muhammad Sahabi
                                                                         Zaria












بسم الله الرحمن الرحيم

BAYANI KAN AZUMI
Muna farin cikin taya ku murnar shigowar watan Ramadana, muna roqon Allah ya taimake mu da yin kyawawan ayyuka.
 Wannan wata ’yar maqala ce da ta qunshi bayani kan azumi da hukunce-hukuncensa, da  Tarawihi/Tahajjudi da hukunciin sallar Tahajjudi da Amsakuwa (speaker) lailatul qadari, da bayani kan I’itikafi, da zakkatul-fitir, (Zakkan Kono) da sallar Idi.  Allah ya taimake mu Amin.
Azumi wata ibada ce da Musulmi ke yi, yana barin buqatar ransa don neman yardar Allah. Ta hanyar Azumi, bawa ke samun kusanci ga Allah da kuma samun lada mai yawa.
MA’ANAR AZUMI
Imam An-Nawawiy da Ibn Hajar Sun fassara Azumi da: “Kamewa ko barin wasu abubuwa Kevantattu, a wani zamani kevantacce, da wasu sharudxa kevantattu”. Azumi ya kunshi rashin cin abinci da shan abin sha da saduwa da mace (Jima’i) da kamewa daga qarya, tun da ga fitowar Alfijir zuwa faxuwar rana da niyyar bauta wa Allah.[1]
Ma’anar Ramadana a kalmar Larabci shine tsananin zafi shi ya sa  wasu malaman suke ganin ba a za a ce  kayi azumin Ramadana ba  sai Imamul Bukhari ya qulla babi da ke nuna ba bu laifi don ka ce ka yi azumin  Ramadana.[2]
Kuma azumi shi ne kamewa daga cin abinci da sha da saduwa tun daga fitowar alfijir har zuwa faxuwar rana domin neman kusanci ga Allah.
Allah Yana cewa “Ku ci ku sha har sai farin zare (alfijir) ya bayyana gare ku daga baqin zare (duhun dare)”[3]


WAJABCIN AZUMIN  RAMADANA
An wajabta azumin Ramadana ne a cikin shekara ta biyu bayan hijiran manzan Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam daga Makka zuwa Madina,  Allah  mai girma da xaukaka ya saukar da wajabcin Azumi ne cikin watan Sha’aban shekara ta biyu bayan hijira.[4]
 Manzon Allah sallallahu alayhi wa’alihi wasallam ya yi azumin Ramadana na tsawon shekara tara a rayuwarsa, cikin watan Sha’aban shekara ta biyu bayan hijira sa manzon Allah sallahu alaihi wa,alihi wasallam. [5]
Allah ya ce "Ya ku waxanda kuka yi imani, an wajabta maku yin azumi  kamar yadda aka wajbta ma waxanda suka wuce kafin ku, domin ku sami tsoron Allah…. Ranaku [kwanuka] ne  qididdigaggu.( iyakanttatu)[6]
Manzon Allah sallallahu alayhi wa’alihi wasallam  ya ce, “An gina musulunci a kan Rukunai guda biyar: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi manzon Allah ne, da tsayar da Sallah, da ba da Zakka, da aikin Hajji da Azumin watan Ramadan.[7]

     ASALIN AZUMIN WATAN RAMADANA
Asalin azumin Ramadana ba dole ba ne, wanda ya ga dama ya yi, wanda kuma ya so ya ciyar. Kuma  a wancan lokacin kwana uku a ke yi. Daga baya Allah ya mayar da shi Azumin Ramadan ya zama  wajibi.[8]
Al’umar da suka wuce kafin mu  tun daga zamanin Annabi Nuhu  har ya zuwa farkon zamanin Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Azumi kwana uku a ke  yi  a kowane wata. Amma daga zamanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Allah ya mayar da shi dole [azumin] a kan kowane musulmi.[9]
   Wanda ya qi yin Azumi ko ya fara ya karya da gangan ba da wata laluraba, Ya aikata babban laifi da ya zama wajibi ya tuba. Manzon Allah ya faxi cewa ya ga waxansu mutane a cikin mafarki an rataye su daga Maqyangyamarsu, gefen bakunansu sun varke suna zubar da jini. Da ya yi tambaya game da su, sai aka shaida ma shi cewa su ne waxanda ke cin abinci kafin lokaci ya yi a cikin Azumi, ba sa yin azumi, ko kuma suna karya shi kafin lokacin shan ruwa ya yi.[10]
Ibn Taimiyya ya ce, "Wanda ya halasta ma kansa qin yin azumin Ramadan alhali ya san cewa hakan haramun ne, to ku kashe shi. Idan kuma ya yi hakan saboda rashin biyyaya da               girmama addini amma ya yarda qin azumi haramun ne to ku yi masa azaba [dukan tsiya] saboda yaqi yin Azumi[11].
Imam Zahabiy ya ce tabbataccen abu ne a wurin muminai cewa duk wanda ya qi yin azumin watan Ramadan ba tare da wani qwaqqwaran dalili ba, (Kamar rashin lafiya, tsufa, tafiya da tsoron halaka) wannan mutum ya fi mazinaci da mashayin giya muni, kuma ana shakkar musuluncinsa kuma ana yi masa kallon Zindiqi kuma halakakke.[12]
FALALAR AZUMI
·        Azumi garkuwa ce daga wuta, yana kare wanda ya yi shi daga wuta.
·        Azumi zai yi ceto ga Wanda yake yinsa.
·        Ana tanadar wa mai Azumi gafara da lada mai yawa wadda ba ta da iyaka.
·        Azumi na shigar da mai yin sa Aljanna.
·        Azumi na taimakawa wajen samun tsoron Allah.
·        Wanda ya yi Azumi rana xaya domin Allah, Allah zai nisantar da shi daga wuta na tsawon tafiyar shekara saba’in.
·        Akwai kofa a Aljanna mai suna Rayyan wanda masu azumi ne kawai za su bi ta cikinta lokacin shiga Aljanna.
·        Wanda ya yi azumin Ramadan yana mai imani, Allah ya gafarta masa zunubansa.
·         Mala’iku  suna roqa wa mai azumi gafara har zuwa shan ruwa.
·        Ana gafarta wa mai Azumi a qarshen watan Ramadan.
·        Azumi yana maganin cututtuka masu wuyan magana.
·        Azumi na qara lafiya ga mai yinsa

GANIN WATA
Ana fara Azumi ne daga ranar da aka ga jinjirin watan Ramadan. Kuma ana shan ruwa yayin da aka ga jinjirin watan shawwal.[13]
Ko kuma cikar watan Sha’aban kwana talatin (30). Idan watan sha’aban ya kai kwana talatin ko ba a ga wata ba za a tashi da Azumi domin watan musulunci ba ya wuce kwana talatin, haka hadisi ya tabbatar[14]
  Ana yarda da ganin wata ne ta hanyar gani da ido ba ta hanyar anfani da na’urar hangen nesa ba, ko hisabi na taurari ko qidaya ta kalanda.[15]
Ibn Taymiyyah shi ma bai yarda a yi anfani da hisabi na taurari ko kalanda ba wajen xaukan azumi ko ajewa ba, ya ce abin da Annabi sallallahu alaihi wa’aihiwasallam ya umurce mu shi ne   ganin wata ba kuma ta hanyar hisabi ko kalanda ba, a a ya ma hana mu yin amfani da hisabi ne kamar yadda hadisin Musulim ya nuna.[16]

 Sheikh Hamud bn Abdullahi Tuwaijiri ya ce ‘’Anfani da hisabi ko kalanda bidi’ace a cikin addini ba kuma shari’a ba ce kuma yin amfani da su ya sava ma nassi ingantacce ya yi bayani mai gamsarwa da nuni da a daina amfani da hisabi ko kalanda wajen ibadun mu.[17]

* Idan mutun xaya ya ga wata, za a yi azumi, za kuma a ajiye azumi. Ibn Umar ya shaida wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa ya ga watan azumi, Manzon Allah ya yi azumin, kuma ya ba da Umurni da a yi azumin.[18] Wannan itace Magana mafi ingancin  duk da cewa akwai masu fahintar sai sun kai mutum biyu aqalla, kamar su Sheikh Samir wannan itace fahintarsa amma ba itace ingantatciya ba  magana ingantatciya ita ce ko mutum xaya ne za a yi azumi.[19]  
Haka ma idan mace amintattaciya ta ga wata za a yi azumin Ramadan.[20]
Idan wani gari suka ga watan Ramadan ko shawwal, to ya lazimci sauran garuruwan da suka samu labari su ma su yi Azumi.[21]
Sayyid Sabiq ya faxa a cikin Fiqhus-Sunnah cewa, “Mafi yawan malamai na ganin wajabcin Azumi a kan dukkan musulmai ba tare da la’akari da gari ba, ko qasar da aka ga wata ba saboda manzon Allah ya ce "Ku yiAzumin idan kun gan shi kuma ku sauke idan kun gan shi.” Wannan Annabi sallallahu alaihi wa, alihi wasallam na yin magana ne da duniya baki xaya, wato duk qasar da ta ga  wata, to ya zama wajibi sauran qasashe su xauki azumi wannan ita ce  magana ingantattaciya.
Babu wani dalili daga Allah ko Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da yake nuna cewa kar wanda ya yi   azumi sai ya ga wata,  Allah dai ya ce,’’wanda ya kai watan Ramadana to ya yi Azumi.’’[22]  
Don haka duk wanda ya ji sanarwar an ga wata to ya yi Azumi in ko ya qi yi, yana cikin fushin Allah da Manzonsa kuma yana cikin haxari domin ya sava wa Allah da Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam da kuma Malamai da kuma shuwagabanni.[23]

WAXANDA AZUMI YA ZAMA  DOLE A KANSU
* Musulmi mai hankali baligi kuma mai lafiya. Mazauni ba matafiyi ba. Muna iya cewa wanda Azumi ya zama dole a kansu su ne ;
1. Musulmi banda kafiri.
2. Baligi banda yaro, azumi bai za ma dole ba a kan yaro amma idan ya yi an fi son haka.
3. Mai hankali banda Mahaukaci.
4. Mai lafiya banda mara lafiya.
5. Mazauni banda matafiyi.
6.Yankewar jinin haila banda masu yin haila.
7.Yankewar jinin haihuwa banda masu jinin biqi.
 waxannan su ne sharudxan yin azumi.
Sheikh Usaimin ya xunqulesu wuri xaya ya ce: Al-Islam, Mukallafi(Baligi) AQil (mai Hankali) Qadir (mai iko).[24]

ALAMOMIN GANE BALAGA
1. Fitar maniyi a barci ko a farke namiji ko tamace.
2. Bayyanar gashin mara ko na hammata
3. Cika shekara goma sha biyar ga maza kamar yadda Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya tabbatar  a  lokacin da za a je yaki.
4. Jinin haila, idan yarinya ta fara ganin jinin haila a gabanta ko ’yar shekara takwas ce ta zama baliga kuma dole ne ta yi azumi.
5.  Fitowar mama ga mace inji waxansu malaman.
 Waxannan  su ne alomomin da duk wanda ya gani azumi ya zama dole a kansa ko a kanta.
5. Cika Shekara tara ga ‘ya mace tana iya zama baliga.
An so a umurci yara da yin azumi tun suna ‘yan shekara bakwai matuqar dai za su iya yi kamar yadda Baihaqi ya ruwaito daga   Ar - Rubay bint al Marwadhi. Idan suka qi yi bayan sun kai shekara  goma wasu malamai na ganin za a buge su har sai sun yi.[25]

NlYYA
Wajibi ne ka xaura niyyar yin azumin Ramadan tun da dare kafin fitowan Alfijir. Wanda bai sami labarin ganin wata ba sai ya zamanto ya tashi ba ya azumi idan ya samu labari (ko bayan Sallar la’asar ne sai ya yi niyyar azuminsa a wannan lokacin ya daina cin abinci, kuma  azuminsa  ya yi, don haka ba zai rama ba (amma fa ba a ce mutum ya shantake ba )[26].
Sheihkul Isam   ibn Taymiyya shi da xalibinsa ibn Qaym sunce azuminsa nanan babu komai a gare shi azuminsa yayi basai ya rama ba.[27]

WAXANDA  BA ZA SU YI AZUMI BA AMMA ZA SU RAMA
1. Matafiyi yana yin qasaru kuma yana ajiye azumi,  amma ajiye azumin shi ya fi, ko kuma wanda de yafi masa sauki.[28]
2. Mai haila
3. Wanda jinin haihuwa yake zuban ma ta.
4. ldan mai azumi ya ji tsoron halaka ko samun matsala a qwalqwalwarsa saboda tsananin yunwa ko qishi, ya samu ya karya Azumin nasa daga baya sai ya rama  amma ba shi zai ba kansa hukunci ba sai in wani malami ne ya bashi hukuncin ya karya azumin.[29]
5. Matar da ta yi varin cikin wata biyar yadda za a iya gane halittar da ta yi barin namiji ne ko mace.

WAXANDA  BA ZA SU YI AZUMI BA, BA KUMA ZA SU RAMA BA SAI DAI CIYARWA
1.      Tsoho wanda  ya tsufa sosai. Ibn Abbas Allah ya qara masa yarda   ya ce tsoho babba da mace tsohuwa waxanda ba sa iya azumi sai su ciyar da miskini guda xaya kowace rana.[30]
Haka shi ma Abu Huraira ya ce kullum sai su ciyar da mudu guda xaya na alkama.[31]
Anas shi ma da ya tsufa ciyarwa ya riqa yi ba ya Azumi.[32]
 Tsoho da tsohuwa waxanda baza su iya azumi ba saboda tsufarsu.[33] Wannan hadisi  ya qara mana bayani a fili na rashin asalin azumin tsofaffi wanda yake bidi’a ce wadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hani da a aikata ta (Bidi’a) don haka azumin tsofaffi ba addini ba ne tunda Allah ya ce tsoho ya ciyar. Haka nan kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  bai ce ga wata ibada ta tsofaffi ba amma banda sauran jama’a , don haka Azumin watan Rajab wanda akafi sani da Azumin tsofaffi ba addini bane al’adace kuma bidi’ace domin ganin qarin bayanin haramcin Azumin Tsofaffi duba waxannan littattafan na qasa.[34]
2. Wanda ke fama da rashin lafiya mai tsanani kuma ya yanke qaunar warkewarsa, misali ciwon gyambon ciki ‘ULCER’wanda ba ya iya daxewa bai ci abinci ba shi ciyarwa zai yi ba azumi ba.
   3. Mace mai cikin da ta ji tsoron faxawa cikin haxari ko ta ji ma abin da ke cikinta  tsoron faxawa cikin haxari ta na iya shan Azumi sannan  ta ciyar da miskini kullum har  a gama Azumi.[35]
 Tana iya tara  miskinai guda talatin ta ciyar a rana xaya kamar yadda ibn Umar ya yi, kuma ya umarci  ‘yarsa   da ta yi lokacin da take da ciki. [36] Ijima’i ne gabaxayan sahabbai akan cewa mace mai ciki ciyarwa zatayi ba Azumi ba  babu savani tsakanin sahabbai wannan ijima’in sahabbai ne.[37]
4.Sannan da  mace mai shayarwa, ita ma ta samu ta sha azumi sannan ta ciyar da miskinai guda talatin maimakon azumi da sharadin inzata wahala ko xan da ta  ke shayarwa zai wahala.

ABUBUWAN DA KE KARYA AZUMI
1. Jima’i: Akwai kaffara amma banda matar. Namiji ne kawai zai yi kaffarar.[38]
2. Zuwan Jinin Haila
3. Cin abinci da gangan.
4. Yin amai da gangan.
5. Zuwan jinin haihuwa
6. Shan taba ko wiwi da rana dama ita taba haramun ce shanta ko ba da Azumi ba
7. Allura a matsayin abinci ko qarin ruwa.
8. Yin qarya tana vata Azumi ba karyawa ba
9. Cin duk wani abu mai xaukar sunan abinci da gangan.

ABUBUWAN DA BA SA KARYA AZUMI
1. Kwana da janaba a jiki. Annabi ya kan wayi gari da janaba kuma yana mai azumi.
2. Kurkure` baki da shaqa ruwa.
3. Sanya tozali da rana.[39]
4. Sanya maganin ciwon ido.
5. Sanya   maganin ciwon kunne.
6. Fitar maniyyi ta mafarki da rana[40].
7. Yin qaho [41]
8. Rungumar mace da sumbatarta in ba ka da kaifin sha’awa.
9. Zuba ruwa mai sanyi a fuska ko a kai.
10. Xanxana abinci amma a tofar bayan xanxanawar.
11. Amai ba da gangan ba.
12. Maganin da masu cutar ‘ASMA’ ke anfani da shi wato                   (Inhaler) lokacin azumi ba ya karya azumi.
13. Shaqa maganin mura.
14. Xibar jini a jikin mai azumi ba ya karya azumi [42]
15. Cin abinci da mantuwa. [Allah ne ya ciyar da kai babu komi azuminka na nan].
16. Yin asuwaki ko makilin da burushi.[43]
17. Yin wanka a rafi
18. Zuba ruwa a kai domin jin sanyi.
19. Yin allura  a jiki da sunan Magani bata karya azumi.
20. Cire haqori ko cikesa ba ya karya azumi.[44]
Idan mace tana da ciki sai ta ga jini ya zubo mata a gabanta, babu komai domin wannan ba jinin haila ba ne, azuminta yana nan bai lalace ba, ciwo ne ta nemi magani. Amma da a ce tana haila sai ta ga hailarta ta xauke bayan alfijir ya fito ba zata yi azumi ba.[45]

 SHAN MAGANIN XAUKEWAN JININ HAILA  DOMIN MACE TA  YI AZUMI
Musulinci addini ne mai sauki baya kallafa  ma mutum abin da bai iya wa, akwai hikimar Allah wajen yin hailar mace,  Allah bai xaura wa mace cewa ta sha wani magani domin jinin hailarta   ya tsaya ba, amma da za ta sha wani magani domin hailarta ta tsaya  babu komai kuma azuminta ya yi  matuqar dai wannan jinin ya tsaya, da sharaxin cewa wannan maganin da ta sha baya cutarwa. Babban Malamin Hadisi Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albani ya ce babu laifi don mace ta sha magani don hailarta  ta tsaya don ta yi azumi ko Hajji ba bu kome a gareta kuma azuminta ya yi[46]. Shima Sheikh Mustafal Adawi ya ce babu komai azuminta ya yi indai wannan maganin ba zai cutar da ita ba kuma jinin zai xauke baki xaya, amma da jinin zai dawo azuminta ya vace kuma sai ta rama wannan azumin.[47]
YIN SAHUR
Yin sahur ba wajibi ba ne sai dai sunna ce mai qarfi, manzonAllah sallalLahu alayhi wa alahi wasallam ya ce “Banbancin Azuminmu da na Yawudawa da   Kiristoci (Nasara) shi ne yin sahur.                                                                                                                                                
 Ba dole ba ne mutun ya cika cikinsa da abinci lokacin sahur, ko ruwa da  dabino ya ci. Ana so a jinkirta sahur ya zuwa juzu’i na qarshen dare matukar alfijir ba zai fito ba.
  Kuma kana iya ci gaba da cin abincinka har sai ka gama ba komai a gare ka ko da an kira sallar subahi ne kira na biyu.
                                                 
 عن أبي هريرة
 عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال : إذا سمع أحدكم النداء والإناء على يده فلايضعه حتى يقضي حاجته منه[48]     
An samo hadisi daga AbiHurairah da ga manzon Allah sallallahu alayhi wa alihi wasallam ya ke cewa “Idan xanyaku ya ji kiran sallah ga kwanon abinci a hanunsa kada ya ajiye kwanon abincisa har sai ya gama cin abincinsa[49].
 Amma idan ba ka fara ba a ka kira sallah, ba za ka ci ba[50].
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, ‘Ku yi sahur ko da da kurvar ruwa ne’’.[51]
Wani hadisin Annabi ya ce, “Madalla da sahur xin mumini da ya yi da Dabino’’[52]
Wanda ya ci ko ya sha abin sha tunaninsa alfijir bai fito ba, a she  alfijiri ya fito,  babu komai a gare shi, kuma azuminsa yana nan[53]
Idan ka wayi gari baka azumin ba kasan an ga wata ba  sai da rana  labari ya isheka ba komai a gareka ka  daina cin abinci za kayi, ka azumci ragowar ranar   azuminka  ya yi ba sai ka rama ba wannan ita ce Magana inganttaciya, itace fahintar ibn Taimiyya da ibn Qaym[54]
Idan Afijr ya fito dole ka dena cin abinci ko ba akira sallah ba, idan kuma aka kira sallah kana da tabbas alfijir bai fito ba  ba zaka dena cin abincika ba. Amma sa mutane daina cin abinci da wasu mintuna ko kiran sallah alfijir bai fitoba yin haka Bidi’a ce.[55]

BUXE-BAKI
Ana buxe baki ne da zarar rana ta faxi, ba sai an kira sallah ba. Bidi’a ce jinkirta Shan ruwa wato buxa baki har sai an yi sallar magariba, matuqar  an mayar da yin haka wata qa’ida ce.
Ana son mai azumi ya yi addua yayin Shan ruwa.  adduar kuwa ita ce:  
            ذهب الظمأ وابتلت العروق وثبت الأجر إن شاء الله
"Dhahabaaz zama’u wabtalatil uruqu wathabbatal ajru insha Allah)[56]
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, “Mutane ba su gushe ba suna cikin alheri matuqar suna gaggauta buxa baki’[57]
·        Ana dai son mutum ya sha ruwa ne da zarar rana ta faxi, ba zai jira sai an kira sallah ba, ba kuma zai bari sai ya ga shafaqi ya voye ba. Yin haka kuskure ne a ce sai an ga ba a ganin shafaki. Idan shafaqi ya voye to wannan shi ne lokacin sallar isha’i. Ya kamata ‘yan’uwa su kiyaye wannan kuskuren.
·        Sunna ce mutum ya sha ruwansa [buxe-bakinsa] da Dabino xanye in hakan  ya samu. In kuma bai samu ba ya sha ruwa, ko wasu ’ya’yan itace, kamar Lemu, Mangwaro, Ayaba da dai sauransu.
Wanda ya yi zaton rana ta faxi, sai ya ci abinci ko ya sha abin sha, sai ta bayyana a gare shi cewa rana ba ta faxi ba, to babu komai a gare shi azuminsa yana nan daram-daqam.
 Sai ya qarishe azuminsa. Wannan ita ce fahintar Imamu Mujahid da Al-Hassanul Basariy,da Ishaq da Imam Ahmad bn Hambal wannan itace fahintar su.[58]
Wanda ya sha azumin watan Ramadan saboda rashin lafiya ko tafiya sannan ya mutu kafin ya biya, a dalilin haka ana bin sa. Waliyinsa ko xansa ko xan’uwansa zai ciyar da miskini xaya rabin sa'i na abincin da aka saba ci a gari a madadin Azumin kowace rana.  Wannan shi ne hadisi ya tabbatar ruwayar Abu Hazim.[59]
 Idan azumin alwashi ne ko bakance, waliyinsa zai rama masa azumin  a madadin ciyarwa.

   FAXAKARWA
Idan ka fara azumin aqasarka   sai kaje wata qasa  to bazaka sha ruwa ba  koda qasarka sun sha ruwa, sai  wannan qasar ta sha ko da ko azumin na ka zai wuce  azumi talatin (30) misali ace kai xan Najeriya ne kaje Makka ko Madina labari ya isheka ansha ruwa a Najeriya to kai baza ka sha ba sai Makka sun sha ruwa domin kai kana cikin  hukuncin xan Makka ne  ba xan Najeriya ba.[60]

ABUBUWAN DA AKE SO A YAWAITA SU A RAMADAN
1. Yawaita karatun Alkur’an.
2. Yawaita kyauta.
3. Sadaka.
4. Yin sallar dare.(Tarawihi ko Tahajjudi)
5. Shiga i’tikafi.
6. Yawaita yi wa Annabi salati.
7. Yawaita neman gafara (Istigifari).
8. Zuwa wajen wa’azi.
9. Yawaita yin tuba ga Allah.
10. Ciyar da abinci dafaffe da xanye.

Sheikh Muhammad Salih al-Munajid ya faxa a cikin littafinsa (As-siyam) cewa, “Daga cikin abubuwan da ke wargaza kyawawan ayukkan  mutum kuma su haifar masa da zunubai musamman a lokacin azumi, akwai kallon finafinai, da wasanni, da sharholiya, da zuwa wajen taro mara anfani, da zama a kan kwalbati ko kan hanyar jama’a, da yawo a mota ko mashin a cikin gari ba tare da dalilin da shari’a ta yarda  da ya gajiyar da kansa da rana ba, yadda da daddare ya kasa yin karatun al’qur’ani ko sallar tahajjud.”
Don haka ba a yarda mai azumi ya rinka ;
1  kallon fim xin ‘yan Hausa, fitsararru masu yaxa fasadi da vata tarbiyya, da duk wani fim na batsa ko wanda ya ke nuna rashin kunya ko  rashin kirki.
2.  Zuwa kallon qwallo: Bai halarsta ga mai azumi ya je ya kalle su ba, domin kallon qwallo haramun ne, akwai nuna tsiraici kamar fitar da cinya wanda bai halasta ba ga namiji da mace. Manzon Allah ya ce cinya tana daga al’aura. Haka ya gaya wa wani mutumi  da ya   fitar da cinyarsa.  Sai ya ce masa, ‘Rufe cinyarka domin cinya tana da ga ala’ura.[61]
3. Karta da caca Allah ya hana  su a cikin suratul Ma’ida su ma     haramun ne ga mai azumi da ma wanda ba ya azumi.             
4.         Hira da ‘yammata

WAXANSU ABUBUWAN DA YA KAMATA MAI AZUMI YA QARA NISANTARSU;
1        Mayar da dare ya zama rana.(Dogon hira)
2        Yin barci har lokacin salla ya wuce.
3        Almubazzaranci wajen cin abinci.
4        Tozartar da lokaci.
5        Yin sahur da wuri, kuma a koma a yi barci har lokacin sallar asuba  ya wuce.
6        Qin yin sallar Tarawihi.
ALLAH YA KEVE  WATAN RAMADANA DA
1        Mala’iku na roqa wa mai azumi gafara har ya yi buxa baki.
2        Warin bakin mai azumi  ya fi qamshin  turaren miski a wajen Allah.
3        Ana xaure shedanu.
4        Ana bubbuxe kofofin Aljanna a kuma rufe kofofin wuta.
5        A cikin Ramadana ne daren Lailatul Qadri  yake.
6        Ana gafarta wa mai azumi a qarshen ramadana

UMRA A CIKIN WATAN RAMADANA
 Haqiqa umra tana  daga cikin manya-manyan  ayukka da ke da katafariyar lada mai yawa a wajen Allah  musamman a cikin Ramadan. An samo  hadisi  daga Ibn Abbas Allah ya  kara masa yarda ya ce, ‘‘ Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, ‘yin Umura a cikin ramadana  yana daidai da kamar ka yi aikin Hajji tare  da ni ne’’’ .(wato tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)[62].

TAHAJJUD/TARAWIHI
Tahajjud, Qiyamul-lail, Sallar Tarawihi dukkansu ma’anarsu xaya, matukar dai a cikin watan Ramadan ne,  Mutum ya yi sallar nafila a gida ya fi lada da ya yi ta a masallaci amma banda na watan Ramadan. Sallar tarawihi a cikin azumi  ka yi ta a  cikin jam’i yafi  da ka yi kai kaxai a gida. Sayid Sabiq  ya ce junhuru sun tafi  kan cewa sallar tarawihi/Tahajjudi cikin jam’i  yafi lada da ka yi kai ka xai a gida.[63]  Sheikh  Zainudden Abdurrahaman ib Rajab al-Hambali ya ce ‘’Malamai sun dogara ne da hadisin da ya nuna cewa duk wanda ya yi sallar dare  tare da limani  har ya gama za a rubuta mai ladan ya  sallaci  daren ne baki xaya.[64]

 ADADIN RAKA’O’IN SALLAR TAHAJJUD/TARAWIHI
Sallar tarawihi raka’a goma sha xaya ce. An samo ruwaya daga  Nana A’isha Allah ya qara mata yarda, wanda yake nuna cewa Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam na yin raka’a goma sha uku[65], ita ce ruwayar da mai Risala ya kawo a cikin littafinsa Risalah[66]. Amma in ka duba Bugyatul Mutaxawi’i  ya haxa hadisan duka ya yi  bayaninsu. Don haka idan mutum ya yi sallar tarawihi ba zai yi tuhajjidi ba sai dai in ya tashi ya karanta Al-Kur’ani. Wasu malaman kuma sun ce zai iya yi matuqar bai yi wuturi ba amma in ya yi wuturi ba zai yi ba domin Tahajjudi  sai bayan  an yi barci an farka ake yinta.
Shi kuwa  babban Malami Sheikul Islam Ibn   Taimiyya ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai qayyade  yawan  raka’o’i    sanannu ba, sai dai shi ba ya wuce raka’a goma sha xaya ko sha uku a Ramadan ko ba Ramadan ba. Sai dai ya kasance yana tsawaita raka’o’i, amma a qarshe ya nuna cewa idan ka qara har ta wuce raka’a goma sha xaya ko sha uku ba komai, amma ya nuna cewa da za a tsaya a sha xaya ko sha uku ya fi in dai za a iya  daxewa cikin tsayuwar.[67]
Ibn AbdulBar  a cikin littafinsa  Attamhid’  ya ce ba bu savani tsakanin musulmai  cewa sallar dare  ba ta da adadi  qayyadadde   domin nafila ce, aiki ne na alheri,  wanda ya so ya taqaita wanda ya so  ya yawaita[68].
 Sheikh Mustaphal Adawi ya rubuta littafi mai suna ‘Risalatu Allatifa Fi Adadi Raka’ati Kiyamullaili’ A cikin littafin nasa yana da fahimtar cewa zaka iya wuce raka’a goma sha xaya  ko goma sha uku. Allah shi ne mafi sani[69].
Kamal Abu Malik   ya ce wanda yake tunanin cewa  sallar tarwihi iyakarta  raka’a goma shaxa, ya ce to ya yi kuskure.[70]
Manzon Allah ya yi sallar tarawihi sau uku a cikin jam’i, daga  baya ya bari saboda tsoron kar a wajabta ta a kan al-ummarsa[71].
 Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya ce wanda ya yi sallar tarawihi yana mai imani kuma yana mai neman lada, Allah ya gafarta masa zunubansa. Malamai sun tara dalilai waje xaya suka ce  wanda ya yi sallar tarawihi cikin jam’i ya fi lada don haka a yi a jam’i ya fi,[72]   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wata rana da daddare ya shigo masallaci sai yaga mutane a qarshen masallaci sai ya yi tambaya  ya ce waxancan me su keyi  sai mai magana ya ce mutane ne basu da hadda Qur’ani Ubay bn Ka’ab yake masu limanci  sai  Annabi sallallahu alaihi wa  alihi wasallam ya ce  ‘’sun dace kuma sun kyauta’’.[73]
 Wannan hadisin ya nuna mana a fili lalle sallar Tarawihi tana da asali, domin Annabi sallahu alaihi wa’alihi wasallam ya yi kuma ya tabbatar kamar yadda muka gani a hadisin da ke sama, don haka wanda ya ce sallar Tarawihi/Tahajjudi bidiace to yana qokarin danganta bida ga Annabi sallahu alaihi wa’alihi wasallam da Sahabbansa  Allah ya kauta.
Bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rasu, Sayyadina Umar ya raya sunnar  tarawihi cikin jam’i.  Don haka ba bidi’a  ba ce sallar tarawihi ko Tahajjud a cikin jam’i  domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi ta har sau uku. Kuma  ya bar yi ne don tsoron kar a wajabta ta ga al-ummarsa. Don haka wanda ya ce sallar tarawihi  bidi’a ce wannan  mutumi yana nuna wa duniya cewa lalle shi jahili ne. Kuma yana qoqarin dangata bidi’a ga Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Sahabi mai daraja wanda yana da ga cikin wadanda Annabi ya ce a yi koyi da sunnarsu kuma ya razanar da mu kan bidi’a  mu nisance ta yana da kyau mai karatu ya duba Majmoo’ al-Fataawa, 22/234, 235 na ibn Taimiyya zai ga magana gamsassa da take nuna cewa wanda ya ce Umar yana nufin Tarawihi /Tahajjudi bidi’a ce yayi kuskure babba domin sahabbai basa yin bidi’a yana da kyau mai karatu ya duba domin qarin ilimi.

MATA
Su ma mata suna sallar tarawihi da tahajjud. Hadisai masu yawa sun zo kan zuwan mata masallaci don sallar Tarawihi ko Tahajjud. Sayyidina Umar Allah ya qara masa yarda  ya  sanya limamai guda biyu : Ubayyi  ibn Ka’ab da Tamimud Dari xaya na ma maza limanci xaya nama mata.  Kuma duk sallar da ake yi mata na halarta, kuma raka’a goma sha xaya suke yi[74].
 Hakanan ma Tuhajjudi da ake zuwa cikin dare suma mata ya halasta suje  amma da izinin mazajensu  ko iyayensu in basu da aure iyayensu zasu tambaya kafin su fita zuwa masallaci,  amma in ana tsoron faxawa cikin fitina to babanta ya kaita ko mijinta ya kaita  ko kuma tayi agida in zata iya yi,  baba ko miji kar yahana ‘‘yarsa ko  matarsa zuwa masallaci sallar Tahajjudi koTarawihi tunda Manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam bai hana suba. Hadisi ya zo acikin Bukhari wanda manzon Allah sallallahu alaihi wa’aihi wasallam  ya ce ‘‘Kar ku hana mata bayin Allah zuwa masallaci in matar  xaya daga cikin ku ta ne mi izinin  zuwa masallaci to kar yahanata.[75] Amma kuma duk da haka  da zata yi agidanta yafi lada haka hadisi ya tabbatar koda ko a Makka ta ke ko Madina  tayi a gida yafi da taje masallaci.[76]
Ita kuma matar ko yarinyar dolene ta nemi izini kafin ta fita zuwa masallaci in taje bada izinin uba ko miji ba ta sava ma Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam kuma ana ji mata tsoron faxawa cikin halaka na sava ma Manzon Allah sallallahu alaihi wa’aihi wasallam. Kuma da mata za suyi sallarsu a gida yafi lada da suje masallaci haka hadisai suka tabbatar mace tayi salla a gida yafi da ta je masallaci.
Hadisi ya tabbata Ummu Humaidi ta zo wajen Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam  ta ce ‘’ Ina son in riqayin sallah tare da kai a masallacin ka  sai Manzon sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya ce mata ‘’’ Nasan kina son ki sallah tare dani to amma ki yi sallarki a xakin ki ya fi maki alheri da kiyi sallah a masallaci.’’[77]
SA MA MATA NA SU LIMAMIN
Ba bu laifi in an sa ma mata na su limamin  na masammam in masallacin yana da faxi da tsawo   mu na  iya cewa   yin haka ma  shi ya fi dacewa saboda  halin da muke ciki,  kuma ya tabbata    Nana Aisha Allah ya qara mata yarda tana da wanda tasa ya ke yin mata sallah ita da sauran mata suna binsa, kuma zamanin sahabi umar Allah ya qara masa yarda ya  kasance ya sanya ma mata sahabi Suleiman bn Hasmah ya yi wa mata limanci a  sallar Tarawihi/Tahajjudi. Sahabi Ali Allah ya qara masa yarda shima ya kasance ya na umurtan mutane da yin sallar Tarawihi/Tuhajjudi shine kuma wanda ya ke ma mata limanci.[78]
Shima sahabi Umar  Allah ya qaramasa yarda ya kasance yana  tara jama’a a masallaci suna sallar Tarawihi/Tuhajjudi, ya sanya ma maza na su limamin daban suma mata na su limamin daban wanda sahabi Umar ya sanya ya riqa yin ma mata limanci shine Sulaiman bn Abi Hasmah, su kuma mata  babban sahabi mahaddacin Qur’ani  Ubay bn Ka’ab Allah ya qara yarda da shi.[79]    
Yanayi da mu ke ciki in da hali a sa wa mata na su limamin daban kamar yadda aikin sahabbai ya nuna in ko babu wadatuwar masallatai a gari sai a yi tare ko kuma su matan a nuna masu suyi  sallar su a gida ya fi lada.
Godiya ta tabbata ga Allah yanzu Allah ya sa  masallatai sun yawaita mata akeve masu masallacin su shine daida kuma yin haka shine tafarkin sahabban Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam kuma haka aikin magabata ya nuna kuma shine mafifici da dace.   Gaskiyar labari dai shine mace tayi sallarta agida yafi lada da daraja da taje masallaci ya kamata mata su gane  cewa sallar su a uwar xakin su yafi lada da tayi a falo, haka hadisi ya nuna.  Duba Attamhid na ibn AbdulBar 23/398. Yana da kyau jama’a su gane cewa addini ba yayi ba, shari’a ita ce bin tafarkin magabata.             .                                                                                             
      
BUXE QUR’ANI
Ya halasta a buxe Qur’ani wajen sallar Tarawihi ko Tahajjudi   amma ba kowa zai buxe ba sai  dai Limami ne  kawai zai buxe banda sauran mamu.  Amma ba wai kowa ya buxe yana kallo ba, yin haka  bai da asali.  Amma buxewar limami ba laifi ba ne.[80]
Shima Sheikh bn Baz cewa ya yi  ba bu laifi limami shi kaxai ya buxe Qur’ani.[81]
Akwai hadisi a Bukhari da Muwadda da aka samu Nana Aisha  Allah ya qara yarda da ita  ta sa wani bawa nata mai suna Dhakwan yana masu sallar Tarawihi yana buxe qurani yana karantawa,  amma su Nana Aisha da sauran mamu ba su buxe ba, amma  a ce kuwa ya buxe yana kallo yin haka  ba shara’aba ce kuma bai da asali a addini don haka ‘yan uwa a kiyaye.[82] Wasu Malaman suna ganin kowa ya buxe Qur’ani yana dubawa Bidia ne domin babu wani magabata da su ka yi haka.

     RIYA/ SALLAH DA AMSA KUWA (LAUD SPEAKER) CIKIN DARE
Riya : shine mutum yayi aiki don wani yagani ba don Allah ba ko kuma yin wani aiki don a riqa labarin aikin, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsoratar damu yin Riya,  don  haka yana da matuqar mahimmanci masu yin Tuhajjudi ko Tarawihi a masallatai da su nisanci duk abin da zai kaisu ga Riya komin qanqantarsa.  Manzo Allah tsira da amincin Allah sutabbata a gareshi ya ce ‘‘Dayawa masu Azumi basu da Azumi sai dai yinwa  haka nan ma dayawa Masu sallar dare basu  da ladan sallar darensu sai dai wahala (saboda ba suyi don Allah ba)[83]
 Akwai wasu masallatai da dama zaka ji sun  sa Amsa kuwa (speaker) cikin dare suna sallar Tuhajjudi  ya hana mutune yin barci wannan gaskiya kuskure ne ba addini ba ne, musulunci ya hana quntata mawani bada haqqi ba, ba dolene sai ansa Amsa kuwa ba (speaker) ana iya yin  sallar batare da ansa ta ba domin ba domin mutane ake yi ba ana yini  ne domin neman yardan Allah da neman lada, in har ya zama dole sai ansa Amsakuwa (speaker) to sai asa na cikin masallaci kawai ba sai ansa ta wajeba   ko don gudun faxawa cikin Riya ko quntata ma wasu. Manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ji sahabi Umar Allah ya yarda da shi yana sallah da qarfi cikin dare  sai manzon Allah ya ce ma shi ya sassauta muryarsa.[84]
 Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce ma sahabi Umar  yarage muryarsa ba don komai ba sai dai don kar ya shiga haqqin wasu,[85] don haka ‘‘yan uwa mu kiyaye don Allah.[86]
In ka xauki Sunan AbiDauda za kaga ya kawo yadd manzon Allah sallahu alaihi wa’alihi wasallam yake karatu a cikin sallarsa da daddare  baya xaga muryarsa yadda zai damu waxan da ke barci, ibn Abbas ya ce ‘sallarsa wanda ke xakinsa ne kawai ya ke jinsa’’[87]

عَنْ عِكْرِمَةَ عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ
كَانَتْ قِرَاءَةُ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى قَدْرِ مَا يَسْمَعُهُ مَنْ فِي الْحُجْرَةِ وَهُوَ فِي الْبَيْتِ  
Sheikh Bin Baz  ya yi magana akan sa amsakuwa (speaker) wajen sallar Tahajjudi da daddare yanu yin haka bai da ce ba ba kuma  shara’a ba ce kuskure ne.[88]
Sheikh Albany ma ya nuna yin haka bai dace ba sa amsakuwa,  karatu na tashi yana damun na waje da makwafta ya ce wannan  ba dai dai ba ne. Ya qara da cewa ma su xaga sauti da karatu har ya kai ga  waxansu  quntatawa ne kuma ba dai dai ba ne bai kuma halasta ba[89]
‘Yan uwa ya dai kamata muji tsoron Allah mu daina yin aiki da ka mubar bin son zuciyarmu mun ga dai yadda manya manyan Malamai da duniyar Musulinci ke alfahari da su suka nuna mana cewa babu kyau sa amsakuwa (speaker) wajen yin sallar Tahajjudi cikin dare kuma hadisi ya gabata  Manzon Allah ya ce ma sahabi Umar ya rage muryar sa ka da ya quntata ma masu barci, kuma shi ma Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya kasance baya xaga muryar sa wajen karatun Qur’ani in yana sallah da daddare. Allah yaba mu ikon gyarawa Allah kuma yasa mufi qarfin zuciyarmu mu daina sa amsakuwa domin dacewa da sunnah kuma idan muka lura  za mugane cewa akwai caccakuxa karatun alQurani na wancan masallacin yana shiga na wancan yin haka kuma haramun ne kamar yadda hadisin  Abu Daud yayi bayani akan haka.[90]
SAUKE QUR’ANI  A CIKIN TARAWIHI/TAHAJJUDI
Manzan Allah sallallahu alaihi wa’alihi bai qaiyede iya  ayoyin  da mutum zai karanta ba  a sallar  dare ko Tahajjudi ko Tarawihi, sai  dai shi manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasalam  ya kasance ya kan tsawaita  wani lokaci  wani lokaci kuma ya taqaita ya tabbata wani dare ya yi sallah da surori mafiya tsawo acikin Qur’ani Baqara da Ali’Imirana da Nisa’i  da Ma’idah da An’am da A’araf da Tauba  a cikin dare xaya kuma alhalin bai da lafiya.[91]
Kuma wani dare yayi sallah ya karanta Baqara da Nisa’i da  Ali-Imirana a raka’a xaya kuma yana karantunsa a hankali.[92]
Kuma ya tabbata lokacin da sahabi Umar ya sanya Ubay bn Ka’ab yana ma sahabbai limancin sallar Tarawihi/Tajjudi ya kasance yana karanta aya 200 har mutane suna dogara da sanda sabo da daxewa yana sallah, basa gamawa sai gaf  da alfijir[93]  
Don haka ya danganta ga masu bin limamin ne in za su iya daxewa suna sallar  to ana iya daxewa, hakanan ma in zasu iya sauke kur’anin ba tare da an quntata ma kowa ba to ana iya yi amma ba dole ne sai an sauke Qur’ani ba, don ya tabbata  manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya yi sallah da aya xaya.[94]
Ansamu da ga magabata  suna sauke qur’ani a sallar Tarawihi/Tahajjudi kamar  Imamu Qatadah ya kasance  yana sauke qur’ani a cikin kwana uku a sallarsa a farkon Ramadana amma a goman qarshe kullun dare ya ke saukewa  a cikin sallah amma fa shi kaxe ya ke yin sallarsa.[95]
Sheikh Ibraaheem al-Nakha’i  ya kaance yana sauke qurani duk cikin dare biyu  a goman qarshe na Ramadana[96]
A mazahabar Hanabila da Shafi’i da ruwaya da a kasamo daga al-Hassan da ga Abu Hanifa cewa sunna ne a sauke Qur’ani  gaba xayansa a cikin sallar Tarawihi/Tahajjudi  sabo da jama’a su ji karatun Qur’ani gaba xayansa a cikin sallah. Mazahabar Hanafiya su kuma su ka ce  a sauke sau xaya.[97]
Abu Dawood ya ce an tambayi  Ahmad ibn Hanbal game da mutumin da ya ke sauke qur’ani sau biyu a cikin sallah sai ya ce ya danganta ne ga mutanen da suke binsa ko suna da qarfin da za su iya ko kuwa a kwai ma’aikata a cikinsu.
Ibn Rajab al-Hanbali  ya ce  maganar Imam Ahmad ta nuna mana liman ya lura da masu binsa kada ya quntata masu ko ya koresu ya hana su zuwa wannan ita ce fahintar wasu da ga cikin mazahabar Hanafiya.[98]

DUA’I KHATAMIL KUR’AN
Adduan  da ake yin in an sauke Qur’ani mai  suna  Dua’i KatamilQur’ani  yin wannan addu’an bidia ce. Za ka samu bayan an sauke Qur’ani zaka ji limani ya daxe yana karanta wata addu’a mamu su yi ta kuka wannan addu’ar   bidia ce   duba littafin Sheikh Bakr bn Abdullahi Abi Zaid.[99]

SIFFOFIN YADDA AKE SALLAR TARAWIHI/TAHAJJUDI
 Mai sallar Tarawihi/Tahajjudi  zai  iya yin  raka’a takwas  ba zai  zauna ba sai a  raka’a  ta  takwas sai  ya  zauna ya karanta  tahiya   amma ba zai sallame ba  sai   ya  tashi  ya qaro  raka’a  xaya sai ya sallame.[100]  Wato  raka’a tara  tahiya daya.   Ko kuma ya yi   raka’a 13  ya riqa yin raka’a   biyu  biyu yana sallamewa  sannan sai ya yi wutiri da raka’a uku.[101] Ko kuma  ya yi biyu biyu  yana  sallamewa har ya yi  raka’a shida  sai ya yi wutir da guda biyar   ba zai  sallama ba  sai a raka’a ta qarshe.[102] Zai kuma iya yin biyu ya sallame  yana yin  haka har  ya yi raka’a  goma  sai  ya yi wutiri da raka’a  xaya.    Wannan ita ce wadda muka   saba da ita  amma yana  da kyau mu riqa yin  sauran  nau’ikan, duk wadda muka yi sun inganta  daga Annabi sallallahu alayhi wa’alihi wasallam.


ADDU’AR QUNUTI
Bayan an gama karatun Qur’ani a raka’an karshe  sai ayi addua kafin a je ruku'o ya tabbata manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasalam ya na yi har ma ya koya ma jikansa  Al Hassan bn Ali adduar da zai riqa karantawa  a cikin Qunutinsa kuma ba bu laifi in ansa adduar Qunutin bayan an xago daga rukuo adduar kuwa ita ce.                                                                                                                           
 " اللهم اهدني فيمن هديت وعافني فيمن عافيت وتولني فيمن توليت وبارك لي فيما أعطيت وقني شر ما قضيت فإنك تقضي ولا يقضى عليك وإنه لا يذل من واليت ولا يعز من عاديت تباركت ربنا وتعاليت لا منجا منك إلا إليك
Daga nan sai kai ma Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasalam salati kuma kai ma sauran musulmai addua ta alkhairi sannan aima kafire mummunar addua sabo da sharrinsu da kuma cutardamu da su keyi.  Babu kyau rera Qunuti kamar yadda ake karatun Qur’ani duba littafin Bakar bn AbdulLahi Abi Zaid mai suna Du’ai Katamil Qur’an.[103]

ZIKIRIN DA AKE KARANTAWA BAYAN ANGAMA TARAWIHI /TAHAJJUDI
Ya tabbata  cewa bayan ka gama sallar dare bayan kayi wuturi a  kwai zikirin da zaka karanta sau uku(3) sau biyu ahankali  na ukun sai ka xaga muryarka da qarfi ka karanta,  zikirin kuwa shi ne.
سبحان الملك القدوس سبحان الملك القدوس سبحان الملك القدوس
Subhanal Malikil Quddus, Subhanal Malikil Quddus SUBHANAL MALIKIL QUDDUS

Na karshe sai ka xaga muryarka da qarfi wajen faxi.[104]

I’ITIKAFI
I’itikafi na nufin dimanta, lazimtar wani abu da kuma tsayar da rai a kanshi.  Ma’anar I’itikafi a shari’ance ta qunshi zama a Masallaci don yin ibada cikin wata siffa kevantacciya,  kuma cikin wata kama kevantacciya.[105]
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya kasance  yana yin i’itikafi na kwana goma amma a shekarar da ya rasu ya yi na kwana ashirin.[106]
Kai ma za ka iya yin na kwana ashirin. Ana yin i’itikafi ne a cikin masallaci kamar yadda Allah ya faxa a cikin suratul Baqara.

                ولا تباشروهن وأنتم عاكفون في المساجد          

1.      Ana iya yin i’itikafi a kowane lokaci. Hadisi ya tabbatar cewa Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi  i’itikafi a cikin watan shawwal [107]
An fi so a yi shi a kwanukan goman qarshe na Ramadana kamar yadda sunna ta bayyanar.
2.         I’itikafi sunna ce mai qarfi daga cikin sunnonin da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya dawwama yana aikatawa. Tun da Annabi ya fara i’itikafi bai bari ba har ya bar duniya kuma bayansa matayensa sun cigaba da yin i’itikafi[108].
3.         Imam Muhammad ibn Shihabuz Zuhri ya ce   game da falalar i’itikafi; “Abin mamaki yadda mutane su ke                   barin i’itikafi. Bayan kuwa Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam yakan fara wani aiki ya bar shi, amma Annabi tun da ya fara i’itikafi bai bar  yinsa ba har ya bar duniya”.
Imam Yahaya Ibn Mu’az ya ce “ban ga abin da ke kai mutun ga samun iklasi ba, irin mutun ya keve shi kaxai a masallaci yana tuna Allah.[109]
Akwai mutane bakwai da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce Allah zai sa su cikin inuwar al’arshi ranar da babu wata inuwa sai ta Allah.  Cikinsu akwai mutumin da ya keve shi kaxai ya ambaci Allah idanuwansa suka yin hawaye (kuka).[110]

FA’IDOJIN  DA MAI  I’ITIKAFI ZAI SAMA
1. Mala’iku na nema wa mai i’itikafi rahamar Allah da gafara kasancewarsa yana masallaci.
2. Samun Natsuwa.
3. Allah na biya masa bukatunsa .
4. Samun kusanci ga Allah .
5. Samun lada mai yawa.
6. Koyi da Annabi.
7. Mai i’itikafi na samun rahamar Allah.
8.  Amintuwa daga fitina kasancewarsa  a masallaci.
9.  Samun damar karatun Al-qur’ani.
10. Miqa wuya ga Allah.
11. Neman tuba.
12. Shiga inuwar Allah.
Hikimar yin i’itikafi  ita ce kamantuwa da   Mala’ikun Allah wajen shigar da lokacinka gaba xayansa  wajen yi wa Allah xa’a  da tsare zuciya daga  sha’awe-sha’awe,  da kusanci ga Allah wajen zama a xakin Allah (masalaci).




KWANAKIN I’ITIKAFI
Ana yin i’itikafi ne kwana goma ko abin da ya yi qasa da haka. Mutum zai iya yin kwana biyu ko uku ko  biyar ko shida ko kuma ya yi rana xaya.  Imam Malik ya ruwaito hadisi Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi i’itikafi kwana goma. Malamai sun ce mafi qarancin i’itikafi shi ne kwana xaya, ko kuma a ce rana xaya, ko kuma dare xaya, wato mutum yana  iya yin na rana xaya ko kuma dare xaya[111].
Idan ka yi niyyar yin i’itikafi na rana (yini) xaya, to zaka shiga masallaci kafin fitowar al-fijir [112] domin rana (yini) a lugga na nufin suna ne tsakanin fitowar al-fijir zuwa faxuwar rana.[113]

LOKACIN SHIGA I’ITIKAFI
Ana shiga i’itikafi ne kafin faxuwar rana ko kafin fitowar alfijir sai mutum ya shiga masallaci. Yana kuma iya shiga bayan sallar subahi kamar yadda hadisi ya tabbatar.[114]

SHARUDDAN YIN I’ITIKAFI
Dole ne wanda zai shiga i’itikafi ya cika wadannan sharuddan;
-Dole ne ya kasance Musulmi.
-Mai hankali banda mahaukaci.
-A mazahabar Abu Hanifa sai mutun ya balaga, amma sauran Malamai sun ce yaro ma zai iya  yin i’itikafi, wannan ita ce mazhabar Jumhuri,  ita ce kuma magana ingantacciya.
-Niyya: Dole ne a sami niyya yayin i’itikafi, niyya kuma  a zuci ake yi ba a furta ta. Yin lafazi da niyya bidi’a ce.
-Dole ne mutun ya kasance yana da tsarki banda masu haila da nifasi da mai janaba, waxannan ba sa yin i’itikafi sai sun yi tsarki.
ISTIHADHA
Istihala shi ne fitar jini a gaban mace ba cikin kwanakin haila ba, ko kuma jini ne da mace ke gani wanda ba haila ba ce ba kuma nifasi ba ne ba kuma Kuruh ba ne.[115]
 Idan mace ta saba yin haila kwana bakwai, sai kuma yanzu ta wuce kwana bakwai, to wannan jinin ba haila ba ce istihala ce za ta yi dukkan ibada ba komai.  Zata iya shiga i,itikafi. Mai istihala tana Sallah kuma tana Azumi, don haka malamai sun yi itifaki a kan mace mai istihala tana iya yin i’itikafi, babu sabani bisa cewa zata shiga masallaci ta yi i’itikafi ko na kwana nawa ne. Haka Imamul Xabari da Qurxabi da Imam Nawawi suka ce[116].

ME AKE  KARANTAWA CIKIN   I’ITIKAFI.
1. Karatun Al-qur’an.
2. Yawaita yin istigfari.
3. Yawaita yi wa Annabi Salati.
4. Yawaita salloli na nafila.
5. Yawaita tuba ga Allah.
6. Yawaita sallatul tasbihi.
    Wasu malamai sun ce babu laifi idan Malami ya karantar, ko dalibi ya ga wanda ya fi shi, ya je ya karantar da shi.[117]

ABUBUWAN DAKE VATA I’ITIKAFI.
1. Saduwa da iyali. (Jima’i).
2. Ridda.
3. Zuwan jinin haila.
4. Haihuwa.
5. Hauka.
6. Fita ba tare da uzuri ba.
7. Maye: Idan mutum yasha abinda ya ke sa maye i’itikafinsa ya baci.
8. Suma.
9. Aikata babban laifi kamar zina da shan giya da qarya da qazafi duk suna vata i’itikafi.
10.Hirar banza mara amfani yana vata I,itikafi.
ABUBUWAN  DA SUKA  HALASTA GA MAI I’ITIKAFI.
1. Barci a cikin Masallaci.
2. Fita saboda wani uzuri.
3.Cin abinci acikin masallaci kamar yadda Sahabbai su ke yi.
4. Sa turare da yin Kwalliya.
5. Yanke kunba da aske gashin mara da hammata, da yin aski.
6. Yin  Bukka( gurin zama kevantacce) a cikin masallaci.
7. Kevance wurin zama na musamman wasu Malamai na ganin shi ne ya fi   dacewa a ce kana da wuri kevantacce.
8. Zuwa da katifa ko tabarma. [118]
9. Zai iya bin sallar gawa idan an kawo ta masallacin.
10.Zai iya xaura aure idan an kawo xaura auren masallaci.
11.Zai iya fita domin cin abinci in babu mai kawo ma shi ko kuma ba zai iya dafawa ba.
12. Mutsa jini  mai I’itikafi babu laifi ya motsa jininsa a masallaci.
 FAXAKARWA;
Malamai na yanzu sun ce baya halasta shiga i’itikafi  da wadannan abubuwan;
1. Wayar salula. [Hand Set].
2. Rediyo
3. Jarida
4. Talabijin.
5. Kwamfuta [Computer].

INDA AKE YIN I’ITIKAFI
Malamai sun yi savani bisa Kan nau’in masallatan da za a yi i’itikafi a cikinsu. Ga yadda malamai suka kasu kamar haka;
Wasu na ganin za a iya yin i’itikafi a kowane masallaci, domin fadin Allah a cikin suratul Baqara da Allah ya ambaci yin i’itikafi, bai  ce ga irin masallacin da yake nufi ba, don haka suka ce ayar na nufin umum ne, don “ال’ ‘AL” da ke cikin ayar istigirakiya ce, don haka kowane masallaci. Sai dai sun ce idan zai kai kwanakin da yawa yadda zai haxa da Juma’a, to a je a yi a masallacin Juma’a ya fi domin yin Juma’a[119]
Wasu malamai na ganin sai a masallacin juma’a, wannan ita ce fahimtar Nana A’isha da ibn Abbas da sauran mazhabobi guda hudu (4) duk sun yarda za a yi i’itikafi a cikin Masallacin Juma’a.[120]
kuma wannan ita ce fahimtar sahabban Annabi baki xayansu  banda Sahabi Huzaifa da  tabi’i Said bn Musayyib.[121]
Wasu malamai na ganin ba a yi sai a masallacin Qudus kawai wato a masallaci guda xaya. [122]
Shi kuma Axa’u ya ce sai masallacin Makka da Madina kawai. Haka shi kuma bn Musayyib ya ce ba, a yin i’itikafi sai a masallacin Madina kawai.
Imam Malik da Shafi’i da Abu Hanifa da sauransu  sun ce ana yin i’itikafi ne a kowane masallaci ba sai  masllacin juma’a ba, sai dai kar ya kai zuwa ranar Juma’a.[123]
Wasu na ganin sai Masallatai guda uku; (3)
1.      Masallacin Kudus.
2.      Massalacin Annabi.
     3.  Massalacin Harami da ke Makka Ka’aba.           
Wannan ita ce fahimtar Sahabi Huzaifa ibn Yaman (Allah ya qara masa yarda) Baihaqi ya ruwaito hadisin. Huzaifa ya zo masallacin ibn Mas’ud ya ga ana yin i’itikafi, sai ya ce wa ibn Mas’ud ba ka hana su ba, kana kallonsu bayan ka san babu ittikafi sai a Masallatai guda uku: Masallacin Annabi da Masallacin Makka da Baitil Maqdis (Qudus)?  Sai ibn Mas’ud ya ce masa mai yiwuwa  sun dace kai kuma ka yi kuskure, kuma sun kiyaye kai kuma ka kamanta ne. [124]
            Wannan ita ce fahimtar Huzaifatu bn Yamani ita ce kuma fahimtar babban Malami Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albany daga baya amma daga farko al’amari yana da fahintar za a iya yin I’itikafi a kowa ne masallaci indai na juma’a ne[125].
Amma daga baya Albany ya tafi a kan  ba a yin ittikafi sai a masallatai guda (3): Masallacin Makka da na Madina da Kudus[126] Shi Sheikh Albani yana da fahimtar cewa wannan hadisi  ya yi wa ayar Allah da ke Baqara takasis

                     ولا تباشروهن وأنتم عاكفون في المساجد
                 
“Kada ku shafe su alhali kuna i’itikafi a masallaci.”[127]
 Domin ayar ta zo ne alaq, shi kuma hadisin ya yi taksisi. Kuma ya ce hadisin marfu’i ne saboda ziyadatul siqqah maqabula(wannan qa’ida ce sannan a wajen malaman Hadisi).
 Amma wasu malaman sun ce ba haka qa’idar  take a sake ba ziyadatu siqqah maqabula da sharaxi bai sava wa wanda ya fi shi aminci ba ( wannan ita ma qa’ida ce  sananniya).
  Wasu Malamai suka qara da cewa ai qa’idar ta usul wadda take cewa, “al-khas muqaddan mun alal-alam, ko Almuqayddan alal muttaq”, abin nufi a nan hukuncin da ya zo a iyakance ana gabatar da shi a kan wanda ya zo, ana gabatar da shi a kan wanda ya zo a game, amma da sharadin ba za a iya haxa su ba, a yi aiki da su ba. In za’a iya haxa su ayi aiki da su, to a haxa su a yi aiki da su shi ya fi Aljamm’u Awla Minat Tarjih.
Kuma malaman usulil fiqhu suna cewa a wata qa’ida ta usul
                                        المثبت مقدم على النافي
         Ana gabatar da tabbatacce a kan wanda ya kore.
Don haka hadisin sahabi Huzaifa ya kore, amma kuma hadisin Abdullah bn Mas’ud ya tabbatar, sabo da haka hadisin bn Mas’ud  za a gabatar, wato za a yi i,itikafi a kowane masallaci in dai na  juma’a ne.    
 Waxansu malaman sun ce wannan fahintar Huzaifa ce ba maganar Annabi ba ce, sun ce hadisi ne mauqufi ba marfu’i ba.
        Don haka a haxa hadisan a yi aiki da su shi ya fi kan a ce za a rinjayar da guda xaya, in dai duka hadisan sun inganta.
* Wasu kuma su ka ce akwai nakara a cikin hadisin domin ibn Mas’ud ya yi masa inkarin maganarsa ya ce masa, “Ka manta kuma ka yi kuskure. Su ne suke kan daidai…”                                                   Domin haka ne ma wasu malaman suka ce Huzaifa ya sava wa wanda ya fi shi ilimi wato ibn Mas’ud, suka ce maganar ibn Mas’ud za’a gabatar bisa kan ta Huzaifa.[128]
Wasu kuma suka ce Hadisin bai inganta ba, kuma yana da nakarar sanad da matan domin wanda ya ruwaito shi majahul hal ne.[129]
*Sheikh Kamal Abu Malik ya ce ana yin i’itikafi ne a kowane masallaci sai dai Jumhur sun ce ya kasance masallaci Juma’a amma maganar babu i’itikafi sai a masallatai guda uku (3) wannan maganar Huzaifa ce da Sa’idu bn Musaiyyib. Amma mazhabar Jumhur ta fi karfi, ya ce ‘’domin waccan maganar ta fi karfi, hadasin da ya zo kan guda uku anyi savani bisa ingancinsa[130]. Don haka za a iya yin I’itikafi in dai a masallacin Jumu’a ne.
Sheikh Muqbil Babban Malamin Hadisin qasar Yemen  ya faxa a cikin Littafinsa Risala Fil- i’itikafi ya ce hadisin bai inganta ba; Dha’if ne.
Amru bn Abdulmun’im ya ce a cikin ta’alikin da ya yi ma majmu’atul masa’il na Sheikh Albany ya ce: Hadisin yana da nakara matan da sanad.
Ibn Hazam ya ce wannan shakka ce daga Huzaifa ko ga waninsa ya ce wannan ba maganar Annabi ba ce, da Annabi ya faxi wannan da an samo shi ba shakka a cikinsa don haka Annabi samsam bai faxi wannan hadisin ba[131].
Abu Muhasin ya ce wannan maganar Huzaaifa nasika ce an soke ta don haka musulmai za su yi i’itikafi a Masallatansu domin ibn Mas’ud Allah  ya qara ma sa yarda  ya ce masa ka manta an shafe wannan hukuncin?
Imam  Kasim ya ce wannan in ma ya inganta, to yana nufin mafificin i’itikafi shi ne a masallaci  uku da muka sani.[132]
Sheikh Usaimin cewa ya yi wannan Hadisin tabbas bai inganta ba domin ya sava ma Umumul lafaz.[133]
 Sannan ya ce to idan ya inganta to ba yana hana i’itikafi ba ne yana nufin mafificin i’itikafi shi ne sai a masallatai guda uku: Masallacin Harami dana Madina da Qudus don haka za’a iya yin i’itikafi a kowanne masallaci in dai na Juma’a ne.[134]
Sheikh bn Baz Allah ya ji qansa ya ce ana yi I‘itikafi a ko wani masallaci in dai ana sallar Jam‘i a cikinsa a ko wani gari domin wannan itace  umumin aya ta nuna waddda Allah ya ke cewa
                          ولا تباشروهن وأنتم عاكفون في المساجد
Ya ci gaba da cewa sai dai mafifici  mutum yayi  a masallacin Juma‘a sabo da kada juma‘a ta same shi yana wani wuri yadda ba sai ya fita ba. bn Baz shima fihintarsa zakayi I‘itikafi a kowane masallaci.[135]
Shima Bakar bn Abi Zaid shima ya ce zakayi I’itikafi a kowane masallaci indai na juma’a ne ya ce babu dalili da zai hana ka  yin I’itikafi, hadisin da ya ce a masallatai uku in ya inganta  yana nufin mafificin I’itikafi shine a masallatai guda ukunnan masallacin Annabi sallallahu alaih wa’alihi wasallam da masallacin Qudus da masallacin Makka.[136]
Ana yin aiki da maganar sahabi in dai ba ta sava ma wadda ta fi ta ba. Don haka Huzaifa ya sava ma wanda ya fi shi ilimi (ibn mas’ud).
Fahimtar Imamul Bukhari ita ce yin i’itikafi a kowanne masallaci. Hadisai da yawa sun zo suna bayanin halascin i’itikafi a masallatan Juma’a. Don haka Imam  Bukhari ya qulla babi   a cikin littafinsa Sahihul Bukhari ya ce;

       باب الاعتكاف في العشر الأواخر والاعتكاف في المساجد كلها
 ‘i,itikafi a kowane masallaci,’’ sai ya kawo ayar  Allah da ke cikin   Suratul Bakara mai bayani a kan i,itikafi. Kuma shi Imamul Bukhari babban Malamin Hadisi ne da Fiqhu da tsantseni wanda  gaba xayan duniya ta yarda da iliminsa, da tsoron Allarsa, da kuma ilmin da ya ke da shi na hadisan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Sa‘id ibn Jubair da Abu Qilabh sun kasance suna yin I‘itikafi a masallatan anguwannin su.[137]
Baban Malami Alqali Abubakar ibnul Arabiy  ya ce ‘’ mazahar Malik a fili ya ke  shine yin I’itikafi  ako wani masallaci.
مَذْهَبُ مَالِكٍ الصَّرِيحُ الَّذِي لَا مَذْهَبَ لَهُ سِوَاهُ جَوَازُ الِاعْتِكَافِ فِي كُلِّ مَسْجِدٍ ؛ لِأَنَّهُ تَعَالَى قَالَ : { وَأَنْتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ } فَعَمَّ الْمَسَاجِدَ كُلَّهَا       
Zance mafi dadi shine yin I’itikafi a ko wane masallaci idai na Juma’a ne.[138]

Mai I’itikafi baya yanke qumba acikin masallaci ba ya lanqwasa yatsansa har ta ce qwas a Masallaci  ba ya kuma xaga muryarsa a masallaci ayi ta hirar duniya.
LAILATUL QADAR.
Daren lailatul Qadr ya fi watanni dubu wanda ba   wannan daren a cikinsa alheri, haka Qur’ani ya bayyana alherinsa ya fi na shekara tamanin da wata huxu. Hadisai sun zo suna bayanin samun wannan dare a cikin watan Ramadana ne. Sunna ta tabbatar kamar yadda Allah ya ce;[139]
1.         Kuma ana samunsa a cikin goman karshen Ramadan.
2.         Ana samun wannan dare ne a cikin kwanukan  mara, kamar daren 21,23,25,27,29,
3.         Amma an fi sa ran samunsa a daren ashirin da bakwai (wato bayan an kai azumi na ashirin da shida).                                                                                                                                                                                Amma hadisi ya zo manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce “ku neme shi (daren lailatulqadr) a dare na mara”.
An so mutum ya dage da ibada a cikin wannan daren ya raya sa da nau’o’in ibada, kamar karatun Alkur’ani da nafila da zikiri, hakanan ma an so mutum ya umurci iyalinsa da yin ibada a daren su dukkansu.
4.         Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce wanda ya yi tsayuwar daren lailatul qadri Allah ya gafarta masa zunubansa wadanda suka gabata.[140]
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya wa Nana Ai’sha (Allah ya qara mata yarda)  wata addu’a  da za ta riqa karantawa a wannan dare. 
                 اللهم إنك عفو تحب العفو فاعف عني

“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa fa’afu anni”.[141]


FALALAR DAREN LAILATUL QADR.
1.   Allah ya saukar da Qur’ani a daren.
2.   Allah ya girmama sha’anin  daren.
3.  Mala’iku na sauka a wannan dare da rahama da   albarka da   natsuwa.
4.         Akwai gafarar  zunubai.
5.         Aminci da salama na sauka ga masu imani.
6.         Ibada a wannan dare  ta fi  ibadar  wata dubu a wani dare wanda ba    wannan daren ba.
7.        Daren ya fi wata dubu.
8.       babu mai rasata sai marashin albarka.
9.    kashe garin daren rana kan fito

ALAMOMIN DAREN LAILATUL QADR.
Lailatul qadr na da alamomi da ake gane shi da su. Waxannan alamomi sukan kasance ne cikin daren kansa:
1.         Yanayi zai canza.
2.         Za a ji iska mai daxi, natsattsiya.[142]
3.         Natsuwar zuciya da kimtsuwa.
4.         Farin ciki cikin  zuciya  da samun jin daxin ibada.                                                                                           
5.         Za ka iya ganinshi (Lailatul Qadr) a mafarki kamar             
          Yadda sahabbai suka gani.[143]
6.     Rana zata fito ba zafi  (in lokacin zafi ne).[144]
Waxannan su ne alamomin da ake gane daren lailatul qadr. Amma da ake cewa itatuwa zasu faxi su yi sujada, zaka ga rana a kasa, karnuka za su daina kuka, za a ga taurari a kasa, wannan   qage-qage da tatsuniya  aka qaga a cikin addini wanda kuma ba gaskiya ba ne.

ZAKKATUL FITR.(ZAKKAN KONO)
Zakkatul fitr ita ce zakkar da ake fitarwa a qarshen shekara, wato qarshen watan Ramadana wanda ita ce Hausawa ke kira da zakkar  kono ko zakkar fidda kai. Kana iya fitar da ita a cikin azumi  kwana biyu kafin a  gama azumi kamar yadda Abdullahi bn Umar yake yi.[145]
 Idan ka bari har aka dawo sallar idi, to ya zama sadaka daga cikin sadakoki  amma ba zakkatul fitr ba ce, kamar yadda hadisi ya nuna kuma ita ce magana ingantacciya.

عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الْفِطْرِ طُهْرَةً لِلصَّائِمِ مِنْ اللَّغْوِ وَالرَّفَثِ وَطُعْمَةً لِلْمَسَاكِينِ مَنْ أَدَّاهَا قَبْلَ الصَّلاةِ فَهِيَ زَكَاةٌ مَقْبُولَةٌ وَمَنْ أَدَّاهَا بَعْدَ الصَّلاةِ فَهِيَ صَدَقَةٌ مِنْ الصَّدَقَاتِ . "               
 An karvo daga dan Abbas ya ce Manzon Allah sallalLahu alayhi wa ‘ali wasallam ya wajabta Zakkar Kono ne ta kasance tsarka ka ga waxanda suka yi azumi, sakamakon wargin da ya yi da kuma  maganar da bata daceba da ya  faxa a cikin watan, wanda ya ba yar kafin sallar idi Zakka ce karvavva  wanda ya bayar  bayan sallah Sadaqa ce daga cikin sadakoki ba Zakka ba ce wannan.[146]
Zakkatul fitr Manzon Allah sallalLahu alayhi wa ‘ali wasallam ne ya wajabta fitar da ita a qarshen azumi.
Ita zakkatul fitr ta wajibi ne a kan kowane musulmi, yaro ko babba, mace ko namiji mai ‘yanci ko bawa. Maigida shi ne ke fitarwa ga yaransa ko bayinsa ko matayensa ko wanda ke qarqashinsa.[147]
Ana fitar da ita ne daga sha’ir, dabino, cukwi, sultu da  nau’o’in abincin da mutane ke ci.
 Adadinta sa’i guda xaya shi ne mudunnabiyi sallallahu alaihi wa’alihi wasalam guda huxu kowane. Wata ruwaya ta ce rabin sa’i in zai fitar daga Jar alkama da ko qamhu.[148]
Ba a ba da kuxi, abinci a ke bayarwa  kamar yadda shari’a ta  nuna,ba kuma  a fitarwa ga  jaririn da ke ciki.
Wanda matarsa tahaifu  kafin faxuwar rana na Ramadana ko kuma a ka yi masa rasuwa ko wani ya musulunta ko wani ya yi aure kafin faxuwar rana za a fitar masu da Zakkar Kona, amma in bayan faxuwar rana ne ba zai fitar masu ba.[149]
Wanda aka tara masa Zakkatir fitr da yawa har ya ishe shi shima zai fitar da nasa zakkar.

HIKIMAR FITAR DA ITA.                                                                   
Tana tsarkake mai azumi daga kurakuran da ya yi a lokacin da ya ke azumi da kuma samar da abinci ga miskinai, don haka ne ma ba a ba da ta sai ga miskinai kawai. Bai halasta ba a ba wanda ba miskini ba.[150]
 Yana da kyau mutanen kowane gari su tara zakkarsu  a wuri xaya, sannan daga baya a rarraba ta ga waxan da suka cancanta. Manzon Allah sallalLahu alayhi wa ‘ali wasallam ya yi haka, kuma ya sa Abu Hurayrah ya yi gadinta.[151]
Ita zakkatir fitr zakkar jiki ce da zuciya, kuma bai halasta ka xauke ta  daga garinku  zuwa wani garin ba, sai dai in ba faqirai a garin.
Ta faxi ga matalauta, su wurinsu ba dole ba ne.[152]Amma idan an tara masa kafin idi ya wadata zai fitar da ita.

 FAXAKARWA
·        Badole bane ga miji ya fitar wa matarsa wanda bai riga ya sadu da ita ba, ya aure ta ba ta riga ta tare gidansa ba.
·         Idan matarsa ta bijire masa lokacin Zakkatir Fitr ba dole bane ya fitar mata ba, ita zata fitar makanta ba mijinta ba sakamakon bijire ma miji.
·         Hakanan ma idan matarka Kirista ce itama ba sai ka fitar mata ba.[153]
Ko lokacinta ya wuce dole sai ka fitar da ita sai dai baka da ladan Zakkar sai dai ka sauke nauyin da ke kanka na wajibi kuma sai ka nemi gafarar ubangijinka.[154]


SALLAR IDI.
Sallar Idi salla ce da ake yi bayan an gama azumi, ko kuma wadda ake yi bayan an gama aikin hajji. Hikimar sallar idi  kamar yadda Imamu Dahalawiy ya ce,  “kowace al,uma  tana da ranar da jama’arta ke haduwa a cikinta  suna kwalliya suna fita daga gidajensu  da kwalliyarsu  don nuna farin cikinsu ga wannan rana.[155]
An samo hadisi daga Annas Allah ya qara masa yarda ya ce, “Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya zo Madina ya taras da mutanen Madina na da ranaku guda biyu da suke wasa a cikinsu  a zamanin jahiliya. Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ‘Na zo na taras da ku kuna da ranaku da kuke haxuwa kuna nuna farin cikinku a cikinsu kuna wasanni waxanda kuke da su tun jahiliya. To daga yau Allah ya canza maku da ranaku mafiya alheri,  su ne ranar sallar layya, da ranar sallar buxa-baki.”[156]

HUKUNCIN SALLAR IDI
Sallar idi wajiba ce a kan musulmai maza da mata, har da masu haila su ma wajibi ne su je filin sallah, amma ba za su yi sallar ba. Amma dole su je, su nisanci  wurin sallar kamar yadda hadisi ya tabbatar.[157]
Wannan hukuncin ne Ibn Taimiyya ya xauka a cikin litafinsa Majmu’ulfatawa ya yi bayani mai tsawo da ke nuna wajabcin sallar idi a kan kowane musulmi namiji ne ko ta mace ce.[158]



A INA AKE YIN SALLAR IDI?
Ana yin sallar idi ne a bayan gari, haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi,  ya  kuma karantar da sahabbansa da a je bayan gari. Manzon Allah sallalLahu alayhi wa ‘ali wasallam ya yi sallar idi a bayan garin Madina daga gabas.
  Ya kuma tava yin sallar idi sau xaya a cikin masallaci saboda ruwa. Ibn Qayyim ya ce in ya inganta ya tava yinta a masallaci  amma abin da ya saba yi  koda yaushe shine yinta a bayan gari.[159]
 Bidi’a ce yin sallar idi a cikin gari ba tare da wata lalura mai qarfi ba, kuma karvavviya. Kamar ruwan sama ko wata lalurar mai qarfi kamar yadda ya zo cikin Sunnah.[160].
Ba a kiran Sallah ko iqama a wajen sallar idi.
Ba a yin nafilah kafin yinta ko bayanta.   Sai dai in ka dawo gida kana iya yin nafilarka.
Lokacin yinta lokacin da ya halasta a yi sallar nafila bayan fitowar rana.
Raka’a biyu ake yi.
Ana yin kabbara bakwai a raka’ar farko.
Kabbara biyar a raka’a   ta  biyu.
Ana yin huduba ne bayan an gama sallar kuma an so jama’a su saurari hudubar.
Huduba xaya ake yi, ba a zama a cikin hudubar, ba kamar ta juma’a ba ce. Ba a riqe sanda ko mashi wajen huxubar idi.
Idan Idi ya zo ranar Juma’a in kai idi ba dole bane kaje sallar Juma’a.
Ana fara huxubar ne da
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره  ونعوذ بالله من شرور

Ba a zuwa da munbari filin Idi.[161]
Ana tafiya ne ana  kabbara har filin idi sannan a yi ta yi har lokacin da liman zai zo.
Salllar layyah wato babban sallah anayin Takabiri ne na tsawon kwana uku a ko ina masammam bayan ko wace sallah. Ga yadda ake kabbaran:

 اكبرالله اكبر لا إِلَهَ الا الله والله اكبر الله اكبر والله الْحَمْدُ            الله

         Allahu Akbar, Allahu Akbar, walillahil hamad.
 Ko kuma mutum ya karanta wannan addu’ar: Allahu Akbar, Allahu Akbar, la’ilaha illalah Allahu Akbar, Allahu Akbar, walillahil hamad.[162]
An so mutum ya sa sababbin kaya domin nuna farin ciki.
An so a ci abinci kafin a je wajen sallar idi ta qarama, amma babbar sallah sai an dawo a ke so a ci abinci ka kuma fara da hantar ragon layya idan an yi.
Ba a yin wa’azi kafin liman ya zo, a qyale mutane su yi ta kabbara kamar yadda sunnah ta tabbatar wannan ita ce karantawar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.[163]
Ana son a canza hanya idan za a dawo daga idi.
Sunna ta koyar da a tafi wajen sallar idi  a qasa ne ba a hau mota ko mashin ko keke ba. Manzon Allah sallalLahu alayhi wa ‘ali wasallam yana tafiya a qasa ne yana riqe da kwagiri a hannunsa.[164]
Ya hana sa kaya masu ruwan kwai (yellow).[165]
Ya hana sanya jajayen kaya ya ce jan kaya na kafire ne.[166]
Kana iya kwana da wankanka tun cikin dare kamar yadda Abdullahi ibn Umar yakan yi.
Waxansu malaman sun ce an so mutum ya aske gashin kansa da na hammata da gashin mara da yanke kunba domin yin haka ita ce cikakkiyar tsafta.[167]
Idan mutum bai samu sallar idi ba zai iya yin raka’a biyu nafila ta sigar sallar Idi.suma mata da ba su samu sallar idi ba suma za su iya yinta a gida cikin jam’i.[168]
Idan wani gari ko qauye suka rasa sallar idi sabo da rashin samun labarin ganin wata za su i ya yinta (sallar idin) kashe gari.[169]

BARKA DA SALLAH.
Hausawa sun saba in sallah ta zo in sun haxu da mutum sai su rinqa ce ma junansu Allah ya maimaita mana. Faxin wannan kalma al’ada ce ba shari’a ba ce.   Abin da a ka samo wanda sahabban Annabi suke wa xan’uwansu in sun haxu da shi ita ce

 TAKABBALALLAHU MINNA WAMINKUM”.[170] 

تقبل الله منا و منكم[171]
    
Maimakon Allah ya maimata mana sai a faxi wannan addu’ar don ita ce abin da sahabbai suke ma ‘yan uwansu sahabbai in sun haxu da junansu, kuma in ka kalli wannan maganar sahabbai zaka ga addua ce da kuma fatan aheri.[172] 
Wannan shi ne abin da ya samu na bayani kan azumi da sauransu . Allah ya ba mu dacewa, a qarshe ina wa kaina da ’yan’uwa nasiha da su dage da ayyukan alheri a cikin wannan wata mai albarka domin sau xaya   ya ke a shekara.
BAYAN SALLAH
Haqika bayan Azumin Ramadana a kwai aiyukan alheri, alhare bai tsaya kawai a watan ramadana ba  suma sauran watani suna da na su falalar  da Allah  ya basu manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi ya umurce mu da yin azumi a  sauran watanni, ga wasu nau’ikan azumi da a ka  kwaxaitar da mu yin su domin samun kusance ga Allah.

AZUMI GUDA SHIDA A WATAN SHAWWAL.
Ana son musulmi ya yi azumi guda shida a watan shawwal, Manzon Allah sallallahu alaihi wa’aihi wasalam ya ce  idan mutum ya azumci watan Ramadan kuma ya bi shi da guda shida na shawwal kamar ya yi azumin shekara ne. Mutum zai iya yin su a jere in ya so, ko kuma ya yi su a rarrabe duk xaya ne wannan ita ce fahintar  Imam Ahmad bin Hambal. Shi kuma Abu Hanifa da Shafi’iyya suna ganin yin su a jere shi ya fi falala. [173]
Amma fa yana da kyau mu gane cewa wanda  ake binsa azumi ba zai yi  azumin shawal ba sai ya rama azumin da a ke binsa wannan ita ce magana ingantatciya kamar waxanda suka sha sabo da haila ko haihuwa  da sauransu  sai sun rama na Ramadana sannan za suyi sitta sahawal haka ibn Rajab al Hanbali ya faxa.[174]

AZUMIN TARA GA WATAN ZUHIJJAH ( RANAR ARFA)
Sunnace yin azumin ranar arfa, amma ga wanda yake gida banda mahajjaci, yin wannan azumi yana sa Allah ya gafarta mai zunubansa na shekarar da ta gabata da wacce za ta shigo.[175]

AZUMIN GOMAN FARKO NA DHUL HAJJ.
Nana A’isha Allah ya kara mata yarda ta ce Manzon Allah ya kasance yana yin azumin goman (Farko) na Zul Hajj. Waxannan kwanaki aikin alheri a cikinsu yana da tsananin Mahimmaci da falala a wajen Allah.
            Malamai sun qara wa juna ilimi a kan cewa, shin goman farkon Zhul Hajj suka fi falala ko kuwa goman qarshen Ramadan? Wasu sun tafi a kan cewa goman farkon Zul-Hajj sun fi, wasu kuma suka ce goman qashen Ramadan. Ibn Kayyim ya kawo maganan malaminsa ibn Taymiyya wadda ta ke nuna cewa dangane da dararruka, dararen goman karshen Ramadan sun fi falala, amma dangane da yini (wato ranaku) kuwa goma farkon Zhul Hajj sun fi falala .[176]

AZUMIN ASHURA.
Yin wannan Azumin yana sa a gafarta ma wanda ya yi azumin ranar  zunubin shekara guda kamar yadda hadisi ya tabbatar.[177]

YIN AZUMIN NAFILA A WATAN MUHARRAM
 Yin azumi a cikin watan Muharram na daga cikin azumin da suka fi falala bayan watan Ramadan kamar yadda Muslim da Abu Dauda da Wasunsa suka Ruwaito.

YAWAITA AZUMI AWATAN SHA’ABAN.
Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya kasance yana yawaita azumin nafila a watan Sha’aban kamar yadda  NanaA’isha ta gaya mana.[178]
AZUMIN ALHAMIS DA LITININ
Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya kasance yana yin azumin Alhamis da litinin inda ya nuni da cewa ana bijiro da ayyukan bayi ne a waxannan ranaku, inda ake gafarta wa muminai.[179]
YIN AZUMIN KWANA  UKU A KOWANE WATA.
Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya nuna cewa duk wanda ya kasance yana yin azumin kwanaki uku a kowane wata kamar ya yi azumin shekara ne baki xaya. An so idan mutum zai rika yin wannan azumi, to ya yi a cikin AYYAMUL BIDI wato Ranakun 13, 14, da 15, na kowane wata.

AZUMIN  KWANA  XAYA  KA  AJIYE   KWANA
 DAYA
Wannan shi ne mafificin azumin nafila. Kuma shi ne azumin Annabi Dauda wanda Manzon Allah ya nuna cewa shi ne mafi falalan azumi (Nafila) kuma mafi soyuwa a wajen Allah, kamar yadda ya tabbata.[180]
KWANAKIN DA SUKE HARAMUN NE  AZUMUNTAN SU
Wajibi ne musulmi ya guji yin azumi a waxannan ranaku masu zuwa.
1.                  Ranar idi (Babban sallah da qaramar Sallah).
2.                  Kwanaki ukun bayan babbar Sallah.
3.                  Ranar Juma’a kaxai ba tare da haxa ta da wata ranar a jere ba.
4.                  Ranar Shakka, (wato ranar da ake shakkar cewa tana cikin Ramadan ne ko sha’aban.
5.                  Yin azumin kwanakin shekara baki xaya.
6.                  Bai halatta mace ta yi azumin nafila alhali mijinta na nan ba, ba tare da izininsa ba. Amma idan baya nan ya yi tafiya babu laifi a gare ta idan ta yi ko ba da izininsa ba.









                 KAMMALAWA
Wannan shi ne abin da ya sauqaqa na bayani kan azumi Allah ka taimake mu baki xaya kuma ka gafarta mana zunuban
mu amin. Wanda ya ga  kuskure ko gyara yana iya kirana  insha Allahu zan amsa masa kuma ina maraba da gyaransa zan  kuma gyara kuskuren da yardan Allah.  
A qarshe ina roqon addua ta alheri  ni da iyaye na  ga duk wanda ya karanta littafi na, na gode Allah ya saka da alheri amin.
                      
‍ والله تعالى أسأل أن يجعل هذا العمل مقبولاً، مباركاً، خالصاُ لوجهه الكريم، وأن ينفعني به في حياتي وبعد مماتي، وأن ينفع به كل من انتهى إليه؛ فإنه سبحانه خير مسؤول، وأكرم مأمول، وهو حسبنا ونعم الوكيل، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم،                         
وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لاإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك
               Wassalamu alaikum warahamatullahi barakatuhu
                                Harun Abubakar shika
                08030582333-08020900001-08054533361
                   http://harunaabubakarshika.blogspot.com


[1] معنى الصيام الشرعي، وهو الإمساك عن الطعام والشراب والشهوة تعبداً لله تعالى، واستجابة لأمره، ومسارعة لرضاه                                                                                     
Muslim sharhin Nawawi 181/8 da Fathul Bari 197/4
[2] Bukhari  
[3] AlBaqara 187
[4] Fiqhu ala mazahibul Arba’a da Nayl alAwwatar as shaukany
[5] Fatawaa Imamin Nawawi 152 da ZadulMa’ad 2/26
[6] Baqara 183-183
[7]  Bukhari  hadisi 63
[8] Zadul Ma’ad 29/2
[9] Tafsirul Ibn Kasir
[10] Sahihu Targhib wattarhib Imamul Munzir 1005
[11] Maaju’ul fatawa
[12] Fiqh as Sunnah Sayid Sabiq
[13] Bukhari da Muslim
[14] Bukhari da Muslim
[15] Sahihu fiqhus sunnah
[16] Maajamu`ul Fatawa
[17] Qawa’idul adillah fi raddu ala man Awwala Hisab fi Ahiliah. Wannan zai nuna mana kuskure anfani da Kalanda  wajen fara azumi,  magabata da dama sunyi hani akan yin ibadu tahanyar amfani da kalanda ko qayyade yin amfani da agogo wanjen yin sallah, ba shakka yin haka kuskure ne mu  ta’allaqa ibadarmu qarqashen yin amfani da kalanda ko agogo,littafen Fiqhu duk sun nuna mana yadda ake gane lokacin sallah ba wai anfani da agogo ba ko kalanda kuma kusan duk littafin  hadisai  sun nuna mana yadda ake gane lokacin  sallah, kuma manzon Allah sallahu alaihi wa’alihi wasallam ya nuna ma alummarsa yadda ake gane shigar lokacin sallah  ba wai amfani da agogo ba, gaskiya  kuskure ne babba yin amfani da kalanda ko agogo wajen  yin sallah ko azumi   muyi qoqari mu koyi yadda shari’a ta koyar da mu wajen gane lokutan ibadunmu abin baqin ciki yau an wayi gari mutane duk sun koma amfani da kalanda/Agogo wajen yin sallah har kaga ana qayyade lokacin sallah ba a la’akari da yadda shara’a ta koyar  ko canjin lokaci ba, Allah ya bamu ikon gyarawa amin.
[18]  Bayhaqee da Abu Dauda
[19] al ilmam fi Ahkamil wa’adabil Siyam 16-17 da Zadul Ma’ad
[20] Sharhul Muntah da Muhalla lbn Hazam
[21] Irwa ‘ul ghalil 
[22] Baqara
[23] Akwai waxansu zakaji suna cewa me yasa azuminmu  kullum 29 bai kaiwa talatin wannan maganar alamace ta wanda ya ke faxenta baya zuwa makaranta ko kuma yana bin son zuciyarsa ne ba shari’a  ba ne  domin dama asalin watanin Musulunci 29 ne sai in ba a gansaba akeyin 30 kuma mutambayi tarihi shin Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya tavayin azumi talatin 30?.   Kuma ya gaya ma Nana Aishatu  Allah ya qara mata yarda cewa wata 29 ne duba Bukhari qissar qauracewarsa ga iyalinsa.
[24] Al-Jami’u Ahkami fiqhussunnah 2/199 da Mulaksul Fiqhiyah
[25] Muguni ibn qudma
[26] Nayl Autar da Sifatus Saumin Nibiyy
[27]Majamu’ul fatawa 109/25 da Zadul ma’ad 74/2 da MuktaraatulJalila na ibn Sa’adi 60.  
[28] Al-Jami’u Ahkami Fiqhu Sunnah  101-102
[29] Lajnatul Da’imah.
[30] Bukhari
[31] Darukudini
[32] Darukudini
[33] Bukari.
[34] Ladi iful ma’arif   na ibn  Rajab da Kitabul Hawadif  wal Bidi’i na Imam Abubakar Xarxusi da Al-manir Munif fil  Ma’a ihi Dha’if  na ibn Qayyim da  Bayanil ajaa’ib fima warada fi Fadhali Rajab na  ibn Hajar
[35] Tafsirul Xabari, Xabarani Baihaqi.
[36]  Baihaqi da ibn Jarud
    
[37] Irwaulghalil
[38]  Majmu’ul fatawa
[39] Fathul Bari
[40] Subulussalam
[41] Bukhari
[42] Fatawas-siyam,  Uthaymin
[43]Siyamu ramadan na Jamil Zainu.

[44] Munajjid  70 question on Fasting.
[45] Fatawa siyam Usaimin.
[46] Fatawa Sheikh Albani 232
[47] Jami’u Ahkamun Nisa’i na Sheikh Mustafal Adawi 2/393
[48] Ahmad da Abu Dauda da ibn Kuzaima
[49] Ahmad da Abu Dauda da ibn Kuzaima
[50] Ahmad, Abu Daud, Ibn Jarir da Hakim
[51] Ibn Hibban
[52]Abu Dauda da Ibn Hibban
[53] Fathul Bari 4/200
[54] Majmu’ul Fatawa110/25 da Ummu 95/2  da Zadul Ma’ad   amma wasu malaman suce zaka rama  wallahu  A’alam
[55] Saba’una  mas’alah fi siyam da Majmu’ol Fatawa 25/210
[56] Abu Daud 2357 da Nasa’i fil Kabir 10131-339
[57] Bukhari
[58] Fathul Bari   4/200
[59] Ahmad
[60] Fauzan Dalilil Siyam wa’adabuhu
[61] Ahmad
[62] Bukhari da Muslim
[63] fiqhuSunnah
[64] Shi kuwa Imam malik yana ganin ka yi a gida ya fi  shi yasa ma yake yin nasa sallar Tarawihin/Tahajjudinsa a gida, dogaransa da  maganar Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam  da ya ke cewa ‘ Mafificiyar sallar mutum wanda ya yi a gida sai dai in ta farilla ce’’ wannan itace hujjarsa su kuma Junhurun Malamai hujjar  su  ita  ce hadisin da ya ce ‘‘ wanda ya yi sallar dare tare da limami  har yagama za a rubuta mai ladan ya sallaci daren ne baki xaya’’duba Muguni na ibn Qudamah 607/2 da Qiyamu Ramadan 19-20. Imam Ahmad bn Hambal yana yin sallar Tarawihi ne a masallaci yana bin limami  har sai angama sallah saboda ya sami ladan da Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya faxa na ladan wanda yabi liman sallar dare har ya gama,  Malamai dai sun rinjaya a kan yin sallar Tarawihi/Tahajjudi a masallaci ya fida lada da  kayi kai kaxai a gida, wallahu a’alam.
[65] Bukhari
[66] Risalah ta Abi zadil al Qiyrawan
[67]  Majmu,ul fatawa mujalladi 22 shafi 272-273.

[68] Attamhid
[69] ‘Risalatu Allatifa Fi Adadi Raka’ati Kiyamullaili’
[70] Sahih fqhu Sunnah  1-415
[71]Bukhari da Musulim.
[72]Salatut Tarawihi
[73] Baihaqi
[74]Muwatta
[75] Bkhari 
[76] Duk wanda ya hana ‘yarsa ko matarsa zuwa masallaci lalle ya sava ma Allah ana ji masa tsoron faxawa cikin musiba.   Sahabi Abdullahi bin Umar ya ce kar ku hana mata zuwa masallaci sai Xansa ya ce sai ya hana su saboda  abubuwan da suka qago sai Abdullahi bin Umar ya ce ina gaya ma kar ahana su kana cewa sai ka hana su Abdullahi bn Umar ya yi masa mummunan zagi wanda bai tava yi ba. Nana Aisha Allah ya qara mata yarda ta ce da manzon Allah sallahu alaihi wa’alihi wasallam ya rayu  har  yanzu  da ya hana mata zuwa masallaci sabo da  abubuwan da su ke yi  amma ba wanda zai hana su tun da Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam bai hana su ba.
[77] Ahmad 6/371 da ibn Khuzaimah 3/95. Gaskiyar labari dai shine mace tayi sallarta agida yafi lada da daraja da mutunci da taje masallaci ya kamata mata su gane  cewa sallar su a uwar xakin su yafi lada da tayi a falo, haka hadisi ya nuna.  Duba Attamhid na ibn AbdulBar 23/398 ya yi bayini sosai da ke nuna sallar mace a xakinta ya fi lada da taje asallaci. Mutane yanzu sun mai da addini yayi ba shara’a ba ya dai kamata Malamai su nuna ma mata abin da ya ke daidai ba yayi ba. A duba littafin Ahkamun Nisa’i na Amru bn Abdul Mun’in shafi na 20.
[78] Baihaqi 494/2
[79] AbdurRaz  fi Musannaf 4/258
[80]Wasayan Nisa.
[81] AlJawabusSahih min Ahkami SalatilLaili  da Salati Tarawihi 26-27
[82] Buxewan kowa yana hana natsuwa da kuma tadaburin ayoyin da ake karantawa ga kuma hana ka natsuwa tun da ba kai ne liman ba.
[83] Bukhari da Musuim za mu iya tunawa da sahabin  ya ce yaga Taurariya ta faxo daren jiya sai ya yi sauri ya ce amma ba sallah ya ke yiba, ya faxi haka ne don gudun RIYA, saboda riya vata aiki ta keyi don  haka a kula.
[84] Bukhari
[85] Wannan zai nuna mana rashin kyautawan masu sa karatun Kur’ani cikin tsakiyar dare   su hana mutune sakat gaskiya yin haka kuskure ne don Allah ‘yanu uwa a kula Kur’ani yana da qa’idoji a yi qoqarin kiyayewa kar muzama kamar ‘YanBidia masu sa shirme cikin dare ko kuma wani mara kirki ya shiga masallaci cikin dare ya kama wasu  ayayyaku na rashin mutunci da ya kamata,  mutane na da haqqi kar mu shiga haqqinsu kowa a kiyaye masa haqqinsa, Allah ya shiryemu amin.
[86] Ba hujja ba ce a ce ana sa Amsakuwa (speaker) domin a tashi wasu, shima sahabi Umar ya ce ma Manzon Allah  sallallahu alaihi wa’alihi wasallam  yana yi ne domin ya tayar da mai barci amma Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya hana shi ya ce yayi qasa da muryarsa don gudun kar ya shiga haqqin  masu barci a wannan lokacin, kuma yana da kyau mugane  ba dole ne lokacin da ka ke  yin naka sallar  nima yazama dole sai nayi a wannan lokacin ba.
[87] AbuDauda,  akwai abubuwan da ya kamata makaranta Kur’ani suji tsoron Allah su barsu don basu cikin karantarwan Manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam kamar  haxuwa a sauke Kur’ani domin wata biyan  buqata ko wani  ya ba da kuxi a sauke  masa  Qur’ani  domin wata buqatarsa yin haka Bidi’a ne ba addini ba ne, da Musabaqar Karatun alQur’ani  da a keyi, babu wani ahlulSunnah   na gaskiya da zai kawo  hujjar Musaqa domin babu Aya ko Hadisi  ko da mai rauni da ya  halasta yin musabaqa  kuma munsan cewa karatun Qur’ani ibada ne ba  a  kuma a yin  ibada sai da dalili daga Allah ko Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam musabaqa kuwa babu dalili ko mai rauni, yadda mu kasan Maulidi bai da hujja ko mai rauni to itama musabaqa babu hujja ko mai rauni don haka itama bidi’ace, in Allah ake nufi mubari  in ko wani abune  na duniya  ake nema, to wannan kuma wani abune,wasu na cewa wai ta haka yara ke haddace Qur’ani to abin tambaya anan shin yaya yaran magabata suka yi suka haddace Qur’ani, kuma Sahabin Annabi sallallahu alaihi wa’aihi wasallam  Huzaifa ya ce ‘‘ kuji tsoron Allah ya ku makaranta Qur’ani kubi kar ku qirqiro’’ kuma hadisi ya tabbata a Bukhai daga Abu Huraira ya ce mazon Allah sallahu alaihi wa’alihi wasallam  ya ce ‘‘Waxan da za su fara shiga wuta sune makaranta (mahaddata) al-Qur’ani  saboda ba su  yi don Allah ba.  Musabaqa  kuma gashi tana sa riya  yau an wayi gari ta koma kamar  wasan  Qwllo kowa da wanda ya ke goyan baya ‘yan gari kaza suna goyan bayan nasu waxancan gari suna goyan bayan nasu wannan ba shi ne manufar saukar da Qur’ani ba mu dai ji tsoron Allah kuma mu guji Bidi’a, komai qanqantarta  yana da kyau makaranta su ji tsoron Allah su san cewa Allah zai tambayesu ranar Qiyama yana da kyau a  nemi littafin Dabibul Namla da Bidi’ul Qurra’a na Bakr bn Abi Zaid Ahlul Sunnah basa yin komai  sai da hujja, lalle  muji toron Allah mu guji aikin da bamu da hujja daga Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasalam. Kai a halin yanzu yadda musabaqa ta ke ko don Sadduz Zari’a ya kamata a daina musaqa, inma da ta halasta, kuma ya kamata mu lura da  qaidar DAF’UL MABSADA MUQADAMUN ALA JARHIL MAN FA’A wannan qa id ace sananna kuma Mazahabar Malikiyya ba ta yarda da Musabaqar Qur’ani ba akwai wani babban Malami a Saudiya mai suna Suleiman Nasihil Ulwan ya rubata littafi masamman da ta ke nuna haramcin yin Musabaqa.  Kuma hadisi ya inganta da manzon Allah sallallahu alayhi wa a lihi wasallam yake  cewa ‘' Ba bu musabaqa sai a abubuwa guda uku tsere da Raqumi da tsere da Doki da kuma kibiya" Ahmad ya ruwaito wannan hadisi. Wannan hadisin Annabi sallallahu alayhi wa a lihi wasallam bai ambaci   musabaqar karatun Qun’ani ba to   mu ina hujjar mu. Allah Akbar Allah ya jiqan Sheikh Ja’afar Mahmud Adam  ya zo gidan Redion Nagarta da ke Kaduna aka tambaye shi hukuncin maulidi ya ce Bidia ne wani bawan Allah ya bugo  waya ya  tambaye shi  to ita kuma Musabaqa fa sai Sheikh Jaafar  ya  ce ita ma Bidi’a ce.  Mai karatu ya ne kaset xin da ya yi bayani akan son Manzon Allah ya yi shi ne a Kaduna a gidan Redion Nagarta a shekarar 2006.
Kuma bincike ya tabbatar da cewa mafiya rashin Tarbiyya a yau   masu rena Malamansu sune ‘Yan musabaqa mazansu da matansu, Allah ya shirye mu ya ba mu ikon gyarawa amin.
[88] Majmu’ul Fatawa na bn Baz 12/392
[89] Kaifa yajibu alaina an Nufassirar Qur’an  17 sannan ka duba wani littafi mai suna  Muktasaru Mukalifatu Daharatu Was Salah
[90] Yi ba  amsakuwa yafi dacewa yafi kuma kyautata zato kuma rashin sa amsa kuwa zai taimaka wajen rashin shiga haqqin waxansu da kuma kariya daga riya.
[91] Hakim da Zahabi
[92] Muslim
[93] Malik
[94] Ba wai abinda ragwage ke xauka quntatawa ba, sunfi son shap-shap  a riqa karanta  surori qanana  wannan ba gaskiya bane gakiyan labari  a yi yadda manzon Allah  sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya koyar .
[95] Siyaamu Ramadhan Fadhailuhu wa Ahkam 35
[96] Fatawaa bn Baz
[97] al-Mawsoo’ah al-Fiqhiyyah 27/148
[98] Lataa’if al-Ma’aarif  ya xai kamata liman ya lura da mabiya kar ya quntata masu ya hana su zuwa ashan ko Tahajjudi mu tuna da qissar sahabi Ma’az bn Jabal da ya ke tsawaitawa a ciin sallah har mutane su qosawa sai   manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam  ya ce masa kana so ka zama mai kawo fitina ne, sannan Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce masa in kazo zaka yi sallah ka sassauta domin akwai raunana da marasa lafiya da ma su mabuqata, don Allah ‘yan uwa mu kulla da shariar Allah kar mubi son zuciyarmu.
[99] Dua’i Khatamil Qur’an
[100] Muslim1233
[101] Muslim 1284 da AbuDauda 1159da ibn Majah 1352
[102] AbuDauda 1152 ruwayar A’ishatu
[103] Idan bala’i ya faxa wa musulmai za  su yi Qunuti a sallolin su guda biya Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya tava yin haka duba zadul Ma’ad na ibn Qaym. Muma ya kamata mu kwakwayi abin da Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi muyi ta addua akan azzalumai akan cutar da mu da suka yi suka riqa kashe musulmai sabo da zave, kuma Arnan Zankuwa da na Kafancan da na Jos muyi ta aika masu da adduo’in Allah ya saka mana.   
[104]  Sahih Abi Duaud 1284
[105]  Sublusalam.
[106] Bukhari da Muslim.
[107] Bukhari
[108] Bukhari
[109] Risalatul Kushari.
[110]Muslim
[111]  I’itikaf na Mustapha Kasim
[112] (Hiliyatul Ulama da alkafi  na ibn Qudama
[113]Almuguni Ibn Qudamah


[114] Bukhari
[115] Musawali Fiqhi.
[116] Alkafi na ibn Quama da Sailul Jarrah na Shaukani
[117] Bidiyatul mujtahi bn Rushid
[118] Siffatu Sawm Nabiy
[119]Mu’utta Saratu, Abiy Muhsin. al- hanafi 158-145).
[120] Fathul Bari
[121] Fathul Bari.
[122] Fathul Bari.
[123] Bidiyatul mujtahi wanihayatul muqtasid
[124]Baihaqi Fissunan 316
[125] Qiyamur Ramadhan bugu na xaya
[126] Silsilatul al-Ahadisus Sahiha hadisi na 2786 da Qiyamur Ramadan bugu na karshe
[127] Baqara
[128] Albany yana amfani da wannan qaidar duba Tamamul  Minna wajen rashin halascin maimaita jam’i a masallaci mai limami ratibi  ya rinjayer da ibn Mas’ud  akan Annas ya qara dacewa  sahabi Annas ya sava ma wanda ya fishi  sani.  Tamamul Minna 155
[129]Tarikul Bagdad 151 mujalladi na hudu (4).
[130]Sahih Fiqh Sunna II 151
[131] Muhalla bn Hazam
[132]  Al-I’itikaf ahkam wa Adabuhu na Ahmad Mustapha Kasim 54-56.
[133] fatawa saum 685
[134]sharhin mustaqan’i .
[135]  Dalilil Sa‘imi 22
[136] Muktasaru  fikhuhul I’itikaf da Fikhul I’itikaf  dukkansu na Sheikh Bakar bn Abdullahi Abi Zaid.  Yin  I’itikafi a kowane masallaci shine fahintan  sahabban Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam baki xayansa  in banda Sahabi Huzaifa , shima Albany fahintarsa kenan a  farko daga baya ne ya canza duba Qiyamu Ramadan bugun Farko, amma wannan fahintarsa ne su kuwa Juhurun malaiama sun tafi akan kowane masallaci  kamar yadda yake shi ne fahintar sahabbai baki xaya.wannan Magana ita ce gaskiyar labari kamar yadda shima babban Malami Sheikh  Dr Khalid Aliyu alMushqih yafaxa a cikin littafisa Fiqhul I’itikaf duba Ahkamul Qur’an na Alqadhi Abubakar ibnul Arabiy Almaliki al-Andalusi cikin suratul Baqara ya tabbatar da cewa  za kai I’Itikafi a kowai masallaci.
[137] Al-Muguni 7/577
[138] Ahkamul Qur’an na Alqai Abubakar  ibnul Arabi al-Maliki  al-Andulusi
[139]Muslim
[140] Bakhari
[141] Tirmidhi
[142] Ibn Khuzaima da Dayalisi
[143]  Ba wai za ai mafarkin wani tsunburkai ba ne a a za a iya yin mafarkin ga shi ana ibada  a cikin daren za ji karsashi wajen yin ibadarsa.
[144] Muslim
[145]Buhari
[146] AbuDauda 1371
[147] Baihaqi da Darulqudini, Irwa’ul Galil
[148]Ahmad da Dahawi
[149] Zakkatir Fitr na Munajjid
[150]Abu Daud ibn Majah
[151] Buhari.
[152] Siyamu Ramadan wafawa,iduhu na Yusuf AlimuhsinHussain 
[153] Allah ya halasta mana auren Kirista  ba bu laifi, sahabi Umaru ya riqa tsanantawa wajen auren kirista, sai sahabi Huzaifa ya je ya auro Kirista ya ce ba wai yana sonta ba ne  a’a sai dai don ya nuna ma sahabi Umaru kar ya haramta abin da Allah ya halasta, haka shima Sahabi Usman ya auri Kirista shima don ya nuna  ma sahabi Umaru kar ya  ya hana abin da Allah da Annabin su ka halasta shi. Sahabi Umar ya ce shi hujjarsa  ita  ce idan muka koma auren Kiristoci namu matan za su rasa masu auren su. Har yanzu auren Kirista halas ne sai dai waxan da za su aure su  su zama kimtsattsu ba wai waxan da su ke  mazinata ba ko waxanda ba su san addini ba, kuma su ma kirstoci su zama ba mazunata ba  yana da kyau mai karatu ya duba Ahkamul Qur’an  na Alqadhi Abubakar ibnul Arabiy al-Maliki al-Andalusi cikin suratul Ma’ida.
[154] Sahih FiqhusSunnah Kamal Abu Malik  mujalladi  na biyu shafi na 83
[155]Hujjatullahi baligha
[156] Abu Daud
[157]  Bukhari
[158]Majmu,ulfatawa mujalladi 23-166
[159]Zadulma’ad
[160] Abu Daud da Salatul Idainiy fil Musallah hiyas Sunnah na Sheikh Albany
[161] Bukhari 956 da ZadulMa’ad 140 da Tanbihul Afham 437 da Muslim da Sahih FiqhusSunnah, zuwa da munbari masallacin Idi ba shi cikin karantarwar  fiyayyen halitta Imamul Bukhari babi ya qulla da ya ke nuna cewa ba a zuwa da mumbari sallar idi, zuwa da mumbari waje sallar idi bidi’ace ba sunnah ba ne.
[162]Baihaqi da Hakim
[163] Amma in akayi ba komai ko don varnar da akeyi ranar sallah yana da kyau a tunatar da jama’a da suji tsoron Allah su guje sava ma Allah.
[164] Zadul  Ma’ad
[165]Zadul Ma’ad
[166] Amma ya halasta sanya kaya mai ratsin ja kamar yadda ya zo cikin Bukhari Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya sanya kaya mai ratsin ja. Amma jan kaya haramun ne kayan kafirai ne, ya kamata duk musulmin kirki ya nisanci jan kaya. Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya tava umurtan wani Sahabi ya je ya qona jan kayan da ya sanya ya ce ma shi wannan kayan   Arna ne. duba Fathul Bari da zadul ma’ad .
[167]Bin Baz Dhalilil Siyam
[168] Sayid Sabiq Fiqhu as sunnah
[169] Ahmad da ibn Majah
[170] Ahmad da FathulBari 2-517 da Muguni na ibn Qudama 259/2 da            Tamamul Minna fi Ta’aqi ala Fiqhu Sunnah 356
[171]  Ma’anar wannan kalma shine ‘‘Allah ya  karvana ibadar mu  da ku
[172] Abubuwan da suke haramun ne yinsu musammam  ranar Idi yafi girman zunubi sune; Aske Gemu da gaisawa da mata, shiga gidajen mutane da sanya kayan Arna da Almubazzaranci da  zuwan mata kasuwa, barin sallah har lokaci ya wuce  shiga ta fitsara da mata suke yi zuwa Silma jin Disko da kixa da rashin Tausaya ma faqirai. Duba Salatul Idayn na Sheikh Ali Hassan.
[173]  Sayid SabiqFiqhu sunnah
[174] Laxaiful Ma’arif


[175] . Muslim da Dauda
[176] Zadul Ma’ad 1:10.

[177]  Nemi littafina na SABUWAR SHEKARA TASU’A DA ASHURA DA CIKA-CIKI.
[178] Bukhari da Muslim
[179] Bukhari a cikn Adab
[180] Bukhari