Wednesday, September 14, 2011

HAKKOKIN 'YAYA A MUSULINCI DA DALILAN DA KE KAWO LALACWAN TARBIYA

Godiya
      بـسـم اللـه الـرحـمـن الـرحـيـم                                                                                                   
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره  ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادى له، وأشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله.
أما بعد                                                  
 Haqiqa ina wa Allah godiya da ya bani ikon rubuta wannan littafin taqaitacce wanda ya ke magana a kan “Haqqokin ‘ya’ya da kuma dalilan da ke jawo lalacewar ‘ya’ya”. Na rubuta wannan littafi ne saboda kusantar da sunnar Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ga al’ummarsa game da haqqoqin ‘ya’ya a wajen iyayen su, ganin yadda iyaye suke sakaci akan ‘ya’yansu kai ka ce ba bu wani nauyi da Allah ya xaura masu, shiya sa naga ya kamata in rubuta littafi da zai bayanin haqqoqin ‘ya’ya akan iyayensu don iyaye su karanta su ga nauyi da ke kansu, da fatan littafin ya amfanar da musulmi baki xaya amin.
Kamar yadda ya ke ta’adatace duk littafin da nake rubutawa ba na kawo ra’ayi na ina taqaituwa ne qarqashin al-Qur’ani da hadisi da maganganun magabata na kwarai. Ina roqon duk wanda zai karanta wannan littafin ya karata shi da zuciya xaya, kuma don Allah in ya ga gyara ko shawara ko kuskure ya aiko man da gyaransa  da ya gani, ko shawararsa da yardan Allah zan gyara. Duk maganar da na faxa ina kawo inda na ciro ta a qasan shafi. Babu shina yiwa in manta da Malamina Malam Ahmad Bello Dogarawa haqqiqa yana qarfafa na matuqa da kuma Dr Ahmad Bello Sardauna shugaban tsangayar qididdiga da lissafin kuxi na Jami’ar Ahmad Bello Zariya (H.O.D Accounting A.B.U Zaria) Allah ya saka masa da Aljanna amin.  Haka shima Malamina Sheikh Imam Mikail Isah Shika (Limamin Juma’a Shika) shima Allah ya saka masa da Aljannah Allah ya ji qansa da gafara da kuma Malamina Alqali Malam Muhammad Amin Jumare da Alqali Malam Harun Ishaq Shika dukkanin su Allah ya sakama su da Aljannah, Malam Abubakar Jumare Gixaxo Zaria da Malam Musa Muhammad Sahabi godiya ta musamman da fatan alheri agare su, haka shima  Injiniya  (Engineer) Muhammad Sani Bakori Allah ya saka masa da Aljannatil Firdausi amin shine ya xauki nauyin buga wannan littafin.  A qarshe ina wa mahaifiyata Fatimatu Xalhatu Zaria da mahaifina Malam Abubakar Ibrahim adduar Allah ya ji qansu ya yi masu sakamako da AljannatilFirdausi amin summa amin.
A qarshe ina qara cewa don  Allah  duk wanda ya ga gyara ko shawara kofa abuxe take kuma zanyi farin ciki da gyaransa ko shawaransa, za a iya samun sauran littattafan dana rubuta a mudawwanata ta yanar giza-giza mai alamar  http://harunaabubakarshika.blogspot.com ina roqon addua ta alheri ga duk wanda ya karanta littafi na nagode.
                                 Wassalamu alaykum warahamatulLah.
                           12/Sha’aban/1431- 2/8/2010
             Harun Abubakar Shika
                      08030582333-08054533361-08020900001  
                     Harunaabubakar99@yahoo.com  
        



       بسم الله الرحمن الرحيم                                                 
YA‘YA NI’IMA CE DAGA ALLAH
Lalle yana daga cikin ni’imar Allah ga xanAdam da Ya ba shi  ni’imar ‘ya’ya, duk wanda ya yi aure bai samu xa ba, ba shi cikin kwanciyar hankali. Kullun fatarsa Allah ya ba shi haihuwa.Mun ga yadda Annabi Zakariyya yake roqon Allah ya ba shi xa wanda zai gaje shi duk da cewa Allah ya ba shi Annabta amma bai tsaya ba saboda neman samun xa wanda zai gaje shi. Wannan ya sanya yake tashi cikin dare yana roqon Allah ya ba shi xa wanda zai gaje shi. Allah ya amsa addu’arsa ya ba shi yaro mai suna Yahya wanda shi ne na farko mai wannan sunan kuma Annabi.  Allah ya ba mu labarin Annabi Ayyub bayan ya warke daga rashin lafiyar s a kuma Allah ya ba shi ‘ya‘ya.[1]
Abin da zai qara nuna mana mahimmancin ‘ya‘ya shi ne yadda Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi wa Anas addu’ar Allah ya ba shi yawan ‘ya‘ya, Allah ya amsa addu’arsa ya ba shi ‘ya‘ya xari da ashirin da biyar (125). Guda casa’in sun rasu[2] sakamakon annobar  da aka yi a Madina, biyu ne kawai mata duk sauran maza ne.[3]
Annabi Ibrahim sai da ya tsufa sannan Allah ya ba shi xa. Allah ya ce masa rahama ce da albarka ga gidanka. Manufar aure ita ce domin a hayayyafa yadda manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam zai yi alfari da yawan mu ranar kiyama[4]. Haka kuma ya kwaxaitar da a auri mata masu haihuwa. Wani bawan Allah ya sami matar da yake so amma kuma ba ta haihuwa, sai manzon Allah ya hana shi ya aure ta. Sau uku yana zuwa wurin Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam amma bai ba shi izinin auren ta ba saboda ba ta haihuwa. A na ukun ne sai ya ce masa,
جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رَسُولِ اللهِ فَقَال                                   َ
: يَا رَسُولَ اللهِ إِنِّي أَصَبْتُ امْرَأَةً ذَاتَ حَسَبٍ وَجَمَالٍ،وَلَكِنَّهَا لاَ تَلِدُ أَفَأَتَزَوَّجُهَا ؟ فَنَهَاهُ،ثُمَّ أَتَاهُ الثَّانِيَةَ،فَقَالَ مِثْلَ ذَلِكَ : فَنَهَاهُ،ثُمَّ أَتَاهُ الثَّالِثَةَ،فَقَالَ مِثْلَ ذَلِكَ : فَقَالَ: تَزَوَّجُوا الْوَدُودَ الْوَلُودَ فَإِنِّي مُكَاثِرٌ بِكُمْ الأمم يوم القيامة."                                               
Wani mutumi ya zo wajen manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ya RasulalLah na sami mata kyakkyawa ‘yar dangi amma ba ta haihuwa. Sai ya hana shi  auren ta. Ya qara dawowa karo na biyu ya qara maimaita maganar auren ta,amma Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya hana shi. Ya qara zuwa a karo na uku sai Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce masa, “ Ku auri waxanda kuke son su suke son ku (waxanda suka iya soyayya) masu haihuwa  domin in yi alfahari da yawan ku ranar Qiyama.”[5]
Idan  aka natsu da kyau a cikin wannan hadisi za a fahimci irin matar da ake so a aura. Ita ma mace idan ta san wanda yake son ta ba ya haihuwa, to shari’a ba ta yarda ta aure shi ba. Akan gane mace mai haihuwa ne ta vangaren mahaifiyarta.  Kuma mun fahimci auren dole haramun ne. Muddum yarinya ba ta son mutum to kada a matsa mata a ce dole sai ta aure shi.[6]

AMFANIN  ‘YA‘YA
‘Ya‘ya suna da matuqar mahimmanci ko da bayan rasuwar mutum ne. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Idan xan Adam ya rasu dukkan ayyukkansa sun yanke sai dai ta hanyoyi guda uku: Sadaka mai gudana[7] ko ilimin da ya koyar ake amfana da shi ko kuwa xa na qwarai da ya ke masa addu’a.[8]
Wata ruwayar Manzon Allah sallahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Haqiqa ana xaukaka darajar mutum a gidan Aljannah. Sai ya ce, “Ya  Allah wannan matsayin fa?” Sai Allah ya ce masa, “Addu’ar xanka ce da ya ke yi maka  bayan rasuwar ka.”[9]
Wata ruwayar daga Abu Huraira Allah ya qara masa yarda ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘Mutum bakwai ladarsu na  gudana ko bayan rasuwar su, suna qabari ana rubuta masu lada: Wanda ya koyar da ilimi  kuma ya yaxa shi ko wanda ya gina dam ko ya gina rijiya ko ya dasa dabino (zamanin Annabi dabino shi ne kayan icen da ake yawan ci a yanzu kuwa dukkan wasu itacen da ake shan ‘ya‘yansu sun shiga ciki)  ko ya gina masallaci ko ya gadar da Qur’ani ko ya bar xa yana yi masa addu’a bayan rasuwar sa.’”[10]

YARDA DA QADDARAR ALLAH
Dole ne uba da uwa su yarda da qaddarar Allah a kan namiji ne Allah ya ba su ko ‘ya mace ce. Alama ce ta jinin Jahiliyya mutum ya ce ya fi son ‘ya‘ya maza.
Allah ya gaya mana a cikin suratunNahal ya ce,
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُمْ بِالْأُنْثَى ظَلَّ وَجْهُهُ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌ يَتَوَارَى مِنَ الْقَوْمِ مِنْ سُوءِ مَا بُشِّرَ بِهِ أَيُمْسِكُهُ عَلَى هُونٍ أَمْ يَدُسُّهُ فِي التُّرَابِ ألا سَاءَ مَا يَحْكُمُونَ   “Idan aka yi wa xayansu bushara da haihuwar ‘ya mace fuskarsa zata kasance baqi , yana mai cike da  baqin ciki yana voye wa jama’a kar su gansa( yana voyewa  saboda an haifar masa ‘ya mace) saboda mummunar busharar da aka yi masa. Sai  ya riqe (‘ya macen ) cikin wulaqanci ko kuma ya je ya turbuxeta cikin qasa.” Allah ya ce, “Wannan hukunci da suke yi ya munana.” [11]
Wannan Jahiliyyar tana faruwa har gobe, Duk wanda Allah ya ba shi ‘ya mace ya yi wa Allah godiya kawai domin bai sani ba mai yiwuwa ita ce mafi alheri. Kuma maganar da babu ko tababa a kan ta ita ce ‘ya’ya mata sun fi maza tausayi da nuna qauna ga iyayensu, Allah yana cewa,[12]
لِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ يَهَبُ لِمَنْ يَشَاءُ إِنَاثًا وَيَهَبُ لِمَنْ يَشَاءُ الذُّكُورَ أَوْ يُزَوِّجُهُمْ ذُكْرَانًا وَإِنَاثًا وَيَجْعَلُ مَنْ يَشَاءُ عَقِيمًا إِنَّهُ عَلِيمٌ قَدِيرٌ Mulkin sammai da qassai gaba xayan su na Allah ne. Yana halittar abinda ya so yana ba da kyautar mata ga wanda ya so yana kuma ba da kyautar ‘ya‘ya maza ga wanda ya so, ko ya haxa wa mutum maza da mata ga wanda ya so, ko kuma ya bar shi bakarare (mara haihuwa). Lalle shi Allah masani ne kuma mai iko ne.[13]
 Annabi Luxu gaba dayan ‘ya’yansa mata ne babu namiji ko daya amma bai damu ba, Annabi Ibrahim kuma shi gaba xayan ‘ya’yansa duk maza ne amma dukkaninsu godiya su ke ma Allah.
Tarbiyyar ‘ya‘ya mata ta fi garavasa da tagomashi da ragadada fiye da maza, kamar yadda hadisi ya nuna duk wanda Allah ya ba shi ‘ya‘ya mata ya ba su tarbiyya har suka balaga, to za su zama sutura a gare shi daga shiga wuta ranar kiyama. Sannan a wani hadisin ma’aiki yake cewa,
 مَنْ عَالَ جَارِيَتَيْنِ حَتَّى تَبْلُغَا جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَنَا وَهُوَ هَكَذَا وَضَمَّ إصْبَعَيْهِ.                                                                    
‘’Duk wanda ya kula da ‘ya’ya mata guda biyu (cikin iyalansa) har suka balaga zai zo ranar al-Qiyama dani das hi haka muke sai ya gwama yatsunshi guda biyu.”
Wannan hadisin   ya ce, “Xayanku bai kasance yana da ‘ya‘ya mata guda uku ba. Ko ‘yan’uwa mata guda uku kuma ya kyautata masu face ya shiga Aljannah.[14]
لاَ يَكُونُ لأَحَدِكُمْ ثَلاَثُ بَنَاتٍ،أَوْ ثَلاَثُ أَخَوَاتٍ فَيُحْسِنُ إلَيْهِنَّ إلاَّ دَخَلَ الْجَنَّةَ                  A wani hadisin kuwa manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam cewa ya yi,
لا تُكْرِهُوا الْبَنَاتَ، فَإِنَّهُنَّ الْمُجَهِّزَاتُ الْمُؤْنِسَاتُ "                  
“Kada ku riqa qyamar ‘ya‘ya mata domin sune masu kimtsawa masu xebe kewa[15]
 YA‘YA AMANA CE ALLAH YA BA MU
Duk wanda Allah ya ba shi ‘ya’ya to Allah ya ba shi ni’ima ne kuma amana ce wadda zai tambaye shi a kan ta ranar tashin qiyama. Wanda yake da ‘ya’ya komai yawansu, ranar qiyama Allah zai tambaye shi game da tarbiyyar su. Shin ya ba su haqqinsu ko ya tauye masu haqqinsu? Xaya bayan xaya Allah zai tambaye shi tsakanin sa da Allah. Babu wanda zai yi masa fassara, haka Manzon  Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce a hadisin muslim. Wani hadisin manzon sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce,
  ما من عبد يسترعيه الله رعية يموت يوم يموت وهو غاش لرعيته إلا حرم الله عليه والجنة                                          “Babu wani bawa da Allah zai ba shi kiwo, ya mutu ranar   mutuwarsa yana mai algushu ga abin kiwon da Allah ya ba shi face Allah ya haramta masa shiga Aljannah”[16]
Babu abu mafi tsada da uba zai ba ‘ya’yansa kamar ya tarbiyyantar da su. Tarbiyya kyakkyawa kuwa ita ce kyauta mafi tsada da zaka ba ‘ya’ya. Haka manzon Allah sallal Lahu alayhi wa sallam ya ce.
ما نحل والد ولدا من نُحلٍ أفضل من أدب حسن                       Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Uba bai ba xansa kyaututtuka ba daga cikin kyauta fiye da ya ba shi kyakkyawar tarbiyya.”[17]

    HAQQOQIN  ‘YA‘YA  A  KAN  IYAYENSU
‘Ya‘ya suna da haqqoqi a kan iyayensu kamar yadda su ma iyaye suke da haqqoqi masu girma a kan ‘ya’yansu. Yana daga cikin haqqoqin ‘ya’ya  a kan  iyayen su waxanda musulunci ya xora masu. Kuma dole ne iyaye su sauke wannan nauyi da ke kansu domin samun tsira ranar qiyama. ‘Ya‘ya amana ce Allah ya ba mu zai kuma tambaye mu game da amanar da ya ba mu.  Ga haqqoqin kamar haka:

ZAVEN MACE TA QWARAI MAI ADDINI[18]
 Yana daga cikin haqqin da yaro yake da shi a kan mahaifan sa su zava masa uwa ta qwarai ko uba na qwarai. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi umurni da duk wanda ya tashi yin aure ya auri mace mai addini.[19]
Wata ruwayar manzon Allah  sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Mafi alherin taskar  da mutum zai samu ita ce mutum ya sami mace ta qwarai.”[20]  Wannan shi ma ya nuna mana mahimmancin auren mace mai addini gidan mutunci. Ba gidan da basu da tarbiyya ba. Domin idan ka auri mace a mummunan gida ‘ya’yanka za su taso da munanan xabi’u sakamakon gidan  da ka yo aure ba sa da tarbiyya. Wannan ya sa a wani hadisin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku zava wa maniyunku inda za ku zuba shi, domin xabi’a naso take yi, jijiya take bi. [21]
عن عائشة قالت قال رسول الله صلى الله عليه وسلم تخيروا لنطفكم وانكحوا الأكفاء وأنكحوا إليهم     
    Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya tava hana sahabi Aliyu auren wata yarinya ‘yar Abu Jahal. Yayin da ya ji labarin zai auri ‘yar Abu Jahal manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce ba zai tava yiwuwa a haxa ‘yar Annabi da ‘yar shugaban maqiya addinin Allah ba. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce sai dai in zai saki Nana Fatimah. Wasu malaman sun ce Manzon Allah sallal Lah alayhi wa alihi wa sallam ya hana sahabi Aliyu ne saboda xabi’a tana bin jijiya.[22]
 Na daga cikin abinda Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya karantar da musulmai su tabbata a gare shi. Ya ce, “Ku zavar wa 'ya'yanku uwa tagari..[23] Ita ma ta zavar wa ‘ya’yanta uba na qwarai  mai addini.
 Uba yana zava wa ‘yarsa miji na qwarai kuma ya gaya mata dalilin da yasa ya zava mata miji, haka ya faru da Nana Fadimatu Allah ya qara mata yarda, Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam  ya ce ‘’Ya  Fatimatu baza ki farin ciki ba in aura maki wanda ya riga al’umata shiga musulinci? wanda kuma ya fi su ilimi kuma ya fi su haquri.[24] Yana daga cikin hanyoyin zaven mata tagari yin istihara (addu’a ce manzon Allah ya koyar da  al’umarsa. Duk  wanda  ya tashi neman aure ya yi istihara.[25] Ita  wannan sallar  raka’a biyu  ake yi  sannan a karanta addu’ar), Ba  a yarda mutum ya fara nemman aure ba, ba  tare da ya yi istikara ba. Bayan ya yi istihara sai kuma ya shawarci mutanen kirki da waxanda suka santa. Domin mace ita ce uwa ta farko ga ‘ya’yanka. Yara suna tasowa ne a kan xabiunta da halayenta. Uwa tana da tasiri babba a kan mijin ta da ‘ya’yanta. Wani mutum  ya ce, “Mutum yana kan addinin matar ne sabo yadda ya ke karkata a gareta.[26]
Ya tabbata hadisi ingantacce daga Sahabban Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa sallam Allah ya qara masu yarda sun ce, “Annabi sallal Lahu alayhi wa sallam yana koya mana istihara kamar yadda yake koya mana Fatiha.”
  Duk Wanda ya ke yin istihara kuma ya ke yin shawara, to ba zai yi nadama ba, ba kuma zai yi hasara ba: Ga addu’ar kamar haka:
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلَا أَقْدِرُ وَتَعْلَمُ وَلَا أَعْلَمُ وَأَنْتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ  -sunanta  ko sunansa za ka ambata anan wurin- خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي أَوْ قَالَ عَاجِلِ أَمْرِي وَآجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَsai ka fadi sunanta ko sunansa شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي أَوْ قَالَ فِي عَاجِلِ أَمْرِي وَآجِلِهِ فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي
A qarshen  wannan addu’ar sai ka sake ambaton buqatarka. Ba a yin mafarki. Idan aka yi istihara za ka ji ka samu natsuwa, ko kuma ka ga Allah ya sauqaqe maka. Sheikh Majadiy ibn Mansur bn Sa’id As Shurah  ya ce, “Babu laifi mutum ya maimata istihara fiye da xaya.”[27]
 Sheikh Dr Abu Aminah Bilal Philip  ya ce ya halasta uba  taya  ‘yarsa istihara, amma bai halasta ba wani malami ya yi wa wani ko wata. Ita ma uwa zata iya taya ‘yarta, sai dai an fi son ita ‘yar ta yi da kanta kuma ta yi ta maimaitawa. Ana so ka kyale ta ta yi istiharar bayan ka gama taka. Akwai wani tsafi da waxansu ke yi. Waxannan mutane suna amfani da wani littafi ne mai suna Qur’atul Anbiya’i. Wannan littafi haramun ne yin amfani da shi. Domin yana iya kai mutum zuwa ga kafirci, wasu kuma wajen bokaye suke zuwa Allah ya kyauta. Duk wanda ya je boka ya gaya masa magana kuma ya yarda, to ya bar musulunci. Idan ya gaya maka magana baka yarda ba, sai ka kwana arba’in kana sallah ba a amsa ba.[28] 
Wani mutumi ya kawo qarar xansa wajen  Umar ibn Kadxab  yake  cewa, “Xana  baya yi mani biyayya.” Sai Sahabi Umar ya sa aka kira xan ya yi masa nasiha ya tsorartar  da  shi illar rashin yi wa iyaye biyayya. Daga nan  sai yaron ya ce wa Sahabi Umar, “Shin su ma ‘ya’ya  suna da haqqi a kan  mahaifansu?” Sai Sahabi Umar ya ce, “I akwai!” Sai yaron ya nemi a yi masa bayani. A nan ne Sahabi Umar ya ce, “Na farko uba ya zava wa ‘ya’yansa uwa tagari kuma ya sanya masa suna kyakkyawa. Sannan ya koyar da shi littafin Allah. Da wannan yaro ya ji haka sai ya ce wa sahabi Umar, “Babana bai yi mani ko xaya ba. Babana da ya tashi yin aure  bai  auro mani uwa tagari ba. Babana ya auro mana karuwa ne daga cikin karuwan Maguzawan qasar Sudan. Sannan da ya tashi sanya mani  suna sai ya  sanya mani suna ‘Gungura kashi’. Bai kuma koya mani komai daga littafin Allah ba.” Daga nan sai Sahabi Umar ya ce masa, “Ashe kai ne ka sava wa xanka tun kafin ya zo duniya, ka wulaqanta xanka.”.[29]
Wannan qissar tana nuna mana haqqoqin ‘ya’ya a kanmu. Don haka iyaye su tambayi kansu wace iriyar mata suka aura? Kuma su ma mata su kiyaye kada su yarda su auri mara addini mara xabi’a. Kuma yana da kyau mutane su gane cewa manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam bai ce  idan zaka yi aure ka auri mai karatu ba. Cewa ya yi in zaka yi aure ka auri mai addini. Ke ma mace idan zaki yi aure ki auri mai addini ba mai karatu ba. Al’umma su lura da bambancin mai addini da mai karatu: Hadisi ya tabbata  daga Abi Huraira Allah ya qara yarda da shi ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce,
 إذا أتاكم من ترضون دينه وخلقه فزوجوه ، إلا تفعلوا تكن فتنة في الأرض وفساد عريض".                                                               
‘Idan wanda kuka yarda da addininsa da xabi’unsa ya zo neman aure wajenku ku aura masa. Idan  bakuyi haka ba, fitina da varna mai yawa zata kasance a bayan qasa.’”.[30]

 Ba a lura da kyawon mace wajen aure, domin ba shi ne mazon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce a lura da shi ba. Ya ce ne a lura da mai addini da xabi’u. Fifita kyau a wajen aure alama ce ta mara addini.[31] Wani hadisin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ba da labari yake cewa,

          تُنْكَحُ الْمَرْأَةُ لأَرْبَعٍ لِمَالِهَا وَلِحَسَبِهَا وَجَمَالِهَا وَلِدِينِهَا،فَاظْفَرْ بِذَاتِ الدِّينِ تَرِبَتْ يَدَاكَ                                                                      

 “Ana auren mata saboda abu huxu (4): Wasu suna auren mace saboda dukiyarta, wasu kuma suna auren mace saboda kyawonta, wasu kuma suna auren mace saboda danginta, wasu kuma suna auren mace saboda addininta[32]. Sai Annabi ya ce na horeka da ka aure ma’abociya addini.”[33]

Wani hadisin da ibn Maajah ya ruwaito Manzon Allah sallal Lahu wa alihi wa sallam  ya ce, “Kada ku auri mata saboda kyawon su, kyawonsu yana iya juyar da ita.( ta kasance mai girman kai.) Sai ya qara da cewa, “Kada ku auri mata saboda dukiyarsu: Ana sa ran dukiyarsu ta sanya su girman kai. Sai dai ku aure su saboda addini.”[34]
لاتزوجوا النساء لحسنهن فعسى حسنهن ان يرديهن ولاتزوجوهن لأموالهن فعسى اموالهن ان تطغيهن ولكن تزوجوهن على الدين                                              
A qarshe muna cewa ya na daga haqqin ‘ya’ya akan iyayensu su tabbatar sun auri mace mai addini kuma gidan mutunci, kuma yana da kyau mu gane cewa addini daban karatu daban.
Aktham ibn Sufiy ya  ce wa xansa, “Ya kai xana kada ka yarda kyawon mace ya ruxe ka har ka manta da asalin yarinyar, mai addini ce ko kuwa? Domin aure gidan mutunci shi ne mashigar mutuncinka da xaukakar ka”.[35]
Abu Aswadu Dualiy ya ce wa ‘ya’yansa, “Haqiqa na kyautata maku yarintar ku da tsofar ku, tun kafin a haife ku!” Sai suka ce, “Yaya ka kyutata mana tun kafin a haife mu?”  Sai ya ce, “Na zava maku uwar da ba zaku zarge ta ba (wato ba zaku kushe ta ba.)[36]
Wani bawan Allah ya je wajen Hasanul Basri ya ce, “Ina da ‘ya wacce nake son ta, jama’a da yawa suna sonta. Wa zan aurarwa? bani shawara?” Sai Hasanul Basri ya ce, “Ka aurar da ita ga mai tsoron Allah idan yana sonta. Sai ya karrama ta. Idan kuwa ba ya son ta ba zai zalunce ta ba.” (saboda tsoron Allan sa).[37]
Wani mutumi ya je majalisin Safiyanu bn Uyaynah ya ce, “Ya Aba Muhammad ina fama da matata tana wulaqanta ni matuqar wukaqantawa. Sai Safiyanu bn Uyaynah ya yi shiru kaxan sannan ya ce, “Me yiwuwa ka aure ta ne saboda ka samu xaukaka.” Sai mutumin ya ce, “Lallai haka ne. Sai ya ce, “Duk wanda ya auri mace saboda neman xaukaka, to Allah zai qasqantar da shi. Wanda kuma ya auri mace saboda dukiya Allah zai jarabce shi da talauci. Wanda ya auri mace saboda addini Allah zai haxa masa xaukaka da dukiya da addini.[38]
Kuma yana da kyau duk wanda ya tashi yin aure, to ya auri budurwa. Domin budurwa ta fi alheri, kuma ita ce zaka xora ta a kan abinda kake so. Kuma budurwa manzon Allah ya fifita ta a kan bazawara. Budurwa ta fi yarda da kaxan. Ga wani hadisi da manzo yake kwaxaitar da mu  a kan auren budurwa:
عليكم بالأبكار فإنهن أنتق رحما ، وأعذب أفواها ، وأرضى باليسير                                                                                          Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Na hore ku idan zaku yi aure ku auri ‘Yammata’ (budurwa) domin mahaifarsu ta fi tsafta kuma bakinsu ya fi daxi kuma suna yarda da xan kaxan.”[39]
Amma su ma zawarawan akwai alheri, sai dai ba su kai ‘yammata ba. Idan mutum yana da ‘ya’ya da yawa, idan ya tashi qara aure sai ya auri bazawara saboda yawan ‘ya’yansa. Ko kuma idan an mutu an bar masa qannai da yawa sai ya auri bazawara. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ga sahabi Jabir ibn Abdullah ya yi aure, sai ya ce masa, “Ka yi aure ne?”  Sai ya ce, “Na yi aure ya Rasulil Lah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam.” Sai ya tambaye shi budurwa ko bazawara? Sai ya ce bazawara ce. Sai Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Aiya! Ina ma budurwa ka aura.” Sai ya ce, “An mutu an bar ma ni qananan yara ne shi ya sa na auri bazawara.”[40]

ADDU’AR  DA  ZAKA  YI   WA   AMARYA  RANAR  DA  KA SHIGA  XAKINTA.
Yana daga cikin hanyar samun zuriya tagari yin sallah ta nafila raka'a biyu, lokacin da ka shiga xakin amarya a daren farko. Sannan mutun ya xora hannunsa a kan matarsa, sai ya karanta addu'ar da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya koyar. Addu’ar kuwa ita ce:
اللَّهُمَّ إِنِّى أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا    وَمِنْ شَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْه                                                                           
Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu           bika  min sharri ha wa sharri ma jabaltaha alayhi.[41]


ADDU’AR SADUWA.  
  Haka nan ma yin addu'a yayin jima'i domin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam   ya ce duk wanda ya yi addu'a yayin Jima'i, idan Allah ya qaddara samun xa a lokacin saduwar (Jima’i), shaixan ba zai cutar/ shafe shi ba da iznin Allah. Ga addu’ar kamar haka:
بسم الله، اللهم جنبنا الشيطان، وجنب الشيطان ما رزقتنا     
BismilLahi Allahumma jannibina Shayxana wajannibi Shayxana ma razaqatana[42]
Wannan  addu’ar duk yayin da ka zo saduwa da matarka ana buqatar ka da ka karanta ta, ita ma matar tana iya karantawa  babu laifi.
           Haramun ne saduwa da mace ta dubura. Wani hadisin ma Manzon sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam   ya ce Allah ya tsine wa wanda ya sadu (jima’i) da matarsa ta dubura. Wani hadisin kuma cewa ya yi wannan mutum ya bar musulunci wanda ya sadu da matarsa ta dubura.  Ya halatta mutum ya sadu da matarsa a tsaye ko a kwance ko a rigingine ko ta yi goho. Duk dai yadda mai gidanta ya so ta yi masa, amma kada ya sadu da ita ta dubura. Allah yana cewa:
﴿نساؤكم حرث لكم فأتوا حرثكم أنّى شئتم﴾                  
“Matayenku gonakinku ne ku je wa gonakinku ta yadda kuka so.”
 Allah bai ce ta inda kuka so ba,  sai ya ce ta yadda kuka so. Haramun ne saduwa da mace ta dubura.
  Hadisi ingantacce ya tabbata ya ke cewa, “Tsinanne ne wanda ya sadu da matarsa ta dubura.”[43]
 (ملعون من يأتي النساء في محاشّهن. يعني : أدبارهن ))     
Wata ruwayar ta ce duk wanda ya sadu da mai haila ko ya sadu da mace ta dubura ko ya je wajen boka ya kuma yarda da abinda ya faxa masa, ya kafirce wa abinda aka saukar wa Muhammadu. (Wato ya bar musulunci”
(من أتى حائضاً، أو امرأة في دبرها، أو كاهناً فصدقه بما يقول؛ فقد كفر بما أُنزل على محمد
Wannan hadisin ya nuna mana wanda ya sadu da mai haila ko ya sadu da matarsa ta dubura ya bar musulunci.[44]

 SANYA MASA SUNA NAQWARAI
 Yana daga cikin haqqin ‘ya’ya iyayensu su sanya  masu suna naqwarai   kamar yadda muka gani a qissar baya.  Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce’  “Lallai ku za a kira ku ranar alkiyama da sunayenku da sunayen iyayen ku. Saboda haka ku kyautata sunayenku (da na ‘ya’yanku)"[45]
  Mafificin sunan da Allah ya fi so, Abdullahi da Abdurrahman.[46]
إِنَّ أَحَبَّ أَسْمَائِكُمْ إِلَى اللَّهِ عَبْدُ اللَّهِ وَعَبْدُ الرَّحْمَنِ                    
Vangaren mata kuma Amatul Lahi ko Amatur Rahaman[47]. A guji sanya mummunan suna domin za a kira mutum da mummunan sunansa ranar Kiyama. Kuma mai mummunan suna zai tashi da xabi’u munana da mummunan hali. Wannan ya sanya  a  wani hadisin manzon Allah sallal Lahu alayhi wa sallam ya ce,
عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ   " إِنَّكُمْ تُدْعَوْنَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ بِأَسْمَائِكُمْ وَأَسْمَاءِ آبَائِكُمْ فَأَحْسِنُواأَسْمَاءَكُمْ
An karvo daga AbidDarda’i ya ce “Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Lallai za a kira ku ranar kiyama da sunayenku da na iyayenku. Ku kyautata sunayenku...[48]
 Wannan hadisin  yana  umurni ne a riqa kiran mutum da sunan mahaifinsa, kamar yadda zaka ga wasu mata ana kiransu da sunayen mazajensu. Yin haka kuskure  ne sava wa Allah ne da Annabinsa. Abinda yake daidai a kira su da sunayen iyayensu ko bayan sun yi aure. Yana daga munanan sunaye kamar:      Zaqquma, Humairah, Samirah, Dudu, Hurairah, Mal’unatu, Lantana, Maraqisiyyah, Safinatu, Baxxatu, Barratu,Shadiyyah, Jatthama,Huyaam,Nuhaad,Iqilima,Nadiya,Adama,Abdul-Muxxalib,Abduln-Nabee, Diana,Zaituna,Bashariyyah,Maashixa, Qamariyyah       da sauransu aje atambayi Malamai. Suna yana bin yaro ko yarinya. Suna kyakkyawa yana da tsananin tasiri a kan ‘ya’ya haka shima suna mummuna yana da tasiri a wajen ‘ya’ya[49].  Taron suna da akeyi rana ta bakwai a kofar gida na maza bidia ce haka nan ma  sa suna a masallaci wanda ake yi bayan sallan subahi ana raba dabbino ko goro ko minti shima bidia ne.Amma ya halasta a faxi haihuwa da sunan yaro a masallaci ba tare da an raba komai ba, ba tare da ance ai masa addua ba, domin ya tabbata acikin Sahihu Muslim Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya faxi haihuwan xansa mai suna Ibrahim Mu’azam a cikin masallaci kuma ya sanya ma wasu yaran suna a masallaci amma ba a samo an raba dabbino ba kogoro ba ko a ce ayi masa addua bayan sallah ba.[50] taron suna na mata shima bidia ne, na mata ma yafi muni ya kamata duk AhlusSunnah na gaskiya ya hana taron suna na mata kamar yadda Allah ya taimaka aka daina na maza suma mata a  hana su wannan shine gaskiyan labari, duk inda bidia ta ke sharri ke aukuwa, mafificiyar shiriya ita ce shiriyar manzon Allah.

TAHANEEK
Bayan an haifi yaro ana tauna dabino a xiga masa ruwan dabinon a bakinsa. Yin haka Sunnah ce. Idan babu dabino wasu malaman sun ce ana iya amfani da zuma. An ruwaito daga  Abi Musa  ya ce, “An haifar mani yaro, na kai shi wajen Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya sanya masa suna Ibrahim ya tauna dabino ya xiga masa a bakinsa  ya yi masa addu’a ya ce Allah ya yi mashi albarka.[51] Yadda ake Tahaneek shine bayan an tauna dabbinon za a xiga ruwan a bakin yaron  sannan a goggoga masa ruwan dabbinon saman bakinsa da qasansa da harshensa da hanqansa da dasashin sa.

KIRAN SALLAH
Ya shahara wajen mutane maganan kiran sallah a kunnin jariri lokacin da aka haife shi, amma sai dai bincike ya tabbatar da cewa wannan maganan ba ta inganta ba duk hadisan da su ka zo kan kiran sallah Dha’ifai ne Sheikh Kamal Abu Malik ya ce hadisan da su ka zo kan kiran sallah dukkaninsu ba su ingata ba, ba a kafa huja da su.[52]
Cikin mazajen da suka ruwaito hadisin kiran sallah akunnin jariri akwai Asim shi kuma Asim Dhaifi ni a ruwayasa, ibn Hajar ya faxi acikin Tahazib mutum ne mai rauni kuma tataccen maqarya ci ne.[53]
Akwai ruwayar Hammad ibn Shuaib ita ma Munkara ce inji Imamul Bukhari, Maganan kiran sallah a kunnin jariri ba su inganta ba.[54]  Ita kuma ruwayar Bayhaqi shi da kansa ya ce hadisin dhaifi ne.[55]
Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albani ya ce hadisan kiran sallah dha’ifai ne duba Silsilatu Dhaifa 321-393.
Hadisin iqama  a kunnin jariri ba  shakka wajen malaman hadisi cewa hadisi ne baragulbi xanjabu bai inganta ba, abin da ya ke daidai ba a kiran sallah ko Iqama a kunnin jariri[56]

 YANKA RAGO
Yana da ga cikin haqqin xa ko ‘ya bayan haihuwa ana yanka wa yaro raguna guda biyu idan kuma mace ce za a yanka mata guda xaya ne.[57] Ana yanka rago ne rana ta bakwai. Idan hali bai samu ba an so a yanka a rana ta sha huxu ko rana ta ashirin da xaya kamar yadda hadisi ya nuna kuma hadisi ne ingantacce.[58] Hakanan kuma ya tabbata manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya yanka ma sayyina Hassan raguna  biyu  a rana ta bakwai shima sayyidina Hussaini raguna biyu aka yanka masa.[59] Ita Nana Aishatu Allah ya qara mata yarda ta ce ‘’ namiji raguna biyu  ake yanka masa mace rago xaya.[60]
Wanda ya yanka ma xansa rago xaya ana binsa rago xaya da zai yanka masa domin yadda Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya karantar raguna biyu ne mace ce rago xaya.
 Ana yanka rago ne ko tunkiya ko qadduwa ko bunsuru, amma ba a yanka saniya ko raqumi, kuma ana yankawa a rana ta bakwai ba ta takwas ba[61]. Idan aka yi maka haihuwa ranar Juma’a, za ka yanka rago ne ranar Alhamis. Domin idan ka qirga zaka ga ranar Alhamis ce bakwai. Muddum  ya kai Juma’a  to ya zama kwana takwas ke nan.[62]  Kuskure ne rashin qirgawa da ranar haihuwa. Tun daga ranar haihuwa zaka qirga, ba a yanka saniya ko raqumi. Qanwar nana A’ishatu ta haihu aka ce a yanka raqumi sai Nana A’ishah ta ce Allah ya tsare ta manzon Allah bai ce ba.
Zance mafi daxi dai ba a yanka Sa ko Saniya ko Raqumi ba. Wanda ya yanka kafin rana ta bakwai ya sava ma shara’ar musulunci, hadisi dai ya ce rana ta bakwai ibn Hazmin ya ce sam bai halasta ba yankawa kafin rana ta bakwai. [63]

matashiya/shin ya halasta karya qashin ragon suna
Ba kyau karya qashin ragon suna ana so ne a zare naman amma kar a datsa ko karya qashin, ana  dafawa ne da qashin sai a savule naman wannan ruwayar ta zo cikin Bayhaqi da Musannaf na AburRazaq, Hafiz ya tabbatar da wannan maganar a cikin Talkis[64]  Haakim ma ya kawo wannan hadisin   daga Nana Aishatu Allah ya qara mata yarda ta ce, “Yaro ana yanka masa raguna biyu yarinya rago xaya ba a qarya qashin ana yankawa ne  rana ta bakwai ko shahuxu ko Ashirin da xaya, ana cin naman ne kuma ayin sadaka  da naman ragon ya kasance a rana ta bakwai. An tambayi Imam Ahmad aka ce mashi ya ya za a yi da naman ragon suna ya ce ba a qarya qashin ragon suna ana ci ne ayi kuma sadaka da shi.[65] Imam Malik ya ce “ ba valla qashin ragon suna ba a sayar da fatansa ko namansa  sannan ya ce ba yanka gurguwa ko mai vallallan qaho. [66] Sheikh Mustafal Adawi ya tabbatar da ingancin hadisin a cikin ta’aliqin da yayi ma Tuhafatul Maulud na ibn Qaym ya ce hadisi ne ingantacce, ba a qarya qashin ragon suna, rashin karya qashin yana taimakawa wajen tarbiyan yara.[67]

 YADDA AKE RABA NAMAN RAGUNNAN SUNA
Ana ba anguwan zoma karfata (kafan gaba) wanzami shima ana bashi, ita kuma mai jego abata rabi idan namiji ne anyanka raguna  biyu sai aba mai jego guda xaya xayan kuma aba anguwan zoma karfata, wanzami shima a ba shi nasa rabon.
Bayan da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya yanka ma sahabi Hassan raguna biyu, sai sahabi Aliyu Allah ya qara masa yarda ya kyautar da karfata ga unguwar zoma.[68]

YI WA JARIRI  ASKI
Ana yi wa jinjiri ko jinjira aski a rana ta bakwai, shi ma ya tabbata a karatarwar manzon Allah sallal Lahu alayi wa alihi wa sallam. Qin yi wa ‘ya’ya aski sava wa Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ne. Bayan askin sai a shafawa jariri/jaririya  man za’afaran akansa ko akanta, sai kuma a yi sadaka da kwatankwacin nauyin gashin ( wato za a sanya gashin a sikeli, nauyin da ya nuna sai a yi sadaka da shi: Idan kilo biyu ne, sai ka yi sadaka da azurfa biyu.)[69]

KACIYA
Ana yi wa jinjiri kaciya. Wajibi ne ga namiji, ga mace kuwa sunna ce. Kuma mutunta mace ne yi mata kaciya kamar yadda mai Risalah ya ce. Kuma hadisai masu yawa sun zo suna nuna mana sunna ce yi wa mata kaciya.[70] Ya kuma tabbata a sunna yi wa mata kaciya.  Ana yin kaciyar ne rana ta bakwai da haihuwar jinjirar, yin haka Sunna ce kuma shi ne mafifici ga addini da kuma yaron.[71]
Lalle wajibi ne yin kaciya, domin babu Annabin da bai da kaciya. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Kaciya tana daga cikin Fitra ta muslunci,”[72]  Wani hadisin kuma Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Abu biyar tarbiyya ce ta musulunci: Kaciya da aske gashin gaba da rage gashin baki da yanke qumba da tsige gashin hammata”[73].
،قَالَ رَسُولِ اللَّهِ الْفِطْرَةُ خَمْسٌ: الْخِتَانُ،وَالاسْتِحْدَادُ،وَقَصُّ الشَّارِبِ،وَتَقْلِيمُ الأَظْفَارِ،وَنَتْفُ الإِبْطِ
 Wanda ya fara yin kaciya shi ne Annabi Ibrahim yana xan shekara tamanin (80) Allah ya umurce shi da ya yi wa kansa kaciya da fatanya, kuma ya je ya yi kaciyar da fatanyar.[74] Shi ya sa Allah a Qur’ani ya yabe shi a matsayin mai cika alqawari. Kuma Allah a suratul Nahal ya ce mu bi tafarkin sa. Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albany ya ce ijima’i ne cewa kaciya ga maza wajibi ne kuma ya tabbatar da yin kaciya a rana ta bakwai dogararsa da hadisin da Xabarani ya ruwaito.[75]
Imam Ahmad ibn Hambal ya ce “kar kuci yanka wanda bai da kaciya, wanda bai da kaciya ba a karvan sallarsa da aikin hajjinsa har sai ya yi kaciya.[76]
Idan akai ma yaro kaciya arana ta bakwai ya fi saurin warkewa kuma ta kamewa gashi kuma yin haka shine daidai, yana da kyau iyaye suyi qoqari suyi ma ‘ya’yansu kaciya arana ta bakwai kamar yadda shari’a ta koyar. Kuma a likitance yin kaciya arana ta bakwai yana da nasa fa’idan.

SHAYARWA
Yana daga cikin haqqin ‘ya’ya a kan iyayen su mata su shayar da su nonon da ke jikinsu. Kada a shayar da su nonon gwangwani ko nonon shanu, Allah yana cewa,
 “Iyaye mata suna shayar da ‘ya’yansu shekaru biyu ga wanda ya ke so ya cika shayarwar.[77]
وَالْوَالِدَاتُ يُرْضِعْنَ أَوْلاَدَهُنَّ حَوْلَيْنِ كَامِلَيْنِ لِمَنْ أَرَادَ أَن يُتِمَّ الرَّضَاعَةَ       
Kuma ana so a yaye ‘ya’ya da wuri yana taimaka masu wajen zamantowar su masu qwaqwalwa, haka ibn Qaym ya ambata. Idan da hali a yaye su kafin su kai shekara biyu.[78]
Ana so uwa ta yawaita cin xanyan dabbino yana kawo nono ga jariri ko jaririya kuma yana da amfani wajen  zamantuwar yaro ya kasance mai hazaqa. Malamai sun ce yana daga cikin hikimar da Allah ya ce wa Nana Maryamu mahaifiyar Annabi Isah lokacin da ta haife shi aka ce mata ta girgiza gututtiran dabbino xanyan dabbion zai faxo ki xauka ki ci.[79]
وَهُزِّي إِلَيْكِ بِجِذْعِ النَّخْلَةِ تُسَاقِطْ عَلَيْكِ رُطَبًا جَنِيًّا

BAKIN YARO YA BUXE DA KALMAR TAUHIDI
Wannan zai kasance ne ta   abinda mahaifiyarsa ke yawaita faxi a gaban xanta ko ‘yarta.  Kamar su kalmar shahada, tasbihi, sai yaro ya taso da faxar su, amma idan mahaifiya ta kasance tana yawaita zagi, ko wasu maganganu da basu dace ba sai yaro ya taso da zage-zage.  Yana daga cikin tarbiyya ga 'ya'ya janyo su a jikinka da sakar masu fuska. Ta haka ne mutum zai fahimci matsalolin su har ya iya yi masu gyara.
Bakin ‘ya’yanku ya buxe da kalmar shahada haqqinsu ne. An ruwato daga  ibn Abbas Allah ya qara masa yarda ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya ce, ‘Bakunan ‘ya’yanku su zamanto farkon abinda zai buxe da shi  kalmar لاإله إلا الله   La’ila ha ilLalLah,  kuma ku umurce su da faxar  لاإله إلا الله La’ila ha ilLalLah  lokacin da su ka zo mutuwa.[80]   Haqqin  ‘ya’ya  a kan iyayen su  ne su tabbatar kalmar farko da  bakin yaro  zai buxe  da ita ta kasance faxar Kalmar.    لاإله إلا الله Wasu malaman sun ce wajibi ne a tabbatar bakinsa ya buxe da kalmar .hahadas  Ya tabbata sahabiya UmmuSulaym tana  umurtan xanta Anas da faxin  لاإله إلا الله Lailaha illalLah ta na ce masa xana ka ce لاإله إلا الله  La’ilaha illalLah  ka ce أشهد أن محمدا رسول الله Ashadu anna Muhammadar RasulilLah tana koya masa faxar wannan kalmar  ne kafin yaye.[81] 
Ana so uwa ta riqa ta maimaita kalmar a gaban ‘ya’yanta. Yana da kyau iyaye su kiyaye  jin kixe-kixe[82] domin ‘ya’yansu  bakunansu zai buxe da waka,  uwa idan tana zage-zage  yaronta bakinsa zai buxe da zagi. Abinda mahaifiya ta ke yawaita faxi a gaban xanta ko ‘yarta, kamar su kalmar shahada, tasbihi, hamdala, sai yaro ya taso da faxar su, amma idan mahaifiya ta kasance tana yawaita zage-zage, ko wasu maganganu waxanda basu dace ba sai yaro ya taso da zage-zage.  Bayan ya iya faxin Kalmar Shada  da faxin As-Hadu anna Muhammadar Rasulillah daga baya sai agaya masa ma’anarsu, kuma a nuna masa Allah yana sama kamar yadda ayoyi da hadisai suka tabbatar da cewa Allah na sama da zatinsa yana ko ina da iliminsa da ganinsa wannan itace aqidar Annabi  sallalLahu alayhi wa alihi wasallam cewa Allah nasama kuma itace aqidar sahabbai da tabi’ai, shiya sa Sheikh Abu Zaidul  al-Qiyrawani a tabbatar da cewa Allah nasama a littafinsa Risalah tun agabatarwar sa ya  kawo dalilai da ke nuna Allah nasama da zatinsa yana ko ina da ilimnsa.

CIYAR  DA   ‘YA’YANKA  HALAS
Yana daga cikin haqoqin ‘ya’ya a kan iyayensu ciyar da su halal. Duk uban da yake ciyar da ‘ya’yansa halal ya sauke nauyin da ke kansa kuma yaransa za su zamanto na kirki. Kuma iyaye su guje wa ciyar da ‘ya’yansu abinci na haramun. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Dukkan tsokar da ta tsiro ta hanyar haramun wuta ita ce makomarta.”  Sahabi Abubakar Siddiq ya tava qwaqulo amai saboda wata madara da ya sha. Bayan ya sha aka gaya masa yadda aka samo ta  sai ya amayar da ita. Bayan ya yi aman sai ya  ce  Annabi ya ce, “Tsokar da ta fito ta haramun wuta ita ta fi dacewa da ita.”[83]
Ya zama wajibi iyaye su kula da abincin da suke ba ‘ya’yansu. Ciyar da su haramun shi zai sa su taso da cin haramun da kuma munanan xabi’u da rena iyaye.
Ibn Abbas  ya  ce an tava karanta wannan ayar a gaban Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam:
يَا أَيُّهَا النَّاسُ كُلُوا مِمَّا فِي الْأَرْضِ حَلَالًا طَيِّبًا                                        
Sai Sahabi Sa’ad  ibn Abi Waqqas ya miqe ya ce,  “Ya RasulalLah ka roqar mani Allah in zama in na yi addu’a Allah ya amsa mani addu’ata. Sai  Manzon Allah  sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya  ce, “ Ya Sa’ad ka tsarkake abincinka zaka zama in ka yi addu’a Allah zai amsa maka.”[84]
يَا سَعْدُ أَطِبْ مَطْعَمَكَ تَكُنْ مُسْتَجَابَ الدَّعْوَةِ                             
Muna roqon iyaye da su kula da abincin da suke ci domin wanda ya ke ciyar da ‘ya’yansa haramun ya tauye masu haqqinsu kuma za su taso cikin haramun, ko da sun roqi Allah, Allah ba zai amsa musu ba. Manzon Allah sallal Lahu alayi wa alihi wa sallam ya bamu labarin wani mutum da ya taso cikin haramun ya xaga hannunsa yana roqon Allah, manzon Allah sal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Yaya Allah zai amsa masa bayan an ciyar da shi haramun!”[85] iyaye su guje ciyar da ‘ya’yansu abinci na haramun domin tsira gaban Allah ranar tashin Qiyama.
An samo hadisi daga Jabir Allah ya qara masa yarda ya ce,

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : (( يَا كَعْبُ بْنَ عُجْرَةَ إِنَّهُ لَنْ يَدْخُلَ الْجَنَّةَ لَحْمٌ نَبَتَ مِنْ سُحْتٍ )

” Haqiqa manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce,’ Ya Ka’ab ibn Ujurah lalle kasani cewa bazai shiga Aljannah ba duk tsokar da tsiro ta haramun”’[86]  wato duk wanda ya ke abincinsa na haramun ne  da shi ya ke ciyar da iyalinsa bazai shiga Aljannah ba.

KOYA MASU SALLAH
Wajibi ne ga iyaye su umurci ‘ya’yansu da yin sallah kamar yadda Allah ya ba mu labarin ya umurci Annabi sallal Lahu alayhi wa ali wa sallam a cikin suratu Xaha, inda Yake cewa, “Ka umurci iyalinka da yin sallah kuma ka yi haquri a kanta (sallah da kuma umurtar iyalin naka da yin sallah) ba ma buqatar wani arziqi  daga gareka, Mu Muke azurta ka, qarshen makoma kyakkyawa tana ga masu tsoron  Allah.”[87]
 وَأْمُرْ أَهْلَكَ بِالصَّلَاةِ وَاصْطَبِرْ عَلَيْهَا لَا نَسْأَلُكَ رِزْقًا نَّحْنُ نَرْزُقُكَ وَالْعَاقِبَةُ لِلتَّقْوَى
 Ana umurtar ‘ya’ya da yin sallah lokacin da suka kai shekara bakwai, amma kuma babu laifi in an umurce su da yin sallar kafin wannan lokaci. Amma dai yadda hadisi ya tabbata shi ne  in sun kai shekara bakwai (7) a umurce su da yin sallar, ko da wani lokaci uba ya riqa tafiya da xansa masallaci ita kuma uwa ta umurci ‘yarta da yin sallah da zaran lokacin sallah  ya yi.
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku umurci ‘ya’yan ku da yin sallah lokacin suna da shekara bakwai, ku buge su lokacin da suka kai shekara goma 10 kuma ku raba wajen kwanansu”.[88]
مُرُوا أَبْنَاءَكُمْ بِالصَّلاَةِ لِسَبْعِ سِنِينَ،وَاضْرِبُوهُمْ عَلَيْهَا لِعَشْرِ سِنِينَ،وَفَرِّقُوا بَيْنَهُمْ فِي الْمَضَاجِعِ                                                                                               
 Idan aka tarbiyyanci yaro da yin sallah da tsoron Allah  zai taso tasowa cikin tsarki da zama mutumin  kirki. Allah ya yabi Annabi Isma’il a cikin suratu Maryam Allah ya ce,
“ Ka basu labarin Annabi Isma’il ya kasance  mai gaskiyan (cika) aqawari ne ya kuma kasance manzo ne kuma Annabi ya kasance yana umurtar iyalinsa da yin sallah da bayar da zakkah ya kasance a wajen ubangijinsa yardajje ne.”[89]
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ إِسْمَاعِيلَ إِنَّهُ كَانَ صَادِقَ الْوَعْدِ وَكَانَ رَسُولا نَبِيًّاوَكَانَ يَأْمُرُ أَهْلَهُ بِالصَّلاةِ وَالزَّكَاةِ وَكَانَ عِنْدَ رَبِّهِ مَرْضِيًّا
Abin baqin ciki a yau sai ka ga uba ya tafi masallaci ya bar yaransa a gida, wannan kuskure ne. Kuma mai yin haka zai yi bayani gaban Allah ranar Qiyama. Wani lokaci uba sai ya tafi masallaci ya bar matarsa tana kallo ko tana girki, wannan ma kuskure ne kuma haxari ne ga magidanci. Akwai wani abin ban takaice zaka ga yara sun zo masallaci ana koransu,wannan kuskure ne zamani manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam yara suna zuwa masallaci amma ba wanda ya hana su, wata rana ma Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya yi ruku’o jikansa Hussain ya hau bayansa, manzon Allah  sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya daxe bai taso ba har sai da Hussain ya sauka da kansa, abin farinciki ne mu ga yaran mu a masallaci don yara suna wasa a masallaci ba a hana su zuwa. Na tava jin wani daqiqi yana cewa wai zai iya zama haramun zuwan yara masallaci, wannan maganar kuskure ne ba wanda ya isa ya haramta wani aiki sai da Aya ko Hadisi ko ijima’in malamai, muna roqon masu dukan yara a masallaci da su bari don Allah.


KOYA MASU KARATUN QUR’ANI
Yana daga cikin al’amari mai mahimmanci kuma yana cikin haqqin ‘ya’ya uba ya tabbatar ya koya masu karatun Qur’ani. Cikin Qur’ani xaukaka take kuma nan tsira take. Wanda ya ke son ‘ya’yansa da alheri da xaukaka duniya da lahira to ya kwaxaitu wajen koyar da ‘ya’yansa karatun Qur’ani da hardarsa da tuntuntunin ayoyinsa da kuma aiki da shi. Manzon Allah sal Lahu alyhi wa sallam ya ce, “Mafifici a cikin ku wanda ya koyi karatu Qur’ani kuma ya koyar da shi.” [90]
Imam Shafi’i ya hardace Qur’ani yana xan shekara bakwai, ya kuma hardace Muwaxxa yana xan shekara goma (10)[91]. Imam Nawawi ya hardace Qur’ani  yana xan shekara goma. Ibn Taymiyyah  kafin balaga ya hardace Qur’ani, haka shi ma Bin Baz.(Babban malami a saudiyya Allah ya ji qansa)
Sahal ibn Ma’az Aljuhaniy  ya ce, “Haqiqa Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya ce, ‘Duk wanda ya hardace Qur’ani kuma ya yi aiki da shi Allah zai sanya wa mahaifinsa hular mulki, haskenta ya fi hasken ranar duniya.’ Sai manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  ya ce, ‘Me  ku ke  zaton  wanda ya yi aiki da wannan.’”[92]
Ibn Mas’ud da sahabi Aliyu Allah ya qara masu yarda sun ce, “Ku tarbiyyantar da ‘ya’yanku xabi’u guda uku : Son Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam da son Ahlul Bayti[93] da karatun al-Qur’ani. Domin mahardata  al- Qur’ani suna cikin inuwar al-Arshin Allah ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa. Suna tare da Annabawa da zavavvun bayin Allah”.[94]
Wannan maganar sahabbai ce, amma tana da hukunci maganar Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, ka xauke ta kawai Annabi ne ya faxe ta saboda wata  qa’ida.
Allah ya taimaki iyayen su sauke wannan nauyin da ke kansu kuma yana da kyau iyaye su gane mutuncin ‘ya’yansu, shi ne su hardace Qur’ani.


ZAVA  WA  ‘YA’YA  ABOKAI/QAWAYE
Qa’ida ce uba ya zava wa ‘ya’yansa abokai, domin abokai suna da tasiri a wajen abokansu tasiri mai yawa. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa, alihi wa sallam ya ce,
وعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ،قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللهِ  : الْمَرْءُ عَلَى دِينِ خَلِيلِهِ،فَلْيَنْظُرْ أَحَدُكُمْ مَنْ يُخَالِلُ. "         “Mutum yana kan addinin Abokinsa ne kowa ya duba da wa zai abota.[95]
Idan ya kasance qawayen ‘yarka mutanen banza ne, zata kwaikwaye su itama ta zama na banza. Haka idan abokan xanka mutuanen kirki ne shi ma zai zama na kirki. Waxansu ‘ya’yan sukan taso da xabi’u kyawawa. Amma sakamakon abokansu mutanen banza ne sai su ma su canza. Don haka yana da kyau iyaye su zava wa ‘ya’yansu abokai idan kuma ka ga ‘ya’yanka da wasu  waxanda baka san su ba, ka kore su. In ko ba haka ba, to za su lalata maka yaro ko yarinya.

    ZAVA MASA MAKARANTA 
 Wajibi ne ga mahaifi ya zava wa ‘ya’yansa makaranta tagari wacce ba zata gurvata ma’ya’yansa tarbiyyar ba. Kuma ko da makarantar Islamiyya ce aguje kai yara makarantar Islamiyyar da Malamanta ke hira da ‘yanmata ko makarantar da zaka ji malamai na labarin ‘yan fim xin Hausa fitsararru  gurvatattu ko makarantar da xalibai ke zuwa don ‘yan mata, dole ne iyaye su kula da wace makaranta za su kai ‘ya’yansu,idan uba ya kai yaransa makarantar da ya ke malamanta basu da tarbiyya to suma yaran za su ta so da rashin tarbiyya.  Idan da hali uba ya kai ‘ya’yansa makarantar da take ba yara bane malamanta.[96] Haka nan makarantar  boko  a guji kai  yara  makarantun Kiristoci[97].
Uba shi zai sanya yaronsa /yarinya makarantar da ta dace, ba wadda yaron ya ke so ba. Kuma ba  inda abokan xanka suke ba. Kada kuma uba ya damu da cewa wai shi yana son makarantar da take kusa da gida.
Makaranta tana da tasiri mai yawa wajen zamantowar yaro ya zama na kirki ko na banza. Domin mafi yawan lokacin yaro/yariya yana qarasar da shi ne a makaranta. Idan kuma ya dawo makaranta ana so ka tambaye shi abinda aka koya masa.

ADALCI  TSAKIN  ‘YA’YA                       
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi wasiyya da yin adalci tsakanin ‘ya’yanku wajen bayar da kyauta. An samo hadisi daga Nu’uman ibn Bashirin Allah ya qara yarda da shi ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa a lihi wa sallam ya ce, ‘Ku ji tsoron Allah kuma ku yi adalci tsakanin ‘ya’yanku wajen bayar da kyauta kamar yadda kuke so ‘ya’yanku su yi maku biyayya.’” [98]  
Babu Kyau  uba ya nuna   wa ‘ya’yansa ya fi son wani daga   cikin su.[99]

TARBIYYANTAR  DA  SU  KAN  SON  MALAMAI
Yana daga cikin haqqin ‘ya’ya a wajen iyayensu nuna masu darajar malamai. Babu wanda ya kai malamai daraja a bayan qasa bayan Annabawa. Kuma Allah ya  ce, a yi masu biyayya a cikin suratu Nisa’i. Yana da kyau uba da uwa su nuna wa ‘ya’yansu darajar malamai. Malamai su ne magada Annabawa, Annabawa kuma ba su bar kuxi ba.” Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Malamai su ne magada Annabawa, su kuma Annabawa ba su bar gadon Dirhami ko Dinare ba. Annabawa sun bar gadon ilimi ne. Wanda ya yi riqo da ilimi ya yi riqo da rabo mai girma daga cikin gadonsu. “[100]
Faxar laifin malamai da kurakuran su ba siffar Ahlussunnah ba  ce.  Wulaqanta malamai ya na haifar da haxari mai girma ga al’umma. Bai dace ba uba ko uwa su riqa zagin malamai gaban ‘ya’yasu ba, yin haka sava wa koyawar musulunci ne kuma ruguza shari’ar Muslunci ne. Ko ba malami ba, shari’a ba ta yarda ka riqa faxar laifin sa ba. Musulunci ya koyar da ka rufa wa xan’uwan ka asiri,balle malami. Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Aljannah ta yi daxi ga wanda laifin kansa  ya hana sa tuna laifin wani.”  Yana daga cikin alamar AhlulSunnah na gaskiya girmama malamai kuma a ga kana girmama mahaifan malaminka da matarsa da kuma ‘ya’yansa. Ka riqa yi wa malamin ka hidima da mutunta sa. Idan ka ce kana girmama malamin ka amma kana wulaqanta ‘ya’yansa ko matarsa, to qarya ka yi ka ce kana girmama malamin naka, domin in ka wulaqanta matar malaminka malamin naka ne ka wulaqanta ba ita ba. Xalibi na gaskiya ba ya faxar sunan malaminsa saboda girmamawa, ba ya zama a kujerar malaminsa saboda girmamawa.

NUNA WA ‘YA’YA DANGIN KA  DA  NA  MAHAIFIYAR  KA
Musulunci ya koyar da mu zumunci kuma akwai katafariyar lada ga wanda yake sadar da zumunta. Kuma Allah a Qur’ani ya tsine wa wanda yake yanke zumunta acikin suratu Ahqaf.  Manzon sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “wanda ya ke yanke zumunci ba zai shiga aljannah ba.”[101] Wani hadisin  Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam  ya ce, “Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar tashin Qiyama to ya sadar da zumunta.”[102]
Idan aka bibiyi tarihi za mu ga yadda magabata suke nuna wa ‘ya’yansu dangin su, dole ne uba ya tabbatar ya nuna wa ‘ya’yansa danginsa. Ya riqa zuwa da su domin yaro ya taso da sanin danginsa.
 Rashin zumunci yana haifar da talauci da kuma mutuwa da wuri. Sadar da zumunci yana sa mutum ya daxe a duniya kuma Allah ya yalwata masa dukiyarsa.[103] Masu yanke zumunci Allah  ya tsine ma su. Allah yana cewa “Waxanda suke warware alqawarin Allah bayan an qulla shi kuma suke yanke abinda Allah ya yi umurni da a sadar da ita (yanke zumunci yana haifar da varna a bayan qasa. Lallai waxannan Allah ya tsine masu kuma suna da mummunan gida.” (ranar qiyma)[104]
HIJABI
‘Ya’ya mata su taso da sabon sanya hijabi tun suna ‘yan qanana, Kuma hijabi cikakke ba hijabin zamani ba. Hijabi wanda Allah ya yi  umurni  a cikin Suratul Ahzab Allah ya ce,
Ya kai wannan Annabi ka ce wa matanka da ‘ya’yanka da matan muminai su kusantar da manyan kayansu da ke kansu zuwa qasa (wato hijabansu tun daga saman kansu har  zuwa qasa) wanna shi ne ya fi dacewa da a gane su (matayen muminai). Ba kuma za a cutar da su ba. Kuma   Allah Ya kasance mai gafara ne kuma mai jinqai.[105]
يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن ذلك أدنى أن يعرفن فلا يؤذين وكان الله غفورارحيما                                  
Mai karatu ya nemi littafina na “Sharuxxan Hijabi a Musulunci.” Ba zan tsawaita ba yana da kyau iyaye su gane cewa dole ne su saba wa ‘ya’yansu da hijabi. Hijabin kuma na gaskiya ba na yaudara ba wanda ya cika sharuxxan hijabi a musulunci.
KOYA WA ‘YA’YA GASKIYA
Manzon Allah sallal Lah alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Gaskiya ta na shiryar da mutum ya zuwa  ga Birru,  ita kuma Birru  tana shiryarwa ya zuwa Aljannah. Duk mai gaskiya Allah yana son sa. Wani hadisin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Idan kuna so Allah ya so ku, to ku riqe amana kuma ku mayar da amana, ku yi gaskiya idan zaku yi magana. Sannan ku kyautata wa makwabci.”[106]
عن عبد الرحمن بن أبي قراد قال قال رسول الله «إن أحببتم أن يحبكم الله تعالى ورسوله فأدوا إذا ائتمنتم، واصدقوا إذا حدثتم، وأحسنوا جوار من جاوركم»
Waxansu iyayen su suke koya wa yara qarya. Idan yaro ya biyo baba ko mama sai su ce masa ya koma za su sayo masa biskit. Kuma sai su dawo babu biskit xin. Wannan qarya ake koya wa yara. Idan kana da yaro ya yi qarya kada ka kyale shi, ka tabbatar ka hukunta shi domin ya gane illar yin qarya.

KOYA  WA  ‘YA’YA   AMANA
Allah ba ya son mai cin amana mara gaskiya mai cuta xan damfara (419) Allah yana cewa,
  إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ مَنْ كَانَ خَوَّانًا أَثِيمًا                  
 “Haqiqa Allah ba ya son wanda yake mai yaudara mai yawan zunubi”[107] 
Allah ba ya qaunar wanda yake siffarsa ita ce yaudarar jama’a ko cin dukiyarsu da mutuncinsu da yawan aikata abinda Allah ya hana.

NUNA  WA  ‘YA’YA  GIRMAMA  NAGABA
Dole ne uba ya nuna ma ‘ya’yansa girmama nagaba. Yaro ya san girman yayansa da abokan uba da qawayen uwa. ‘Ya’ya su taso suna ganin girman duk wanda ya ke gaba da su, su gan su da mutunci da karamci.
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ba shi tare da ni, wanda ba ya ganin girman nagaba da shi.” Ibn Taymiyyah ya yi bayani ya ce. Wannan hadisin yana da ban tsoro, domin yadda Annabi ya  ce ba ka  tare da shi. Wata ruwayar cewa ya yi, “Ba ka tare da mu, wanda bai girmama nagaba da shi.”
KOYAR  DA  SU  SON  ALLAH  DA  MANZONSA
Iyaye su koyar da ‘ya’yansu son Allah da manzonsa sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam da kuma  gaskiya. Duk wanda ya rasa qaunar manzo Allah ya kafirta. Wannan ya sanya ‘Yan Bidi’a suke yi mana sharri suke cewa wai ba ma son Annabi. Bayan kuwa Ahlul Sunnah ya fi kowa son Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, Allah ya na cewa,
قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ                                                                        
 “Idan dai da gaske kuna son Allah to ku bi ni (Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam) Allah zai so ku kuma ya gafarta maku zunuban ku lalle Allah mai gafara ne kuma mai tausayi ne.”[108]
Alamar son Annabi to a ga kana bin umurninsa da koyi da shi. Kuma ka yi riqo da Qur’ani da Hadisi bisa fahimtar magabata naqwarai. Ka so Sahabbai da Ahlul Baiti.[109]

KOYA  WA  ‘YA’YA  YADDA  AKE  CIN  ABINCI
Ana so iyaye su koya wa ‘ya’yansu yadda ake cin abinci, a koya masu su ci da hannun dama kuma su ci abincin da ke gabansu kuma su ce BisilLahi. Su taso sun saba da abincin da ake ba su, ba wai wanda suke so ba. Manzon Allah ya ce wa wani yaro ya ci abinci da hannun dama kuma ya ci abincin da ke gabansa[110] kuma ya ce bismilLahi.
عن عُمَر بْنَ أَبِي سَلَمَةَ قال : (( كُنْتُ غُلامًا فِي حَجْرِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَكَانَتْ يَدِي تَطِيشُ فِي الصَّحْفَةِ فَقَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : يَا غُلامُ سَمِّ اللَّهَ وَكُلْ بِيَمِينِكَ وَكُلْ مِمَّا يَلِيكَ ، فَمَا زَالَتْ تِلْكَ طِعْمَتِي بَعْدُ)

 Ya tabbata Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yana cin abinci da yatsu uku ne idan kuma ya gama cin abinci yana cewa “Alhamdu lilLah” san kuma ya  suxe kwanon abincin kafin ya wanke hannunsa.[111] Har yadda ake zama wajen cin abinci akoya wa ‘ya’ya, a koya masu shan ruwa a zaune ba a tsaye ba.

KOYA  WA  ‘YA’YA  YADDA  AKE  SALLAMA
Yaro ko yarinya in zasu shiga xaki su yi sallama, Manzon Allah sallallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya koya wa wani yaro yadda ake sallama, ya ce masa, “Ka ce assalamu alaykum in shigo?” Haka ake so uwa ta koya wa ‘ya’yanta.

ADDU’A
‘Ya’ya suna buqatar addu’ar mahaifansu. Iyaye su yi haquri idan ‘ya’yansu sun vata masu rai su bar tsine masu. Zagin yara da tsine masu yana jawo wa yara hasara da bala’i a duniya da Qiyama. Mafi yawancin ‘ya’ya sukan shiga harkar shaye-shaye da sace-sace da zinace-zinace ne ta sanadiyar tsinuwar  da iyayensu suke yi masu.
Wata rana ana tafiya da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam sai wata mata ta bugi raquminta ta tsine wa raqumin. Sai Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa sallam ya ce, “A tsaya a cire kayan da ke kan raqumin domin mu ba za mu yi tafiya da wanda aka tsine masa ba.” Yar’uwa kin ji dabba ma ke nan balle mutum. Ko da kaza kike da ita a gida kina tsine mata, to idan ta yi qwai sai ta shanye sakamakon tsine mata da kike yi. Addu’ar mahaifa Allah yana amsawa. Idan aka tambayi tarihi za a ga yadda  Imamul Bukhari ya ke. An haifi Imamul Bukhari yana makaho ne amma saboda addu’ar da mahaifiyar sa take yi kullum tana roqon Allah ya sa idon xanta ya buxe. Sai wata rana tana barci da dare ta yi mafarki da Annabi Ibrahim. A cikin mafarkin Annabi Ibrahim ya ce mata in Allah ya so gobe idon xanki zai buxe.  Da garin Allah ya waye tana zaune da safe tana karatun Qur’ani sai ga Imamul Bukhari ya rugo da gudu yana cewa mama idona  ya buxe.[112] Allah sarki! Wannan ya samu ne sakamakon addu’ar mahaifiyarsa. Yau duniyar musulunci tana cigaba da amfana da shi. Allah ya ji qan sa  amin.

WASIYYA  GA  ‘YA’YA
A Wannan vangaren ba za a yi magana mai yawa ba, duk mai buqatar bayani sosai ya nemi littafina “Haqqoqin Miji a Kan Matarsa da Haqqoqin mata a Kan mijn ta,’’ (Wanda zai fito in sha Allah ba da jimawa ba).
      Sahabi Annas ya ce gaba xayan sahabban Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam sun kasance suna yi wa ‘ya’yansu mata wasiyya idan za su aurar da su. Suna yi masu wasiyya da a riqa yi wa miji hidima da kuma kyautata masa.[113] Magabata suna yi wa ‘ya’yansu mata wasiyya da karrama miji da nuna masu mijinsu mutun ne mai daraja mai mutunci da kuma haquri da shi, domin shi ke sama da ita.[114]

KOYAR  DA  ‘YA’YA  DOGARO  GA ALLAH  DA-KAI
Yana da kyau iyaye su koya wa ‘ya’ya zamantowa masu dogaro da kansu. Musulunci ya hana zaman banza kuma ya koyar da sana’a, kamar yadda dukkanin Annabawan Allah suke da sana’arsu. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yana da sana’arsa. Allah ya faxa a cikin suratul Furqan, ya kasance yana zuwa  fatauci. Sahabban Annabi sallalLahi wa alihi wa sallam duk suna da sanar’su.
Annabi Idris ya kasance  masaqi (maxiki) ne, sannan kuma annabi Dauda ya kasance maqeri ne, annabi  Ibrahim  yana kasance magini ne, annabi Ismail ya kasance  mafarauci ne. Bai dace ga iyaye su bar ‘ya’yansu su zama masu zaman banza masu zaman xumama benci ba. Wannan bai da ce ba. Babban abin baqin ciki iyaye su bar ‘ya’yansu su zama ‘yan bangar siyasa masu saran jama’a. Bayan su ‘yan siyasar  ‘ya’yansu suna makaranta suna karatu ko kuma suna aikin Gwanati, su kuwa waxannan ‘yan bangar siyasar sai shan wiwi. Allah ya kyauta kuma Allah ya shirye mu.
KOYAR DA ‘YA’YA YADDA AKE KWANCIYA
Yana daga cikin haqqin ‘ya’ya koya masu yadda ake kwanciya Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam yana kwanciya da matashi yana sanya hannunsa na dama aqasan kumatunsa na dama, ya hana kwanciyar rif da ciki ya ce kwanciyace ta ‘yan wuta. Yana da kyua iyaye su hana ‘ya’yansu kwanciyar rif da ciki kuma su koyar da su kwanciya da alwala.

DALILAN  DA  KAN  SANYA  YARA  LALACEWA
Ga kaxan daga cikin abubuwan da kan sanya yara su lalace, na kawo su ne a taqaice. Ga su kamar haka:
·        Ciyar da ‘ya’ya haramun: Cin haramun shi ne na farko cikin abubuwan da ke sanya ‘ya’ya su lalace, yau mutane basa damuwa da abincinsu halas ne ko haramun ne, Allah ya kyauta. Iyaye suji tsoron Allah su tabbatar abincinsu na halas ne, akawai magana mai qarfi da take nuna cin abincin haramun yana hana amsar Ibadan mutum.
·        Samun kai cikin masifar talauci.
·        Barin yara cikin yunwa.
·        Rigima tsakanin uwa da uba.
·        Maraici.
·        ‘Ya’ya su taso ba mahaifiyarsu a gidan.
·        Barin yara da munanan abokai.
·        Xaura ma ‘ya’ya talla masamman yara mata.
·        Barin ‘ya’ya ba karatun addini ban a boko.
·        Kallon finafinai. ‘Yan fim xin Hausa fitsararru marasa tarbiyya masu yaxa varna a bayan qasa da Fim xin Indiya da dai sauran finafinan  qasashen waje.
·        Garin da mutum yake zaune idan mutanen banza ke zaune a garin, to ‘ya’ya zasu kwaikwaye su.
·        Anguwar da kake zaune kart a zama ta mutanen banza.
·        Sanya wa ‘ya’ya munanan sunaye.
·        Shayar da yara nonon dabbobi ko madarar gwangwani.
·        Rashin zaman mahaifa a gida, kullum basu tare da ‘yayansu..
·        Mummunar addu’a ga ‘ya’ya da kuma zagin su.
·        Nuna wa yara son duniya fiye da lahira.
·        Yarda da ‘ya’yanka baki xaya.(wato a xauka ba sa laifi musamman mata ko bayan sun yi aure ne).
·        Aikata munanan ayukka gaban ‘ya’ya.
·        Faxa tsakanin uwa da uba  a gaban ‘ya’ya.
·        Sanya ‘ya’ya makarantar arna ko makaranta mara tarbiyya.
·        Rashin koya masu sallah.
·        Fifita karatun boko a kan na addini.
·        Rashin ba ‘ya’ya uzuri.
·        Rashin ba su tarbiyyar addini.
·        Barin koyarwar musulunci.


HANYOYIN TARBIYYAN ‘YA’YA
Ga wasu  hanyoyi da shawarwari da ake fatan in Allah ya yarda idan iyaye suka bisu  za a samu tarbiyyar ingantatta.
1-     Sa ma ‘ya’ya karatun Qur’ani agida suna saurare
2- Zuwa da su masallaci da wuraren wa’azi
3        Basu tarihin  Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam   da    na sahabbai Allah ya qara masu yarda.
4        - Yaban’ya’ya
5- Yafe masu in sunyi kuskure wani lokaci.
6– Tsawa da barazana a wani lokaci
7-     Xaukansu a jiki lokaci bayan lokaci
8-     Keve masu lokacin wasa
9-     Basu kyauta a matsayin qarfafa masu gwiwa
10-Fita dasu  waje ko cikin gari domin shaqatawa.
11-Sakin masu jiki domin sanin matsalolinsu.
KAMMALAWA
Wannan shi ne abinda ya samu na haqqoqin ‘ya’ya a kan iyayensu. Littafin da zai fito nan gaba shi ne, “Haqqoqin iyaye a kan ‘ya’yansu”.  Ina roqon Allah da ya amfanar da al’umar musulmi. Kuma duk wanda ya karanta wannan littafin ina roqonsa da ya yi mani addu’a ta alheri. Sannan ina kira ga iyaye da su ji tsoron Allah su san nauyin da Allah ya xora masu. Gyaruwar ‘ya’yansu ita ce tsirarsu duniya da lahira. Kuma su fahimci cewa Allah zai tambaye su ranar qiyama game da ‘ya’yansu.Maganata ta qarshe: Duk wanda ya ga kuskure ko gyara, qofa a buxe take, ya aiko mani da gyaransa ko kuskuren da ya hango, zan yi farin ciki sosai kuma zan gyara da yardar Allah. Ina yi wa mahaifa na addu’ar Allah ya ji qansu Allah ya ba su AljannatilFirdausi. za a iya samun sauran littattafan dana rubuta a mudawwanata ta yanar gizo-gizo na  http://harunaabubakarshika.blogspot.com ina roqon addua ta alheri ga duk wanda ya karanta littafi na nagode.
والله تعالى أسأل أن يجعل هذا العمل مقبولاً، مباركاً، خالصاُ لوجهه الكريم، وأن ينفعني به في حياتي وبعد مماتي، وأن ينفع به كل من انتهى إليه؛ فإنه سبحانه خير مسؤول، وأكرم مأمول، وهو حسبنا ونعم الوكيل، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم،  وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لاإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك
Wassalamu alaykum warahamatulLah  wa barakatuhu
12/Sha’aban 1431- 3/8/2010
Harun Abubakar Shika
           08030582333-08020900001-08054533361


[1] Allah ya bamu labarin Annabi Ayyub acikin suratul Anbiya’i ya yi ciwo qafa na tsawon shekara sha bakwai baya iya ko fita ‘ya’yansa suka rasu dukiyarsa ta qare, bayan ya warke Allah ya bas hi wasu  ‘ya’yan da kuma dukiyarsa. Duba Tafsirin ibn Kasir da Sahihul Bukhari za a samu cikakken qissarsa.
[2] Bukhari da FathulBari 11/73229 da Muslim 24781 da Ahmad 3/108
[3] Cikin addu’ar da Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi wa Anas ya roqa masa Allah ya ba shi tsawon rai. Annas ya shekara xari da hamsin (150) a duniya, saboda daxewa har sai da ya makance. Yana cikin makantar tasa ne ya kira babbar ‘yarsa mai suna Umainatu  ya tambaye ta yawan ‘ya’yansa. Sai ta ce sai an qirga. Da aka qirga ne aka samu xari da ashirin da biyar. Casa’in sun rasu. Kuma abin ban sha’awa dukkanin ‘ya’yan nasa sun hardace Qur’ani. Annas ya yi wa Manzon Allah hidima ta tsawon shekara goma. Bayan wafatin  Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, kullun dare sai ya yi mafarki da Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam saboda qaunar da yake masa. Idan ya faxi wannan maganar sai ya fashe da kuka. Kuma  daga cikin baiwar da Allah yayi masa in ya yi addu’a Allah yana amsawa. Wata rana mai kula masa da gonarsa ya zo wajensa ya ce wa Annas, “Babu ruwa amfanin gonarka ya yi yaushi. Sai Annas ya tashi ya yi alwala ya yi sallah raka’a biyu ya roqi Allah. Nan take Allah ya yi ruwa mai yawa. Amma iya bakin gonarsa ruwan ya tsaya.
[4] Family Planning (Qayyade yawan iyali) ba shi cikin manufar aure a musulunci, Allah ne yake ciyar da mu. Haka ya faxia cikin Al-Qur’ani ya ce, “Kada ku kashe ‘ya’yanku don tsoron talauci, Mu muke azurta ku ku da ‘ya’yan naku.”  Yahudawa maqiya addinin Allah  ne suka kawo mana domin su rage yawan mu. Kuma duk wanda ya ke bincike ya san qasashen da suke zuga mu da mu yi Family Planing  su ba sa yi. Duk matar da ta yi family planing kawai don tsoron talauci ta sava ma Allah da Annabinsa, kuma akwai wani hadisi mai ban tsoro da ke cikin Muslim da yake cewa duk ‘ya’yan da aka zubar da cikin su ranar Qiyama Allah zai ba su dorina ta wuta su riqa dukan iyayen da suka zubar da cikin su,suna tambayarsu laifin da suka yi aka zubar da cikin su. Duk wadda ta san ta tava zubar da ciki, to ta ji wannan hadisin sai ta shirya amsar da za ta gaya wa Allah. Malamai suna fassara ayar da  Allah yake cewa, “Idan aka tambayi waxanda aka rufe su laifin me suka yi aka kashesu”   waxanda zuka zubar da ciki su ma sun shiga ciki. Allah ya kyauta. Zubar da ciki dai haramun ne laifi ne da ke kai mata wuta Allah ya tsare mu.
[5] Abu Dauda  2685 da Ibn Hibban 4056 da Mustadarak na Hakim Imamul Munzir ya kawo shi  a cikin Attargib wattarhi kuma Albany ya inganta shi.
[6] Hadisai mabambamta sun tabbata da suke nuna mana haramcin auren dole. Ya tabbata wata mata ta je wajen Annabi sallal Lahu alayi wa alihi wa sallam ta ce, “Baba na ya yi ma ni auren dole.” Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya kashe auren ya ba ta wanda take so. Wata matan ita ma ta je wajen Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ta gaya masa an yi ma ta auren dole. Sai  Manzon Allah ya yi niyyar kashe auren, amma sai yarinyar ta ce a bar  auren. Ta ce tana so ne a nuna wa iyaye ba kyau auren dole. Idan mutum yana son yarinya iyayenta ba sa son sa, to ya kyale ta wannan shi ne zance mafi daxi. Kada ya matsa ya ce dole sai ya aure ta, yin haka sava wa shari’a ne.
[7] Sadaka mai gudana ita ce (wacce ladanta ke gudana batare da yankewaba) kamar: gina masallaci ko ka ba da filin, ko ka gina makarantar Islamiyya ko itacen da ake shan ‘ya’yansa ko ka gina rijiya a hanyar jama’a suna shan ruwan rijiyar da sauransu.
[8] Muslim  163 da AbuDauda 2880 da Tirmidhi 1376
[9] Ahmad 17/357 da ibnMaajah 3660
[10] Abu Na’im fi Hiliyatul Auliya’a 2/344 da  Bayhaqi Shu’ubul Iman 5/122
[11] Suratu Nahal 59
[12] A Jahiliyya idan matansu suka haifi ‘ya mace zuwa suke yi su gina rami su rufe ta da ranta. Akwai wani sahabi kullum ya zo wurin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam  sai ya zauna cikin vacin rai. Wata rana aka tambaye shi mai ya sanya kana wajen Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam kullum cikin damuwa? Sai ya ce yana tuna abin da ya aikata zamanin Jahiliyya ne. Ya ce matarsa ta haifi ‘ya mace  sai ta ce kar ya kasha ta. Ya yarda ba zai kasha ta ba. Wata rana bayan ya yi tafiya ya dawo ya tarar da yarinyar har ta yi girma, sai ya ce wa mahaifiyar ta ta yi ma ta kwalliya zai yi tafiya da ita. Matarsa ta yi ma ta kwalliya sannan ta ce ma shi kada ya manta da alqawarin da suka yi  na ba zai kasha ta ba. Ya xauke ta ya fito bayan gari da ita, sai ya tuna dajin da ya fi muni a garin, sai ya tafi can. Da ya ya je cikin dajin sai ya tuna inda ya fi muni a dajin, sai ya tafi can. Da ya            je sai ya ga rijiyoyi guda uku, ya duba wadda ta fi muni. Ya aje ta ya rugo da gudu zai jefa ta, sai ta ce, “Baba ka tuna alqawarin da kuka yi da Mama da ka ce ba zaka kashe ni ba. Sai ya tsaya. Sai  da ya yi haka sau uku. A na ukun sai ya jefa ta. Da ya jefa ta sai ya ji ta yi qara, sai ransa ya vaci. Ya qara da cewa ba wai yana baqin cikin qarar ta ba ne, yana baqin cikin har yanzu tana da  rai ne. Daga nan sai ya nemo marmara ya yi ta jefawa cikin rijiyar har sai da ya ji ya fasa qwaqwalwarta sannan  ya tafi. Daga nan sai ya xaga kansa ya kalli Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Sai ya ga hawaye na zubowa a idonsa. Sai Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Wallahi  da zan zartar wa wani hukunci a kan abin da ya aikata kafin zuwan musulunci, to da kuwa na zartar maka. Amma sai dai musulunci ya yafe abinda ya wuce. Wannan shi ne yadda ake yi wa mata a jahiliyya. A yanzu kuma sabuwar Jahiliyya mata zuwa suke yi su zubar da cikin da suka samu. Wasu kuwa sai sun haihu su je su jefa su cikin rijiya ko shadda (masai) Allah ya kyauta.
[13]  Shurah 50
[14]  Abi Shayba  13/95 Hadisine hasaan
[15] Byhaqi Shu’ubul Iman 11/154 hadsi ne hasan
[16] Bukhari da Muslim
[17] Tirmidhi
[18] Babu kyau mutum ya fara  maganar  aure da yarunya  batare da ya nemi izinin iyayenta ba, Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasalam ya je wajen sayiddina Abubakar ya nemi izin neman auren Nana A’ishatu shima sahabi Abubakar ya je wajen Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya nemi izinin neman auren Nana Fatimatu  Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya ce ya yi haquri akwai abin da Allah yak e nufi. Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya aiki sahabi Hatim Ibn Abi Balta’a ya je ya nema masa izinin  neman auren Ummu Salma, hal ila yau ya aiki Sayiddina Zaid ya je ya nema masa izinin  neman auren Nana Zainab haka ma Nana Hafsah sai da ya aika yana neman izini wajen sahabi Umar haka shima Umar sai da ya nemi izinin neman auren ‘yar Sahabi Aliyu, shima Sahabi Aliyu sai da yaje neman izinin neman auren Nana Fatimatu, sahabi Bilal ya ga yarinya bai mata Magana ba sai da yaje wajen iyayenta yana mai neman izini. Dalile suna da yawa waxan da suke nuna mana cewa abinda yake daidai dole sai ka nemi izinin iyaye kafin kai ma yarinya magana. Alamace ta rashin sanin addini mutum yaje nemen aure bai nemi izinin iyaye ba kuma suma iyaye yana da kyau su tabbatar da cewa an nemi izini kafin ai magana da ‘ya’yansu.
Bai dace ba iyaye su qyale  kowa ya zo wajen ‘ya’yansu ba tare da niman izin ba.
[19] Bukhari  5090 da muslim 1466 da AbuDauda 2047
[20] Haakim filmusdarak 2/363
[21] Ibn maajah 1968 Sheikh Albani ya ingantashi acikin Sahihu ibn Majaah 1067   wato idan ka auro yarinya a gidan da ba su da tarbiyya ‘ya’yanka zasu zama marasa tarbiyya. Shi ya sa yana da kyau mutane su kula da kyau wajen aure domin ‘ya’ya suna biyo iyayensu mata ne. Yana da kyau uba ya gane cewa haqqin ‘ya’yansa ne in ya tashi yin aure to ya auri mai addini kuma mai xabi’a kyakkyawa gidan mutunci. Ita ma mace haka zata tabbatar ta auri mai addini mai xabi’a ta qwarai.
[22] Amma bayan mutuwar Nana Fatimah Sahabi Aliyu ya qara aure. Cikin waxanda ya aura har da matar wansa Ja’afar. Matar Ja’afar ta auri Sahabi Abubakar, kuma bayan shi kuma ya rasu sai sahabi Aliyu ya aure ta. Sahabi Ja’afar ya yi shahada ne a yaqin Mu’uta. Wannan ya nuna mana halal ne kuma abin arziqi ne ka auri matar wanka  bayan rasuwarsa ko in ya sake ta. Kuma an fahinci sava wa Allah da Annabinsa wasan da Hausawa suke yi tsakanin wan miji da qanin miji. Wasan qanin miji da wan miji ta’addanci ne ba addini ba ne. Bai halatta mace ta yi wasa da kowa ba sai mijinta.
[23] Ya halatta mace in ta ga namijin kirki mai addini ta ce masa tana son sa da aure, ko babanta idan ya ga mutumin kirki zai iya ce masa ya zo ya auri ‘yarsa.  Magabata na qwarai suna yin haka. Misali sahabi Umar ya nemi sahabi Abubakar da  ya zo ya auri ‘yarsa Nana Hafsah,.Daga baya Manzo Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya aure ta. Shi ma Sahabi Aliyu ya nemi Sahabi Umar da ya zo ya auri ‘yarsa UmmuKhulsum. Sahabi Umar kuma ya aure ta Allah ya qara masu yarda baki daya. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa sallam ya ba Sahabi Usman ‘ya’yansa guda biyu. Da ta qarshe ta mutu sai ya ce, “Da muna da wata da mun  aura ma ka.” Tabi’i Sa’id ibn Musayib ya tambayi xalibinsa in yana son ‘yarsa. Xalibin ya amsa da cewa yana so. Sa’id ya aurar da ‘yarsa ga xalibin nasa domin samun tsira ga ‘yarsa tasa.
[24] Ahmad da Dabarani
[25]  Ya halatta ka yi istihara a komai ba sai wajen aure ba kawai. Duk yayin da ka dimanci yin istihara a komai zaka ga fatahi da gam-da-katar.
[26] Adabu Duniya wad Din 129
[27] Tuhufatul Arusain
[28] muslim
[29] TarbiyyatulAulad fil dha’ikitabi Wasunnah 12
[30] Tirmizi  1075da ibn majah 1967 Albany ya ingantasu hadisi ne ingantacce duba Sahih Jami’u 270.
[31] Wani lokaci zaka ga namiji yana cewa shi in zai yi aure sai farar mace, amma shi kuma baqi ne, ko kuma ka gan shi mummuna. Ko kuma ya riqa kawo wasu qa’idoji da yake so mace ta cika amma kuma shi bai cika ko xaya ba. Yana da kyau ya gane cewa yadda yake son wasu abubuwa a wajen mace, ita ma tana son waxannan abubuwan. Shi ya sanya Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya fifita addini. Kai ma, ko ke ma idan dai addini ne a ranka/ki, to  ka|ki zavi mai addini.
[32] Wannan hadisin labari yake bayarwa ba umurni ba. Akwai ‘yan acavan addini da suke cewa wai wannan hadisi yana nuna mana mutum ya zavi kyakkyawa. Wannan maganar kuskure ce. Waxanda suke auren mace saboda dukiya su ne Yahudawa. Masu auren mace saboda danginta su ne Larabawa.  A zamanin Jahiliyya masu auren mace saboda kyau su ne Turawa. Masu auren mace saboda addini su ne Musulmi na gaskiya. Amma idan Allah ya sa addini ya haxu da kyau, ya zama anwar kenan riban qafa. Wallahu A’alam.
[33] Bukhari 5090 da Muslim 3708
[34] Ibn Majah  da Bazzar ibn Kasir ya ce hadisi ne da’ifi saboda a cikin isnadinsa akwai al Ifriqi kuma al Ifriq da’ifi ne amma kuma babban Malamin Hadisin qasar Misra Sheikh Ahmad Shakir ya ce hadisi ne ingantacce yaqara da cewa ifriqin da ke cikin ruwayar amintacce ne  ya ce duk wanda ya ce dhaifi ne ya yi  kuskure kuma sai ga ruwayar Bayhaqi, Sheikh Ali Bassam ya tabbatar da ingancinsa acikin littafinsa Taudhihul Ahkam  5/236  saboda haka hadisin bai da qura balle har ya sami targaxe.
[35] AdabudDuniya wadDinn 132
[36] AdabudDuniya wadDinn 132
[37] Taudhihul Ahkam 5/237
[38]  Hiliyatul Auliya’a na Abu Na’im 7/ 289 NikahusSalihah Thamaruhu wa Asaruhu  24 
[39]  Ibn Maajah da Silsilatul AhadisusSahiha 623.Kuskure ne babba ace  yarinya sai ta gama makaranta sannan za ai mata aure, yariya ko wane irin darasi ta ke karantawa ayi mata aurenta shine daidai ta ci gaba da karatun ta agidan mijinta. Sheikh Abu Ishaqal Kuwaini ya tambayi Sheikh Albani cewa suna so ‘ya’yansu mata suyi karatun Likitanci, amma suna jin tsoron yanayin karatun Bokon mata kar su lalace, kuma ga shi ana so mata su karanta likitanci (Medicine)?  Sai Sheikh Albani ya ce “ In dai matanbaza Musulmai suna karanta Likitanci, to ku ku aurar da naku” kada suma su lalace. Gaskiya kuskure ne ace ana jira sai yarinya ta gama Boko sannan ace za ai mata aure, sha’awa kamar yinwa ce maganin yinwa cin abinci ita ma sha’awa maganinta biyan buqata, ya kamata iyaye su kula da kyau in yarinya ta balaga a aurar da  ita, kar ja jawo abin faxa shine gaskiyan labara, aure baya hana karatu, karatu baya hana aure. Mai aure ta fi mara aure gane karatu.
[40] Itama bazawarar a tabbatar mai addini ce, mhm duk wanda ya auri mace ba don addini ba zai rena kansa, amfanin auran mai addini yana da yawa Imamu Shafi’i babansa ya rasu tun yana xan jariri amma da yake uwarsa mai addini ne a wajenta ya haddace Qur’ani da Muwadxa. Imam Ahmad bn Hambal ya ce shekaransa talatin da matarsa amma bata tava sava masa ba ko jayayya da shi bata tava yi da shi ba, Amfanin mai addini ke ne kenan, sahabi Umar yaji wata mata tana jayayya da ‘yarta akan ta daina zuba ruwa a nono, da yaji haka ya tura xansa Asim ya auri yarinyar ita matar da ya aura ita ce ta haifi Umar bn AbdulAziz babban khalifa wanda tarihi bazai manta da shi ba, amfani auran mai addini kenan.
[41] Abu Dauda 2162 duk saduwar da aka karanta wannan addu’ar da yaddan Allah za a samu xa ko ‘ya ta qwarai domin Annabi sallalLahu alayhi wa’alihi wasallam ya ce idan Allah ya qaddar xa a wannan saduwar shaydan ba zai cutar da shi  ba wato ana fatan Allah zai kare shi daga vata da yaddan Allah
[42] Bukhari 5165
[43]  Ibn Adiyu hadisine hasan.
[44] ‘Yan luwaxi dama su hukuncinsu kashe su akeyi mata masu yin maxigo Allah ya tsine masu in suka mutu suna yin maxigo (Lesbiansm) baza su shiga Aljanna ba haka suma maza masu yin  luwaxi  (Homosexualism) su ma tsinannu ne tun a duniya Allah zai wulaqanta su in ba su tuba ba.  Luwaxi na kawo cututtuka da xaukewar albarkan qasa da abinci, duk wanda ake Luwaxi da shi duburansa na rarikewa duk wanda yake yin luwaxi tsutsotsi na taruwa  a cikinsa shi ya sa waxanda suke yin luwaxi su ke zuwa akwashe tsutsotsin da ke cikinsu, in ba a kwashe ba suna taruwa aciki sai ka ga mai luwaxi yayi ciki kamar   mace  daganan sai mutuwar qasqanci tun a duniya kafin lahira.
[45] Ahmad da Abu Dauda
[46] Sahih Muslim  5709
[47] Mafifici shine sanya suna a ranar da akai maka haihuwa domin duk haihuwar da akai ma Annabi sallalLahu wa’alihi wasallam a ranar haihuwa ya ke sanya suna duba, wani wajen kuma umurni yake bayarwa da a sanya sunan  Tuhufatul Maulud na ibn Qaym
[48] Sahih ib Hibnan  13/5818   Albany   ya  ce    hadisi ne hassa da Abu Dauda4950   4950 hadisi ne ingantattace
[49] Yana da kyau iyaye bayan sun sanya ma yaro suna kyakkyawa an so a yi masa Alkuya da suna mai kyau, misali kamar an ma yaro suna Yusuf ana iya masa Alkunya da  Abu Xabarani ko Abu Amina ko Hamdana ko dai wani suna mai kyau. Ya halasta canza suna mummuna Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya canza sunaye munana. Taron suna da mata sukeyi in anyi haihuwa Bidia ce yana da kyau magidanta su hana taron suna na mata kamar yadda Allah ya taimaka aka daina na maza suma mata ahana su shi ne gaskiyan labari.
[50] Addua bayan sallar farilla bidia ne domin babu hadisin da ya ce a yi addua bayan sallar farilla sai dai zikirori da su ka tabbata daga fiyayyen halitta, mafi munin bidia ita ce yin addua cikin jam’i bayan sallar farilla da ‘yanbidia suke yi, amma ya tabbata ka xaga hannunka ka yi addua bayan sallar nafila, amma sallar farilla babu dalili daga Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam duba Majmo’u Fatawa na ibn Taymiyyah da Zadul Ma’ad na ibn Qaym za a ga bayani gamsasshe.
[51] Bukhari  5467 da  Muslim 2145. A ruwayar Imam Ahmad ya ce “ ya sanya mashi suna AbdulLahi, Ya halasta kokuma ka ce mafifice shine in akai maka haifuwa ka sanya  ma shi  suna ranar da aka haife shi, Manzon Allah sallalLahu alayhi wa’alihi wasallam   duk haifuwar da akai mashi yana sanya suna ne ranar da akai masa haifuwa ne, haka duk yaran da aka kawo masa yana sanya masa suna ne a ranar da aka haife su. Duba Tuhufatul Maulud na Ibn Qaym ko Zadul Ma’ad.
[52] Sahihu FikhusSunnah 3/
[53] Attahazub 5/42
[54] Majmu’u Zawa’id 4/60
[55] Bayhaqi fi Shu’ubul Iman  6/8620
[56]  Ahkamul Maulud fi Sunnatil Muxaharah 34-39 za a ga bayani masu gamsarwa da su ke nuna ba tabbatacciyar huja  akan kiran sallah da iqama
[57] AbuDaud 2835 da Tirmizi da Nasa’i 4217
[58] Sheikh Albany ya inganta hadisin a cikin Sahihu Jami’u 413 da Raudhun Nadhir 166, ya inganta hadisin ne daga baya, da ya raunata shi a cikin Irwa’ul Ghalil 1170 amma  daga baya ya ce hadisi ne ingantacce. Sheikh Abu Ishaq Alhuwainiy ya ce hadisi ne ingantacce bai da qura duba littafinsa “Al-inshirahu fi Adabi Nikah 102
[59] AbuDaud 284 da Imamun Nasa’i165-166/7 da Abu Naim cikin Hiliyatul Auliyaa 1161//7
[60] Ahmad 251/6 da Bayhaqi 301/9
[61]  Ya halasta ka yanka ma kakan bayan ka girma ka ji labarin iyayenka ba su yanka maka ba, ya tabbata Manzon Allah sallalLahu alayhi wa’alihi wasallam ya yanka ma kansa bayan an aiko shi Annabi duba Muskal na Xahawi 1/461 da Xabarani fil Ausax 1/529.
[62] Al-Majmu’u 8/250 na Imam an-Nawawi da Sharhu al-Mumti’u 3/400 na Uthaymin da Mudawwanatu al-Kubra 5/279 da Muhalla 8/157 zance mafi daxi dai shine yanka a yini na bakwai  akeyi  ba na takwas ba, in an yi haifuwa ranar Juma’a zaka yanka rago ranar Alhais, idan ranar Alhamis aka yi maka haifuwa zaka yi yanka ranar Laraba ne. Idan ko bayan dare ya shiga ne to za ka fara qidayanka daga yini  na  gaba ne, misali  anyi maka haihuwa ranar juma’a bayan sallar Magariba, zaka yanka Rago ne ranar juma’a saboda ranar ta fita, amma da ace bayan sallar Juma’a akai maka haihuwa za ka yamka ragonka ranar Alhamis ne. Ataqaice ana fara qirga ne daga ranar haihuwa . Mai karatu ya qirga daga ranar Juma’a  zuwa Alhamis  zai sami kwana bakwai ne, idan ko ya kai Juma’a ya zama kwana takwas ne Allah ya bamu ikon gyarawa.
[63] Muhallah 7/523
[64]  Talkis  4/47
[65] Masa’il Abdullahi ibn Ahmad 267
[66]  Attamhid na ibn AbdulBarri 4/317 Al-inshirah na Abi Ishaq Khuwani shafi na 100
[67] Mai Risalah Abu Muhammad Abdullahi ibn Abi ZaidilQirawani ya ce ba laifi in an karya qashin Ragon suna, amma Ibn Qaym da wasu Malaman hadisi suna da fahintar ba a karya qashin Ragon Suna والله أعلم .
[68] Duba sunan Bayhaqi
[69] Yanzu tunda bama amfani da azurfa sai mutum ya ji tsoron Allah ya yi sadaqa da kuxi gwargwadan abin da Allah ya hore masa kar  dai ya yi qwabro.
[70] Ahkamul maulud fi sunnsti mudahharah
[71] Bayhaqi fil Kubra  8/324 hadisi ne hasan
[72] Muslim
[73] Bukhari 5891 yana da kyau duk sati mutum ya riqa yin  aski  sunna ce amma qwalkwabo a zaman gida ba wajen aikin Hajjiba Bidi’a ce duba Ihya usSunnah na Xanfodio, kuma duk ranar Juma’a ka yanke kumba. Aske gemu haramun ne bai halasta ba ka aske gemu, ibn Jauzi acikin littafinsa Talbisul Iblis ya ce mai aske gemu ko bacci yake yi ana rubuta ma sa zunubi, aske gemo koyi ne da Yahudawa kuma kamanta kai ne da mata, Manzon sallalLahu alayh wa’alihi wasallam ya ce Allah ya tsine ma wanda ya kamanta kansa da mata. Mala’iku har tasbihi suke yi suna cewa tsarki ya tabbata ga wanda ya qawata maza da gemu, mai gemu yana samun ladan gemun sa kullum sabo da koyi da manzon Allah sallalLahu alayhi wa’alihi wasallam.
[74] Muwaxa da Bukhari 6297 da Bayhaqi  3270 da Ahmad 2/322-418
[75]  Tamamul Minnah 68- 76
[76] Al-Inshirah fi Adabil Khidiba shafi na115-116
[77] Baqara233
[78] TuhufatulMaulud
[79] Suratu Maryam 24Amru ibn Maymum ya ambaci mahimmanci cin dabbino ga mata masu shayarwa yana da kyau mata masu shayarwa su yawaita cin dabbino. Idan mai shayarwa bata da nono ko kuma nono bai zuwa sai a same garin hilba da ruwan zafi da zuma a haxa ana sha da yardan  Allah ruwan nono zai zo.  Amma wankan jego da matan Hausawa suke yi, ba addini bane al’ada ce kuma wanka jego yana da illoli masu yawa, yana da kyau a tambayi Likitoci za aji bayanin illolin wanka jego.
[80] Bayhaqi fi Shu’ubulIman 11/128
[81] Siyar aAlamunNubala 2/305
[82] Ibn Abbas ya ce sauraren kixa yana haifar da munafinci a zuciya kamar yadda ruwa yake fitar da tsiro kuma har ila yau ya ce hanyar da ke kai mutum ya zuwa ga zina nan danan ita ce jin kaxe-kaxe. Wani hadisin ya ce da ka ji kixa gara a zuba ma ka mutum narkarkiyar dalma a kunninka ya fi maka sauki.
[83] Bukhari da Ahmad da Xabarani da Abu Naim Sheikh Albany ya inganta shi acikin Sahihu Jami’u 4519
[84] Xabarani  Ausad 6688 Dhaif ne hadisin
[85] Muslim  2393 da  Bayhaqi fi shu’ubul Iman 2/388 iyaye su ji tsoron Allah su bar ba ‘ya’yansu haramun domin su tsira agaban Allah ranar kiyama.
[86] Ahmad 13919 da  Daarami filRiqaq 2657 da ibn Hibban Sheikh  Muhammad Nasirudeenil Albany ya inganta shi
[87] Suratu Daha 132
[88] AbuDauda 495 da Ahmad 3/648
[89] Suratu Maryam 54-55
[90] Bukhari 5027
[91] Siyar 11/10
[92] AbuDauda 1453 da Ahmad 24/302-303
[93] Nemi littafina mai suna Tasu’a da Ashurah  da cika-cika  za ka san Ahlul Bayti
[94] Xabarani da ibn Najr
[95] Abu Dauda 4833 da Tirmidh 2378 da Ahmad 3/195
[96] Bai dace ba asa waxanda basu da aure su riqa karantar da matan aure ba, mai aure shi ya san matsalolin masu aure ya kamata a kula da wannan nuxuqan.
[97] Zaka ga wasu makarantun Boko suna hana xalibansu sanya xankwali, wasu makarantun zaka ga bajen makarantan Janjami ne (cross) a jikin rigar su waxannan makarantun haramun ne musulmai su kai yaran su wannan makarantar, wasu kuma suna hana sanya Hijabi a makarantar su Allah ya kyauta duk musulmin kirki ba zai kai ‘yarsa makarantar da ake hana sanya Hijabi ba wasu ma zaka ga basa yarda xaliban makarantar su  su sanya xankwali Allah ya kyauta.
[98] Bukhari da Muslim
[99] Wanda ke da mata fiya da guda xaya in ya nuna yafi sona wani daga cikin ‘ya’yansa zai haifar masa da matsala babba za a sami savani tsakanin matan daga nan sai mummunan kishi  ya taso kuma ita uwar da ta fahinci ba a san ‘ya’yanta sai ta qulla gaba tsakaninsa xanta da sauran ‘ya’yan nasa da kuma sauran matansa.
[100] Ahmad 21715
[101] Bukhari fi AdabulMufrad 5984 da Muslim 2556
[102] Bukhari fi 6137 da Muslim

[103] Ahmad, Abin baqin ciki a yau zaka ga waxansu  iyayen ba ruwansu da zumunci kusan waxansu  yaran basu san danginsu ba idan uba ya mutu shikenan zumunci ya yanke Allah ya kyauta dole ne iyaye su nuna ma ‘ya’yansu zuriyarsu.
[104]  Suratur Ra’ad
[105] Suratul Ahzab
[106] Sahihu Jami’u
[107] Suratun Nisa’i 107
[108] suratu AliImmarana 31
[109] Lalle iyaye su nuna ma ‘ya’yansu haxarin addin Shia da ‘yanQalaqato da ‘yanBidi’a.
Maganar  ‘YanBidia da suke cewa wai  duk wanda bai Maulidi bai son Annabi wannan maganar tayi muni faxin wannan maganar kafirta mutane ne,bayan  ga shi su da kansu sun ce Annabi bai yi Maulidiba kuma Sahabai ba suyi ba, Imam Malik da AbuHanifa da Shafi’i da Ahmad bn Hambal da Tabiai baki xaya ba su yi Maulidi ba shin suna so su ce  waxannan basa son Annabi ne ko kuwa me su ke nufi Allah ya shirye waxannan mutanen su  gane cewa Maulidi ba addini ba ne.
[110] Idan yaro yana cin abincin gaban wani zai taso mai renuwa  ko mai  ya  samu baya godewa ya na kallon abin da ke wajen wani,babu kyau cin abinci da zafi.
[111] Muslim 3791
[112] Siyar a-AlamunNubala na Zahabi 12/393
[113] FiqhusSunnah
[114] Almar’matil muslimah amamaTahaddiyya 457

4 comments:

  1. Gaskia Malam ba abunda za muce sai dai "jazakallahu khairan" ubangiji Allah ya qara ilimi da basira, amin. Kuma naji dadin wannan jawabai naka sosai.

    ReplyDelete
  2. Allah ya qara basira Allah ya yawaita mana irinku #malam, gaskiya naji dadin waxannan jawabai naka masu qasqantar ðä zuciya zuwa bin ubangiji.

    ReplyDelete
  3. Allah ya saka da Alkhairi, ya qara basira da hasken makaranta

    ReplyDelete
  4. Gaskia Malam ba abunda za
    muce sai dai "jazakallahu
    khairan" ubangiji Allah ya qara
    ilimi da basira, amin. Kuma naji
    dadin wannan jawabai naka
    sosai.

    ReplyDelete