ABUBUWAN DA SUKE CIKI
Shafi
Godiya - - - - - 1
Taqarizi - - - - - 3
Matsayin Mata - - - 5
Ma’anar Hijabi - - - - 8
Sharuddan Hijabi - - - - 9
Niqabi - - - - - - - 38
Niqabi Yana da Asali -
- - -
39
Fahintar malamai a kan Niqabi -
- 44
Nasiha Ga Isah Hassan Tikuma - - 55
Mahimmancin Sa Hijabi - - - 58
Illar Rashin Sa Hijabi - - - 59
Yadda Ake So Mace ta yi tafiyarta -
59
Hattara Mata - - -
- - 60
Kammalawa - - - - - 63
GODIYA
GODIYA
بـسـم اللـه الـرحـمـن الـرحـيـم
إن
الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ
بالله من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادى
له، وأشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله.
أما بعد: فإن خير الحديث كتاب الله،
وخير الهدي هدي محمد، وشر الأمور محدثاتها، وكل محدثة بدعة، وكل بدعة ضلالة، وكل
ضلالة في النار.
Haqiqa
ina wa Allah godiya da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi taqaitacce Wanda
yake Magana a kan “Sharudxan hijabi a Musulunci” da bayani akan Niqabi da yadda
ake so tafiyar mace ya kasance, Ina
rokon Allah daya anfanar da shi. Dubi ga
halin da muke ciki na ga ya kamata a yi rubutu da ke bayanin tufafin mata a Musulunci
ta yadda kowace ‘yar uwa musulma zata
karanta ta gane haqiqanin tufafin da Allah ya ce, wa manzansa ya gaya ma
matayensa da ‘yayansa da matayen
mumuinai su riqa sanyawa (wato shigarsu
ta kasance ko da yaushe yadda Allah ya ce[1]). Domin Yahudawa maqiya addinin musulunci kullun qoqari suke yi
safiya da maraice wajen ganin sun lalata mana tarbiyyarmu masamman mata domin
sun san in suka lalata mata to kamar sun lalata al’uma ne, da ma burinsu kullun
so suke musulunci ya karye a daina jin labarinsa da tasirinsa a bayan qasa,
kuma su Yahudawa so suke shigar matayenmu ta zama shiga ceta kafirce.
Wannan
littafin shi ne bugu na huxu (4) ya taqaitune qarqashin Qur’an da Hadisi da maganganun
sahabbai da magabata na qwarai (salafusSalih) ina roqon duk wanda ya karanta
wannan littafin da ya yi ma ni addua ta alheri, kuma duk wanda yaga kuskure to
kofa a buxe take ya aiko da gyaransa in sha Allahu za a gyara kuma muna
farinciki da gyaransa. Ba zan gushe ba
ina mai godiya ga malam Abubakar Jumare Gixaxo Zaria da ya duba littafin
tundaga farko har qarshe ya gyara kurakuran da ke ciki da kuma ba da shawara,
Allah yasa ka ma shi da Aljanna amin. Ba kuma
zan manta da malami na ba malam Ahmad Bello Dogarawa wanda
koda yaushe yakan qarfafaman muhimmanci
yin rubutu domin ‘’yanuwa su anfana shima Allah yasa ka ma shi da Aljanna
amin.
Malam
Haruna Ishaq Shika Alqali da Malami na malam Mikail Isah Imam da Malam Muhammad Amin Jumare
Maqarfi Alqali suma Allah ya sakamasu da Aljanna amin. Da duk wanda ya taimaka wajen ganin wannan
littafi ya fito Allah yasa kama shi da alheri amin.
.
A
qarshe ina wa mahaifiyata Fatimatu Dalhatu Zaria da mahaifina malam Abubakar
Ibrahim adduar Allah ya saka masu da
Aljannatil Firdaus amin.
Wassalamu alaykum Harun Abubakar Shika
25 Ramadan 1429 / 24/9/2008
08030582333 -08054533361-08020900001
بسم الله الرحمن الرحيم
TAQARIZI
Lallai
gaodiya ta tabbata ga Allah muna gode masa
muna neman taimakonsa kuma muna
neman gafaransa muna roqon Allah ya tsaremu
daga sharrin kawunan mu da
munanan aiyukanmu, Duk wanda Allah ya
shiryatas ba bu mai vatar da shi, haka
kuma wanda Allah ya vatar dashi babu mai shiryar da shi ina shedawa babu abin
bauta na gaskiya sai Allah shi
kaxai ba shi da abokin tarayya, kuma
ina sheda cewa lallai Annabi muhammadu
sallalahu alaihi wa,alihi wasallam bawansa ne kuma Manzansa ne. Naga littafin
da xan uwa malam Harun Abubakar Shika (Izzah) ya wallafa wanda yake magana a
kan Hijabi da Niqabi da wasu nasihohi da faxakarwa ga nau’oin jama’a
daban-daban kamar mata masu fita irin ta jahiliyya da masu kuskuuren fahinta da
jahilai masu sanya rigar ilimi da ‘yanBidia da sauran su babu Shakka mawallafin
ya kyautata bayani kuma ya ilmantar kuma yayi nasiha Allah ya qarfafe shi don
ci gaba da yin talifi, ya kuma yawaita mana irinsu. Dukkan wani mumini masoyin
Allah mai kishi akan shiriyar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa’alihi
wasallam zai yi farinciki da irin bayanin da littafin ke xauke da shi ganin
cewa littafin bai qetare hujja daga Qur’ani da Sunnah da maganganun magabata na
qwarai da suran Malaman musulunci ba, sai dai
shaixan da rundunarsa za suyi baqin
ciki da abin da ke cikin littafen.
ومن يرد الله فتنته فلن تملك له من الله شيئا
Kuma kowane mumini zai burin Ina ma ace duk matayen
musulmi zasu qawaci wannan littafi kuma suyi aiki da shi. Allah yasakawa malam
Haruna da alheri duniya da lahira ya kuma taimakemu wurin Neman gaskiya da aiki
da ita ya kuma shiryi matayen mu.
.
AbuAbdurRahaman
Abubakar
Jumare Gixaxo
4/1/1430 - 31/12/2008
بسم
الله الرحمن الرحيم
MATSAYIN MATA
Haqiqa Allah ya yi wa muminai baiwa da ya aiko masu manzo a cikinsu, ya bayyana masu
shariar Allah, haqiqa Mata
suna xaya daga cikin al’ummar da Allah ya karrama su ya kuma girmamasu ya kuma ba su kariya, kuma manzon Allah sallallahu
alaihi wa,alihi wasallam ya yi umarni
da a kyautata ma su, kuma a karrama su kuma a ba su kariya kuma musulinci ya
bayyana mana cewa idan mace daya ta yi karatu kamar an koyar da al’umma ne idan
kuma ta gyaru kamar al,uma ce ta
gyaru,.mata suna da daraja mai girma. A
na cin nasarar al, uma ne in aka lalata
ma su matansu kuma musulinci yana
alfahari da mata, ba kuma zai manta da gudunmuwar da suke bayarwa ba tun, daga
zamanin Nana khadijah Allah ya qara ma ta yarda, da
Sumayyatu har ya zuwa yau. Iyayenmu mata sune makaranta ta farko da ke
tarbiyar yara, shi ya sa musulunci kullun ya ke qarfafa kulawa da su kulawa ta
masammam.[2]
Yahudawa
maqiya addinin Allah kullun yaqi su ke
yi safiya da maraice wajen ganin sun
lalata mata domin sun san su ne qashin
bayan al’umma sun san cewa mata suke bada tarbiyan yara, kuma sune tubalin
gina al’umma. Idan muka lura da kyau
zamu ga yadda suke fito mana da abubuwan
lalata dabi’u kamar fina finai, ( fim)
da waqe – waqe da tufafin tsaraici da
qyaman aure, da kuma yadda Yahudawa suke wulaqanta su (mata)
wajen sa hotunan su kan tituna kamar ِAllan bakin Titi (signbol) da kayan
sayarwarsu kamar sa hotonsu a jikin sabulu ko kayan sawa da manshafawa da kwalaye don wulaqanta su, da sa
su tsaran shago cikin shiga ta baxala, da kuma
qoqarin nuna masu shiga ta
addinin muslinci qauyanci ne kuma ci baya ne[3],
saboda mata a wajen maqiya addinin Allah ba su da qima[4]. Lura da halin da muke ciki na ga ya kamata a
yi ma yan’ uwa bayani yadda Allah ya umurci mata su rinka sa tufafinsu da kuma
sharudxan hijabi, da yin bayani akan kayan da suke haramun ne ga matan musulmai
su sa, da kuma bayanin kayan mata ‘yan wuta, da manzon Allah sallalahu alaihi
wa, alihi wasalam ya ce, al’ummar sa za
su rinka sa wa a qarshen zamani, kuma za mu yi bayani kan Niqabi ta mahangar
Kur,an da Hadisi da maganganu magabata na qwarai.
Lallai yana daga cikin kariya ga mata da Allah
ya yi masu wajen kare su daga dukkan tozarci, ya ce su sanya hijabi in za su
makaranta ko aiki ko asibiti ko ziyara kai duk in da zata, ta sa cikakken
hijabi wanda Allah yayi umarni da a sa cikakke wanda zai nuna cewa ita mace ce kamammiya, mai mutunci da
sanin ya kamata, mai bin Allah da Annabinsa sallalahu alaihi wa,a lihi
wasallam. Hijabi Aqida ce wadda dole ne musulma ta sa shi in dai ta yarda da
Annabi (sallalahu alaihi wa, alihi wasallam.)
kuma shi hijabi kamar sauran shari’o’ine wanda Annabawa suka yi bayani,
to shi ma Annabi Muhammad (sallalahu
alayhi wa alihi wasllam) ya yi bayanin
yadda ake so Hijabi ya kasance,
kuma yana da sharudxan sa kamar yadda sallah da zakka da aikin hajji da
azumi da sauran ibadu Suke da nasu
sharudxan, shi ma hijabi yana da na sa wanda dole ne hijabi ya cika su
sannan ya zama hijabin musulunci, wanda Annabi sallallahu alaihi wa,
alihi wasallam ya yi umurni da a sanya, idan har waxan nan sharudxan ba su cika
ba, to haqiqa hijabin bai cika hijabi
karvabve ba.
Haqiqa kunya tana cikin kyawawan dabi’u
wanda Allah ya aiko Annabi (sallalahu alaihi wa, alihi wasallam) da ita,
[kunya] ta na da ga xabi’u kyawawa wanda
manzon Allah sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya sanya ta yanki da
ga cikin rassa na imani[5]
kuma babu mai inkari (musu) a kan kunya abar so ce, kuma sharia ta yi umurni da
ita, sanya hijabi yana daga kyawawan xabi’u wanda Allah ya yi umurni da a sa
sannan manzansa yayi bayani yadda ake sa shi kuma ibada ce sanya shi (hijab).
Idan mu ka bibiyi tarihi za muga ba a
ci nasarar Daular musulunci ta Qasar ANDULUS
(SPAIN) ba sai bayan da matayen
qasar suka daina Sanya hijabi suka riqa fita, fita ta fitsara Wanda haka ya
jawo lalacewar xabi’un mutanen qasar ta sanidiyar rashin Sanya hijabi har aka
ci nasara a kan su. Don haka ya zama dole mu kula da matan mu da yaran mu, mu
tabbatar suna sa hijabi cikakke wadda shara`a ta yadda da shi.
MA,
ANAR HIJAB
Hijabi a
cikin harshen larabci yana nufin shamaki ko
kariya, amma a ma’anarsa ta shara’a. Hijabi shi ne dukkan wani mayafi
mai kauri da mata suke amfani da shi wajen rufe jikinsu baki daya har da
fuskarsu duk da cewa akwai savani tsaqanin malamai kan rufe fuska.[6]
Manufar
umurnin da Allah ya
bayar na sanya hijabi shi ne domin mace ta voye kwalliyar ta (ado) kar
wani ya gani sai dai mijinta ko xaya daga cikin waxanda Allah yayi wa izini a
cikin suratun Nur domin tsare mutuncinsu da kuma toshe kofar varna da fitina (
fasadi.)[7]
An wajabta sanya hijabi ne bayan hijrar
manzan Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallam daga Makka shi da sahabbansa Allah ya kara masu yarda. Wato a garin Madina ne aka
wajabta sanya hijabi. Ibn Qayyum Allah ya jiqan shi da gafara ya ce an saukar
da ayar hijabi ne bayan shekara ta uku dayin hijran Manzan Allah sallallahu
alaihi wa, alihi wasallam, ko kuma a shekara ta biyar bayan hijaran manzan Allah
sallahu alaihi wa,alih, bayan kuma Annabi ya auri Zainab kuma lokacin da ya yi
bina,i(tarewa) da Nana Zainab bintu
Jahash Allah ya qara yarda da ita [8]
SHARUDXAN HIJABI
Ga
sharudxan Hijabi a jere Kamar haka.[9]
1.
Ya rufe dukkan jiki sai abinda aka togace.
2.
Ya Zama mai kauri ba shara- shara ba.
3.
Kada hijabi ya zama mai ado(kwalliya)
4.
Ya zama yalwatacce ba mai kunci ba.
5.
Ka da a sanya masa turare.
6.
Kada hijabi ya yi Kama da tufafin maza.
7
Kada hijabi yayi kama da tufafin Arna (Kafirair
8
Kada ya zama tufafin alfahari.
9
Kar a sa masa hoto.
10
kar ya yi kama da na ‘yan bidi’a
11
kar ya kasance yana da janjami (Cross)
Idan a aka bibiyi ayoyin Alqurani da hadisan ma’aiki
sallalLahu alaihi wa alihi wasallam da maganganun sahabbai da sauran magabata na qwarai (salafusSalih)
zakaga waxannan sharudxa baki xaya da suke nuna mana sharudxan hijabi a muslunci.
1-
SHARAXI NA FARKO YA RUFE DUKKAN JIKI SAI INDA AKA TOGACE
Yana da ga cikin sharudxan hijabi dole ne ya
rufe dukkan jikin mace kamar yadda
Allah ya faxa a cikin suratul
Ahzab.
يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك
ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن ذلك أدنى أن يعرفن فلا يؤذين وكان الله غفورارحيما
Ya kai wannan Annabi
ka ce ma matayenka da ‘ya’yanka da matayen muminai su kusantar da manyan
kayansu da ke kansu zuwa kasa (wato hijabinsu tun daga saman kansu har zuwa kasa) wanna shine ya fi dacewa da a gane
su (matan mumina) bakuma za’acutar da su ba, kuma Allah yakasance maigafara ne kuma mai
jinqai,
Sheikh Abubakar
Mahmud Gumi da ya zo bayanin jilbab a wannan ayar a Tafsirin sa sai ya nuna ta rufe jikinta duk kan sa ta bar ido
xaya domin ganin hanya in zata fita.[10]
Sannan ayar da ke
cikin suratu Nur ita ma ta nuna mana
mace ta rufe duk kan jikin ta sai dai in da
aka togace. Haka shi ma Imamu
Dabariy ya kawo a tafsirin qarashin
wannan aya.[11]
وَقُلْ
لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ
زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا
‘’Ka ce ma
muminai mata su runtse daga
ganinsu kuma su tsare farjinsu,kar su
bayyanar da kwalliyarsu sai dai abin da ya bayyana daga gare ta……...[12]
Manzon Allah Sallalahu alaihi wa, alihi wasallam ya ce ‘’wanda ya ja
tufansa yana mai girman kai Allah ba zai ma shi kallo , kallo na rahama ba
ranar Tashin kiyama.Sai Ummu salma matar manzon Allah sallalahu alai hi
wa,alihi wasallam, Allah ya kara mata yarda ta ce yaya za mu yi da hijabanmu da
ke janqasa ?’’ Sai Annabi sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce to ku sake shi yana jan qasa dani xaya
(tikan hannu). Sai ta ce ‘’Qafafuwanmu
zasu bayyana.’’ sai Annabi (sallalahu alaihi wa,alihi wasallam.) ya ce, to ku
ja shi qasa kamu xaya kar ku qara a kan haka (wato kada a qara ya wuce kamu xaya
a qasa)[13]
Sheikh Nasiruddeenil Albany ya ce, a
cikin littafinsa ’Jilbab’ wannan hadisin
yana nuna mana a fili cewa lalle dole ne
hijabi ya rufe qafafuwan mace, wannan dole
ne sai ya rufe mata qafa[14]
Shi ma Imamu Baihaqi haka ya
ambata ya ce wannan hadisin dalili ne a
kan dole ne mace ta rufe qafafuwanta.
Wani hadisin ya nuna cewa ko da ya tava qazanta ba komai qasar gaba ta
tsarkake shi (hijab) haka Annabi
sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya faxa.
Hadisin ya zo cikin Muwadxa
عن أم ولد لإبراهيم بن عبد
الرحمن بن عوف أنها سألت أم سلمة زوج النبي صلى الله عليه وسلم فقالت : إني امرأة
أطيل ذيلي وأمشي في المكان القذر ؟ قالت أم سلمة : قال رسول الله صلى الله عليه
وسلم يطهره ما بعده An karbo hadisi
daga Ummu Ibrahim bn AbdurRahaman bn Auf ta tambayi UmmuSalama matar Annabi sallalahu alaihi wa, alihi wasallam ta
tambaye ta ta ce, ‘’Ni
na kasance mace ce mai dogon hijabi
yana jan qasa kuma ina tafiya a wuri mai najasa ? Sai Ummu salama ta ce, Tsarkinsa (hijabin) qasar
gaba manzan Allah sallalahu alaihi wa, alihi wasallam yace qasar databiyo baya ta tsarkake shi[15]
Wannan bayanin a fili yake ba komai
don hijabi ya tava qazanta, wata
mata wata rana ta ce ma manzan Allah
sallahu alaihi wa, alihi Ni hanyar da na kebi zuwa masallaci a kwai qazanta yaya zan yi da hijabina da ke jan qasa ?
Sai Annabi sallalahu alai wa alihi wasallam ya ce,’’ Ashe ba akwai wata mai tsarki ba bayan ta to wannan da wancan’’ (wato qasar gaba ta
tsarkake ta baya)
وعن امرأة من بني عبد الأشهل قال (
قلت : يا رسول الله إن لنا طريقا إلى المسجد منتنة فكيف نفعل إذا مطرنا ؟ قال :
أليس بعدها طريق هي أطيب منها ؟ قالت : قلت : بلى قال : فهذه بهذه
Don haka wannan hadisin ya nuna mana
don hijabin da ya taba qazanta ba Komai a gare ki. Jeki muwadxa babin da ke
bayani a kan kayan da a ka hana mata
su sa na tufafi, Imam Malik ya kawo hadisin da Hafsatu ‘yar Abdulrahaman ta
shiga wajen Nana Aisha Allah ya qaramata yarda, da hijabin da baidace ba xan qarami, sai taqwace shi ta yayyaga shi, sai ta sa ma
ta hijabi mai kauri babba.[16]
Don haka yana daga cikin sharaxin hijabi ya rufe
dukkan jikin mace kuma ya ja qasa.
Ya rufe ma mace qafafuwanta wannan dole ne bai
halasta a ga qafarta ba.
Sheikh Nasurudin Albani ya ce[17]
‘’ ya yin da aka tambaye shi game da
qafar mace. Sai ya amsa da cewa, ‘’qafar mace al, aura ce da bai halasta ta buxe ba
ko da a wajen sallah ne, kuma
matayan sahabbai sun kasance suna rufe qafafuwansu.Yace ya zo a cikin Sunan na
Abi Dauda dake nuna mace idan ta zo
sallah ya zama dole ta rufe qafanta baki xaya.
Babban malami
Sheihk bn Baz shi ma yayi bayani mai gamsarwa
inda yace duk matar da tayi sallah qafarta a waje bata da sallah ko tana
sallah qafarta ta fito bata da sallah.[18]
Shima Sheikh
Usaimin fahintarsa kenan haramun
ne mace tafitar da qafarta waje yayin da
ta fito daga gida ko kuma tana sallah.[19]
Shieikh
Muhammad Jamil Zaynu ya ambata a cikin littafinsa cewa lalle dole ne mace ta
rufe qafarta in tana sallah ko kuma in zata fita waje, ya qara dacewa idan Mace
tayi sallah qafarta a waje Allah bazai amshi sallarta ba ya ce ko ta sanya safa
ta rufe qafarta. Haka hadisi ya nuna ruwayar Abu Daud.[20]Idan
mace tayi sallah qafarta a waje bata da
sallah wannan itace fahintar Nana A’ishatu Allah ya qara mata yarda da Nana Maimunatu da Ummu Sallama dukkan su matayen manzon Allah sallallahu
alaihi wa’alihi wasallam sun ce idan mace ta yi sallah qafarta a waje bata da
sallah sai ta sake sallarta.[21]
Don haka dole ne hijabi ya rufe qafar mace
wannan sharaxi ne. Haka nan hadisi ya zo mai lamba 173 cikin lttafin Tirmidhi da littafin sunan na Imam Nasa’i mai lamba 29
wanda Ibn Umar yaruwaito duk suna nuna mana dole ne mace ta rufe qafarta a waje ko yayin da take sallah.
Amma mata
masu fitar da qafafuwan su a fili ga
mazajen da ba suna aure dasu bane kuma ba muharransu ba lalle sun sava ma Allah
da manzon sa, kuma suna cikin fushin Allah. Haka nan ma yana daga cikin abin
baqin ciki za ka ga mata musulmai suna tuqa mashin qafafuwansu a waje wannan
haramun ne kuma bai dace da su ba a matsayinsu na musulmai masu mutunci, sannan wata babban musiba da ke
damun duniyar musulman Arewacin Nijeriya itace yadda mata suke hawan ‘’yan
acava wanda yake haramun ne namiji ya
goya matar da ba tashi ba a kan mashin wannan babu savani a tsakanin
malamai cewa haramun ne mace ta hau (Expresss) acava ; shi ma haramun ne
ya xauke ta ya goya ta a mashin. Ya
kamata masu yin acava da su ji tsoron Allah, su sani fa da su haxa jikinsu da
jikin matar da ba tasu ba ; yafi masu sauqi su sa jikinsu a garwashin wuta kamar yadda hadisi ya zo a kan hanin na miji yahaxa jikin
sa da matar da batashi ba. Wani hadisin ma cewa ya yi gara ya sami qarfe mai
tsini ya sossoke idonsa ya fi mashi da
ya haxa jikinsa da mace wadda
batasa ba[22], wani hadisin manzon Allah cewa ya yi da mutum ya haxa jikinsa da matar da
bat asa ba ya fi mashi sauki ya je ya rungumi aladen da ya cakuxu da tavo qazanta (kwata) da ya haxa
jikinsa da wata mace.[23] Allah ya kare mu. Balle masu fita, fita ta
fitsara gashin kansu a waje. Masu tafiya ko hijabi babu sai gyale, wanda ko
munsani cewa sa gyale haramun ne ”ya mace tasa gyale ta fito waje. Lalle mata
masu sa gyale su ji tsoron Allah su
sani fa cewa
addinin Allah bawasa ba ne kuma
su tuna mutuncin da qima da martaba da
Allah ya yi ma su, su kiyaye dokokinsa.[24]
2. SHARAXI NA BIYU KADA YA
KASANCE MAI KWALLIYA
Yana daga cikin sharaxin hijabi ya zama ba mai
kwalliya ba, (wanda babu ado a jikin sa) babu cin baki, mai daukar hankali ko
wani ado a jikin shi, domin faxan manzon Allah (sallallahu alaihi wa,alihi
wasallam). Mutane uku kada kayi tambaya
a game da su, domin halakakku ne : mutumin da ya rabu da jama’a ya saba ma shugabansa, ya
mutu mai sabon Allah. Da kuma bawa ko baiwa da ya guje ma uban gidansa sai ya
mutu. Da matar da mijinta ya yi tafiya ya bar mata abin da zai wadace ta na
buqata, amma sai ta yi tabarraji ta fitar da kwalliyarta a bayan shi, to manzon
Allah sallahu alaihi wa,alihi wasallam
ya ce, ‘’kar ka yi tambaya a kansu domin suna wuta.[25]’’
Bai halasta ba a yi ma hijabi ado ba. Duk wani
nau’i na kwalliya bai dace mace ta yi ma hijabinta ba. Allah ya kawo mu wani lokaci da mata ke sa wani irin gajeren hijabi
mai santsi bai da kauri wai sunansa sorry
ustaz, Alhamdu lilLahi shi dama Ustazu baya
sha’awar fasikai balle a ce masa sorry,
الخبيثات للخبيثين والخبيثون للخبيثات
والطيبات للطيبين والطيبون للطيبات
Ko a tsokani shari’a, ko kuma suna kiran sa Rubber hijab ko Jahannama ga fasinja ko please call me. Da kuma wani wai shi made in France, ko Half breast ko Breast line[26]da wani wai
shi show me your breast, ko half sunnah da Baba na balaga da talaka bai da rabo Zura
hannunka masoyi subhanallah لا إلَهَ إلا اللهُ wallahi ‘yar uwa abin kiyi kuka ne
haba ! haba ! haba ! don Allah ki tuna darajar da Allah ya
yi maki, dukkan waxannan hijaban dai ba
su halasta mata su sanya su ba.
Kamar yanzu za ka ga
waxansu mata da hijabi mai
kyalkyali, wannan bai dace ba domin wannan qyallin kwalliya ce.Ko wasu ka ga sun sa ma hijabinsu fulawa, ko kuma ka ga an yi ma shi
aiki kamar irin wanda suke kira da suna Made
in France ko wanda su ke yayi a
yanzu kamar wanda suka yi yayinsa da
wannan Sallar bana a shekara 1429 (2008).kuma kowace shekara su kan fito da wani sabon salon na
savo.
Shi yasa ma wasu malaman suke ganin bakin hijab
yafi dacewa a ko wane zamani da lokaci
koma shi ne mafifici domin bai da ado ko wani kwalliya a jikinsa.[27]
Shi yasa wasu Malaman suke ganin rashin dacewar mata masu aikin Hajji da suke
xinka fararen kaya don ihrami kuma gashi bai cika wannan sharrudxan ba, da mata za su dinka bakin Hijabi wajen aikin hajjinsu
da yafi kamar yadda sauran alhazan duniya suke yi. Ya kamata muma namu matan su
daina xinka fari domin dacewa da
alkhari.
Wani abin ban takaici da baqin ciki da
mamaki shi ne a kwanakin baya mata suna qoqarin
shiga yadda Allah da manzansa
suka yi umurni. Idan kai tafiya cikin garuruwanmu zaka ga
‘’yan kaxan ne daga cikin mata ba sa sanya
hijabi cikakke yalwatacce.
Kuma zaka ga sun zama daban kuma suna jin kunya. Amma wannan sallar abin ya canza inda mata
suka sa qananan hijabai masu kwalliya abin gwanin ban takaici. Allah ya kyauta
kuma muna roqon Allah ya ba ‘’yan uwan mu mata damar gyara shigarsu amin.
Haramun ne uba ya bar yarinyarsa ta sa irin
wannan hijabin da a ka yi yayinshi da wannan sallar(Rubber hijab ko sorry ustaz,
ko please call me ko a tsokani
shara’a ko sai na shiga ko jahannma ga fasinja ko half sunnah) mai qyalli ko xan qarami ko
shara-shara idan uba ya bar ‘’yarsa
tana sa hijabi mai kwalliya ko gajere wanda bai rufe qafa ba yin haka zai haifar masa da shiga
cikin fushin Allah shi da ‘’yartasa. Don haka ya zama dole uba
ya kiyaye kar ya faxa cikin azabar Allah shi da ‘’yartasa.
Manzan Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam
ya ce duk matar da tafitar da kwalliyarta a waje to ita mazinaciyace. Hijabin
da su ke kira da suna please call me kamar tana cewa ita mazinaciya ce a
kirata, Allah ya tsare mu.
3.
SHARAXI NA UKU YA ZAMA
MAI KAURI BA SHARA-SHARA BA
Dole ne hijabi
ya zama mai kauri ba mai
shara-shara ba. Manzon
Allah sallahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce, ’Da sannu a qarshen al’ummata, wasu
mata zasu saka tufafi amma tsirara suke, wato a
tsiraice su ke,kawunansu kamar tozan
rakumi, manzon Allah ya ce’’ Ku la’anance su, domin la’anannune.’’ A wata
ruwaya manzon Allah ya ce, Ba za su shiga al’ jannaba (waxannan matayen masu sa
kaya shara – shara), ba kuma za su ji qamshim al’janna ba.
Qamshinta a na samu na tsawon shekara kaza da kaza[28]
Dole ne
hijabi ya kasance mai kauri wanda bazai
nuna jikinta ba. Wannan hadisin yana nuna mana cewa mata masu karin gashi ko
masu sa gwaggwaro ko masu sa matsatsun kaya duk sun shiga cikin wannan siffar
da Annabi sallahu alaihi wa, a lihi
wasallam ya ce a tsine masu a cikin hadisinsa.[29]
4. SHARAXI NA HUDU YA ZAMA YALWATACCE.
Ya zama
yalwatacce mai faxi sosai
banga-banga, ba mai
qunciba, saboda kada ya nuna wani
abu na jikinta kamar ; Ya
siffantar da wani abu daga jikinta kamar ya nuna alamar
tudun nonanta ko tudun duburarta. Ko cinyarta ,ko dai wani wuri da zai
iya jawo fitina ga maza ,Usama bn zaid
ya ce,’’ manzon Allah (sallalahu alaihi wa,alihi wasallam) ya tufatar da
ni wata riga mai kauri daga abin da
Dhiyatul kalbiy ya ba shi kyauta, ni kuma sai na tufatar da mata
ta ita sai manzon Allah Sallalahu alaihi
wa, alihi wasallam ya ce me ya sa baka
sa ba ?, sai nace na tufatar da
matata ita. Sai manzon Allah sallahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce.’’To ka umurce ta da ta sanya wata a
qarqashin ta domin ina tsoron kada
ya siffanta nauyin gavuvuwanta.[30]
Wanan yafito da maganar a fili ta
buqatar hijabi ya kasance yalwatacce mai fadi so sai.
Hafsatu yar AbdirRahan tashigo wajen Nana Aisha
Allah ya kara mata yarda da wani dan qaramin mayafi mara kauri kuma gajere.
Nana Aisha ta kwace shi ta yayyaga shi, sannan ta sa mata mai kauri babba[31]
Don haka sharaxi ne hijabi yazama mai faxi sosai
kuma mai kauri ba fake-fake ba.
5. SHARAXI NA BIYAR
KADA A SA MA SHI TURARE
Ka da a sa ma hijabi turare, turaren nan na ruwa ne ko turaren
wuta ne da sauransu hadisai masu yawa sun zo suna haramta ma
mata su sanya
turare in za su fita daga gidajensu.
Ga wasu hadisan
kamar haka: Abu Huraira ya ce manzon Allah sallahu alaihi wa,a lihi wasalam ya ce “Duk matan da ta
sa turare kada ta je sallar
Isha’i tare da mu.’’’[32]
Abu Musa al’
ash,ariy ya ce manzon Allahsallahu alaihi wa,alihi wasallam
ya ce, Duk matar da ta shafa turare ta wuce wajen wasu mutane domin
su ji qamshinta, to ita
mazinaciya ce.’’’ [33]
Manzon Allah sallalahu alaihi wa,a lihi wasallam ya ce, idan xayarku zata
masallaci kada ta kusanci turare[34]
… Don haramun ne mace ta shafa ma hijabinta turare ta fita waje, ko ta shafa man shafawa mai
qamshi ta fita waje, kuma mun fahimci
abin da hadisin ya ce idan mace
tasa turare to ta zama tamkar mazinaciya
ce in dai da ta sa ta fito waje. Allah ya kyauta. Don haka mata ya
kamata ku ji tsoron Allah,ku san ce wa Allah yana ganinmu,ku bar shafa turare a
tufafinku in za ku bar gidajenku, domin
sa turare in za ku fita bai halasta
ba a gare ku(mata), saboda hanin
da Manzan Allah sallalahu alaihi
wa,alihi wasallam ya yi.
Wani hadisin
ma manzon Allah sallallahu alaihi wa’alihi wasallam cewa ya yi “Duk matar da ta
sanya turare ta fito waje ta wuce ta wajen wasu mutane don suji qamshin
turarenta to ita mazinaciyace[35]
Amma kuma
akwai hadisin da Annabi sallallahu alaihi wa`alihi wasallam yace turaren mata
wanda launasa ya bayyana amma qamshinsa ya voye (wato turaren mata su kaxai
suke jin qamshin abinsu in sun sa wani ba zai ji ba sai dai su kaxai kawai za su ji qanshin).
Waxanan
hadisan ba suna hani ba ne a Kan mace tasa turare baki xaya ba. A’ a zata Sa
abinta a cikin gidan ta don mijinta yaji qamshin turaren nata don ta burge mai
gidanta, bai dace ga matar aure da ta zauna a cikin gidanta tana wari ko
biji-biji ba kyan gani.[36]
6. SHARAXI NA SHIDA KADA YAYI KAMA DA TUFAFIN ARNA.
Kada ya yi
kama da tufafin Arna [kafirai] An samo hadisi daga Abdullahi bn Ummar Allah ya
qara masa yarda, ya ce, ‘’Manzan Allah
sallahu alaihi wa,alihi wasallam yaga
tufafi masu ruwan zinariya [gold]
a jiki na sai ya ce “Haqika wannan yana daga cikin tufafin kafirai, don haka
kar ka sanya su.[37]
Wannan
hadisin ya haxa har da maza, su ma haramun ne su sanya kayan arna.
Sannan wani
hadisi daga Ali Allah ya qaramasa yarda ya ce ‘’Manzan Allah sallahu alaihi
wa,alihi wasallam ya ce”Na hane ku daga sa tufafin fastoci ,fada-fada, domin
duk wanda ya yi shigar ta su ko ya yi kama da su to shi yana tare da su[38]
kamar Academic gown da ake sawa a makarantu ranar bukin rantsar da su (Matriculation)
wannan rigar asalinta daga Coci take, yakamata
“yanuwa su guji sa wannan rigar.
Wannan hadisin shi ma ya
game gaba dayan musulmai da su
daina shiga ta Arna Kayan da a ka san Arna da su haramun
ne shi musulmi ya sa. Kamar wanda a kan sanya yayin yayen dalibai a makarantun
gaba da sakandere da kuma Lauyoyi a kotuna. (Sai ai hattara)
Wani hadisin cewa ya yi wanda yayi kama da wasu
jama’a yana tare da su.
Ibn
Taimiyya ya yi bayani sosai kuma mai gamsarwa kan haramci sa kayan Arna da koyi
da su[39]
7-SHARAXI NA BAKWAI KADA YA YI KAMA DA TUFAFIN MAZA.
Kada ya yi
kama da tufafin maza, Manzon sallahu alaihi wa,alihi wasallam yace ‘’Bashi
tare da ni namijin da ke kamantuwa da mata wajen sa tufafi. Da mace da ke sa tufafin maza’[40].
Hadisai ingantattu sun zo suna tsine ma matar
da ke sanya kayan maza.’’’
Abu Dauda ya ruwaito hadisin da manzan Allah
sallallahu alaihi wa’alih wasallam, ya
ke tsine ma namijin da ke sa tufafin mata,da matar da ke sa kayan maza[41].
Allah yakare mu.
Yanzu zaka ga mata na sa kaya matsattsu da wanduna su fita waje ba sa
jin kunyar Allah da Manzansa. ko kuma su xinka yadi da yake maza kawai a ka san
su da shi balle uwa uba Xan daudu wanda
mazon Allah sallahu alaihi wa, alalihi wasallam ya tsine ma shi, Allah ya shirye smu baki xaya.
Manzon
Allah sallallahu alaihi wa`aihi wasallam ya ce a wani hadisin ‘’ Allah ya tsine
ma matar da ta kamanta kanta da maza da
namijin da ya siffanta kansa da mata’’[42]
Sabo da haka yana da ga cikin
sharaxin hijabi ka da
ya yi kama da kayan maza.
8-SHARAXI NA TAKWAS KADA
YAZAMA TUFAFIN ALFAHARI.
Kada ya zama
tufafi na alfahari wato mace ta sanya kalan hijabin da
yake yadin na kece
raini ne ko na alfahari ko
na nuna isa da ji-ji da kai Manzon Allah
ya ce ‘’wanda ya sanya tufafin
alfahari a duniya, Allah zai sanya masa tufafin qasqanci a ranar
alqiyanah, kuma sannan a hura wuta a cikin ta"[43]
Kuma dama musulunci ya
hana girman kai wani hadisin yana gaya
mana bazai shiga Aljannah ba wanda yake a cikin zuciyarsa akwai
qwayar zarra na girman kai[44]
.
An samo hadisi daga Abi Huraira Allah ya qara mashi yarda ya ce ‘’’Mazan Allah sallalahu alaihi
wa’alihi wasallam ya ce ‘’wata rana wani mutumi yana tafiya rigarsa (ta
alfahari) ta burge shi nan take Allah ya girgiza qasa da shi yayi qasa manzon Allah ya ce, Har yanzu yana cigaba da
tafiya cikin qasa har ya zuwa tashin qiyama.[45]
9-SHARAXI NA TARA KADA YAKASANCE YANA DA KUROS.
Yana
daga cikin sharaxin hijabi kar ya
kasance yana da Kuros gecciye (cross)
a jikinsa. Ba ya halasta a sa tufafin da
ya ke akwai kuros a jikinsa, hijabi ne
ko riga ce, domin kuros alama ce ta
Nasara kiristoci ,kuma suna raya cewa
Annabi Isah ne suka gicciye wanda ko
karya ce suke yi, Allah ya qaryata su a cikin suratu Nisa kuma Annabi Isah
bai mutu ba zai dawo a karshen duniya haka Annabi ya yi
bayani kuma kur’ani ma bai ce Annabi Isah ya mutu ba yana a raye a sama manzan Allah ya ganshi lokacin daren Isra’i
وقولهم
إنا قتلنا المسيح عيسى ابن مريم رسول الله وما قتلوه وما صلبوه ولكن شبه لهم وإن
الذين اختلفوا فيه لفي شك منه ما لهم به من علم إلا اتباع الظن وما قتلوه
يقينا بل رفعه الله إليه وكان الله عزيزا
حكيما
Ka nemi Tafsirun
Imamun Nasa’i zakaga bayani gamsasshe
kan cewa Annabi Isah bai mutu ba kuma
zai dawo.[46] .
Abin da ke qara nuna mana
haramcin sa tufa da ke da Janjami (cross) korus a jikin sa shi ne hadisin da Iman bn Haddan
ya ruwaito Nana Aisha Allah ya kara ma ta yarda ta gaya ma shi cewa haqiqa
manzon Allah sallallahu alaihi wa, alihi
wasallam ya kasance ba ya barin wani gida da yake da kurus face ya kawar da shi[47]
Yana da kyau musulmi in zai sayi kaya ya tabbatar babu Janjami kuros (cross) ko alamarsa ajikin kayan
kafin ya saya akwai wata akwatin kamo qasashen waje (Receiver) mai xauke da
Kurus sunanta PAUXIS, duk wani abu daya ke da kuros haramun ne musulmi ya kawo shi gidan sa. Anan
zamu fahinci ‘’yan uwan mu da ke sa rigar qwallon (Jesi) na BERCELONA da
na REALMADRID da ke xauke da kuros da su ji tsoron Allah su daina sanyawa tun
da bayani yagabata da ke nuna mana
haramcin sa kaya mai Janjami (cross).[48]
Abin da ke qara nuna mana haramcin
sa tufa da ke da janjami (cross) korus
a jikin sa shi ne hadisin da
Iman bn Haddan ya ruwaito Nana Aisha Allah ya qara ma ta yarda ta gaya ma shi
cewa haqiqa manzon Allah sallallahu
alaihi wa, alihi wasallam ya kasance ba ya barin wani gida da yake da kurus
face ya kawar da shi[49]
Shi yasa Ibn hajr a cikin ‘’Fathul
Bari’’ ya ce wanna hadisin yana bayani ne har da kayan sawa haramun ne musulmi
ya sa kaya mai janjami (cross) kuros.
Shi kuma bn Malhi almaqdis ya
ce abin qyama ne ga musulmi ya sa tufan
da ke da kuros. Shi kuma bn Hamdan ya ce haramun ne. [50]
Imamu
Safaarani ya ce haramun ne sa tufa mai kuros a jikinsa. Ya yi bayani mai tsawo. Ya kuma kawo maganganun
magabata da ke nuna haramcin sa kaya
masu kuros.
Akwai makarantar da yake janjami
(cross)ne bajen su bai halasta musulmi
ya kai xansa wannan makarantar ba.
10- SHARAXI NA GOMA KADA YA KASANCE YANA DA HOTO.
Sharadi na goma kada hijabi
ya kasance yana da hoto a jikinsa,
gabadayan junhurun malamai sun tafi kan haramcin rike wani abu da yake xauke da
hoton abin da ke da rai wannan hoto na Xan Adam ne ko Dabba ce
wannan hoto a bango akasa shi ko
a jikin tufafi ne. Ko a labule akasa shi
kai ko mene haramun ne a sa hoton abin da ke da rai.[51]
An
samo hadisi da ga Xalhatu Allah ya qara
masa yarda ya ce manzan Allah sallallahu
alaihi wa, alihi wasallam ya ce, ‘’Malaikun rahma ba sa shiga gidan da ya ke akwai hoto
ko kare[52]
Hadisi
ya zo daga Nana Aisha Allah ya qara mata
yarda ta ce, ‘’ manzan Allah sallalahu alaihi wa, alihi wasallam ya shigo xaki
na na sa
labule mai xauke da hoto da ya
gani idon sa ya canza fuskarsa ta canza yasa hannu ya yayyaga
shi san nan yace ‘’haqiqa waxanda
suke shiga azaba mai tsananin ranar kiyama sune
ma su yin kwaikwayon halittan
Allah.[53]
Bai
halasta a sa ma hijabi hoton wani Shehi ba, ko wani malami ba ko wani irin hoto
ne dai haramun ne, in dai hoton halittar
tana da rai ko da wannan hoton ba na
abin da ke da rai ba ne, ba
a yarda a sa shi a jikin hijabi
ba. Shi ya sa wasu malaman suke cewa baje (na alamar
makaranta) shi ma ya shiga domin zai
kasance ya bada kwalliya a jikin
hijabin.[54]
Yazama dole Alhazan
su gyra su daina xika kayan aikin hajji da hoton Gwabnonin su wannan kuskure ne kuma bayyanar da jahilci ne
a gaban musulman duniya ga kuma sava wa Allah da Annabinsa.
11. SHARAXI NA GOMA SHAXAYA KADA YAYI KAMA
DA TUFAFIN ‘’YAN BIDI’A.
Ya na daga cikn sharadin hijabi kada
yayi kama da hijabin ‘‘yan Bidi’a kamar
masu bin addinin Shi’a dake sa
hijabinsu, su tsaga qasansa su matse fuska bai kaiwa
qasa. Fuskarsu a matse, ba ya kaiwa kasa.
Kamar ranar Ashura 10 ga
watan Muhararram[55]
suna da hijabin da suke sanyawa na
masammam domin wannan ranar baqaqe suke
sawa domin baqin cikin wannan ranan, Sheikh Usaimin ya ce yin haka Bidia ce[56]
Wadannan su ne sharuddan hijabi
wanda ya ke dole ne ko wane hijabi sai ya cika su sannan
ya zama hijabi wandaAllah ya ce a sanya, dama mun san cewa sa gyale haramun ne,
Nana A’ishatu taga wata mata da gyale ta ce mata Allah wadanki’’[57]
kuma lalle mata su ji tsoron Allah, su sani fa
manzon Allah sallalahu alaihi
wa,alihi wasallam ya ce mata, su ne suka fi yawa a gidan wuta, don haka su rinqa shiga wanda Allah
Ya yi umurni da shi. Kuma su guji yawon
banza - da kallon fitsararru 'yan firm xin Hausa masu yada varna a bayan kasa masu
lalata tarbiyan yara marasa kunya masu
koyar da zina da yaxa ta.
إن الذين
يحبون أن تشيع الفاحشة في الذين آمنوا لهم عذاب أليم في الدنيا والآخرة والله يعلم وأنتم لا
تعلمون
Kuma iyaye su sani fa Allah ya ba su amana ne kuma zai tambaye su, sannan
su tuna da cewa Allah yace ku kare kanku da iyalanku daga wuta wadda
makamashinta duwatsu ne da
mutane[58].Yana
da kyau uba ya tabbatar yaransa nashiga
wadda Allah ya yi
umurmi da ita, domin kokarin sauke
nauyin da Allah ya xaura masa na kula da tarbiryar yara.[59]
Kuma hatta ranan sallah a tabbatar sun sa hijabi kar a barsu da hijabin da su ke ce ma shi sai na shiga ko sorry ustaz ko robber hijab ko please call me’ ko half sunnah ko Jahannama ga fasinja, ko
half lenght ko have
breast ko baba na balaga ko saka hannunka masoyi ko Alhaji kar ka bar banza ko talaka bai da rabo ko karuwa a Masar ko tayani gantali ko maraba da
Aljanu waxannan hijaban haramun ne Mace musulma ta sa su, haba ‘’yar’uwa ke da
ga jin sunan kinsan akwai izgili da tozaci da wulaqanci ga addini Allah, bayan ko Allah yana cewa :
أبالله
وآياته ورسوله كنتم تستهزؤون
“shin Allah da ayoyin Sa da
manzon Sa ne ku ke ma isgili”
Tarbiya dole ne iyaye su kula da ita
kula ta masammam kuma Annabi ya ce wanda bai da kishi bazai shiga Aljanna ba yana daga
rashin kishi kabar matarka ko ‘’yarka tana fita ba hijabi cikakke wanda Annabi
yayi umurni da a sa. [60]
Kuma yanzu bincike ya tabbatar da cewa mata masu sanya hijabi sun fi saurin samun mazajen Aure kuma anfi
son su.
NIQABI
Niqabi wani kyalle ne da mata ke
amfani da shi wajen rufe fuskarsu daga maza. Baki ne ko fari ne ko wane irin qyallene. Nikabi da safar
hannu sanannu ne ga mata tun zamanin Annabi sallalahu alaihi wa, alihi wasalam, Ana sa Niqabi da safan
hannu kamar yadda yazo a cikin Bukhari,
manzon (Sallallahu alaihi wa,a lihi wasallam) ‘'ya ce ‘’Masu
aikin Hajji mata kada su sa Niqabi da
safar hunnu. Wannan yana nuna mana cewa akwai
Niqabi da safan hunnu ga mata tun zamanin manzo
Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi. Kuma wannan niqabin
ba ace sai kyakkyawa ba. Domin kai ne a wajen ka mummuna amma wajen wani ita
kyakkyawa ce. Akwai karin maganar Larabawa
da suke cewa kowace tsintuwa akwai mai xaukarta.
Kuma yadda aka umurci maza su cire hula ko rawani a lokcin aikin hajji.
Kenan idan ba aikin hajji sananen
al’amari ne namiji zai sa hularsa a koina. To haka itama mace game da sha’anin
Niqabi.[61]
matayen manzon Allan sun sanya Niqabi, matayen sahabai suma sun sanya niqabi matayan Tabi,ai, suma sun
sa Nikabi sunna ce a wajen wasu malaman,
wasu kuma suka ce sunnace mustahabbiya, wasu malaman su kace suna ganin wajibi ne sa Niqabi, muna
iya cewa Malaman Musulunci sun kasu kan
NIQABI kamar haka.
1-
SUNNA CE
2-
SUNNACE MUSTAHABBIYA
3-
WAJIBI NE (Dole ne mace ta rufe fuskanta).
NIQABI YANA DA ASALI
Da farko dai ga hadisai dake
nuna mana kasancewar Nikabi yana da
asali tun zamanin Manzan Allah sallahu alaihi wa, alihi wasallam.[62]
1. An samo daga Nana Aisha
Allah yaqara mata yarda ta ce
"Mun kasance a wajen aikin Hajji tare da manzon Allah sallallahu alaihi
wa’alaihi wasallam idan mahaya suka zo wucewa ta wajen mu sai mu saki Niqabin mu, mu rufe fuskarmu,
idan sun wuce sai mu bude fuskarmu"[63].
2. Haka ma
hadisi yazo a cikin Bukhari yayin da
aka tafi aka bar Nana Aisha Allah ya qarama ta
yarda a kan ba a sani ba, domin ta tafi neman abin wuyanta,da ta dawo ta taras sun tafi sai ta zauna a wurin da take,sai barci
ya xauke ta. A kwai wani sahabi mai suna Safuwan
bin Mu'adilassalami yakan biyo baya ko wani ya bar kayansa sai ya xauko ya taho da shi.
A ne mi mai shi a ba shi. Daya zo sai ya ganni dama ya san ni
kafin a saukar da ayar Hijabi sai ya ce subhanallahi sai nafarka da istirja'insa sai na rufe fuskata da
hijabi na.[64]Wannan hadisi ne shahararre Wanda a ka
fi sani da Hadisatul ifki.
3. Nana
Asma'u 'yar Abubakar Saddiq ta ce,’’ Mun kasance muna rufe fuskarmu daga
maza kafin haka a
wajen aikin hajji ba ma rufewa.’’[65]
4. Haka nan da matar Ikirama ta musulunta, ita ma ta sa Niqabi ta
rufe fuskarta domin ta musulunta a wannan lokaci ta je
wajen manzon Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam’ [66]
5. Hadisi ya zo daga Anas a cikin qissar Nana Safiya a lokacin
yakin khaibar, manzon Allah ya zavi Nana Safiya ma kansa [a matsayin
matarsa sai Annabi ya fito bayan ya
sadu da ita sai ya sa ta a kan rakumi, kuma yasa bargonsa ya rufe mata bayanta da fuskanta.[67]
6. An samo daga Nana Safiya ta ce "Na ga Nana Aisha tana
dawafi a wajen aikin hajji tana sanye da Niqabinta.’’[68]
7. An samo da ga Fadhimatu bin munzir ta ce,’’ Mun kasance muna
rufe fuskarmu kuma mun kasance wajen aikin hajji muna tare da Asma'u yar Abubakar Siddiq [da
niqabi ba wanda ya yi mana inkari.’’[69]
Imam Baydawi ya faxi qarqashin ayar da Allah ya ce "Ku yi qasa da jilbab" ya ce su rufe fuskansu da dukkan jikinsu[70].
A Mazhabar Shafi`iyya da Malikiyya, da Hanabila sun tafi kan cewa fuskar
mace al'aura ce kuma dole ne ta rufe fuskarta wajibi ne, bude fuska haramun ne Albany ma ya kawo wannan maganar a
littafinsa Jilbab shima mai Tarbiyatul
Aulad Nasihil Ulwan yakawo wannan maganar.
Mazhabar Hanafiyya sun ce fuskar mace ba dole ba ne ta rufe fuskarta ya halasta ta buxe fuskarta In dai ba'a tunanin faxawa cikin fitina. In an
tabbatar ana lokacin aminci to ba komai tana iya buxe fuskar ta. Tambaya anan
shin yanzu muna lokacin aminci ?
8. Abdullahi
bin Umar " ya ce, Nana Safiya ta ga Nana Ai'sha da Niqabi a
tsakiyar mutane kuma ta gane ta[71]
9. Ummu
Salma matan manzon Allah (S.A.W) " ta ce ‘’Mun kasance ba ma rufe fuskanmu idan muna gida, amma idan zamu fita sai
mu rufe fuskarmu [72]
10. Manzon Allah ya ce, ‘’Masu aikin hajji mata ba sa sa Niqabi ko safar hannu.’’[73]
Shaikhul Islam bn Taimiyya ya ce wannan Hadisin yana nuna mana a
fili qarara cewa lalle akwai Niqabi tun zamanin manzon Allah kuma shara'ar
Allah ce mata su rika sa Niqabi. Yace
waxanda basu je aikin hajji ba suna sa Niqabi da safar Hannu.[74]
Kuma matayen Annabi suna sa
Niqabi suna rufe fuskarsu daga maza. Kuma
matayen Annabi suna sa Niqabi
kuma matayen sahabbai suna sa Niqabi, kuma matayen tabi'ai su ma suna sa Niqabi.
11. An samo daga Asim xan
Ahwal ya ce, "Mun kasance muna
shiga wajen Hafsatu 'yar Sirin wadda
ta haddace Qur'ani tana da shekara goma sha-biyu, ta mutu tana da shekara saba'in. I dan muka shiga sai ta ja Jilbab xinta ta rufe
fuskarta da Niqabinta.’’[75]
12. Wata mata tazo wajen manzon Allah sallallahu
alaihi wa,alihi wasallam ana kiran ta da suna UmmuKilad
ta zo tana sanye da Niqabinta, tana tambaya game xanta. Manzon Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce’’ Xanki na da lada ta shahidai biyu. Sai ta ce ‘’Sabo-da mene ? Sai Annabi ya ce saboda Ahlul kitabine suka kashe shi’’.[76]
ta zo tana sanye da Niqabinta, tana tambaya game xanta. Manzon Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam ya ce’’ Xanki na da lada ta shahidai biyu. Sai ta ce ‘’Sabo-da mene ? Sai Annabi ya ce saboda Ahlul kitabine suka kashe shi’’.[76]
Sahabi Abdullah ibn Abbas Allah ya
qara masa yarda ya ce Allah ya umurci matan mumuinai idan za su fita
da ga gidajensu domin wata buqata
su rufe fuskokinsu da jalabib din
su su bar ido daya.[77]
13. An samo hadisi acikin al-Musannaf na Abi Shaybah idan
sahabi Umar yaga baiwa da Niqabi dokanta yakeyi ya ce ta cire shi domin ita
baiwa ce ba ‘ya ba ce. (idan mace ta
fito ba niqabi ana xaukanta baiwa ce ba
‘ya ba shi yasa sahabi Umar ya ke dukan
wadda ta sa niqabi in baiwa ce) wannan ya nuna mana a fili niqabi yana da
asali.[78]
Waxannan hadisai suna nuna mana falalar Niqabi
da kuma nuna mana yana da asali a
addinin musulunci kuma ta’adace [dabiace] ta masu karamci da kunya,[79] kuma manzon Allah
ya tabbatar. Kuma da sanya
Niqabi ba sharia ba ce da manzon Allah yahana da kuma matayan sahabbai basu sa ba
kuma da an samo wani magabaci ya
yi rubutu yana nuna cewa babu
kyau, ko bidiace ko kuma su yi rubutu
suce sai kyak kyawa. Babu masu cewa sa
niqabi ba kyau ko su faxi maganar da ba
tadace ba sai yan bidia "yan Bidi'a ma kiya
sunnar Annabi sallahu alaihi wa’alihi wasallam da kuma Yahudawa makiya addinin
Allah, da Jahilai.
Waxannan su ne Hadisai da suka zo suna mana bayani a kan
sa Niqabi akwai shi (tunzamanin manzon Allah, kuma
matayen masu karamci da mutunci da
daraja sun,sanya(niqabi), masu cewa sa Niqabi Bidi'ace su ji tsoron Allah su sani cewa ilimi yana da faxi, idan baka karanta ba
karkace babu, domin yin haka zai nuna ma duniya cewa kai
jahiline kuma, ka na suka ne kan matayen Annabi sallallahu alaihi waalihi
wasallam da matayan sahabbai da matayan Tabiai Allah ya qara yarda da su
bakixaya,kuma halin da muke ciki bai
dace a hana mata sa Nikabi ba, don Annabi
bai hana su ba, kuma sahabbai ba su hana su ba, kai
ma yanzu baka da ikon hana su
kuma kar ka ce sai kyakkyawa duk
wadda ta sa ta kyauta kuma ta yi koyi ne
da matayen Annabi sallalahu alaihi wa,alihi wasallam da kuma matayen sahabbai
da Tabiai waxanda suke su ne
mafifitan al,uma ta harshen kur’ani da
Annabi sallallahu alaihiwa,alihiwasallam, don haka nasiharmu ga masu zagin masu sa nikabi su daina
su ji tsoron Allah, in ka duba tafsirin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Raddul azhan ila ma’anil Kur’an cikin suratul Ahzab aya ta 59, za ka ga
bayani da ke nuna tabbatar dasa Nikabi.[80]
Malamai na da da na yanzu sun kasu kan matsayin sa niqabi shin wajibine ko kuwa sunnnace ko
kuwa mustahabbi ne.
Waxannan kashi
ukun basu da na hudu a
matsayin niqabi a wajen malaman mu na Musulinci, wasu na da fahinta dole ne mace ta rufe fuskanta
wasu kuma suka ce sunna ce wasu kuma suka ce mustahabbi ne sa Niqabi.
FAHINTOCIN
MALAMAI KAN NIQABI
1. SHEIKH MUHAMMAD NASIRUDDEEN ALBANY.
Babban malamin hadisi ya ce sa
Niqabi ba dole
ba ne wato mace ta rufe fukarta ba
wajibi ba ne amma sunna ce mustahabbiya.
Ya ce halin da muke ciki da mata:za
su sanya Niqabi daya fi domin yin
haka yafi da'cewa kuma ya fi alkairi yaci gaba da cewa da za su rufe fukar su da Niqabi to wannan
abin da muke so ne a gare su kuma muna
kiran su da su sanya (Niqabi) ya ce amma muce wajibine bamu da hujja, fuskar mace ba al'aura bace.amma su rufe
fuskar na su shi yafi, domin yin hakan
alamace ta matan kirki[81]
Albani ya yi bayani a
cikin littafinsa na qarshe akan
hijab mai suna ''RADDUL MUFHIM) ya ce
fuskar mace ba dole ba ne ta rufe ta, sunna ce kuma mustahabbi ne amma
ba dole ba ne, amma da zasu rufe
da Niqabi to da ya fi,[82]
An tambayi
Sheikh Nasiruddeen Albany Allah ya ji kansa
game da hukuncin rufe fuskar mace, sai ya ce, ‘’Ba musan wani daga cikin sahabbai
ba wanda ya ce dole ne mace ta rufe fuskarta? Sai dai abin da yake mafifici shine mata su rufe fuskar su shi yafi da cewa ya
fi mutunci. Amma mu ce wajibi ne bai dace wani
mutun ya ce wajibi ne ba ya ce ya zo daga Ibn Abbas nassi
inganttace da ke nuna cewa fuskar mace da tafin hannunta ba
al'aura ba ne[83].
Masu cewa fuskarta al'aura ce su ne 'yan kaxan daga cikin malamai, amma masu
cewa ba al'aurabane sune suka fi yawa da ga cikin malamai. Ya qara da cewa Hadisin da ke cewa "Mace al'aura ce in ta fito shaixan yana qawata ta
(wato maza su ganta kyakkyawa) " ingantattace ne, amma ba haka ya kamata a fahimce shi
ba.[84]
Sheikh Albany ya ce amma da za su rufe, an fi son haka. Sheikh ba ya kushe sa nikab
ko hanawa shi abin da bai yadda ba a ce wajibi ne amma
sa niqabi shi yafi alkhairi. Ya
yi ma Sheikh Tuwaijari raddi mai tsawo a
cikin littafinsa Raddul mufhim.
الرد
المفحم
على من خالف العلماء وتشدد وتعص
وألزم المرأة أن تستر وجهها وكفيها وأوجبئ ولم
يقنع بقولهم : إنه سنة ومستح
Kai da jin suna
littafin kasan Albany yana da fahintar Niqabi sunna ce kuma yana kira da a
sanya Niqabi ne, Sheikh har yabar duniya bai taba cewa kar a sa niqabi ba.[85]
2. SHEIKH bn BAAZ.
Babban malami shugaban masu ba da fatawa na
qasar Saudiya Allah ya ji qan sa. Shi a wajensa wato
a fahimtarsa
SHEIKH
MUHAMMAD SALIHIL UTHAMIN,
Allah ya ji qansa
ya tafi a kan cewa niqabi wajibi ne, ya ce, Kasani yakai musulmi
mace ta sa hijabi tsakaninta da maza tarufe fuskanta
umurni ne wanda yake wajibi ne wanda Qur'ani da hadisai suka nuna da Qiyasi ya ce manzon Allah yayi umarni da mata
su rufe tafin kafansu kar su buxe qafansu,
kuma duk malamai baki xaya sun yi ittifaki akan qafar mace haramu ne ta buxe ta,
sai yace to ai fuska nan ne wajen fitina, kuma kowa fuska ya ke fara kallo
kafin qafa domin nan ne wajen fitina to ai ya isa hujja mace ta rufe fuskanta
tunda akace ta rufe qafarta, ya qara da cewa
hadisi da yace mace al aurace
gaba xayanta sai dai fuskarta da tafi hannuta yace bai inganta ba, kuma hadisi ya inganta da ya yake cewa
mace al'aura ce don haka, Usaimin yana
da fahimtar dole mace ta
rufe fuskarta ko don (saddu zari,a) wato toshe kafar varna.[86]
A
cikin fatawarsa an tambaye shi hukuncin buxe fuskar mace ya ce bai
halasta ba yace da za a ce ma ga wata
mata mai kyan qafa amma mummunace a
fuskar ta, yace baza ka so ta ba, sai ya
kara da cewa ai Annabi ya ce a rufe qafa to ai fuska ita tafi cancanta da a
rufe.[87]
Usaimin ya ce fuskar mace nan ne matattarar fitina kuma nan ne
wurin farko da mace zata rufe kuma
mutane da dama suna sakaci wajen barin yaran su na fita fuskar su a buxe wanda
bai kamata ba[88]
Shi kuma sheikh Muhammad bn
AbdulMaqsud yana da fahimtar mace ta rufe dukkan jikinta baki daya kar ta bar
komai sai dai idonta da za ta ga hanya, hujar sa hadisin bn Mas`ud
wanda Imamu Tirmidhi yaruwaito da
isnadi igantacce ‘’’ Mace al`aurace mu kuma an umurce mu da mu rufe al`aura ’’’[89]
SHEIKH
MUSTAFAL ADAWI
Ya faxa a cikin
littafinsa Jami’u ahkamul Nisa ya kawo wannan ayar
{وإذا سألتموهن متاعًا فسألوهن من وراء حجاب ذلكم أطهر لقلوبكم
وقلوبهن
Sai ya kawo hadisin da imamul Bukhari ya kawo da wasu
hadisan a qarshe dai bai wajabta ba amma yana ganin waxanda suka ce wajibi ne
suna da hujjojinsu kuma masu qarfi.Sai ya rufe maganar sa da cewa ko da mutum
bai yarda niqabi dole ba ne, to amma sa
shi shi ya fi dacewa, kuma mafi kusanci ga tsoron Allah.
أن
الأفضل
والأقرب
للتقوى ومرضاة الله ورسوله: هو ستر كل البدن بما في ذلك الوجه والكفين.
‘’Mafifici kuma mafi kusanci ga tsoron Allah da neman yardansa dana Manzonsa :
shine mace ta rufe dukkanin jikinta da
abin da ya haxa da abin da ke tare da shi na fuska da tafukan hannu !!
Ya dai fi
karkata wajen waxanda suke ganin wajabcin rufe fuska[90]
Haka Immul
Qurdubi shima yaxan karkata wajen rufe fuskar mace a cikin tafsirinsa cikins
suratul Ahzab aya ta 59.
SHEIKH
BAKR bn ABDILLAHI ABU ZAID
Ya ce a cikin Littafinsa
Hirsatil Fadhilah[91]
shi ma yana da fahimtar Niqabi, wajibi ne domin kamar yadda ya ce ayoyi da hadisai suka wajabta sa Hijabi ga mata Muminai, to gaba
daya tana nufin har da fuskarta da
tafukan hannuta za'ta rufe.
Bai halasta ba ta buxe fuskarta a gaban maza. Ya qara da cewa Allah da ya ambaci .Jilbab
ma'anar Jilbab a Larabci tufa yalwatattace
wadda zai rufe gabaxayan jiki tun daga sama har qasa. Shi ma Bakar yana da
fahimtar Niqabi wato mace ta rufe fuskarta wajibi
ne. Bayan haka ya ce ba'a samo daga wani ba a cikin musulunci da ya halasta ma mace
ta buxe fuskanta ba a zamanin da
musulunci ya ke da rauni da lalacewa. Ya ce yadda mutane suka lalace a yanzu to ya zama dole mata su
rufe fuskansu ga maza, kuma rufe wan ita
ce za ta toshe kafar varna balle ma a
halin da muke ciki.[92]
Ku san gaba xaya malaman Saudiyya suna ganin wajibi ne mata su rufe fuskansu.
5.
ALIYU SABUNI
Ya faxi a cikin "Rawa'i ul Bayan, ba wai an
wajab ta ma mace ta rufe fuskarta
ba ne don a quntata mata ba,
sai dai don kariya da kunya.Imamul Bagawi yana da fahintar mata su rufe fuskansu
domin su bambanta kan su da bayi mata ya ambaci haka ne a cikin Tafsirinsa har
ya kawo maganan Ibn Abbas Allah ya yarda da shi
in da yake cewa :
·
ثم نهى الحرائر أن يتشبهن بالإماء فقال جل ذكره عليهن من جلابيبهن} جمع
الجلباب وهو الملاءة التي تشتمل بها المرأة فوق الدرع والخماروقال ابن عباس وأبو عبيدة:
أمر نساء المؤمنين أن يغطين رؤوسهن ووجوههن بالجلابيب إلا عينا واحدة ليعلم أنهن
حرائر
An
hana mata ‘’yaya su kamanta Kansu da mata bayi wajen sa hijabi Allah yafadi haka ne qarqashin fadansa “ su saukar da jilbab xinsu”
yace Jalabib shine tufar da mace zatayi amfani da shi a saman mayafin ta ya qara da cewa ibn Abbas da Abu Ubaydata sun ce “An umurci mata Mumine su rufe kawunansu da fuskokinsu da jilbab
xisu sai dai ido daya da za su bari domin
ganin hanya kuma ta hakane za`a gane su “yaya ne ba bayiba.
Shi
ma dai Imamul Bagawi yana da fahintar sa Niqabi shine umurnin Allah.
6. SHEIKH
NASIRUS SA’ADIY
Ya
ce a cikin, tafsirinsa. Tafsiru KarimurRahaman
mannan ya
ce mace ta rufe Jikinta baki xaya kar ta bar komai sai idonta guda xaydon ganin hanya..
7 SHI MA ABUBAKAR JABIR AL JAZAIRI
Mawallafin littafin Minhajul muslim ya ce
mace kar ta buxe fuskarta, ba a so ta bayyanar da fuskarta, sai dai wajen lalura, kamar karvar wani abu da hannu ko ido xaya ko biyu domin ganin hanya. Hadisi yazo mace gaba xayan ta alaurace sai dai fuskanta da tafukan hannunta ama a wajen Sallah.[93]
mace kar ta buxe fuskarta, ba a so ta bayyanar da fuskarta, sai dai wajen lalura, kamar karvar wani abu da hannu ko ido xaya ko biyu domin ganin hanya. Hadisi yazo mace gaba xayan ta alaurace sai dai fuskanta da tafukan hannunta ama a wajen Sallah.[93]
8. SHEIKH
TUWAI JIRI
Ya yi magana gamsasshiya bisa muhinmancin sa Nikabi da kuma raddi ga
masu cewa ya halasta mace ta buxe fuskarta, domin shi a wajensa sa Niqabi wajibi ne,
sannan kuma ya yi ma Albany raddi da ya ce mace ba dole ba ne. ta rufe fuskarta ya ce dole ne ta
rufe fuskarta a cikin littafinsa (Assarimul
mas shur alat tabaruj wassufur wa fi
Raddu al kitabul Albany). Duk da cewa Albany bai yarda da cewa wajibi ne rufe
fuska ba amma kuma matansa da 'ya'yansa suna sawa. Ya ce
kuma'sawan shi ne mafi alkairi.Tuwaijari yafi kowa tsanantawa wajen fahintar
mata sai sun rufe fuskar su kuma
sai sun
sa safar hannu kuma shi ne ya fi yin ma Albany raddi kan nikabi[94].
SHEIKH FAUZANIL FAUZAN
Sheikh yana da fahintar rufe fuskar
mace dole ne yafaxi haka a littattafansa da dama ya fasassara Hijabi da cewa:
الحجاب الشرعي هو أن تستر المرأة ما يجب
عليها ستره من الوجه والكفين، ومواضع الزينة من بدنها، كموضع الكحل والخضاب
والسوار والقلادة وغير ذلك مما يستلزم النظر إليه رؤية موضعه من بدن المرأة. فستر
هذا كله وإخفاؤه داخل في مفهوم الحجاب الشرعي،
Sheikh
Abdullahi Salihil Fauzan ya fasassara Hijab da cewa shine
mace ta rufe abin da yake wajibi
ne rufe shi a gareta wanda ya haxa da fuskarta da tafukan hannunta da qafafuwanta da wurren kwalliyanta na jikinta kamar Tozali qunshi da sarka da sauransu, ga abinda
yake yana jawo kallo ya zuwa gareshi na
daga jikin mace................................[95]
Yana da fahintar dole ne mace tarufe
fuskarta kamar yadda ya yi bayani a wani
littafinsa mai suna Tanbihatun
ala Ahkamin taktassu bil muminat.
Wato shima a wajen sa sanya
niqabi dole ne. Malaman da suke
ganin sa Nikabi ba dole bane amma sun yarda sa nikabi shi ne mafi
alkhari kuma mafi kusance ga tsoron
Allah, kuma sun yarda a sa Niqabi a wannan zamanin shi yafi dacewa ga ko wace ‘’ya mace.
Kuma
har ila yau sun yadda cewa
Nikabi na zama wajibi ga dukkan macen da
tasa Tozali ko hoda ko jan baki ko ja gira
ko dai wani nau’in kwalliya a fuskarta to dukkan macen data yi daya da cikin wadannan abubuwa to niqabi
yazama dole a gareta wato dole ne ta rufe fuskarta.
Haka nan ma duk wadda tayi Dayis
(kwalliyar da mata suke yi da lalle ko taki) a hannu ko tasa jan kunba to itama dole ne tasa safan hannu ta rufe
hannunta. Kuskure ni ki sa niqabi amma qafarki a waje dole ne ki rufe qafarki.
SHEIKHUL ISLAM BN TAYMIYYAH
Yana da fahintar
wajabcin mace ta rufe fuskanta wato sanya Niqabi dole ne ya yi bayani mai tsawo acikin
littafinsa majmu’ul fatawa ya fara da cewa haqiqanin al’amari shine Allah ya
sanya kwalliyar mace (qawa) kashi biyu
akwai kwalliya ta bayyaane, kwalliya ta bayyane ya halasta mace ta buxe
ga wanda ba mijinta ba, ya qara da cewa
mata kafin saukar da ayar Jilbab sun kasance suna fita fuskan su a buxe amma
tun da aka saukar da ayar da ke cikin suratu Ahzab mata in za su fita suna fita
ne fuskansu a rufe, a qarshe ya ce
“hannun mace da fuskanta da qafanta bai halasta ta buxe su ba ga wanda ba
mijinta ba, ba kuma muharraminta ba. Ya ce jilbab shine abin dake rufe jiki baki xaya har da fuska
shine Allah ya ambata acikin suratu Ahzab.[96]
Wannan ne fahintarsa mata su rufe fuskansu, Allah ya jiqansa amin. Shima
xalibinsa ibn Qaym shima fahintarsa kenan, da kuma ibn Rajab al-Hambali shima
yana da fahitar wajabcin mace ta rufe
fuskanta .[97]
Babban malamin malikiya al-Qadhi
Abubakar al-Arabi al-Andalusi ya ce
“mace dole ne ta rufe fuskanta ka da maza su ganta in zata fita waje, awajen aikin hajji ne kawai aka yarda ta buxe
fuskarta.[98]
In ka na son ganin bayani sosai sai
ka duba littafin Imamul Kurdubi ko Tafsirin
Baydawi ko ibn Kasir ko Mahasinu Tanzil ko ka duba
Jilbabul mar atil muslimah na Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albany ko Audatul hijab da Libasul Yaum na Ammru da Sarimul mashur alt
Tabarurj, gaba xayan malaman Tafsiri sun tafi akan cewa rufe fuskan mace wajibi
ne.[99]
Bincike ya tabbatar da cewa sanya
Niqabi yana bada kariya daga kamuwa daga cutar T B (Tarin fuka) cutar da ake kamuwa da ita ta iska, kuma Niqabi yana gyara
ma mata fuskar su da kariya daga cutattukan da ake kamuwa da su ta iska. Bala’i
ne da musiba mai girma mace ta sanya Niqabi sannan kuma ta hau Acava (xan
yasfiris) wannan mata ta shiga uku, ko ba ki sanya Niqabi ba ai haramun ne ki
hau acava balle kin yi shiga ta matan kirki.
NASIHA GA ISAH
HASSAN TIKUMA DA MASU MUMMUNAN RA’AYI IRIN NA SA.
Isah HassanTikumah wani mutum ne mai koyar
da social studies a Jamiar Ahmadu Bello Zaria wanda asalinsa xan Ghana ne zama
ne ya kawo shi Zaria.
Yarubuta littafi da ke cin mutuncin masu sa niqabi da wulaqanta musulmai a fuskar kafiran duniya baki xaya da karya ta
ilimi da qago maganar da take bahaka take ba kan Albany wanda acikin littafin
nasa shi Tikuma yana ganin bai kamata a
rika barin mata suna sa nikabi ba sabo da a yanzu masu sa nikabi suna yin aikin
banza har ya kawo wani misali wanda ya
faru a Jama’a Hospital wanda a qarshe ya nuna shi ma bai da tabbas
akan labarin amma ya kawo shi a littafin
nasa da labarin abin da yafaru a Pakistan a Red mosque da wani labarin qanzan kurege kan masu koyan karatun
Kurani da niqabi wanda a littafin ya
nuna malaman Nigeria basu da amfani
kuma ya qara da cewa bai kamata a bar mata su riqa yin Defence na Masters da niqabi ba, kuma ya
nuna sa niqabi kamar wani imani ne na qarya. Nayi mashi nasiha ni dashi
a ofis xinsa amma ya qi ji na kuma nuna ma sa kurakuren da ke cikin littafinsa
hujja daga Kur’ani da Hadisi amma ya qi yarda a qarshe sai yana ceman wai su
wane ne malamai na girman kai ya kamasa.
Isah Tikumah da farko dai ka ji tsoron
Allah ka tuba kan littafin da ka rubuta kuma ka sani idan wani ya yi
shiga ta mutanen kirki yaje ya yi aikin banza
ka sani baka da daman da za kace
a daina wannan shigar kuma kai a yanzu ba ka isa ka hana sa niqabi ba tunda
Annabi bai hanaba kai yanzu a wane za ka hana , Isah ga wani masali yanzu wanda
suke da gemu suke zuwa suna aikin banza sai muce yanzu a daina barin gemu tun
da a na samon mutanen banza suna
bari gemu, kuma yanzu sai a daina aure
sabo mata na zina, kamanta da cewa manzon
Allah sallalahu alaihi wa alihi wasallam ya ce, “Alumarsa basa haxuwa kan
vata ko da yake ba mamaki tunda kai ba
addini ka karanta ba kuma tunda Allah ya
sa an san cewa kai xan Bidia ne kuma jama’a ma suna tunanin mai yiwa Yahudawa suka saye ka don kai ma su aiki tun da labari ya tabbatar da qasar da
kayi karatunka. Allah ya shiryeka.
Game da magananr da ka kawo kan Albany da
sanadiyar barinsa Madina to ba haka maganan take ba kuma ba Jilbab ba ne yafara rubutawa kan
hijab kaje ka tambeyi malaman da ke kusa da kai don samon bayani, kuma ina so
ka sani shi Sheikh Albany bai da mummunar
fahimtarka ta hana sa niqabi jeka ka duba littafin sa Hijab ko Jilbab ko
Raddul mufhim za kaga yana goyon bayan
sa niqabi shi abin da ya ce ba dole ne ba, kai ko kana so ne a hana sawa
kamar yadda kai mawata yarinya a
ajinka .
Kana ta kawo magananr Sheikh Qardawi to ka
je ka duba littafinsa da ya yi kan hijab za kaga shima yana
goyon bayan sa niqabi shi ma Qardawi
matsayin Albany ya xauka. Ina ma da kai ma ka xauki fahintar waxanda suke
ganin sa niqabi ba dole ba ne amma a sa
shi ne alkhari, amma ina sai ka xauki kanka matsayin Malami,
malamin ma babba, Kai yanzu a fahintarka yanzu har hijabi ma bai
kamata a riqa sawa ba. Kuma kai ka xauki
malaman Najeriya matsayin marasa
amfani sabo da kai malaman
ka basa Najeriya
kuma ka nuna ma duniya kai baka da kunya kuma baka da tarbiya shi yasa
ka ci mutuncin malaman Najeriya
kasani malami duk inda yake ya wuce wulaqanci a wurin
mai mutunci mai tarbiya, muna maka adduar Allah ya shirye ka kai da masu irin wannan mummunan
ra,ayin da bai da
magabaci, abin ban mamaki sai ga shi
ya qara rubuta wani littafin daya ke qoqarin kiran niqabi da cewa
fasiqanci ne ko bidia, Allah ya tsare mu daga shiga cikin wannan ta’addanci ne mi littafina da na rubuta ‘’Guiding
principles of Hijab /Nikab and Nasiha to Isah Hassan Tikuma’’ za kaga nasihar
da nayi ma shi kuma muna roqa mashi Allah ya shirye shi ya tuba daga yin ma
Yahudawa aiki.
Ka duba littafin da na rubuta mai suna
‘’Guiding principle of hijab’’ na yi mashi nasiha da kuma nuna masa kurakuran da yayi a cikin
littafin sa mai suna (The Abuse of Islam and the dormancy of
Islamic scholars Evidence from the misuse of nikab (face veil) in Nigerian
society”.Malamina malam Ahmad Bello Dogarawa yayi masa raddi acikin littafinsa
“Tarbiyyar ‘ya’ya a muslinci”. Abin
vacin rai da baqin ciki sai gashi ya rubuta wani littafin da ya kira
Niqabi da abin qyama mummunar bidia ya
sanya ma littafin suna “NIQAB (FACE-VEIL) AN EXEMPLARY SUNNAH OR A REPUGNAT
INNOVATION” a wannan littafin nasa ya nuna zindiqancinsa a fili Allah ya shirye
shi amin.[100]
MUHIMMANCIN SA HIJABI
1.
Bin umurnin Allah da Annabi
2.
Kariya daga fitina
3.
Alama ce ta tsarkin zuciya
4. Kyakkyawan xabi'a ce
5. Alamar mumina ce
6.
Yankewa daga hanyar Shaixan
7.
Kare kunya
8.
Garkuwa daga faxawa cikin halaka
9. Sutura ce daga al'aura
10. Kariya daga mazaje marasa mutunci
11. Kariya daga Aljanu
12. Kariya daga shiga cikin azabar Allah
13. Bautar Allah ne sanya hijabi
ILLAR RASHIN SA HIJABI.
1 Rashin
sa Hijabi sava ma Allah ne da Annabi
2. Rashin sa Hijabi Zunubi
ne mai halakarwa
3. Rashin sa Hijabi Sifface ta
'yan wuta
4. Rashin sa Hijabi alfasha
ce
5. Rashin sa Hijabi ta,
addanci ne da rashin kunya
6. Rashin sa Hijabi
Koyi ne da Yahudawa
7. Rashin sa Hijabi Koyine da Nasara
(Kiristanci)
8 Rashun sa hijab`shiga
ce ta Jahiliyya
9. Rashin sa Hijabi
Dabbbanci ne
10. Rashin sa Hijabi ci baya
ne
11. Rashin sa Hijabi sharri
ne
12. Rashin sa hijabi rashin
kunya ce
13. Rashin sa Hijabi qauyanci ne.[101]
14. Rashin sa Hijabi alamace ta
munafinci.
YADDA AKE
SO MACE TA YI TAFIYARTA
Lalle ya isa mutumtawa da karramawa da
muslunci ya yi wa mata yadda bai qyale su haka nan ba. Hatta tafiya sai da ya
nuna ma su yadda ake so su yi don dai karrama su da mutuntasu. Hadisi yazo
cikin Bukhari, Manzan Allah sallalahu
alaihi wa,a lihi wasalam yace ‘’ Mata wajen tafiyarsu, su
bi gefen hanya.’[102]’ Mata a zamanin Annabi sallallahu alaihi
wa’alihi wasallam sabo da bin gefen hanya har hijaban su yana yagewa saboda
tava bango[103] Don
haka ana son mata in suna tafiya
subi gefen hanya kuma kansu na kallan
qasa kuma suna tafiyansu cikin sanxo
banda sauri.[104]
Wani lokaci waxan su matan sukan sa
Niqabi amma qafarsu a waje ko hijabin
nasu bai rufe masu qafaba wannan kuskure
ne. Dole ne mace tarufe qafarta indai za ta fita daga gida. Kuma ta
yi tafiyarta yadda Annabi
sallallahu alaihi wa, alihiwassalam.yace.
Waxansu matan zaka ga ba sa
sanya hijabi in kai magana sai suce wai
tsoran Allah a zuciyatake wannan maganar
kuskure ne domin ba matar da ta kai
matayen Annabi sallahu alihi wa, alihiwasallam tsarkin zuciya amma kuma suna sanya niqabi. Ma su yin
wannan magana Allah ya shiryesu wasu kuma suna cewa hijabi a zuciya yake suma masu yin wannan maganan
qarya ce tsantsa sukeyi domin abin dake zuciya shike fitowa gangan jiki,
Bahaushe ma yana cewa labarin zuciya a tambayi fuska. Suma muna masu adduar Allah yashiryesu amin.
HATTARA MATA
Haba ‘’yaruwa musulma ai ya ishe
ki darajar da Allah ya yi maki da ya ce
ki sanya hijabi kuma aka nuna maki yadda akeso kiyi tafiyarki kuma aka hanaki ki nuna kwalliyarki sai ga
wanda shara’a ta yardam mashi da ya gani. To amma duk da wannan mutunci da
Allah ya yi ma ku sai ki ga wasu sunyi
watsi da wannan darajar, sun shigar da kansu cikin fushin Allah da tsinuwarsa
da kuma tsinuwar Annabi sallahu alaihi wa’alihi wasallam suna cire kayansu suna
shiga cikin fitina da abin da zai kai su wuta suna yin qwallo.
إنا لله وإنا إليه راجعون
wai a
ce mace zata yi qwallo, ke da aka hanaki ki cire kayanki a ka hana wani ya ga
jikin ki sabo da qimar da jikinki yake
da shi, sai mijinki kawai, amma kuma sai ki ka qi yarda da abin da Allah ya ce
ki ka shiga cikin waxanda Annabi ya ce
ba za su shiga Aljanna ba manzon Allah sallallahu alaihi wa alih wasallam yana
cewa ‘’Duk ya yin da wata mace ta cire kayanta ba a cikin gidan mijinta ba ta
ruguza suturar da ke tsakanita da
Allah’’[105]
kinji abin da Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce kin ruguza
kariyar da Allah ya yi maki da ga shiga
wuta, kin shiga cikin layin masu shiga wuta don haka qwallon mata shari ne
yahudawa maqiya addinin Allah suka kawo
mana don su ruguzamana tarbiyar mu da addininmu da kuma jefamu cikin
bala’i. Mun sani Annabi ya hana maza su
buxai cinyarsu ya ce cinya al’aurace[106]
maza kenan balle ke mace da aka ce
kirufe gaba xayan jikin ki sabo da qimarki da darajarki da mutuncinki amma
sai ki sanya gajeran wando ki
fito gaban maza ana ganin cinyarki da nonan ki da duburarki haba ‘’yar
uwa ki yi kuka wannan abin kiyi kuka ne domin kin shiga cikin waxan da Annabi
ya ce baza su shiga Aljannaba wani
hadisin Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce, ‘’Siffar mutane biyu
‘’yan wuta ne mata ne sun sanya tufafi
amma tsirara suke (saboda rashin kaurin tufan nata ya nuna wuraren fitina dake
jikinta)…………… a qarshen hadisin Annabi ya ce baza su shiga Aljanna ba[107]
Wani hadisin Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya ce, ‘’ Mata ma
sharranta sune masu nuna tsaraicinsu (masu sanya kaya matsattsu) ma su yin
yanga su ne munafukai baza su shiga Aljanna ba sai dai misalin
hankaka mai jan baki’’[108] idan muka kalli yadda addini ya ce mata su
rufe jikin su kuma su yi tafiya a
hankali a kwai hikima cikin wannan umurni.
Akwai wasu abubuwan da ke cire ma mace budurcinta, idan tayi
aure mijinta yajita tamkar wani namiji
ya tava saninta a ‘’ya mace (wato kamar ta tava saduwa da wani na mijin) sune
mace tariqayin gudu, gudu yana cire ma mace budurcinta gabanta ya lalace, da kuma
yin tsalle yin tsalle-tsalle yana cire ma mace budurcinta da kuma xaukan kaya
mai nauyi shima yana cire ma mace budurcita[109]
da kuma sauri shima yana cire ma mace budurcita da kuma yin magana da qarfi
shima yana cire ma mace budurcinta idan ki ka kalli waxannan za ki gane musibar da ke cikin qwallon mata domin
waxannan abubuwan da ke xauke ma mace budurcita duk sun taru a qwallon mata suna da yawa
kije ki tambayi malaman fiqihu zakiji bayani sosai. To
idan muka kalli waxannan abubuwa za mu qara fahintar sharrin qwallon
mata da kuma muni ta Allah ya kare mu da shiga cikin waxanda Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya tsine
masu, agaskiya duk yarinyar ko mu ce duk matar da tayi qwallo ta
shiga cikin waxanda Annabi ya ce baza su shiga Aljanna ba kuma sun shiga cikin waxanda Annabi ya ce
tsinannu ne kuma ta shiga cikin waxanda Annabi sallallahu alaihi wa’alihi
wasallam ya ce sun ruguza suturar da Allah ya yi masu, haka duk wanda ya
taimaka wajen yin qwallo mata shima ya shiga cikin tsinuwar Ma’aiki sallallahu
alaihi wa’alihi wasallam haka suma masu
kallon qwallon mata suma tsinannu ne kuma yana da cikin abin dake kawo bala’i a bayan qasa da xauke albarkan abinci
shi ne qwallon mata . Duk uban da ya
qyale yarinsa ta yi qwallo ya nuna bai da kishi kuma manzon Allah ya ce wanda
bai da kishi ba zai shiga Ajanna bar ranar tashin qiyanma.[110]An
tambayi babban Malami Sheikh Ibrahim bn
Muhammad game da qwallon mata sai ya ce haramun ne qwallon mata, bai haasta ba kwata kwata
haramun ne bai halasta ba.[111]
A qarshe muna kira ga iyaye da
su ji tsoron Allah su hana yaransu mata
yin qwallo da kuma shuwagabannin makarantun sakandire suma su hana mata yin
qwallo domin kar su faxa cikin bala’i da musiba ya Allah ka shirye mu baki
xaya.
‘YANCIN MATA
Maganganu sun yawaita aduniya musamman a wannan lokacin akan yancin mata
wanda wannan maganar har ta fara tasiri acikin zukatan matan musulmai, duk
yayin da mace tafara tunani akan musulunci ya danne mata haqqinta to lalle ba
bu ko tantama Yahudawa sun yi nasara akanta kuma ta kama hanyar halaka. Idan
muka binciki tarihi za muga cewa addinin musulunci ne yaba mata ‘yanci cikakke
sauran addinai sun tauye ma mata
‘yancinsu ne kuma sun takura su, misali kafin zuwan musulinci mata ba abakin
komai suke ba mata wulaqantattune gadon
su ake yi ana sayar da su yadda ake sayar da dabbobi ana rufe su daransu, idan
uba ya mutu xanta zai gajeta ya ci gaba da saduwa da ita, idan za ai tsafi mata
ake samu a yi tsafi dasu[112]idan
zata yi aure ita take ba da sadaki ba namiji ba kuma mata ke zuwa gona ba maza
ba.[113]
Da musulinci ya zo sai ya haramta
rufe mata ya hana kashe su da ake yi
musulinci ya yi umurni da aba mata gado ya haramta xanta ya aureta, ya
ce abata sadaki yace ta zauna agida aciyar da ita ayi mata sha tara ta arziqi.
Idan muka kalli Yahudawa sun xauki sa hijabi a matsayin quntata ma mata ne
tauye masu haqqi ne shi ya sa su ka kiri
bikin qona hijabi a qasar Misra a shekara ta 20/3/1919 matan duniya su ka haxu
suka nuna kyamar su ga hijabi da mata musulmai su ke yi, bayan qasar Misra ta
yi nata sai kuma qasar Turkiyya itama tayi nata bikin qona hijabin lokacin
mulkin Mustafa Kamal Atatur, shi na shi yafi muni domin daga baya ya hana sanya
hijabi a waxansu yankunan qasar nasa. Bayan Turkiyya daga baya qasar Tunisia
itama tayi abin da Masar tayi qarqashin
mulkin Burgeba, shi Burgeba yayi hauka domin har kiran sallah sai da ya hana ya
ce a rage yawan sallolin da akeyi abar guda biyu subahi da Isha’i wai kar a
taqura ma jama’a ya ce arage azumi abarshi daga safe zuwa shabiyu.[114]
Wannan ita ce haukan da Burgeba ya yi.
A shekaran 1995 matan duniya sun haxu a qasar China a Peking a dandalin
Teanerment nan ma suka yi magana akan ‘yancin su anan kasar tamu Najeriya matar
shugaban qasa na wannan lokacin ta halarci taron ita da tawagarta, wannan fa
duk da sunann ‘yanci kuma kamar mu manta
sun xauki hijabi a matsayin tauye ma mata ‘yanci ne, idan muka lura za muga
mata waxan da ba su da addini sai dai boko kawai za mu ga suna qyaman hijabi,
ba wani abu yasa suke qyamansa ba face sai don wai takura ne sun manta da cewa
dokar Allah ne sanya hijabi kuma akwai
katafaren lada ga wadda ta sanya hijabi,
kuma zunubi ne mai girma ga wadda ta qi
sanya hijabi, muna roqon Allah ya shirye matayen da basa sanya hijabi amin.
Kuma duk yana cikin ruxin da
Yahudawa su ke yi na ‘yancin mata suka qirqiro masu da qungiyoyi misali akwai women
empawerment da women in politice da what a man can do women can do even better
da women society da Jam’iyar matan Arewa da women right da sauran su dukkanin
waxan nan qugiyoyin Yahudawa ne suka qirqiro su da nufin su kawar da mata daga
addinin Allah, Allah ya ganar da mu amin.[115]
KAMMALAWA
Wannan shi ne abin da ya sauqaqa kan
sharudxan hijabi Allah ya taimake mu, kuma Allah ya ba mu ikon aiki da
abin da na rubuta, Allah ya sa ya
anfanar da ‘’yan uwa baki xaya.
Ga masu zagin mata in sun sa hijabi yana jan qasa ko sun sanya Niqabi da
suji tsoron Allah su sani cewa duk ya yin da kazagi mai niqabi to kana neman aibanta matayen
Annabi ne da matayen sahabbai.
KumaAllah ya hana isgilanci ga masu addini, Allah ya faxa cikin suratul Tauba "yanzu Allah da
ayoyisa da manzonsa ne ku ke ma isgili babu wani uzuri da za Ku kawo kun
kafirta bayan da kun kunyi
Imani’’ kuma dubi da halin da muke ciki bai kamata ka hana matarka ko
"yarka ko qanwarka ko ‘’yar uwar ka sa Niqabi ba. In ka zagi mai sa niqabi
wannan zagi ko tozarcin zai koma zuwa ga
matayen
Annabi ne da Sahabbansa, Allah ya
kare mu da ga aibanta matayen magabata amin. Iyaye su tuna da girman haqqin da
ke kansu na ‘ya’yansu, su ba su tarbiyyah ingantacciya domin tsira gaban Allah[116]
kuma yana da kyau iyaye su lura da sharrin da ke fuskanto mu na koya
ma yara ilimin jima’i a da Gwanati ta ke qoqarin kawo wa a cikin manhajar (curriculum) makaranta boko za a kira
yaro ace ya tava nonon mace
ita kuma ta kama gabansa sai malamin ya tambaye su me suka ji
إنا لله وإنا إليه راجعون
Wannan abin muyi koka ne wallahi domin musifa ce a fili Yahudawa suka kawo mana domin su lalata mana tarbiyar mu, kuma so
suke zina ta yaxu ta zama ruwan dare, iyaye ya zama dole su kula da ‘ya’yansu.[117]
Allah ka taimake mu baki xaya kuma ka gafarta mana
zunuban mu, amin.
Wanda ya ga kuskure ko gyara ko shawara qofa a buxe take yana iya
kirana insha Allahu zan amsa masa kuma
zan gyara kuskuren da yardan Allah. Xan uwanku a cikin addinin Allah.
Wassalamu alaykum
warahamatullahi Barakatuhu Daren 25 Ramadan 1429 wanda ya yi daidai da
24/9/2008.
والله تعالى أسأل أن يجعل هذا العمل مقبولاً، مباركاً، خالصاُ لوجهه الكريم، وأن
ينفعني به في حياتي وبعد مماتي، وأن ينفع به كل من انتهى إليه؛ فإنه سبحانه خير
مسؤول، وأكرم مأمول، وهو حسبنا ونعم الوكيل، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي
العظيم وسبحانك
اللهم وبحمدك أشهد أن لاإله إلا أنت أستغفرك
وأتوب إليك
والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته
Harun Abubakar shika
08030582333-08020900001- 08054533361
harunaabubakar99@yahoo.com
[1] Suratul Ahzab
[2] Shi ya sa malaman
muslinci kullum suke rubuce- rubuce domin ba su kariya wajen ganin
yahudawa maqiya addinin Allah ba
su lalata tarbiyanr su ba da aqidarsu ba.
[3] In zamu iya tunawa anyi wani fim Na Hausa da ke wulaqanta
mata masu sanya hijabi inda fim din ya nuna mata masu sa hijabi zina suke
yi.Wannan duk aikin Yahudawa ne na cikin gida maqiya addinin Allah.
[4] Mata a wajen
Yahudu kamar haja ce ta
sayarwa kowa na iya zuwa ya gani
kuma ya taba kuma ba sa ba su wata qima sai dai qimar tozarci da
wulaqantawa, suna qyamar zaman auren
da matan musulmai suke yi a gidajensu
shi ya sa suke qirqiro ma su qungiyoyi da sunan nema ma mata yancinsu. Ko su ce kar su yi aure sai sun kai wani
lokaci ko wani matsayi na duniya ko muce wani matsayi na karatun Boko, wannan duk maqircin Yahudawa ne
maqiya addinin Allah, mace ta yi aurenta da wuri shine mutuncinta, aure ba ya
hana karatu, karatu ba ya hana aure.
[5] Manzon Allah sallalahu alaihi wa ‘alihi wasalam ya ce,”
kunya da Imani tare suke idan daya ta tafi ita ma dayar zata tafi “Kunya da
imani tare suke ba a raba su.Wani hadisin
ma cewa ya yi kunya alkhai ri ta ke jawo wa kuma duk wanda bai da kunya kamar wanda bai
da imani ne.
Don
haka yana da kyau mata su kula da kyau kar su rudu da kiran da Yahudawa su ke
masu na su nemi ‘’yancinsu. wanda wannan
da,awar ta su karya ce da yaudara. Duk
duniya ba addinin da ya ba mata ‘’yanci
kamar Muslinci, ya kuma ba su kariya.
[6] Muqaranatu baynalhijab wassufur
[7]
Allah ya ba da umurni ne na sanya hijabi domin darajar da mata suke da shi,
kuma da ma duk abin da yake da daraja zakaga voye shi akeyi a na ba shi kula kula
ta musamman domin darajar sa.sannan duk abin da yake a
rufe ya fi daraja kuma ya fi kyau.
[8] Bukhari da Zadul ma,ad da Isaba.
[9] Jilbabul Mar’atil muslima
da Hijabulmar,atil muslima da
Raddul mufhim dukkansu na
babban malami Sheikh Nasirudden
Albany da Iqtiyaratul fiqhiyah inda
Sheikh Albany Jilbabul Mar’atul
muslima Na Amru AbdulMun’im
[10] Raddu Azhan ila ma’anil Kur’an Suratul Ahzab.
[11] Ya kawo maganar Ibn
Abbas kan fassarar wannan ayar.
[12] Suratun Nur 31 da kuma tafsirn Imamul Xabari za a qaru da
bayanin magabata masu daxin karatu.
[13] Tirmizi da Ahmad da Abu Dauda
[14] Jilbabul mar,atil muslimah
da hijabulmar,atil muslima
[15] Muwadxa ta Imam malik
[16]Muwadda ta Imam Malik
[17] Fatawa Madina
[18] Majmu’ul Fatawa
na Baz
10/409
[19] Majmu’ul Fatawa
[20]
Adxaaharatu was Sallatu 54
[21]
Bidayatu mujtahid na ibn Rushid 124
[22] Asalin acava Arna mata ke hawa, an fara yin acava ne a Kaduna ,amma yanzu abin bakin ciki ya
canza har mata musulmai suma suna hawa acava, abin da yasa ake ce masu
‘’yan Acava shi ne in sun dauki mata su ka yi
gudu dasu suka taka birki Nonan
matar ya taba jikin sa sai
‘’yanuwansa su ce mashi ya CAVA
yar’uwa kin ji asalin dalilin da yasa ake cewa “YAN ACAVA, Kuma babban abin baqin ciki har da masu sa
Niqaabi za kaga suna hauwa ِ
Acava. ِِAllah
ya kyauta sai dai lalura mai qarfi to
ta iya hawa Acava , kamar mace tana cikin rashin lafiya na fitan hankali wanda in bata hau acava
ba tana
iya mutuwa .
[23]
Xabarani Mu’ujamul Kabir
[24]
Haka nan ma haramun ne mace
ta buxe kanta ga matar da take kafira,
wato babu kyau mace ta bude gashin kanta ga Arniya kafira da sunan
kitso, ko wani abin sai dai lalura mai
qarfi, kuma wani sharri da bala’i da ke
faruwa sai kaga mata a makarantun Sakandire malamai maza na buxe masu
kansu wai da sunan duba tsafta wannan bala’i ne da masifa kuma hramun ne mace ta bari kafiri yana
kallan gashin kan ta, namiji musulmi ma an hana
shi ya ga kanki balle kafiri ko
kafira don Allah mata kuyi qoqarin
gyarawa tun kafin lokacin nadama Allah
ya kyauta amin. Ana iya duba littafin
Fauzan mai suna Hijabul shar’i ko Littafi Albany Hijabul Mar’atul Muslimah ko Jami’u Ahkamin Nisa’i
ko Littafin ibn Taymiyyah Hijabul Mar’ah
[25] Ahmad 19/6 da
Bukhari Adabul mufrad da Ibn Hibbans
[26]
Breast lenght shine hijabin da mata
masu karatun Anguwan zoma su ke sanyawa a (school
of Nurses) shima haramun ne sanya shi don haka mata masu karatu a wannan waje su yi qoqari su gyara.
[27] Fiqhu Sunna lil Nisa Kamal Abu malik da Sheikh Mustaphal
Adawi Jami’u Ahkamun Nisa
[28] Muslim da Xabarani (Dukkan mata masu sanya tufafi amma ana
ganin jikinsu sun shiga la`antar manzon Allah kuma tsinannu ne Allah ya kauta.
[29] Nisa’u Ahlunnar na
Mustafl murad
[30] Dhiya’ul Maqdis
[31] Muwadda Malik 2/913
[32] Muslim da AbuDauda
[33] Nasa’I 12/203 da AbuDauda
[34] Muslim 328
da Imamu Nisa’I 8/154
[35]
Ahmad 4/394
[36]
Don haka mata in za su makarantan Islamiyya ko boko ko kasuwa suji tsoron Allah su bar sanya Turare ko shafa mai
mai qanshi
[37] Muslim
[38] Dabarani fil Ausad
[39] Iqtidau siradil mustaqim
[40]
Ahmad 2/199-200
[41]
Abu Daud
[42]
Ahmd
[43] Abu Dauda da ibn
Majah
[44] Sahihu
Jami’usSagirs 7674
[45] Bukhari 4/54 Muslim
3/1653-1654.
[46] Manzon Allah
sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya
ambata ya ke cewa wata rana Annabi Isah yana zaune a gidansa
shi da xalibansa su goma shabiyu
sai yace ma Dalibansa yanzu haka anzagaye
gidana da nufin kashe ni waye
zai fita, Allah zai sa mashi kamanni na za a kashe shi mu haxu a Aljannah ba wanda ya
tashi
sai wani yaro ma fi qanqantar shekaru a
cikin su Annabi Isah ya faxi haka sau uku sai dai wannan yaron yake tashi
sai Annabi Isah ya ce mashi to je
ka, yana fitowa sai Allah yasa mashi siffar Annabi Isah su
kuma da suka ganshi sun xauka Annabi Isah ne
sai suka kashe shi, shi kuma
Annabi Isah sai Allah yasa mashi barci
ya buxe saman rufin xakin nasa ya yi sama da shi… da AbuHuraira mai
riwayar hadisin ya kawo nan sai yace ku karanta in kun so وما قتلوه وما صلبوه
ولكن شبه لهم وإن الذين اختلفوا فيه لفي شك منه ما لهم به من علم إلا اتباع الظن
وما قتلوه يقينا بل رفعه الله إليه وكان
الله عزيزا حكيما
Don haka Annabi
Isah zai dawo kamar yadda hadisai suka nuna
wanda ya ce ba
zai dawo ba yana karyata Kur’ani ne da
hadisan Annabi kum hadisai ingantattu. . .
[47] Bukhari da Ahmad
[48] Su ‘yan qallon Ture
suna yin wasanin su ne da manufar su ta kafirci shi ya sa suke sa
alamar kuros a jikin kayan wasanin su don su, sun xauki
qwallansu tamkar suna coci ne kuma su
nuna ma duniya manufar su ta kafirci.
Yakamata mu kula mu daina sa irin
wadannan kayan kuma zaka ga mutum
musulmi ya hardace sunayan ‘yan qwallo
amma bai hardace sunayen Sahabban Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ba ko kuma kaga yadda yake son ‘yan qwallo ya
fi yadda yake san Annabi sallalahu alaihi wa,alihi
wasallam lalle wannan musiba
ce Allah ya kare mu. Kwanaakin baya ansami wani Xan
Qwallo mai suna BECCHAM aka tambaye shi
wa yafi so ya ce Matarsa akace mashi to wa yafi qi sai ya ce Musulunci da
Musulmai, ya faxi wannan Magana kowa
yaji a duniya amma zaka ga musulmi da
hotan shi a rigarsa sabo da rashin sanin ciwon jikin sa, Allah ya shiryemu baki xaya amin. Balle
kuma bala,i na qarshe Qwallon
Mata da a keyi a sakandere (secondary) duk wadda ta yi qwallo tsinarniya ce haka
shima wanda ya taimaka wajen yin qwallon
Mata shima tsinanne ne da masu kallon qwallon mata suma tsinannu ne haka
hadisin Imam muslim ya ambata.
Wannan
musibar ta fara yaduwa a makarantun gaba da firamire wato makarantun Sakandire Allah ya tsare ma
na matayen mu da yaranmu da yin qwallon mata
[49] Bukhari da Ahmad
[50] Adabu shari’a 3/512
[51] Bn Baz Jawabul
mubin fi hukmu taswir
[52] Bukhari da Muslim.
[53] Bukhari da Muslim
in ki ka duba Adabuz zifaf zaki ga Magana mai kyau kan sa hoto a
tufafiko labule.
[54] Malaman musulimci na Ahlussuna sun tafi kan xaukar hoto haramun ne wannan it ace Magana
ingantatciya kuma ita ce bn Baz da
Albany da sauran malaman sunna su ka
xauka, ki duba littafin Riyadussalihin da Adabuzifaf da jawabul mufid na bn Baz
da silsilatul AhadisusSahiha da ikrtiyaratulfiqhiya na Albany da Bukhari da
muslim da Gayatul maram ko Iziya littafin fiqhulMalikiya zaki ga
bayani kan harmcin xaukar hoto don haka bai kamata ki xauki hoto ba , balle
ma in zaki yi aure ki yi KALANDA wannan
yafi tsananin haramci da muni. Hadisin da manzan Allah ya yaga labule Nana
Aisha bai da inuw don haka kowane irin hoto ne haramun ne ki xauke shi ko ki
manna a Xakin ki ko a kayan ki indai wannan hoton wani abu ne mai rai. Ba a
fara yin shirka ba a bayan qasa sai ta sanadiyar hoto wannan Magana ce
shahararriya maganace daga ibn Abbas
kuma duk kusan littafan tauhidi sun yi bayanin wannan. Za ka ga wasu
hijabin da hotonan wasu mutane da sunan malamai ne ko masu mulki
,ko sarauta duk bai halasta a sa ma hijabi hoto ba ko na wane malami ne bai halasta
a sa hotonan su
a jikin hijabi ba. Ko taurariya da wasu su ke sawa hijabin su suma duk sun shiga cikin hanin.
[55] Ranar goma ga watan
Muharram ita ce ranar da a ke ce mata ASHURA,Manzon Allah ya yi umurni ne da a yi azumi
amma a wajen masu bin addinin‘’Yan SHIA rana ce ta baqin
ciki shi ya sa suke sa baqaqen kaya.Su
kuma mara sani‘’yan Bidia ranar suna yin
cika-ciki ne, shi kuwa cika-ciki Bidiace domin ba shi da asali a shari’ayar
Annabi da Sahabbai da sauran magabata na qwarai.. Su kuma NAWASIBA ranar farin
ciki ne a wajensu shi ya sa suke yin
abinci suna rabawa gida-gida suna farin
ciki su ma abin da suke yi Bidia ce. Su kuma AHLUL SUNNA suna yin
Azumi ne kamar yadda Annabi sallahu
alaihi wa alihi wasallam ya yi umurni da a yi nemi littafina na “Tasu’a da Ashura da Cika-ciki”.
[56] JilbabulMartul muslima
Ammru Abdulmum’in 47
[57] Musannaf Abi
Shayba
[58] Suratul Taharim.
[59] Sanannen abu ne cewa ilmin addini da kwatanta aiki da shi,
sanya sutura ta Musulunci da tarbiya ta
zahiri, alamomi ne da ake lura da su wajen kyautata wa mace zaton cewa tagari
ce (المرأة
الصالحة). To amma kasancewar ana samun akasin haka bayan an yi auren,
wajibi ne kowane Musulmi ya riqa yin addu’a tare da roqon Allah Ya taimake shi
wajen samun mace ta kwarai, mai tsoron Allah, wadda za ta iya yin tarbiyar
kanta da na `ya`yansu,
[60] Iyaye su umurce su da hijabi cikakke idan za su fita gida
zuwa makaranta ko kasuwa ko gidan buki ko asibiti ko ziyara ko wani wuri dabam. Haramun ne a kyale
`ya`ya mata su riqa sanya tufafi shara-shara ko kuma su fita ba tare da hijabi
cikakke ba, da zaran sun balaga – sun fara jinin al’ada. Maganar cewa hijabi
wajibi ne kawai a kan matar aure, ba ta da asali a cikin Musulunci. Allah (Mai
girma da daukaka) Ya ce: “Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu,
kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana qawarsu face abin da ya bayyana
daga gare ta, kuma su sanya da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su
nuna qawarsu face ga mazansu, ko ubanninsu…”[60]
Kuma Ya ce: “Ya kai Annabi! Ka ce wa matanka na aure da `ya`yanka da matan
muminai su kusantar da manyan tufafin da ke kansu kasa……… , bai halasta a ga
wani bangare na jikin tab a. in dai ta
balaga Haka nan, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce:
“Daga qarshen al’ummata, za a samu wadansu mata (na yawo) sanye da tufafi (amma
kuma saboda shara-sharansa), tsirara (suke a zahiri)… Ku la’ance su, domin kuwa
la’anannu ne. A cikin wani hadisin, Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a
gare shi) ya ce: “Ba za su shiga aljanna ba, kuma ba za su ji qamshinta ba.Ke
nan, da zarar yarinya ta balaga (ko da ba ta yi aure ba), wajibi ne ta sanya
hijabi na Musulunci idan za ta fita. Amma kasancewar itace ana tanqwara shi ne
tun yana danye, ya kamata iyaye su himmatu wajen koya wa `ya`yansu sanya hijabi
da saba masu da fita da shi, maimakon gyale ko abin tatan qullu. Shaykh Muhammad Saalih ibn al-‘Uthaimeen ya
ce: “Ya ku `yan’uwa, iyayen `ya`ya mata! (A yau) Sanya wa `ya`ya mata gajejjerun
tufafi ko tufafi matsattse da ke siffanta jiki ko tufafin da ke bayyana launin
jiki saboda shara-sharansa, abu ne da ya yadu a tsakanin mutane kuma aka dauke
shi da sauqi. (Ku sani cewa) wanda duk ya sanya wa `ya`yansa mata irin wadannan
tufafi ko kuma ya ke qyale su da gyale,
to yana sanya masu tufafin `yan wuta ne, kamar yadda ya tabbata daga Annabi
(tsira da aminci su tabbata a gare shi).s Ya kai uba musulmi! Yanzu za ka so wa
`yarka kuma masoyiyarka shiga wuta? Ka yarda ka riqa sanya wa `yarka tufafin da
zai nuna rashin kunyarta, bayan kuwa kunya na daga imani? Ka yarda `yarka ta
mayar da kanta kamar wata hajar (kayan) sayarwa…?
[61] Sa hula xabiace ta mutane masu mutunci da
karamci da sanin yakamata da
kamala, Tafiya kai ba hula xabiace ta
Arna haka yafarune bayan zuwan Turawa qasashen musulmai duba Tamamul minna za
ka ga Magana gamsasshiya, don haka ‘’yan uwa su kiyaye su daina tafiya kai ba
hula. Hadisin da aka ce Annabi ya cire
hularsa ya yi sutura da ita lokacin da yazo sallah ba sutura wannan hadisin bai
tabbata daga Annabi ba hadisi ne na qarya,duba Silsilatul Ahadisul Dhaifa da
Tamamul minna fi taliqi ala fiqhu Sunnah.
[62] Yana da kyau masu aibata mata masu sa nikab da su yi hakuri
su fadada karatun su ko kuma su je su tambayi malamai ma su
ilimi su bar fadin abin dab a su da ilimi a kan shi dasu bar maganar da ke bayyanar da jahilcin
su.
[63] Bukhari.
[64] Bukhari. 9365
[65] In ki ka duba
Suratu Nur zaki ga wannan kissar ko ki
duba Bukhari zaki ga bayani.
[66] Audatul hijab
[67] Ahmad 6/30
[68] Ibn Said 49
[69] Muwadda ta Imam Malik
[70] Tafsirul Baydawi
[71] Ibn Said
[72] Ibn Majah
[73] Bukhari
[74] Hijabul mar,atul muslima
[75] Bayhaqi 8/93
[76]
Imamun Nawawi yana da fahintar sanya Niqabi wajibi ne idan dai ana gani zamani
ya lalace kuma ana tsoron faxawa cikin fitina
to mata su rufe fuskokinsu shi ya fi alkhari.
[77] Fafirru ilallah na Abi Zaid
[78]
Musannaf Abi Shaybah 2/231-6294 isnadinsa sahihi ne
[79] Wadannan hadisai da muka kawo sun nuna mana
a fili karara cewa Niqabi yana da
asali kuma mata masu daraja sun sa , nasihar mu ga masu aibata niqabi da suji tsoron Allah su sani yin haka zai ja masu haxari ga
imanin su kuma aibata masu sa
Niqabi zai koma ne zuwa ga matayen
Manzan Allah sallalahu alaihi wa,alihi wasallam da matayan sahabbai da Tabi’ai,
domin sune farkon waxan da suka fara sa Nikabi kafi kowa ko kafin
wata ta ta sa.
[80] Raddul azhan ila ma,anil Kur,an
[81] Hijabul mar, atul muslima.
[82] A cikin littafin sa
Raddul mufhim yagoyi bayan sa nikabi
domin ya kawo hadisai da su ke nuna sharia ce mace ta rufe fuskar ta
kuma matayen Annabi sallalahualaihi wa,alihi wa,sallam da sahabbai sun sa amma
a ce dole ne ba mu da hujja a kan haka
sai dai sunna ce kuma mustahabbi ne mata su sa niqabi amma ba dole ba ne amma
su sa shi ya fi.
[83] Abu Dauda 4/41 sai dai wasu malamai sun ce hadisin mai
raunine saboda a cikin isnadinsa
a kwai illoli guda hudu
1Khalid
bn Dharayk bai hadu da nana Aisha ba
isnadinsa Munkadi’I ne.
2Qatada
yayi an an kuma mudalis ne.(yaiy jurwaye a cirato
hadisin kuma gashi shi kansa dama mai mguxe ne)
3
Sa,id bn Bishir Dhaif ne musamamam ta wajen Qatada.
4.
Khalid bn Muslim yayi an an kuma
shima mudalis ne.
[84] Fatwa Madina 10
[85]
Imamun Nawawi yana da fahintar sanya Niqabi wajibi ne idan dai ana gani zamani
ya lalace kuma ana tsoron faxawa cikin fitina to mata su rufe fuskokinsu shi ya
fi alkhari.
[86] Risala fil hijab
[87] Majmu’ul fatawa usaimin.
[88] Usratul muslima. Sheikh usaimin ya yi Magana mai yawa kan dole ne mace ta rufe fuskarta yana da
kyau a duba littafinsa wanda muka kawo a
baya.
[89] Fatawaa Mar`atul Muslimah 602
[90] Ahkamun Nisa da Hijab adillatul nujibina wa shubuhul
mukalifina.
[91] Hirsatul fadhilah 77
[92] Hirsatulfadhilah 45-65
[95]
Dhawabidul Hijabi Shar’i
[97] Fathul Bari na
ibn Rajab al-Hambali 1/507 da Tahzibuz Sunanan 5/198 da I’ilamul
Muwaqqi’ina
[99] Dukkan wadannan malaman ba su yi wannan fihinta tasu kan
ra’ayi ba sai dai don Allah da kuma kyakkyawar niya don haka wanda ya ce sa nikabi dole ne dogaransa da hujjojin wadanda suka ce wajibi
ne ba za a zarge shi ba don yana da
magabaci kan fahintarsa in kuma ka ce ba dole ba ne amma sanyawan shi yafi
alkhari shima ya na da magabaci kuma shima yana da na sa hujjar.Inda illar ta
ke kace ba kyau ko bai da asalin ko bidia ne nan ne fa malamai za su yi maka
raddi kan bayyanar da jahilcin ka a fili.
[100] Babu
ko shakka Yahudawa suke amfani da shi wajen cin mutuncin musulici.
[101] Duba Nisau
Ahlinnar
[102]
Bukhari
[103]
Bukhari
[104]
Wani abin ban takaice a yau sai kaga mata suna tafiya tsakiyar hanya ba sa ko
jin kunya, wani lokacima har ka ga suna haxa jikinsu da maza sabo da matsatsin
hanya, a gaskiya yin haka kuskure ne muna roqon ‘yan uwanmu mata da su gyara
don girman Allah in suna tafiya su bi
gefen hanya kamar yadda Annabi sallahu
alaihi wa’aihi wasallam ya koyar da mu, Allah ya taimake mu amin.
[105]
Ahmad
[106]
Ahmad. Sheikh Mashur Hassan Salman ya rubuta littafi wanda ya ke nuna harancin
qwallon qafa sunan littafin ‘’Kurratul Qadam”qwallo dai ga maza ma ba ta
halasta ba balle mata.IbnTaymiyyah yayi bayanin hukunci qwallo a Majmuol Fatwa
da asalinta yana da kyau aduba
bayaminsa.
[107]
muslim
[108]
Baihaqi
[109]
To ma su xaura ma yaransu mata talla sunji xaukan kaya mai nauyi yana kawar ma
mata budurcinsu sai abi a hankali. Kuma dama talla tana cikin abin da ke lalata
tarbiyar yara mata har ma ya kai su shiga zinace- zinace ta sanadiyar talla,
wulaqanta mata ne ariqa xaura masu talla, iyaye su ji tsoron Allah su kula
‘ya’yansu, su tuna da cewa amana ne Allah ya basu zai kuma tambaye su akan
amanar ‘ya’yansu.
[110]
Ahmad
[111]
Fatawaa Mar’atil musimah 603
[112] Za mu iya tunawa a qasar Hausa sarakuna da mata suke tsafi a yave su da rai
ajikin gida ko ganuwa kafin jihadin Xanfodio.
[113] Har yanzu a qasar Indiya akwai masu yin haka, kuma aqasar Indiya har yanzu
mace zata iya auren maza fiye da guda xaya Allah ya kyauta amin.
[114] Burgeba ya mutu a wulaqanci haukacewa yayi Allah ya tsare mu, a lokacin sa ya kasha maya-mayan malaman Musulinci, malaman
duniya sun bad a fatawan cewa Burgeba ya kafirta, haka ya faru da shi ne saka
makon neman ‘yanci
[115] Matan har yanzu a Turai basu da qima domin kuwa acikn tsarin mulki (consitution) na Faransa ya
halasta ma magidanci idan yana fama da taulauci ya xauki matarsa ya jinginar da
ita, ‘yar uwa ina ‘yanci yake anan, an tava shiya tattaunawa a qasar Ingila wai
shin mata dabbobi ne kuma mutane ne ina
za a sa su, ina ‘yanci yake, a Amurka mata sun tava kai qara akan wai ana
taqura masu da ake cewa su riqa sa rigan mama in za su shiga wanka a rafi
(swiming pol) su ka ce baza su qara sawa ba sai in suma maza za su riqa sawa,
irin wannan ‘yanci ne ake so ki nema !. yana daga cikin ‘yancin mata
awajen Yahudawa abar mata su riqa auran
junan su mace ta auri mace لا
إلَهَ إلا اللهُ
Allah ya tsare mu.
[116] Nemi littafina ‘Haqqoqin ‘Ya’ya akan Iyayensu”
muna ruqon iyaye da su kula da ‘ya’yansu masamman mata domin yanzu wani bala’i
ya faxo mana yadda ‘yan Film xin Hausa suke vata mana tarbiyyar ‘ya’yanmu muna
roqon Allah ya kare mu daga sharrin ‘yanfilm da ‘yan maxigo (lessbianism) Allahumma amin.
[117] Jaridar Weekly Trust ta tattauna da
malamai akan koya wa yara ilimin jima’i
(sex education) abin farin
ciki dukkanin malaman mu na musulinci ba
su yarda ba kai har da na Kiristoci suma
ba su yarda ba, amma abin baqin ciki
wani daqiqin malami na musulinci a Kaduna ya ce a koya wa yara ba komai yana da
kyau Allah ya kyauta Allah ya shirye
shi.
Allah kara Basirah ya sheikh.
ReplyDelete