GABATARWA
بـسـم اللـه الـرحـمـن الـرحـيـم
إن
الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ
بالله من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادى
له، وأشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله. أما بعد: فإن خير الحديث كتاب الله،
وخير الهدي هدي محمد، وشر الأمور محدثاتها، وكل محدثة بدعة، وكل بدعة ضلالة، وكل
ضلالة في النار أما بعد:
Ina
godiya ga Allah da ya bani ikon rubuta wannan littafi taqaitacce wanda yake
magana akan hukunce hukunce janaza wanda ya shafi tun daga rashin lafiya jinya
zuwa qabari.
Wannan littafi ya zo ne sakamakon shawarar da
Malamina Malam Ahmad Bello Dogarawa ya
bani na in rubuta littafin da yake bayani akan yadda shara’a ta koyar da mu game da Janaza, ya bani wannan shawarar
ne bayan munta shi karatu ya xauko ni a motarsa ya kawo ni inda zan shiga mota
in dawo gida, bayan na dawo gida naba Allah zavi akan shawar da ya bani sai na
same natsuwa akan rubuta wannan littafi taqaitatce akan hukunce-hukuncen janaza
daga Qur’ani da Hadisai bisa fahintar magabata na qware. Don haka lalle
malamina yana da falala mai yawa akaina Allah ya sakamasa da Aljannatil
Firdausi amin.
Gaskiya duniyar musulincin qasar Hausa ta na
buqatuwa ya zuwa ga wannan littafi kusa kana iya cewa dukkan wani musulmi yana
da buqatuwa ya zuwa ga wannan littafin masammam waxanda suke iya karatan Hausa
domin yau an wayi gari an maida sha’ani janaza ya zama al’ada an jivinta janaza
ya zuwa ga waxanda ba su san me shara’a ta ce ba, na ga mahimmanci fitar da
wannan littafin cikin gaggawa saboda duka ranar da naje na halarci janaza nakan
dawo gida cikin damuwa ganin yadda ake yin aiki da ka ba tare da la’akari akan
me shara’a ta ce game da gawa ba.
Na
fara littafin nawa tun daga rashin lafiya da neman magani da hukuncin shan
magani da yadda ake jinya da ladubban zuwa ziyarar mara lafiya da yadda ake so likita ya kula
da mara lafiya da mutuwa da alamomin mutuwa da alamomin kyawawan cikawa da
alamomin munanan cikawa da me ya kamata ayi ma mutum da zaran ya rasu da yadda
ake wankan gawa da likafani da yadda ake sanya sa da dai sauran su za a gani
insha Allah.
Kamar
yadda yake al’adata ce littafina yana taqaituwa ne qarqashen Qur’ani da hadisi
bisa fahintar magabata na qwarai (SalafusSalih) ina roqon duk wanda ya ga
kuskure ko shawara qofa a buxe take kuma ina lale maraba da gyransa ko
shawaransa
Addua
wadda bata da iyaka da fatan alheri ya zuwa ga mahaifana Malam Abubakar Ibrahim
da Malama Fatimatu Dalhatu Zaria Allah ya jiqansu ya sakama su da Aljannatil
Firdausi amin Allah ya albarkaci zuri’ar su
ya yafe masu zunubansu amin.
Godiya
zavavviya ga Malam Musa Sahabi Zaria Allah ya saka masa da alheri gaskiya yana
taimaka man sosai wajen ganin naci gaba da talifi haka shima Malam Kidir
Ibrahim Zaria alherin Allah ya je ya zuwa gare shi yana zaburar da ni akan
cigaba da rubutu. Malam Abubakar Jumare Allah ya saka masa da Aljannah ya yi
iya bakin qoqarinsa na ya duba wannan littafin amma Allah bai yarda ba saboda
yanayin jikinsa Allah ya bashi sauqi amin kuma Allah ya sa kaffara ne. Babu shina
yiwuwa in manta da Malamina Sheikh Muhammad Aminu Jumare Alqali Allah ya yi mai
sakamako da Aljannah haka shima Malam
Haruna Ishaq Shika shima Alla ya saka masa da Aljanna amin. Allah ya jiqan
Malamina Imam Malam Mika’il Isah Shika Allah ya bashi Aljannah amin.
B azan manta da Dr Ahmad Bello Sardauna
ba shugaban tsangayar qidaya da lissafin kuxi na Jami’ar Ahmad Bello Zaria
(H.O.D Accounting) ya bayar da gudun muwa mai girma wajen ganin wannan littafi
anfitar da shi Allah ya yi mai sakayya da gidan Aljanna shi da mahaifansa Allah
ya albarkaci zuriarsa amin. Za a iya samun sauran littattafan dana rubuta a
mudawwanata ta yanar giza-giza http://harunaabubakarshika.blogspot.com
ina roqon addua ta alheri ga duk wanda ya karanta littafi na nagode.
Wassalamu alaykum warahamatulLahi wa barakatuhu
25 Ramadan 429
Harun Abubakar Shika
08030582333-08054533361- 08020900001
RASHIN LAFIYA (CIWO)
Ciwo
daga Allah ya ke babu bb wanda ya fi
qarfin Allah ya jarrabe shi da ciwo ko wane iri ne, in muka bibiyi tarihi za mu
ga bayin Allah da dama sun yi fama da rashin lafiya ba don kome ba sai dai
don Allah ya xaukaka darajarsu da kuma kankare
ma su zunubansu. Gwargwadon imanin mutum gwargwadon yadda Allah zai
jarraba shi. Manzon Allah sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam ya gaya mana cewa girman lada na tare da girman jarrabawar
da Allah ya jarrabe ka da ita, haqiqa idan Allah ya so wasu mutane sai ya jarraba
su (da wata cuta), wanda ya yarda da hukuncin Allah to yana da yarda, wanda ya yi
hushi to yana da sakamakon fushinsa.[1]
Don
haka ciwo ba abin zargi ba ne domin akwai wani
sakamako wanda Allah ya ke bai
wa wanda ya yi ciwo, haka ma’aiki
sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya faxa mana a wani hadisi da aka samo
daga Anas Allah ya qara masa yarda ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi
wa sallam ya ce, ‘Idan Allah ya so bawansa da alheri sai ya sa masa wata cuta
(uquba) a nan duniya, amma idan Allah ya nufi bawansa da sharri sai ya qyale
shi da zunubinsa har ya cika masa da shi ranar qiyama.’”[2]
Wannan
magana ta manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ta nuna mana ashe duk wanda ciwo ya same shi ya yi haquri
ba kansa ne farau ba, manyan mutane su ma sun yi ciwo na tsawon lokaci mai tsawo, misali kamar Annabi Ayyub da Allah ya gaya mana ya yi
ciwo na tsawon lokaci wanda har ya kai na shekara 18 ba ya fita saboda ciwo, wanda har ya kai ga
gaba xayan dukiyarsa ta qare ‘ya’yansa duk suka mutu baki xayansu saboda
tsananin ciwo, sai da ta kai gaba xayan
jikinsa ba ya amfani sai zuciyarsa
kawai, wasu malaman tafsirin ma cewa
suka yi sai da ya kai jikinsa ya kasance yana yankewa yana faxuwa qasa. Wata rana matarsa[3]
ta ce masa ya roqi Allah ya ba shi lafiya mana, sai ya ce shekarata saba’in lafiyata
lau amma in kasa haquri da rashin lafiya ta shekara sha bakwai?[4]
الله أَكْبَرُbayin Allah ke nan
shekara da shekaru suna fama da rashin lafiya amma suka yi haquri, haka aka san bayin
Allah cikin haquri ko da yaushe.[5]
Kusan idan muka bibiyi tarihi zamu
ga yadda Allah Ya ke jarraba bayinsa da cututtuka ba don komai ba sai don Ya
qara masu daraja da xaukaka. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa salam
ya yi ciwo, haka shi ma babban sahabinsa
Abubakar shi ma haka, haka shi ma Imam
Malik ya yi rashin lafiya har ya kai ba ya zuwa masallaci sai a gidansa yake
yin sallah,haka ya mutu cikin wannan rashin lafiya. AllahYa rahamshe shi amin. Shi ma xalibinsa Imamu Shafi’i ya yi rashin lafiyar da ta kai in ya hau doki
jini na zuba a duburarsa, har ya cika
masa huffinsa (takalminsa). A qarshe dai
ina mai cewa ciwo ko rashin lafiya daga Allah ne kuma ba abin zargi ba (ba aibu ba ne) ne domin jarrabawa
ce daga Allah, kuma akwai sakamako mai
yawa ga wanda ya yi haquri kuma ya miqa
al’amarinsa ga Allah. Imam Ahmad shi ma ya yi ciwo mai tsanani har ta kai ga yana
nishi da qyar, kuma a cikin wannan ciwon ya rasu Allah, Ya rahamshe shi amin.
Ana
so mara lafiya ya yi haquri da cutar da ta same shi ya miqa lamarinsa ga Allah
kuma ya yi haquri, babu abu mafi tsada fiye da Allah Ya ba ka haquri, kuma
Allah Ya yabi masu haquri a cikin littafinsa kuma Ya yi ma su bushara da lada
mai yawa kuma Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya faxi irin falalar
haquri, shi mumini duk abin da ya same
shi lada ne.
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
ya ce, “Abin sha’awa ga al’amarin mumini
komai nashi lada ne. Idan abin farin ciki ya same shi ya gode wa Allah alkhairi
ne a gare shi, in kuma abin baqin ciki ko damuwa ya same shi ko ciwo ne ya yi
haquri alkhairi ne a gare shi.”[6]
Manzon
Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce wanda Allah ya nufe shi da
alkhairi sai ya sanya ma shi wata cuta.[7] Babu wata damuwa ko baqin ciki ko ciwo ko
wani abu mai cuta da zai sami mumini face lada ne a gare shi. Har qaya idan ya
taka face Allah Ya kankare masa kurakuransa.[8]
Ibn
Mas’ud ya shiga wajen Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya taras da shi yana zazzavi, sai ya ce ma shi, “ Ashe kai ma kana zazzavi zazzavi mai tsanani haka?” Sai Manzon Allah
sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Haka ne abin yake, ni ciwon mutane biyu nake yi.” Sai Ibn Mas’ud ya
ce, “Kana nufin kana da lada biyu ke nan?” Sai Manzon Allah sallal Lahu alaihi
wa alihi wa sallam ya ce, “Na’am.” Sannan sai ya ce, “Babu wani ciwo ko qaya da zai sami
musulmi face Allah ya kankare masa munanan
ayyukansa kamar yadda itaciya take kakkave ganyayen ta,[9]
NEMAN MAGANI.
Haqiqa
Allah Ya halasta shan magani ta harshen Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Malamai sun kasu gida biyu: Wasu na
ganin halascin shan magani, wa su kuma suka ce rashin shan magani shi ne
mafi alheri. Ga dai hujjojin masu ganin
halascin shan magani kamar haka:
HUJJOJIN MASU SHAN MAGANI.
Ya
zo cikin musnad na Ahmad Ibn Hanbal Hadisi daga Usamatu ibn Sharik ya ce, “Na kasance
wajen Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa
alihi wa sallam sai wani baqauye ya zo wajen Annabi Salla Llahu alayhi wa alhi wa sallam ya ce wa Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam,
‘Wani mutum ne mafi alheri,’ sai ya ce, ‘wanda
ya fi su kyawawan xabi’u,’ sai ya qara tambayarsa, ‘Shin za mu shan
magani,’ sai ya ce, ‘Na,am ku yi magani ya ku bayin Allah domin Allah bai
saukar da cuta ba face ya saukar da maganinta, ban da ciwon guda xaya.’ Sai suka tambayi ciwon da ba shi da magani, sai
ya ce, ‘Ciwon tsufa.”[10] Wata ruwayar sai ya ce, “Allah bai saukar da cuta ba face
ya saukar da maganinta, wanda ya sani ya sani wanda bai sani ba bai sani ba.[11]
عن أسامة بن شريك قال: جَاءَ أَعْرَابِيٌ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ - صلى
الله عليه وسلم – فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ أَيُّ النَّاسِ خَيْرٌ؟ قَالَ:
"أَحْسَنُهُمْ خُلُقاً". ثُمَّ قَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ أَنَتَدَاوَى؟ قَالَ:
"تَدَاوَوْا؛ فَإِنَّ اللَّهَ لَمْ يُنَزِّلْ دَاءً إِلاَّ أَنْزَلَ لَهُ
شِفَاءً, عَلِمَهُ مَنْ عَلِمَهُ, وَجَهِلَهُ مَنْ جَهِلَهُ". رواه أحمد
Wata
ruwayar: Manzon Allah Sallal Lahu alayhi Wa alihi wa sallam cewa ya yi, “Allah Ya halicci cuta da maganinta, ku yi magani amma kar ku yi maganin da
haramun.[12]
Cikin
Tirmidhi ya ambaci amfanin
Tozalin Ismad a
matsayin maganin ciwon ido.
Wata Sahabiya Allah ya qara ma ta yarda ta ce,
“Manzon Allah Sallal Lahu alaihi Wa alihi wa sallam ya ga wata yarinya a
gidansa, a fuskarta akwai wata cuta sai Annabi ya ce, ‘Ku yi ma ta ruqquya tana
da kambun baka.’”
An samu wani sahabi ya faxa wa Annabi sallal
Lahu alaihi wa alihi wa sallam cewa xan’uwansa yana ciwon ciki, Annabi sallal
Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce ma shi ya je
a bashi zuma zai warke.[13]
Wata
ruwayar Manzon ya ce, “Mafi alherin abin
da za ku yi magani da shi, shi ne Qaho.”[14]
Ya
tabbata cewa tokar keson tabarma tana maganin
quna.
Mun ga Masu ciwon gyambon ciki (ulsa) ya
ce su sha fitsarin raqumi.
Wata
ruwayar daga Usama xan Harik ya ce, “Manzon Allah Sallal Lahu alayhi Wa alihi
wa sallam ya ce Habbatus Sauda’a tana maganin komai amma ban da Rasuwa da
tsufa.”[15]
Wata rana kunama ta harbi Manzon Allah sallal
Lahu alayhi wa alihi wa sallam a
masallaci sai ya ce, “Yanzun nan har Annabin Allah Kunama
ba ta qyale shi ba! sai ya ce a kawo masa
ruwa. Sai ya karanta QUL YA AYYUHAL KAFIRUN ya zuba
gishiri ya zuba a qafarsa.[16]
Hadisi
ya inganta daga Manzon Allah sallal Lahu
alayhi wa alihi wa sallam yake cewa, “Idan xayanku yana zazzavi mai tsanani, ya
sanyaya shi da ruwan sanyi.”[17] Wato
in kana zazzavi matsananci sai ka yi
wanka da ruwan sanyi. Za mu iya fahimtar haka a hadisin da ke Bukhari a lokacin da ciwo ya tsananta ga
manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam sai ya sa aka zuba masa ruwan sanyi a kwatanniya ya je ya yi wanka har sau biyu.[18]
Waxannan su ne hujjojin masu ganin nema da kuma
shan magani dole ne, har Ibn Qaym ya yi raddi a kan waxanda suke ganin ba za a sha magani ba
a littafinsa,[19]
da dai waxansu hujjojin da suke nuna halascin shan magani.
Wasu
malaman na cewa rashin shan magain shi ne mafi alheri suka ce in mutum na da
qarfin imani to ya qi shan magani shi ne
martaba ta qoli kuma qin shan maganin
shi ne mafifici ga hujjojinsu kamar haka
1.
Wata rana Ibn Abbas yana
zaune sai ya ce wa xalinbansa, “Kuna so
ku ga ‘yar Aljanna?” Sai ya ce, “Wata
rana wata baqar mace ta zo wajen Manzon
Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ta
ce ya Manzon Allah ina fama da ciwon farfaxiya, ka roqa min Allah in
warke. Sai ya ce “In kin so in yi ma ki
addu’a ki warke, in kuma kin so ki yi haquri ki
mutu da ciwonki makomarki Aljanna. Sai ta ce a bar ta da cutarta ta mutu ta shiga Aljanna. Amma sai ta ce wa
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ya yi ma ta addu’a in tana
farfaxiyar ta daina yin tsirara, sai
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi ma ta
addu’a ta daina yin tsirara in
ciwon ya tashi ma ta. Don haka suka ce
qarfin Imaninta ya kai na ta qi shan magani.
2.
Sahabi Amru bn Asimim ya kasance ba ya
shan magani, in yana tafiya sai ya ji ana ma sa sallama sai ya tambayi Annabi
sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam cewa
bai san ma su yi ma shi sallama ba. A nan ne Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ya ce, “Mala’iku ne suke yi ma ka sallama saboda qarfin Imaninka.” Amma
wata rana da ya yi rashin lafiya ya yi magani sai mala’ikun suka daina yi masa Sallama, da kuma
ya sake daina shan maganin sai suka dawo da yi masa Sallamar.
3.
Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi
wa sallam ya ambaci wasu mutane dubu saba’in da za su shiga Aljanna babu hisabi,
cikin Siffofinsu ba sa shan magani.[20]
4.
Wani sahabi an sare shi a fuskarsa ranar uhudu har idonsa ya yi qasa zai faxi, sai
ya zo wajen Annabi Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya ce a yi masa addu’a.
Sai Annabi ya ce masa ya yi haquri da ciwonsa ya samu Aljanna, sai ya
ce yana son Aljanna amma a yi masa addu’a domin yana neman aure.[21]
5.
Lokacin da sayyidina Abubakar Sadiq bai da
lafiya an ce ma shi, “A kira ma ka likita? Sai ya ce haqiqa likita (Allah) yana
ganina, ni kuma zan yi abin da yake so ne”.[22]
Abubakar shi ne mafificin mutane a cikin wannan al,umma bayan Annabi sallal Lahu
alayhi wa alihi wa sallam sannan kuma shi shugaba ne kuma abin koyi ne. Wata ruwaya Manzon Allah sallal
Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Likita
shi ne Allah”.
Malamai
dai sun haxa dalilai wuri xaya suka ce babu laifi shan magani. Shi kuma al-Usaineen
ya ce akwai inda shan magani zai iya zama dole amma idan mutum yana da qarfin
imanin da zai iya qin shan maganin, to ya qi shan maganin shi ya fi. Sai dai a
lura cewa babu wanda ya hana shan magani, kuma ko ka sha magani kada ka xauka
cewa magani ne ya warkar da kai, Allah ne ke warkarwa ba magani ba.
A
mazhabar Ahmad ibn Hanbal Shan magani halas ne babu laifi in mutum ba shi da
lafiya ya sha magani, amma kuma a mazahabarsa barin magani shi ne ya fi daraja
kuma ya fi fifiko. Su kuma Shafi’iyya barin shan magani shi ne mafi alheri, har
ma Imamun Nawawi ya ce mazhabarsu wato
Shafi’iyya da Salaf baki xaya da Kalaf
barin shan magani shi ne mafi alheri in dai mutum zai iya. Abu Hanifa shi yana
ganin shan magani dole ne, amma kuma ita mazahabar Malikiyya tana ganin kana
iya shan magani kana kuma iya barinsa.[23]
Shi
kuwa babban Malami Ibn Taymiyyah cewa ya yi shan magani ba dole ba ne wannan
ita ce maganar jumhurun jagororin malamai. Ya ce waxansu ‘yan kaxan daga yankin
Hambali da Shafi’iyya ne suka wajabta shan magani.[24]
HUKUNCIN MAGANI DA ABIN
DA AKA HARAMTA.
Kamar yadda muka gani cewa Allah bai hana mu
shan magani ba, to amma kuma haramun ne yin magani da duk abin da aka haramta
mana. Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Kada ku fara ku yi
magani da abin da aka haramta ma ku”.[25]
Ka yi qiyasi a kan duk wani magani da ka san an haxa shi da abin da yake
haramun, to amfani da shi haramun ne. Misali kamar giya, wiwi, kashi, mushe,
jini, fitsari, da duk abin da ke sa maye ko abin da yake haramun ne babu ko
shakka haramun ne amfani da shi a matsayin magani. Manzon Allah sallal Lahu
Alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Allah
bai sa mana maganinmu a cikin abin da ya haramta mana ba, kuma Allah bai sa mana waraka a cikin abin da ya haramta ba.”[26]
Sahabi
Xariq ibn Suwaydi ya tambayi manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam
game da giya da suke amfani da ita a matsayin magani. Sai Annabi sallal Lahu
alaihi wa alihi wa sallam ya ce masa giya ba magani ba ce cuta ce.[27]
Ka na iya cewa duk maganin da yake bugarwa shi
ma ya haramta a gareka.
HUKUNCIN SHAN MAGANIN
DA KAFIRI YA BA KA.
Bayan
mun fahimci halascin shan magani da kuma zuwa neman sa, to yanzu abin tambaya a
nan shi ne shin ya halasta shan maganin da arne ya ba ka? Sheikh Usaymin ya ce
abin qyama ne kuma bai dace ba musulmi ya je wajen kafiri neman magani. Ya
cigaba da cewa domin shi kafiri ba abin amincewa ba ne, ya ce sai dai in lalura wato idan ya
kasance duk gari babu asibitin musulmi ko babu kyamis xin Musulmi sai ka je
wajen kafirin amana a matsayin lalura, a qarshe ya ce kafiri dai ba abin
amincewa ba ne, ya qara da cewa musamman wajen haihuwa bai dace kafiri ko kafira
ya ko ta amshi haihuwar musulma ba.[28] Shi
ibn Muflihi ya ce, “Taqiyudeen ya ce, ‘Idan Bayahude ko Kirista masani ne ga
likitanci sosai kuma amintattace ne al’umma sun yarda da shi, to babu laifi
musulmi ya je wajensa ya nemi magani tun da dai an amince masa.[29]
Faxakarwa: Babu
laifi mace ta duba namiji a matsayin lalura haka ya faru zamanin Manzon Allah
salla Llahu alayhi wa aihi wa sallam lokacin yaqi mata na sanya wa sahabbai
bandeji a raunukansu, kuma ya tabbata wata
Sahabiya mai suna Asshifa tana bayar da magani.
Yana da kyau mata su karanta likitanci domin taimaka wa addini domin
akwai baqin ciki halin da muke ciki yadda maza arna ke duba mata musulmai,
wannan abin takaici ne, ya kamata mata su share mana hawaye su yi qoqari su
karanta wannan farni.
LADDUBAN
ZIYARAR MARA LAFIYA DA
ABIN DA KE KAN
MAI JINYA DA LIKITA DA AN GUWAR ZOMA.
Kamar yadda muka gani a baya cewa ciwo daga Allah yake
kuma ciwo kaffara ne na zunubai, kuma mun ga cewa hatta manya-manya daga cikin bayin Allah
sun yi ciwo. Musulunci ya koyar da
komai domin hatta yadda a ke zuwa ziyarar/gaida mara lafiya manzon sallal Lahu
alaihi wa alihi wa sallam ya koyar da mu ladubban zuwa ziyarar/gaida da mara
lafiya. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa aihi wa sallam ya kasance yakan je
gaida mara lafiya kuma hadisi ya tabbata daga manzon Allah sallal Lahu alaihi
wa alihi wa sallam da ya ke nuna mana idan mutun ba shi da lafiya yana da haqqi
a kanka na ka je ka gaishe shi, muddin ba ka je ba ka tauye masa haqqinsa.[30] Manzon Allah sallal Lahu
alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku gaishe
da mara lafiya Musulmi, ku ciyar da abinci,ku ‘yanta wuyaye.” [31]
Hakqin
Musulmi ga Musulmi guda shida ne: Idan ya
haxu da shi ya yi masa Sallama,
idan ya kira ka ka amsa ma shi, in ya nemi ka yi masa nasiha ka yi ma shi, in
ya yi atishawa ya kuma ce Alhamdu lil Lah,
ka gasshe shi, in ya yi rashin lafiya ka je ka gasshe shi. Ya ce mai gaida Mara
lafiya yana tafiya a gavar Aljanna ne
har ya je ya dawo.[32]
Ga
ladubban kamar haka;
1. NIYYA KYAKKYAWA:
Domin dukkan ayukka ba sa ingantuwa sai da niyya.
Ana so niyyar ta zamanto kyakkyawa koda yaushe, mai zuwa ziyarar mara lafiya
ana so ya yi niyyar zuwa gasshe da mara lafiya domin Allah ba wai don wani abu ba,
a’a ya je ne domin samun lada wajen Allah, haka Annabi tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ambaci lada mai yawa ga wanda ya je gasshe da mara
lafiya domin Allah.[33]
2.
NEMAN IZINI: Ana so ka nemi izinin mara lafiyan kafin ka
shiga wajensa kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhari Ibn Abbas ya nemi izinin
shiga wajen Nana A’isha Allah ya qara mata yarda lokacin da ba ta da lafiya kafin ya shiga.[34] Kai
ma ana so ka nemi izinin mara lafiya kafin ka shiga wajensa ko da kuwa a asibiti, yayin da Ibn Abbas ya je gaishe da Nana A’ishatu Allah ya qara mata yarda, da
ya je ya nemi izinin shiga sai ta ce kada
ya shigo, sai aka gaya mata Ibn Abbas ne fa xan baffan Annabi
sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, sai ta ce kada dai ya shigo, da aka matsa
mata sai ta ce, “Ina tsoron in ya shigo zai yabe ni, amma ya shigo. Da ya
shigo sai ya ce mata, “yaya jiki?” kamar dai yadda a ka koyar da su, sai ta amsa
da cewa, “Muna fatar rahamar Allah kuma
muna tsoron azabarsa.” Sai Ibn Abbas ya ce, Haba ke da kike matar Manzon Allah
sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam! Ke ce fa wadda Annabi ya fi so, kuma ke
ce wadda aka saukar da aya kaza da kaza saboda ita.” Ya yi ta gaya mata kyawawan ayyukanta. sai ta ce, “Da ma
abin da na ke tsoro ke nan na ce kada ka
shigo, da ma na san sai ka yabe ni sai
ka yi ma ni Kirari.”[35]
Shi Ibn Abbas ya yi abin da Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi
umurni ne da a yi wa mara lafiya, ita kuma ta yi tawali’u ne kuma da ma tawali’u hali ne na
mutanen kirki, don haka babu kyau a rinqa tuna wa mara lafiya munanan
ayyukansa, haramun ne a je ziyarar mara lafiya kana a riqa tuna masa munanan
ayyukansa.
Abdullahi
ibn Umar lokacin da ya ke ciwon ajali Hajjaj ibn Yusuf As Saqafi ya nemi izinin ya shiga ya gasshe shi,
sai Abdullahi ibn Umar ya ce a ce masa ba ya so, ya taqura sai ya
shiga, da ya shiga ya yi sallama
Abdullahi bn Umar ya yi banza da shi.[36]
Bukhari ma ya kawo magana mai kama da wannan da ke nuna ladabin zuwa ziyarar
mara lafiya.[37]
Dattijon arziqi mafifici mai daraja a bayan
qasa bayan manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam Abubakar Siddiq, shi ma ya nemi izinin shiga
ya gasshe da Nana Fatimatu Allah ya qara ma ta yarda lokacin da ba ta da lafiya, ya yi
sallama Sayyina Ali xan Abi Xalib Allah
ya qara ma sa yarda ya fito sai ya ce
masa ya nema ma sa izinin shiga ya gasshe da Nana Fatimah, sai Ali ya shiga ya gaya ma ta Abubakar yana
neman izinin ya shigo ya gasshe ta, sai
ta ce ya shigo, shi kuma ya shiga ya gasshe
ta.
Ana so mai zuwa ziyarar
mara lafiya ya nemi izinin shiga kafin
ya shiga wajen mara lafiya.
3. Yin sallama:Yin sallama
kafin shiga wajibi ne kuma haqqinsa ne.[38]
4. Yi
masa Addu’a: Ana so in an je gasshe
da mara lafiya a yi ma shi addu’a, a ce masa
Allah ya kawo sauqi. Manzon Allah Sallal
Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya kasance in ya je gasshe da mara lafiya yakan yi
ma shi Addu’a sau uku.
5. A yi ma shi wasiya da haquri.[39]
6 A
tsaya wajen kansa a tambayeshi ya ya halin da ya ke kuma yaya jiki?[40]
7. A tambaye
shi me yake so ya ci? Idan har ba zai
cutar dashi ba, to sai a ba shi ya ci.[41]
8. A tava kansa (Goshinsa) ko hannunsa ko cikinsa
sai a ce ya ya jiki?[42]
9. A nuna ma shi cewa wannan ciwon mai sauqi ne
komai tsananinsa, kuma a nuna masa cewa zai warke in sha Allah haka Annabi
Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya ke yi wa duk wanda ya je gaidawa. Yana cewa da sauqi, to kaffara ne a gare ka in sha Allah.”[43]
10. Ana so a tuna masa
ayyukansa na alheri, babu kyau a tuna masa wasu munanan ayyukansa, alherinsa ake
so a tuna masa, hadisi ya zo a Bukhari.
11. Za a iya yi masa tofi
a wurin ciwon nasa, domin ya tabbata Annabi Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam
yana yi in ya je ziyarar mara lafiya. Ana
iya karanta wata addu’a kana a tofa masa wadda ta tabbata.
12. Ana
so a kira sunan mara lafiyan, kana a ce, “Ya Allah ka warkar da wane.” har sau
uku. Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya je gasshe da Sa’ad lokacin yana cikin
rashin lafiya, da Annabi sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya je sai ya ce,
“Ya Allah ka warkar da Sa’ad.”[44]
ya faxi haka har sau uku. Kai ma ana so ka kira sunansa sau uku kana ka ce
Allah ya warkar da shi har sau uku.
ً، اللهم اشف سعداً اللهم اشف سعداً،
اللهم اشف سعداً
13 Ba a so a daxe a wajen mara lafiya
domin kada ya qosa da kai, sai dai idan shi ne ya so da ka daxe saboda ka ga
alamar ya samu sauqi sosai. Xawus ibn
Kaysan ya ce, “Mafificiyar ziyarar mara lafiya ita ce wadda ba a daxe ba.”[45]
Imamul Awza’i ya ziyarci Ibn Sirin lokacin da
ba shi da lafiya, a tsaye ya tsaya bai zauna ba. Amma idan mara lafiyan ya nemi da ka daxe to ba bu laifi idan ka
daxen.
13. Ka ce wa mara lafiya
ya yi maka addu’a. Hadisi ya zo da yake nuna mana Addu’ar mara lafiya
kamar addu’ar mala’iku ce wajen amsawa, har ila yau yana da mahimmanci in ka je
gasshe da mara lafiya ka roqe shi ya yi maka addu’a.
14. Ana so ka tunatar da shi tuba wato ka ce ma shi
ya yi ta tuba ga Allah domin ana so Musulmi ya kasance mai tuba ga Allah koda
yaushe, domin an so Musulmi ya riqa yin tuba ga Allah.[46]
15. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam bai keve wani lokaci na daban ba wanda a wannan lokacin ne kawai za a je gasshe da mara lafiya ba, ya
kasance yakan je da rana yakan kuma je da daddare bai kuma keve wata rana ba ya
ce sai wannan ranar za a je ziyarar mara
lafiya ba, kai ko da wane lokaci za ka iya zuwa.Amma idan shi mara lafiyan ne
ya keve wani lokaci da za a je gasshe
shi, to shi ya san dalilin da ya sa ya keve wannan lokaci.
16. Wasiyya: Ana so a tunatar da shi wasiyya in bai rubuta
ba, ka tuna masa ya tabbatar ya rubuta. Rubuta
wasiyya ya tabbata mai lafiya ma an so ya rubuta wasiyya. Abdullah ibn Umar Allah ya qara masa yarda ya ce Mazon
Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
ya ce, “Babu wani haqqi da mutum yake da
shi da yake so ya yi wasiyya da shi ya kwana biyu face wasiyyarsa tana qarqashin
matashinsa.” A wata ruwayar Mazon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam cewa ya yi, “Ba siffar Musulmin kirki ba ce a
ce ya kwana dare biyu ba tare da wasiyya ba.”
17. Babu laifi
namiji ya je gasshe da mace mara lafiya amma ba zai tava
jikinta ba.
18. A
yi masa bushara da fatar samun lada. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ya je gasshe da wata mata sai ya
ce ma ta, “Albishir a gare ki ya ke Ummu
Ala’I, haqiqa rashin lafiyar musulmi tana
tafiyar da kurakuransa kamar yadda wuta
take tafiyar da dattin da ke jikin zinariya da azurfa.”[47]
19. YAWAITA
ZUWA ZIYARAR SA: kamar yadda Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa
alihi wa sallam ya kasance ya sa a yi wa
Sa,ad bn Ma,az bukka a masallaci lokacin
da aka ji masa rauni a yaqin Kandaq,
ya sanya akai masa
bukka domin ya sami halin duba shi lokaci bayan lokaci,[48]
20. Yi
wa dangin mara lafiyan wasiyya da haquri musamman ma idan rashin lafiyar ya
tsananta.[49]
21. Zuwa gasshe shi lokacin da ba zai zama mai
qunci a gare shi ba: Ahmad bn Hambal ya kasance da azumi
yana zuwa gasshe da mara lafiya da
daddare. Bai kamata mutum ya je ziyarar
mara lafiya da asubahi ba, Ahmad bn Hambal ya kasance ba ya son zuwa gasshe da mutum da tsakiyar
rana ya ce wannan ba shi ne lokacin gasshe da mara lafiya ba.[50]
22. Zuwa gasshe shi da qafa
ba a kan abin
hawa ba idan wajen babu nisa. Jabir bn Abdullahi ya ce, Manzon Allah sallal
Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya zo gasshe
ni da qafarsa ba a kan
doki ba, ba kuma a kan
Alfadari ba.”[51]
23. A
karanta masa wannan adduar sau uku (3):
24.
Ka ce masa ya karanta wannan adduar a wurin ciwon nasa ko wajen da ya ke
masa raxaxi zai karanta sau bakwai Bismillahin farko sau uku 3.[53]
باسم الله باسم
الله باسم الله، : أعوذ بعزة الله وقدرته من شر ماأجد وأحاذر"
15.
Ana so a tuna wa mara lafiya cewa makaruhi ne yin nishi irin nishin mara lafiya wanda aka san mara lafiya
ke yi, an karanta wa Imam Ahmad ibn Hambal cewa Dawus bn Kaysar al Yamani yana karhanta nishin mara lafiya ya ce wannan nishin kai kuka ga wanin Allah ne.
Da Imam Ahmad ya ji wannan maganar Dawus bai qara nishi ba har ya mutu.[54]
Waxannan
su ne ladubban zuwa ziyarar mara lafiya. Babu laifi don mace ta je ta ziyarci
mara lafiya kamar yadda Nana Aishatu ta je gasshe da Sahabi Bilal Allah ya qara
masa yarda, da ta je ta ce, “Ya ya jiki? Allah ya kawo sauqi.”[55]
Ummu Darda ta je ta gasshe da wani mutum mara lafiya
a masallacin Annabi sallal Lahu alayhi wa alih wa sallam shi ya sa Bukhari ya
yi babi a kan
halascin mace ta ziyarci namiji idan ba
shi da lafiya. Ya zo cikin Muwaxxa cewa
Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya je ya gasshe da wata mata
da ba ta da lafiya.[56]
Amma
idan ba’a aminci ma fitina ba wato babu
mamaki idan namiji ya je ziyarar mace ya iya ya fitinu to yana iya bari, ko
kuma ita in ta ziyarci namiji mara lafiya tana iya fitinuwa to tana iya bari,
kuma babu kevewa idan xayansu ya ziyarci xan’uwansa mara lafiya, babu kuma magana
mai tsawo domin gudun kada wani abu mummuna ya faru.[57]
SHIN YA HALASTA ZUWA GAISHE DA KAFIRI?
Lalle musulunci ya bai wa
kowa haqqinsa kuma ya koyar da mu yadda za mu yi mu’ammula tsakaninmu da wanda
ba musulmi ba. Babu laifi idan ka je gasshe da arne a yayin rashin
lafiyarsa, amma da sharaxin za ka jawo
hankalinsa zuwa musulunci. Kamar yadda
ya zo Manzon Allah sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam ya je gasshe da wani Bayahude da ba shi da lafiya, sai wanda
ya ke masa hidima ya bijiro masa da cewa ya musulunta. Sai yaron ya kalli
babansa, sai babansa ya ce masa, “Ka
amsa kiran Abulqasim!” Sai yaron ya musulunta. Manzon Allah sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam ya yi godiya ga Allah
da ya tserar da shi daga wuta. Kuma ya tabbata cewa ya je gasshe da Baffansa
Abu Xalib amma da yake Allah bai nufe shi da musulinta ba, miyagun da ke kusa da shi suka hana shi musulunta,
ya mutu ba musulmi ba. Imamul Bukhari ya yi babi da yake ce wa ‘Babin gasshe da Mushiriki’. Ibn Qaymul
Jauziyya ya nuna halascin zuwa ziyarar kafiri in ba shi da lafiya amma da
sharaxin za ka ce ma sa ya musulunta: Duba littafin nasa,[58] Ya
kawo hadisin Anas da ya ke bayar da labarin yaron da yake wa Annabi sallal Lahu
alayhi wa alihi wa sallam hidima ya yi fama da ciwo Annabi sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam ya je gasshe shi ya ce ma shi ya musulunta.[59]
ABUBUWAN
DA KE KAN
MARA LAFIYA.
1.
Haquri:
Duk wanda ciwo ya same shi ana son ya yi haquri ya
yarda da hukuncin da Allah qaddara a gare ka. Allah ya yabi masu haquri idan ciwo
ya same su. Duba fassarar wannan ayar a cikin baqara.[60]
ولنبلونكم بشئ من الخوف والجوع ونقص من
الا موال والانفس والثمرات وبشر الصابرين . الذين إذا أصابتهم مصيبة قالوا : إنا
لله وإنا إليه راجعو ن. أولئك عليهم صلوات من ربهم ورحمة , وأولئك هم المهتدون
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
ya faxa mana duk wanda ciwo ya same shi ya yi haquri to Manzon Allah sallal
Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce Allah zai ba shi Aljanna.[61]
2.
Babu laifi mara lafiya ya faxa wa waxansu
ciwonsa da nufin ya sami maganin ciwon,
ba laifi ne ba ya faxa wa likita ko abokinsa rashin lafiyarsa. Manzon Allah
sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya
faxa wa Ibn Mas’ud cewa shi yana ciwon mutune biyu ne.
3.
Ya nemi maganin ciwonsa babu laifi,
kamar yadda Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku yi
magani! Allah bai tava saukar da wata cuta ba face ya saukar da maganinta sai
dai ciwo xaya kawai shi ne tsufa.”[62]
4.
Ya rubuta wasiyya, Babu
makawa ana so mara lafiya ya yi gaggawar rubuta wasiyya. Kamar yadda adddini ya yi umurni da rubuta wasiyya
kuma wasiyyar nan ba a yin ta ga waxanda za su gaje ka. Idan mutum ya yi
wasiyya ga magada ya ce a ba su wani sashi
na dukiyarsa, to ba za a cika ta ba. Ko ya ce idan ya mutu a rufe shi a gida,
to ba za a rufe shi a gidan ba, domin
yin hakan sava wa shari’a ne. Muddun dai ya yi wasiyya da savon Allah to ba za
a yi ba, ana so ya rubuta wasiyyarsa da alheri kamar ya yi wasiyya da cewa duk
wanda ya yi masa abin da ya sava wa shari’a bai yafe ba, ya hana a yi masa kuka, ya rubuta sunayen waxanda
yake bi bashi da masu bin shi, da kayan da aka bashi na ajiya, da kuma wanda ya ke so ya yi masa sallah in ya
rasu, kamar dai yadda ta tabbata wasu sahabbai sun yi haka.
5.
Kyautata zato ga Allah.
ALAMOMIN RASUWA.
Allah maxaukakin Sarki
mai tausayi ne ga bayinsa kuma mai son bayinsa ne da rahama, yana daga cikin rahamarsa Ya sanya
ma bayinsa alamar Rasuwa idan ba su da lafiya, ko kuma Rasuwa ta zo masu za su
ga alamomi.
Idan mutum ya zo Rasuwa kuma a ka dace
na kirki ne, to zai ga mala’ikan Rasuwa,
idan mutumin kirki ne zai ga mala’ikun Rasuwa cikin siffa mai kyau yana riqe da likkafani na Aljanna da turare
shi ma na Aljanna, za su zauna wajen kansa iya ganin idon daga nan sai
mala’ikan Rasuwa ya zo ya zauna wajen kansa sai ya ce masa, “Ya wane! Ana maka
bushara da yardar Allah a gare ka (Allah ya sa mu cikin waxanda za a yi wa
wannan bushara). Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce zai
ga masaukinsa a Aljanna, sannan sai mala’ikan Rasuwan ya ce masa, “Ya ke wannan rai tsarkakakiya
fito ya zuwa rahamar Allah da yardarsa.”
Amma
idan wannan bawan Allah yana cikin mutanen banza ne wato xan-wuta, to zai
ga mala’ikan azaba cikin baqar fuska zai
zauna wajen kansa, kuma nan take zai ga
mazauninsa a gidan wuta. Sai
Mala,ikan Rasuwa ya ce ma shi, “Ya ke wannan rai mummuna! fito ana ma ki
bushara da fushin Allah da a zabarsa.”
Cikin
waxannan halayen ne wanda ya zo Rasuwa zai gani.[63]
ALAMOMIN DA MAI
JINYA ZAI GANI NA ALAMAR RASUWAR XAN’UWANSA
.
Mutane
sun sha bamban wajen Rasuwa, wani sa a
xaya ya bar duniya wani kuma yakan iya
sa’a biyu wani kuma yakan kai kwana biyu yana cikin gargara kafin ransa ya fita,
wasu kuwa sukan wuce kwana biyu. mafi rinjaye kuma abin da ya ke mabayyani shi ne mafi yawan waxanda suke cikin gargarar Rasuwa waxannan alamomin masu zuwa za su bayyana a gare su wanda yake
jinya in ya gansu
to wannan bawan Allah
shi ke nan
1.
Gefen diddigensa zai yi sanyi saboda rai
ta diddige yake fara fita. Idan mutum yana cikin gargara in ka tava diddigensa
za ka ji sanyi, in ka tava qwaurinsa za ka ji zafi, bayan wani lokaci diddigen
da qwaurin za su yi sanyi mai tsanani, daga baya cinya ta yi zafi.
2.
Hannunsa zai yi taushi sosai kai ka ce
auduga ce.
3.
Zufa za ta fara fita ta goshin in na
kirki ne.[64]
4.
Maganar da ba a fahimta saboda harshensa
ya karye.
5.
Wani sauti zai riqa fita ta qirjinsa.
6.
za a ga wani qulu ya zo maqogwaro.
7.
Gargara wato zuwan rai ya zuwa maqogoro.[65]
ABIN DA ZA KA YI, KAI
MAI JINYA GA MARA LAFIYA.
1.
Kyautata masa zato ta hanyar ambatonsa
da kyakkyawan zato.
2.
Kar a faxi komai a gaban mara lafiya sai
alheri, Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Idan kun je
wajen mara lafiya ko matacce kada ku faxi komai sai alheri domin mala’iku suna
cewa amin a kan abin da kuke faxa.”[66]
3.
Kiran sunansa a ce masa ya faxi kalmar shahada haka, sunna
ta koyar. Za a yi ta umartarsa har ya
faxa, idan ya faxa a qyale shi kada ya faxi wata maganar daban.
4.
Share masa fuskarsa da qyalle jiqaqqe da
ruwa.[67]
5.
Ba
a so a aje akwatin rediyo mai
hoto Talabijin [TV]
a wajen mara lafiya.
6.
Haka nan ba’a kunna rediyo kana a bar
shi, a yi ta tuna masa Allah dai.
ALAMOMIN KYAWAWAN CIKAWA.
Allahu
Akbar, Allah mai tausayi ne da rahama ga bayinsa, saboda tausayinsa da yake da shi
ga bayin ya sanya waxansu alamomi da wanda duk ya cika da xaya daga cikinsu to ana masa fatar
ya yi Rasuwa mai kyau kuma ana masa fatar samun Aljanna. Allah Sarki, ya kai bawan Allah ka yi murna da wannan bushara kuma ka yi fatar Allah ya ba ka xaya daga cikin waxannan
alamomi, ga su kamar haka;
1.
Faxar kalmar shahada: لا
إله إلا الله yayin
Rasuwa, akwai hadisai masu yawa da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam
ya ce wanda ya kasance kalmarsa ta qarshe لا
إله إلا الله
“La ilaha illal Lahu” xan Aljanna ne.[68]
2.
Rasuwa goshin mutum na zufa: Bureda ya ruwaito
hadisi ya kasance yana garin Khurasan
sai ya je gasshe da xan wansa yana fama da rashin lafiya. Da ya je sai ya ga
zufa na keto masa, sai ya ce, “Allah Sarki! Na ji Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi
wa salam yana cewa, “Mumini yana Rasuwa ne da zufa a goshinsa.”[69]
3.
Rasuwa Ranar Juma’a ko kuma daren
Juma’a.[70]
4.
Rasuwa a fagen fama, wato wajen yaqi
kamar yadda ya faru da sahabbai a Badr da Uhudu da dai sauran yaqoqi waxanda
sahabbai suka yi, Allah ma ya ambaci haka a cikin suratul Baqara da Ali Imrana.[71]
5.
Rasuwa a sanadiyyar ciwon ciki: Wanda ya
mutu sanadiyar ciwon ciki shi ma ana yi masa
fatar shahada ne.[72]
6.
Rasuwa ta sanadiyar Annoba da ta faxo wa qasa(kamar amai da gudawa,
da sanqarau, ko qyanda da sauran su) Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam
ya ce, “Annoba shahada ce ga kowane
musulmi.”[73]
7.
Rasuwa ta sanadiyyar gobara ko mota ta kama da wuta mutane su mutu.[74]
8.
Rasuwa ta sanadiyyar ruwa, wato ambaliyar ruwa ko ruwa ya cinye mutum a rafi. Ko kuma ruwa ne aka yi ya zama sanadiyyar Rasuwarsa.[75]
9.
Wanda kago (gini) ya faxo masa. (wato
yana xaki rufin xakin ya faxo masa, ko katanga ta faxo masa ya rasu)[76]
10. Matar
da ta mutu a sanadiyar haihuwa, ko wajen
haihuwa ta rasu.[77].
12. Rasuwa
wajen kare dukiyarka, xan fashi ya zo maka fashi ka mutu. Sanadiyyar kare
dukiyarka.[79]
13. Rasuwa
wajen kare iyalinka.[80]
14. Rasuwa
ta sanadiyyar ciwon dorina(bulala)[81]
15. Rasuwa
wajen kare kanka.
16. Wanda
ya mutu wajen kare addinin Allah.
17. Rasuwa
wajen dako (Ribaxi).[82]
Rasuwa
a kan aikin alheri.[83]
Misali Ana gama sallah sai mutum ya mutu ko kuma ana cikin yin Sallah, ko bayan
karatun qur’ani , ko bayan ladan ya gama
kiran sallah sai ya rasu
18. Wanda
wani shugaba azzalumi ya kashe shi.
19. Wanda
ya rasu mutanen kirki suka yi ma shi yabo na kirki.
20. Alamar
da za a gani wajen yi wa gawar wanka: Wato kamar a ga xan yatsansa
yana ishara da kalmar shahada, ko hasken
fuska ko murmushi fuskanrshin na yardar Allah da Aljanna , za ka ga mamaci yana
murmushi wanda bata buxe fuska lokacin wanka ko lokacin sanya masa likafani,
wani lokaci masu yi ma gawa wanka zasu sami sauqin wanke ta, ita ma ana sa ran
ta sami kyakkyawar cikawa.[84]
21. Matar
da ta mutu da ciki ana mata fatar
shahada, wasu malaman kuma suka ce budurwar da ta mutu tana son aure amma Allah
bai ba ta ikon yi ba ita ma ana mata fatar ta yi shahada[85]المرأة تموت بُجمع
شهيدة، ويقال بضم الجيم وكسرها وهي المرأة تموت حاملاً،
وقد جمعت ولدها في بطنها، وقيل: هي البكر، وصحح القرطبي والنووي
Waxannan
su ne alamomi na kyakkyawar cikawa. Duk wanda ya sami xaya daga cikin waxannan
ana yi ma sa fata ya yi Rasuwa mai kyau kuma ana masa fatar samun Ajanna. Allah ya ba mu Ajannatu Firdausi Amin.
ALAMUN MUMMUNAR CIKAWA.
1.
Mutum ya mutu kan shirka ko cikin Shirka ko rashin sallah
ko mutum ya mutu yana zina. Allah ya kare mu, ko mutum ya mutu yana shan giya
ko mutum ya mutu a mashayar giya ko Silma
ko yana jin kaxe-kaxe, Manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce
kowane bawa za’a tayar da shi a kan abin da ya rasu (Yake yi).
2.
Mummunar sheda da mutanen kirki za su yi
wa gawar kamar yadda sahabai suka yi wa wata gawa, daga nan ne sai Manzon Allah
sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya
ce wuta ta tabbata a gare ta.
3.
Mumin abin da masu wanka zasu gani wajen
yi wa gawa wanka.[86]
ABUBUWAN DA SUKE WAJIBI GA WANDA AKA YI MASA RASUWA.
Ya zama dole ga dangin mamaci su
riqi waxannan abubuwa;
1.
Haquri da yarda da qaddarar Allah, haka
Allah ya faxa. [87]
Haquri
a kan Rasuwar yaran ka/ki akwai lada mai yawa, musamman ma ga mata, ladar ta fi
yawa kuma a kan su ne hadisi ya zo qarara,
Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Duk matar da yaranta
guda uku suka mutu, za su kasance a gare ta garkuwa daga shiga wuta, sai wata mata
ta ce ko da yara biyu ne? Sai Manzon
Allah Sallal Lahu alayhi wa aihi wa salam ya ce ko da yara biyu ne za su zama
hijabi ne a gare ki daga shiga wuta.[88]
Wannan kariyar daga shiga wuta za ta samu ne
da sharaxin
kin yi haquri, amma in kika kasa yin haquri
kika faxi maganganu na rashin kirki da fitsara da surkulle da shiga wajen bokaye, to ba ta cikin wadanda
Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ambata.Kuma duk mai yin haka tana cikin fushin Allah da bala’i.
2.
Abin da yake wajibi ga dangin da aka yi wa
rasuwa shi ne fadar
إنا
لله وإنا إليه راجعون اللهم اجرني في
معيبتي وأخلف لي خيرا منه
3.
Sai a kira sunan mamaci sannan a yi masa
addu’a kamar yadda A Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi a lokacin da Abu Salma ya rasu.Sai
ka ambaci sunansa a inda aka bar alama. [89]
: اللهم اغفر **********، وارفع درجته في المهديين، واخلفه في عقبه
في الغابرين،واغفر لنا وله يا رب العالمين،وافسح له في قبره ،ونور له فيه
Babu
laifi a buxe fuskar wanda ya rasu a
sunbance shi a kira sunansa a yi masa addu’a. [90]
TAKABA.
Mata
suna yin takaba idan xaya daga cikin waxannan nata suka rasu;
1.
Mijinta.
2.
Babanta.
3.
Xanta.
Na
farko shi ne wajibi idan mijinta ya rasu
za ta yi takaba na wata huxu da kwana goma kamar yadda Allah ya faxa a cikin suratul
Baqara, mace mai takaba ba za ta yi
waxannan abubuwan masu zuwa ba.
1.
Babu sanya tufa mai kala/launi.
2.
Babu sanya ko shafa turare ko da turaren
wuta ne ba zata kunna shi a xakinta ba.
3.
Babu sa tozali. (sai dai in magani ne ko
lalura)
4.
Babu qunshi.
5.
Babu sanya gazar.
6.
Babu sanya jan-baki.
7.
Babu sanya hoda.
8.
Ba za ta shafa man shafawa mai
qamshi ba sai lakuci sharva.
9.
Ba za ta yi kitso ba.
10. Babu sanya sarqa ko zobe, dukkansu haramun ne
a gare ta.
Za
ta bar waxanan abubuwan ne na tsawon wata huxu da kwana goma,
amma ga mijin ne kawai za ta yi na tsawon wata huxu da kwana goma, amma idan
xanta ne ko babanta na kwana uku ne kawai za ta yi, amma ba dole ba ne, idan ma da za ta bar yin takabar ga xanta da
babanta hakan ya fi dacewa kuma an fi son haka duk da cewa ya halasta ta yi
takabar. [91]
Babu
wani abu wai shiga takaba da mata suke yi ko bikin fita takaba ko karatun takaba
wannan duk aikin jahiliyya ne ta maguzawa kuma bidi’a ce da za ta iya kai mata
ya zuwa ga shirka. Akwai kuma wata shirka da ake sa mata na kwanciya da wuqa ko
takobi, wai kada mijinta ya yi mata fatalwa, kai wannan da ji ka san surkulle
ne kuma shirka ne, da yawo da buta wai mijin yana bin sanyin butar, wannan duk surkulle
ne da zai kai mutum ya zuwa ga shirka. Mata a gidajen mazajensu suke yin takaba
musulunci ne ya ce mace ta yi takaba a xakin aurenta idan mijinta ya rasu.
ABUBUWAN DA SUKA KAMATA GA MACE
IDAN XANTA KO BABANTA YA RASU.
1.
Saduwa ya halasta idan xanku ya rasu ku
sadu saduwa ta aure babu laifi, yin haka ma shi ne abin da ya fi dacewa in
buqatan haka ta taso, haka ya faru lokacin Manzo Allah sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ga Ummu Sulayman da mijinta Abu Xalhatul Ansari, xanta ya rasu kuma
suka yi saduwar aure har Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi ma su
addu’a Allah Ya sa albarka ga saduwarsu. Kuma Allah Ya
amshi addu’ar Ya sa albarka a wannan
saduwar.[92]
2.
Yin kwalliya in da buqata.
ABUBUWAN DA SUKE HARAMUN NE AIKATA SU IDAN AKA YI WA MUTUM RASUWA.
Manzon
Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya haramta waxannan abubuwan ga duk
wanda aka yi ma sa rasuwa ya zama haramun ne a gare shi ya aikata
su, idan ya aikata xaya daga cikin su to mutum ya sava wa Allah da Annabi
Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam kuma yana janyo wa mamacin musiba ne da
bala’I, ‘yan’uwa ya kamata a kiyaye.
1.
Kuka wanda ke jin muryar mutum tana xagawa
yana kuka da qarfi. Babu kyau idan an yi wa mutum Rasuwa ya yi kuka yana xaga
murya, wannan haramun ne. Amma kuma wanda babu xaga murya ya halasta. Shi ne
wanda hawaye yake fitowa, ana kiran irin wannan kukan “Yavune”
wannan babu laifi yin haka, yin haka ma alama ce ta tausayi. Wani Hadisin
Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce ana yi wa matacce
azaba a cikin qabarinsa sakamakon kukan da aka yi masa.
2.
Dukan kumatu da yayyaga riga shi ma Manzon Allah
Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya hana. Ya ce ba shi tare da ni wanda
aka yi masa Rasuwa ya rika dukan kumatunsa ya kuma yaga tufarsa yana maganganu
irin na jahilan farko.
3.
Aske gashin kai (qwal-kwabo[93]).
Wani idan aka yi ma sa Rasuwa sai ya aske gashin kansa domin baqin ciki, wani
kuma aske gemunsa yake yi, shi ma yin haka haramun ne[94].
4.
Barin gashin kai na wasu kwanaki saboda
baqin ciki.
5.
Barin gemu na wasu kwanaki saboda an yi
ma sa Rasuwa. Daga baya ya aske.
6.
Sanar da Rasuwa a cikin amsa-kuwwa ta
masalaci “Loud speaker”.
7.
Faxin Rasuwa a gidan radiyo, tare da
ambatar irin xaukaka ko darajar da Allah Ya yi wa wanda ya rasu da faxin yawan
yaransa, ko a shiga kasuwa ana faxi, “Wane xan wane mai yara kaza da kaza ya
rasu.”
MATASHIYA.
Ya
halasta a faxi Rasuwar mutum domin a samu waxanda za su zo su yi mashi sallah kamar
yadda Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya sanar da Rasuwar Najashi[95] Sarkin
Habasha, ya ce a fito a yi ma sa sallah.
Haka nan ma ya sanar da rasuwar Sayyidina Ja’afar yayin da ya yi shahada a yaqin
Mu’uta ya ce a roqa ma sa Allah, kuma a duk sa’ilin da ka faxa wa wani Rasuwar xan’uwanka
ka ce ma shi ya yi ma sa addu’a kamar yadda Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam yake yi wa sahabbansa.
ABUBUWAN DA AKE YI WA MUTUM MUSULMI DA ZARAR YA RASU.
Da
zarar xan’uwanka/ki ya rasu ana so a yi
ma sa waxannan abubuwan masu zuwa:
1.
Rufe masa idanuwansa kamar yanda Manzon
Allah Sallal Lahu alyhi wa alihi wa salam ya yi wa Abi Salamah.[96]
2.
Yi ma sa addu’a tare da kiran sunnansa a
yi ma sa addu’a.[97]
3.
Rufe masa gaba xayan jikinsa kamar yadda Nana Aisha ta faxa mana
cewa haka aka yi wa Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam da ya rasu aka rufe gaba xayan jikinsa, babu
kyau a bar gawa a buxe.[98]
4.
Gaggawar shirya shi na yi ma sa wanka da
yi ma sa likkafani.[99]
5.
Cire ma sa kayan jikinsa da gaggawa.
6.
Xora shi a kan karan-gado ko gadon katako ko dai wani
abu mai bisa, kada a bar shi a qasa. Ga misalin gawa kafin wanka kamar haka:
7.
Miqar da gavovinsa da yatsunsa na hannunsa.
8.
Xaure gemunsa da qyalle kafin a je yi ma
sa wanka, ana yin haka ne don gudun kada ya kunbura.
9.
Xaura wani abu mai nauyi a cikinsa don
gudun kada ya kumbura.[100]
10. Gaggawar
biya ma sa bashi.[101]
11. Istirja’i
wato faxan إنا لله وإنا إليه راجعون اللهم اجرني في مصيبتي وأخلف لي خيرا
منها
12. Ambatar
alherinsa.
13. Faxa
wa dangi rasuwarsa babu laifi.
14. Babu
laifi a jira har danginsa su haxu domin samun yawan Jama’a.
15. A
yi saurin zartar da wasiyyarsa.
LADUBBAN WANKAN GAWA.
Musulmi
yana da tsari, hatta yi wa gawa wanka sai da aka nuna mana yadda za a yi, da sharuxxan ta. Ga sharuxxan wankan gawa kamar haka:
1.
Ya kasance Musulmi, kafiri haramun ne ya
yi wa Musulmi wanka.
2.
Mai hankali banda yaro.
3.
Mai sirri kuma amintacce, banda mai surutu
mara sirri.
4.
Masani game da hukunce hukuncen wankan
gawa.
5.
Ya kasance yana yi ne domin
neman yardar Allah.
6.
Namiji ya wanke namiji, bai halatta
namiji ya wanke mace ba sai dai in matarsa ce ko mahaifiyarsa ko ‘yarsa.
7.
Mace ta wanke mace, bai halatta mace ta yi
wa namiji wanka ba sai dai in mijinta ne ko babanta, ko xanta ko dai wani muharraminta.
Idan kuwa ba haka ba sai dai a yi masa taimama.[102]
Waxannan
su ne sharuxxan wankan gawa kuma haka sunna ta koyar: Miji ya wanke matarsa mata ta wanke
mijinta ko ‘ya‘yanta ba wani ba, haka
bai halatta wani ya yi wa mace wanka ba in dai ta kai shekara bakwai haka
Usaymin ya ammbata.[103]
Kuma
wannan ya nuna mana rashin asalin qeve wasu tsofaffi domin yi wa gawa wanka
waxanda ba su san komai na yadda ake wanka ba sai shirme da surkulle da shirka,
ya kamata a kula da kyau don Allah, yana da kyau a riqa sanya waxanda suke da hakqin yin waka kuma suka san
yadda sunna ta koyar.
WAJEN DA AKE YIN WANKAN GAWA.
1.
Wajen ya kasance mai tsarki mai tsafta,
bai halatta a yi wa matacce wanka a bayi ba, Yi masa wanka a bayi Wulaqanta
gawar ne da kuma cutar da mala’iku Allah.
2.
Wurin ya kasance sitirtacce kuma ya kasance
rufaffe. ana so wurin ya kasance mai sirri. Babban tabi’i ibn Sirin ya ce mustahabbi ne xakin da za’a yi
wa gawa wanka ya kasance rufaffe, mai duhu yadda ba za a ga al’aurar gawar ba. Ya kasance dai xakin rufaffe ba mara rufi ba,
ba kuma fili ba, ba a yi a tsakar gida.
3.
Ya zamanto xakin babu hoton duk wani abu
mai rai domin mala’ikun rahama ba sa shiga xakin dake da hoto ko kare.[104]
4.
Sannan wurin ya kasance ba kowa zai iya
zuwa ba sai dai wanda ake da buqatarsa.[105]
ABUBUWAN DA AKE BUQATA DOMIN YI WA GAWA WANKA.
1.
Ruwa ya
kasance mai tsarki kuma na halas.
2.
Ruwan ya kasance matsakaici tsakanin
sanyi da zafi.
3.
Magarya dakakkiya (garin magarya)da shi
za a yi wanka na biyu.
4.
Kafur shi ma ya zama dakakke (gari) da shi
za a yi masa wanka na uku.
5.
Miski (Turare).
6.
Sabulu.
ABIN LURA KAFIN YIN
WANKA.
1.
A tabbatar da Rasuwar gawar.
2.
A xaura gawar a wani abu mai tudu kamar
gadon qasa ko karan-gado (Gadon Kara) ko gadon katako ko gadon da aka cire
katifa. Ya kasance dai a sama ba a tandarqin qasa ba ko tabarma.
3.
A kunna turaren wuta wato turaren qanshi
a xakin wankan gawar.
4.
Suturta gawa (wato a sami wani qyalle a
rufe gabanta (ala’urarta) ba a so a bar ta tsirara, ya kasance tun daga cibiya
har gwiwarta a suturce.
5.
Ya kasance sun kai su biyu zuwa uku: Wato mai wankan daban mai
zuba ruwa daban da kuma mai juya ta.
6.
Mai wankan ya sanya wani kyalle a
hannunsa kamar safar hannu ko wani abu
mai kama da shi kamar irin safar da likitoci
suke amfani da ita.
7.
Mai wankan ya yi a hankali cikin
tausasawa da jinqai
8.
A tabbatar an cire kayanta (gawa) da zarar
ta rasu, idan ya qi ciruwa babu laifi in an yanke kayan jikinta da reza ko
almakashi.
9.
A yi qoqarin miqar da gavovin gawar
cikin gaggawa.[106]
10. Ba’a
tava farji mace idan dai ta kai shekara bakwai, sai dai in matarka ce.[107]
Idan
gawar ta daxe da rasuwa gavovinta sukan sassandare misali kamar qafarta ko
hannunta, za’a miqar da su, yadda, ake miqar da su kuwa shi ne a samu ruwan
xumi ana mammatsa gavarta da tattanqwara
su (gavovin) a hankali ana yi a hankali
har su mimmiqe.
WAXAN DA SHARI’A TA YARDA
A YI MASU WANKA IDAN
SUN RASU.
1.
Muslumi: Idan Kafiri ya mutu ba’a yi masa
wanka.
2.
Yaro.
3.
Jariri.
4.
Vari in dai ya kai wata huxu zuwa Sama da
haka.
5.
Mahaukaci in dai musulmi ne.
6.
Karuwa.[108]
7.
Wanda ya mutu wajen aikin haji.
8.
Mashayin giya.
9.
Wanda ya kashe kansa amma liman da
mutanen kirki ba za su yi ma shi wanka
ba, ba kuma za su je wajen sallarsa ba.[109]
WAXANDA BA A YIN MASU WANKA.
1.
Shahidi ko da ya mutu da janaba.[110]
2.
Varin da bai kai wata huxu ba.
3.
Wanda ya qone quna mai tsanani ko haxari
ya radaddage. Waxannan ba a yi ma su
wanka.[111]
FAXAKARWA.
Idan
mutum ya rasu da zobe ko haqorin Hajji a bakinsa za’a cire shi.
Sheik
Usaymin yana ganin babu laifi idan mutum ya rasu a yanke masa qumbarsa, a kuma yanke masa gashin hammata da na mara da kuma
rage ma shi gashin baki. [112]
An
samo hadisi daga Abu Ka’ab ya wanke gawa sannan ya ce a kawo ma shi aska ya
aske ma gawar gashin hammatarta.[113]
Amma banda gemu domin aske gemu haramun ne.
Sahabi Khubab ya aske gashin hammatarsa kafin
a kasha shi.[114]
KWANCE KITSON MACE KAFIN WANKA.
Hadisi
ya tabbata daga Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa aihi wa sallam ya yi umurni
da a kwance gashin kan
‘yarsa Zainab,Ummu Adiyah ta ce mun kwance gashin kanta sannan muka yi mata kitso
guda uku a kanta.[115]
Don
haka idan mace ta rasu, to gabanin a yi
mata wanka sai an kwance gashin kanta an tsefe shi wato an taje shi sannan a yi mata kitso guda uku, kamar yadda hadisin Ummu
Adiyah ya nuna, za a yi guda xaya ya nufi bayanta.
SAMFURIN WANKAN GAWA.
Kamar
yadda muka gani wajibi ne idan mutum ya rasu a yi masa wanka, ana iya yi kamar
haka duk wanda ka yi a cikin waxannan nau’o’in ya yi;
1.
Sau Uku.
2.
Sau biyar.
3.
Sau bakwai.
4.
Ya kasance dai mara kamar yadda Manzon
Allah Sallal Lahu alaihi wa alaihi wa sallam ya ce ma masu yi wa Nana Zainab wanka,
ya ce, “Ku wanke ta sau 3 ko 7 ko fiye
da haka in an ga buqatar yin haka.”[116]
YADDA AKE WANKAN GAWA.
1.
Za a kawo bokitin ruwa guda uku
a aje in mun zavi guda uku. Kamar yadda yake cikin ladubban wankan gawa a xora shi
a kan wani abu mai tudu bayan an sa ta a kan gadon katako ko wani
abu mai tudu sai a kwantar da gawar a rigingine wato fuskarta na kallon sama
bayan an tuve ta. Sai dai kada a manta da rufe al‘aurarta daga cibiya zuwa guiwa,
kuma mai wankan kar ya manta da safar hannu ko wani kyalle da zai rufe hannunsa
da shi .
2.
Daga
nana sai a xan xaga kanta kaxan kamar za a zaunar da ita sai a mammatsa cikinta a hankali har sau uku, daga
cibiya zuwa kirji, za a matsa ana yin haka ne idan akwai wata najasa a cikinta to
za ta fito. Daga nan sai mai wankan ya sanya qyale a hannunsa na hagu ya wanke wannan najasar, bayan ya
wanke najasar sai ya yi mata tsarki. Ga yadda za ka yi kamar haka:
3.
Sai a yi mata alwala ta sallah, za a
fara da faxar بسم الله “Bismillah”
yadda dai a ke alwala ta sallah, sai dai
wajen wanke bakin da shaqa ruwa za a sanya tsumman nan jiqaqqe da ruwa ya goge haqoranta da shafa
hancin ana goge cikin hancin.[117]
4.
Bayan Alwala sai a wanke kan gawar zuwa wuyanta
sau uku, sai dai a tabbatar an sa ruwa a
kanta sosai.
5.
Sai vangaren jikinta na dama wato a kasa
jikinta gida biyu a fara wanke vangaren dama daga nan sai na hagu, za a fara ne
tun daga qafar gawar har zuwa qafafuwanta baki xaya. Ita ma qafar hagu kamar yadda aka yi wa na dama, wannan an gama da bukiti na farko ke nan.
6.
A bokiti na biyu wato wanka na biyu sai
a kawo dakakkiyar magarya wadda aka daka tun daga farko a sanya a cikin ruwan a
kaxa sosai sai ya yi kumfa sannan sai a xebi kumfar da ruwan a wanke kan gawar da wuyanta sau
uku. Daga nan sai a wanke sauran jikin, kada a manta za a fara daga vangaren
dama ne daganan sai na hagu.
Idan
ba a samu magarya ba babu laifi a yi amfani da sabulu mai qanshi a yi mata
wanka da shi (gawar).[118] .
7.
A bokiti na uku za a sanya kafur bayan
an mayar da shi gari, sai a zuba a cikin ruwan wankan sai a yi mata wanka da shi kamar yadda aka yi bokiti na biyu. Idan kuma
ba a samu kafur ba sai a yi amfani da turare mai qamshin gaske. Bayan kuma an gama
mata sai a fesa mata turare.[119]
Anfanin
kafur shi ne domin ya na sanya jikin gawa ya yi tsabta da qamshi.
Idan
kuma aka zavi a yi mata (gawar) wanka biyar ne to haka za a yi yadda aka yi wa
mai guda uku, idan ma bakwai ne to duk dai haka za a yi. (wato a na huxu sai a
sa magarya, na biyar a sa kafur ko kuma a jinkirta sanya kafur sai a qarshe (wallahu a alam).
8.
Kada a manta idan mace ce gawar za a kwance
kitsonta a fece shi, bayan kuma an gama wankan sai ai yi mata kitso guda 3 a
jefa kitson bayanta (qeyarta). Wasu Malaman sun ce ana iya yanke qumbar gawar
da rage gashin baki amma banda gemu domin aske gemu haramun ne, kana raye ko
bayan ka mutu. bayan askin sai a sanya abin da aka yanke cikin likafanin. [120]
Ibn Abi Shaybah ya kawo abin da ke nuna halascin yanke wa gawa qumba
da rage mata gashin baki da haxasu a cikin likafani a rufe shi da ita.[121]
Matar
da ta rasu tana cikin al‘ada wanka xaya za a yi mata.[122]
FAXAKARWA.
·
Idan gawar kuturwa ce kuma kuturtar ta yi
muni, toba sai an yi mata wanka ba. A maimakon haka sai a yi mata taimama a maimakon
wanka. Taimama kuwa hannu da fuska kawai ake shafawa. Haka hadisai suka nuna
musamman hadisin Ammar ibn Yasir.[123]
·
Idan ba ruwa sai a yi wa gawar Taimama.[124]
·
Babu laifi mai janaba ya yi wa gawa
wanka.
·
Idan gawa ta kumbura ko wani sashi a jikinta ya
fara yagewa, sai a yi mata taimama. Ko kuma quna ce mai muni gawar ta yi, ita
ma ba sai an yi mata wanka ba, sai a yi mata taimama kawai ya wadatar.
·
Wanda ya rasu jini na zuba a jikinsa
babu laifi a sa magani domin jinin ya
tsaya, ko a sa bandeji ko kuma wani tsumma.
·
Idan mace ta rasu alhali kuwa babu mata
sai maza, to bai halasta mazan nan su yi mata wanka ba. Haka nan ita ma
da namiji zai rasu kuma babu maza, alhali kuma su matan ba muharraman sa ba ne,
to su ma ba za su yi masa wanka ba sai dai su yi masa taimama. An samo Hadisi, “Manzon
Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘Idan namiji ya rasu cikin mata
babu maza, ko mace ta rasu babu mata, taimama za a yi masu a je a rufe su suna matsayi wanda bai samu ruwa ba ne.’” [125]
·
Idan mutum ya rasu a ka je aka rufe shi ba a yi masa wanka ba, jumhurun
malamai da mazahabar Malikiyya da Hannafiyya da Hamabaliyya da Daud da ibn
Hazam sun ce a je a tono shi a yi masa
wanka matuqar dai bai canza ba (Wato bai yi wari ba).[126]
MACEN DA TA RASU TANA DA CIKI.
Idan
mace ta rasu da ciki kuma cikin ya wuce wata biyar, to ana sa ran abin da ke cikin
ya na da rai. Don haka ya halasta a fexe cikin a xauko jaririn kafin a yi mata
wanka. Amma idan an tabbatar ba shi da rai, to ba za a fexe ta ba. Sai dai kuma
idan yana da rai za a fexe ta a xauko jinjirin domin tsirar da rai.[127] Wannan
kuma ita ce mazahabar Abu Hanifa da shafi’i da Ahmad ibn Hambal da wani
vangaren malikiyya.
WANDA YA YI WA GAWA WANKA SHIN SAI YA YI WANKA?
An
so wanda ya yi wa gawa wanka shi ma ya yi wanka amma fa wannan wankan ba dole
ba ne mustahabbi ne. Hadisi ya zo daga ibn Abbas ya ce, “Manzon Sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam ya ce, ‘Ba dole ba ne a kan ku don kun yi wa gawa wanka a ce
sai kun yi wanka, domin matacce ba najasa ba ne. Ya isar maku idan kuka wanke
hannunwanku’. [128]
Saboda
haka mustahabbi ne in an yi wa gawa wanka a kuma yi wanka, amma ba dole ba ne. Wani hadisin cewa ya yi wanda ya yi wa gawa wanka shi ma ya yi wanka,
wanda kuma ya xauki gawa to shi ma ya yi alwala.[129]
Shi
ma wannan hadisin bai nuna wajabci ba kamar yadda malamai suka yi bayani. Abu Ammar
ma haka ya ce: Ba dole ba ne mustahabi ne.
Wajabcin da ke cikin hadisin shi ne wanda malaman Usul fiqhu suke ce masa Wujubul Istihibab.
BIDI’O’IN WANKAN GAWA.
1.
Keve waxansu tsofaffi da sunan wai su ne
kawai za su yi wa gawa wanka kuma ba su san yadda ake yin wankan a shar’ance ba,
sai surkulle da maganganu waxanda suka sava wa shari’a. Ya kamata ‘yan’uwa mu
kiyaye idan an yi rasuwa mu hana irin
wanxannan tsofaffi yin wanka tunda ba su
iya ba, kuma ba
su ke da alhalkin yin wankan ba. Mu tabbatar an yi wa mamaci wanka yadda shari’a ta nuna.
2.
Sanya
kanwa wajen yi wa gawa wanka wannan kuskure ne babba kuma sava wa sunna ne.
3.
Yi wa gawa wanka a bayi haramu ne.
4.
Kunna fitilla a xakin da aka yi wa gawa wanka
na kwana xaya ko biyu ko uku shi ma bidi’a ne.
5.
Yin zikiri yayin yi wa gawa wanka.
6.
Barin gashi ba a kwance ba da qin yi wa
gawa kitso guda uku idan mace ce.kuma laifi ne mai girma.
7.
Shan ruwan da aka yi wa gawa wanka
wannan yana iya zama shirka.
8.
Shafar kwano ko kwatanniyar da aka yi
wankan gawa da sunan wai neman tubarraki wannan shirka ce, Allah ya kyauta.
Waxannan
dukkan su haramun ne a yi su lokacin yi wa gawa wanka ko bayan an gama yi mata
wanka. Sannan bayan an gama wankan sai kuma sanya wa gawa likkafani, to shi ma
manzon Allah sallal Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya koyar da yadda ake yi. Ga
yadda ake sa likafani kamar haka:
LIKAFANI.
Likafani
shi ne suturar da ake wa mamaci bayan an gama yi masa wanka. Wajibi ne a sanya
ma gawa likafani, Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam ya faxa ga
wanda ya faxo a wajen aikin Hajji ya rasu. Ya ce ku yi masa likafani da kayan
jikinsa domin zai tashi yana mai talbiyya ranar Qiyama.[130]
Musad
bn Usman shi ma an yi masa likafani da kayan jikinsa bayan ya yi shahada a yaqin
Uhudu.
A
wata ruwayar Manzon sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku riqa sanya
fararen tufafi kuma ku yi likafani da
shi (farin tufafi)”.A taqaice muna iya cewa likafani wajibi ne a kan Musulmi
namiji ko mace idan xan uwansu ya rasu su yi masa likafani, haka maganar Annabi
Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ta
nuna.[131]
Ana so likafani ya kasance ya cika waxannan sharuxxan masu
zuwa;
1.
Ya kasance fari, haka Annabi Sallal Lahu
alaihi wa alihi wa sallam ya ce, “Ku rinqa sanya fararen tufafi domin farin
tufa shi ne mafi alherin tufa. Kuma ku yi wa matattunku likafani da farin
tufafi ’’.[132]
2.
Likafani ya kasance guda uku. Haka aka yi wa Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam.[133]
3.
Ya kasance na auduga.
4.
Ba a yi wa gawa hula da riga da rawani. Haka
hadisin Nana A’isha Allah ya qara mata
yarda ya nuna, kuma ba a yi wa Manzo Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam hula da riga
ba da ya rasu. Su ma sahabbansa ba a yi masu ba, don haka yin hula da rawani da
riga ba
karantarwar Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ba ce.[134]
5.
Ya kasance mai tsabta kuma kyakkyawa.[135]
6.
A sanya ma likafanin turare bayan an gama
sanya likafanin, kamar yadda sahabi ibn Umar da ibn Abbas suka yi wasiya da a
sanya ma likafaninsu turare.[136]
7.
Kada yadin ya kasance na alfahari domin
Allah ya hana alfahari.
8.
Idan da hali xaya daga cikin likafanin
ya zama Saqaqqe.
Idan ba’a sami sabo ba sai a wanke tsoho
a yi amfani da shi babu komai lalura ce. Ana amfani da tsohone a matsayin
lalura. Kuma idan ba a samu wanda zai rufe masa jikinsa baki xaya ba sai a rufe
fuskarsa, a sa ciyawa ko ganye a qafarsa, haka Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ya yi umurni da a yi wa Mus’ab
ibn Umair a lokacin da ba a samu likafanin da zai rufe masa jikinsa baki xaya ba.[137]
Wanda
ya rasu a wurin aikin Hajji za a yi masa likafani ne da kayan jikinsa.[138]
TANADIN LIKAFANI TUN GABANIN
RASUWA
Mun
san ba a yin likafani sai bayan rasuwa, to amma bai zama laifi ba in aka tanaji
likafanin tun ana raye. Irin haka ta faru a zamanin Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam, bai kuma hana ba. Wato a
lokacin da wani sahabi yake zaune a gaban Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa
sallam, sai wata mata ta kawo masa wata riga saqaqqiya ta ce, “Na
saqa ta ne domin in tufatar da kai ita.” Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam,
ya karve ta yana mai buqatar ta, ya shiga gida ya sanyo ta. Dagan an sai wani
sahabi ya nuna buqatarsa. Sai Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
ya ba shi ita. Sai Sahabbai suka nuna abin
da wannan sahabi ya yi bai kyautu ba. Sai
shi kuma ya ce yana so ne ta zama likafaninsa.
Sahal ya ce ita ce kuma ta zama likafanin
nasa. [139] Shi ma Sa’ad ibn Abi wakkas ya aje bargon da
ya je yaqin Badar da shi ya ce shi ne yake so ya zama likafaninsa.
Bai
zama laifi ba in ka tanaji likafaninka tun kana raye. Imamul Bukhari ya yi babi
musammam a kan
halascin ajiye likafani tun ana raye.
A KAN WA SAYEN LIKAFANI YAKE?
Sayen
likafani yana kan
dukiyar wanda ya rasu ne ko da kuwa matarsa ce. Wannan ita ce magana
tabbatacciya. Haka nan ma da mace mai aure za ta mutu, to sayen likafaninta za a
yi shi ne a cikin dukiyarta ba a cikin dukiyar mijinta ba. Haka nan ma qabari
shi ma cikin dukiyarta za a biya kuxin gini.[140]
Amma da za a
samu waxansu jama’a su sayi likafani su bayar don Allah, to shi babu laifi.
Kuma muna yi masu fatan alheri shi ma mijin idan ya saya a cikin dukiyarsa duk
babu laifi, amma ba dole ba ne a ce sai ya saya, don ba haqqinsa ba ne.
Haka
nan da mace za ta rasu a wajen aikin Hajji, to da kayan jikinta za a yi mata
likafani kamar yadda aka yi wa wanda ya faxo wajen aikin Hajji a zamanin Manzon
Allah Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam. Usaymin yana da fahimtar cikin
dukiyar mamaci za a xauka a saya masa likafani ba cikin dukiyar wani ba.[141]
YADDA AKE SANYA LIKAFANI
Babu
bambanci tsakanin mace da namiji wajen likafani. An yi wa Manzon Allah Sallal Lahu
alaihi wa alihi wa sallam likafani guda uku (3) ne, sahabbansa sun zavi yin uku
ne saboda sun san shi ne karantarwar sa tun
yana raye.[142]
Ga yadda za a sanya likafanin kamar haka.
Za a kawo likafani guda uku.
1.
Za a shinfixa na farko mai faxi yadda zai
rufe daga qirji zuwa qafa ya kuma zova. Misali idan mamacin zai ci yadi biyar ne
idan yana raye, to sai a ninka.
2.
Likafani na biyu ya ninka na farko yadda
zai rufe tun daga kai har ya zova qafarsa.
3.
Iikafani na qarshe ya fi na biyu faxi da
tsawo sai a rufe gaba xanyan jikin gawa har
ya zova, sai a xaure qarshen kan
da qafar gawar da ragowan qyallen da ya zova ko kuma wani zare fari. Kar a
manta an riga
an shinfixa likafanin nan guda ukun tun farko. Idan kuma Allah ya sa ba a sami
likafanin ba sai guda xaya, to sai a yi amfani da guda xayan a matsayin lalura.
Shi guda xaya za a rufe shi ne baki xaya.
Ba a yin hula ko rawani domin bai tabbata ba. Da
ya tabbata da an yi wa manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ko sahabbansa tsira da amincin Allah su
tabbata a gare su baki xayan su.
Ba
wata hujja tabbatacciya da ta ce a yi wa mace likafani guda biyar, don haka ita
ma likafani uku (3) za a yi mata kamar yadda ya zo a karantarwar Annabi sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam ta nuna.[143]
Fauzan
a cikin littafinsa na gawa ya nuna za a iya shimfixa likafanin guda uku a lokaci
xaya watoxaya bisa kan xaya sannan sai a kawo
gawar a xora ta a kan
su, sai ka aikata yadda bayani ya gabata a sama.[144]
Wasu
kuma suna ganin za a sa auduga da turare a toshe hancin gawar da kunni da kuma hammata,
ragowar kuma a sa a idonta. Albany
a cikin Ahkamul Jana’iz ya ce yin haka bidi’a ce don manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam bai koyar da haka ba kuma su ma sahabbai ba
su yi haka ba. Don haka bai halasta ba.
Idan
gawawwaki sun yawaita kuma likafani ya yi qaranci ya halasta a haxa mutane biyu
ko fiye da haka a likafani xaya sai a gabatar da wanda ya fi su qur’ani ya
fuskanci liman.[145]
Bayan
an gama sanya wa gawa likafani sai a fesa mata turare mai qamshi sannan a saka ta
cikin makara,da ga nan a fita da ita filin sallar gawa.
SALLAR GAWA
Hukuncin
wannan sallar ba dole ba ne a ce kowa sai ya yi ta, faradul kifaya ce wato wani
ya iya xauke wa wani ko wasu suna iya xauke wa wasu. Idan wasu suka yi to sun
xauke wa waxanda ba su yi ba. Ma’ana idan wasu suka yi zunubi ya faxi a kan wanda bai samu halin
zuwa wajen salla ba amma waxanda suka yi
su kaxai ne zasu samu ladar sallar.
SHARUXXAN SALLAR GAWA
Wannan
sallah tana da sharuxxa kamar haka:
Niyya:
Ita niyya wajiba ce a kowace ibada kuma ita wannan niyyar a zuciya ake yin ta. Furuci
da niyya bidi’a ce bai halasta ba, yin furuci da niyya a wajen sallar gawa ko
sallar farilla ba.
Fuskantar
Alqibla: kamar yadda ake fuskantar alqibla wajen sallar farilla to ita ma sallar
gawa ana fuskantar alqibla.
Suturce
Al’aura: suturce al’aura wajibi ne, ba a yin sallah tsirara sai dai da lalura
mai qarfi idan ya zama lalura mai qarfi sai a yi sallar tsirarar kamar yadda Askari
ya koyar da mu sai a yi idon mamu a rufe.
Tsarki: Masu sallar da wurin da za’ayi sallah ya kasance mai tsarki.
Alwala: Alwala
a kowace sallah wajibi ne manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ya
ce ba a amsrar sallah sai da alwala. لا تُقبل صلاة بغير طهور [146]
RUKUNNAN SALLAR GAWA
Wannan
sallah tana da rukunai kamar haka:-
1.
Tsayuwa:
Ana yin sallar ne a tsaye, ba a yin ruku’u
babu kuma sujuda babu tahiya.
2.
Kabbara huxu a qalla, zuwa tara.
3.
Karatun
Fatiha: Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa aihi wa salam ya
ce, “Babu sallah ga wanda bai karanta fatiha ba.”[147]Sahabi
Abu Umama ya ce sunnah a sallar gawa ita ce karatun fatiha a asirce[148] .
4.
Salati ga manzon Allah (SAW).
5.
Yin addu’a ga mamacin.
6.
Jerantawa.
7.
Sallama.
SUNNONIN SALLAR GAWA
Wannan
sallah tana da sunnoni kamar haka:
1.
Xaga hannu yayin kabbara ta farko.
2
Yin karatu a voye.
3
Xora hannun dama a kan na hagu (qablu), haka
manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa aihi wa sallam ya koyar kuma haka ya umurta
da a sa hannun dama a kan
na hagu a wajen sallah. Manzon Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam bai
tava yin sallah hannunsa a sake ba kuma su ma sahabbai ba sa sakin hannuwansu a
wajen sallah.
4.
Yin sahu miqaqqe mai faxi yadda ake yin
sahun salloli. Ba a matsewa mammatsewa
wajen sallar gawa bidi’a ce. Ana yin sahu ne mai kyau kamar yadda Annabi sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam ke yi shi da
sahabbansa. Jabir bn Abdullahi ya ce, “manzon sallal Lahu alayhi wa aihi wa sallam
ya yi wa Najashi sallah, muka yi sahu-sahu.”
Sahabi Jabir ya ce, “Na kasance a sahu na biyu ko na uku[149].
5.
Adadin sahun sallar Gawa su kai uku. Komai qarancin masallatan.
Kuma
ana yin sahu ne yadda ake yin sahun salloli, ba a matse sahu ana yin sahu ne da faxi.
6.
Karatun
surah: Karatun sura a sallar gawa Sunna ne.
7.
Yin sallah da takalmi:
Ba a cire takalmi wajen yin sallar gawa.
Wasu malaman suna gani cire takalmi wajen sallar gawa bidi’a ce, Albany
ya kawo wannan maganar a cikin Ahkamul Jana’iz.
YADDA
AKE YIN SALLAR GAWA[150]
Liman zai tsaya a
saitin kan
gawar idan gawar ta namiji ce. Ga misali:
Amma
idan mace ce liman zai tsaya a tsakiyar ta, su kuwa mamu zasu yi sahu a bayan
liman kuma su daidaita sahun kamar dai sahun kowance sallah. Babu matsewa,
kuskure ne babba mammatsewar da ake yi wajen sallar gawa. Manzon Allah sallal
Lahu alaihi wa alihi wa sallam ya koyar da a yi sahu yadda ake sahun salloli. Yin
haka shi ne sunnah savanin haka bidi’a ce. Sannan sai ka xaga hannunka wajen
kabbarar harama. Bayan ka yi kabbarar haraman sai ka sa hannunka a qirjinka, ba
a sakin hannu a kowace sallah haka sunnah ta tabbatar.[151]
Da zarar an yi kabbarar harama sai a yi
a’uziyya da basmala
أعوذ
بالله من الشيطان الرجيم من همزه ونفخه ونفثه
بسم الله الرحمن الرحيم
Basmalah
wato a karanta Auzu billahi da Bismillah a asirce, daga nan kuma sai a karanta
suratul fatiha, ba a karanta addua’r istifta’i kamar yadda Imam Nawawi ya ce a
cikin RiyadusSalihin.
Kabbara ta biyu:
bayan ka yi kabbara ta biyu sai ka yi salati ga manzon Allah (SAW) wato ka ce:
اللهم صل على محمد وعلى آل
محمد كما صليت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم
إنك حميد مجيد اللهم بارك على محمد وعلى آل محمدكما باركت على إبراهيم وعلىآل إبراهيم
إنك حميد مجيد
Allahumma salli ala
Muhhammad wa ala ali Muhammad kama
sallaita ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim innaka hamidun majid, Allahumma barik
ala muhhammad wa ala ali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim
innaka hamidun majid.
KABBARA TA UKU : Bayan
ka yi kabbara ta uku sai ka yi addu’a ga mamacin wato sai ka ce:
اللهم اغفرله وارحمه وعافه واعف عنه وأكرم نزله ووسع مدخله واغسله بالماء
والثلج والبرد ونقه من الخطايا كما ينقى الثوب الأبيض من الدنس وابدله دارا خيرا
من داره وأهلا خيرا من أهله وزوجا خيرا من زوجه وادخله الجنة واعذه من عذاب القبر
ومن عذاب النار
Allahumma agfir lahu warhamhu wa afihi
wa afu anhu wa akrim nuzulahu, wa wassi’i mudkalahu wagsilhu bil ma’i was salji,
wal baradi wanakkihi minazzunibi walkhadaya kama
nakkaita saubi-abyad mina ddanasi, wa ab dilhu da’ran khairan mindarihi wa
ahlan khairun min ahlihi, wa zaujan khairan min zaujihi, wa adkhilhul Jannata
wa aizhu min azabil kabar.
KABBARA TA HUXU: Bayan kabbara ta huxu sai ka sake yin addu’a sai ka/ki ce:
اللهم اغفر لحينا وميتنا، وحاضرنا وغائبنا، وصغيرنا وكبيرنا، وذكرنا وأُنثانا،
اللهم من أحييته منا فأحيه على الإسلام، ومن توفيته منا فتوفه على الإيمان، اللهم
لا تحرمنا أجره ولا تضلنا بعده
((اللهم
أعذه من عذاب القبر))
Allahumma agfir
lihayyina wa miyyitina wa shahiduna wa ga’ibina wa sagirina wa kabirina
wazakarina wa unsana Allahumma man ahyaytuhu minna fa ahyihi alal islami waman
tawaffaitahu minna fatawafahu alal imani, allahumma la tuharrimna ajarahu, wa
taftina ba’adahu. Da zazar an gama wanna addu’a sai ayi
sallama daga nan kuma sai a xauki gawan zuwa makabarta
Ko
ka karanta wannan adduar:
اللهم اغفر
لحيِّنا وميِّتنا، وشاهدنا وغائبنا، وصغيرنا وكبيرنا، وذكرنا وأنثانا، اللهم من
أحييته منا فأحيه على الإسلام، ومن توفيته منا فتوفَّه على الإيمان، اللهم لا
تحرمنا أجره ولا تُضلَّنا بعده
IDAN GAWAR MACE CE
Idan
gawar da za a yi wa sallar ta mace ce, to sai a yi amfani da lamirin mace wajen
yin addu’ar, wato idan ka yi kabbara ta
uku misali, sai ka ce:-
Allahumma
agfir laha warham ha har zuwa qarshe
wato duk wurin da hu yake sai
amayar dashi ha.
SALLAMA: Sallama
a sallar gawa ya halasta, ka taqaita a kan
sallama xaya. Ya tabbata a hadisi ingattace daga Abu Hurairah Allah ya qara masa yarda, ya
ce “Haqiqa manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi ma gawa
salla, ya yi kabbara guda huxu, sannan ya yi sallama xaya.[152]
أبي هريرة رضي الله تعالى عنه : " أن رسول
الله صلى الله عليه وسلم صلى على جنازة ، فكبر عليها أربعا ، وسلم تسليمة واحدة
Amma sallama biyu ma ta inganta. Ana
iya yin sallama biyu wajen sallar gawa, kai ko ba sallar gawa ba ya halasta ka
yi sallama xaya amma kar a manta sallama biyu ta fi inganci. Kuma kar a manta
sallamar a hankali ake yi ba a yi da qarfi
kamar a sauran salloli.
IDAN
GAWAR TA YARO CE KO YARINYA
Idan
gawar da za a yi sallar yaro ne ko yarinya waxanda ba su balaga ba. Za a yi
addu’a ne kamar haka:-
Allahumma
ij’alhu faraxan wa zukharan li walidaihi wa shafi’an mujiban allahumma sakkil
bihi mawazinahuma wa a’azzim bihi ujurahuma wa alhikhu bi salihil mu’uminina
waja’alhu fi kafalati ibrahima wakihi birahmatika min azabil jahim.
Ko
kuma ka ce:
((اللهم اغفر لحينا وميتنا، وحاضرنا
وغائبنا، وصغيرنا وكبيرنا، وذكرنا وأُنثانا، اللهم من أحييته منا فأحيه على
الإسلام، ومن توفيته منا فتوفه على الإيمان، اللهم لا تحرمنا أجره ولا تضلنا بعده.
Sannan
ka karanta wannan adduar:
(اللهم
اجعله لنا فرطاً وسلفاً وأجراً.
((اللهم
اغفر لوالديه وارحمهما
Wato
za a yi wannan a madadin wancan addu’ar da ake yi bayan kabbara ta uku.
WANDA YA ZO A MAKARE
Wanda
ya zo ya tarar da an fara sallar gawa, to daga zuwan sa zai yi kabbara ya dasa daga inda ya same su, idan liman ya yi
sallama sai ya yi sauri ya rama kabbarorin da suka kubce masa. Idan zai yiwu ya
rama ba tare da an xauke gawar ba to sai ya yi addu’ar a bayan kowace kabbara.
Amma in har za a xauke gawar ba tare da ya gama ba to zai gaggauta yin kabbarorin
ba tare da ya yi wata addu’a ba.
MATASHIYA
ü Ana so idan
mutum ya rasu a yi gaggawar sanar da mutane domin su zo su halarci sallarsa.
Sannan kuma ya kamata a jira mutane su taru sa’annan a yi sallar idai jiran ba zai tsananta ba. Saboda Annabi
ya ce babu wani mutun da zai rasu a sami al’umma cikin musulmi waxanda zasu kai
su xari (100) dukkanin su suna riqo da sunnah face Allah ya ba su ceton sa.
ü Sannan kuma ya
halasta mata su yi sallar gawa wato su yi sahun su a bayan sahun maza kamar
yadda ya tabbata cewa mata sun halarci janazar Ummukulsum Bintu Aliyu matar
sayyidina Umar[153]
Allah ya qara masu yarda amin.[154]
ü Sannan kuma sun
samu su yi sallar su kaxai ba tare da maza ba, wato a kai masu gawar cikin gida
ko masallaci su yi wa gawar salla su kaxai. Bayan sun gama sai a fito da gawar
waje maza su yi mata salla, kamar yadda Nana Aisha ta yi wa sahabi Sa’ad ibin Abi Waqqas.[155]
ü Ya halasta a yi wa
jariri salla matuqar ya fito duniya da ransa.
ü Hakanan ma varin
da ya kai wata biyar ko huxu shi ma ya halasta a yi masa salla, sai a yi wa
mahaifiyar addu’a ta alhari.
ü Limamin da zai ma gawa sallah kar ya manta ya gaya
ma jama’a abin da ake karantawa,kabbaran farko akarata fatiha da sura kabbara
ta biyu akaranta salati Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam kabbara ta
uku ayi ma gawar addua ta alheri da fatan tsira kabbara ta huxu a yi gava xayan
musulmai addua.
XAUKAR
GAWA
Imam
Musulmi ya fitar da hadisi daga
Abu-Huraira Allah ya qara masa yarda ya ce,
“Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘wanda ya fita tare da gawa
daga gidanta har aka yi mata salla sannan ya raka ta ya zuwa maqabarta, har aka
rufe ta yana da yankin lada guda biyu ko
wani yankin lada guda xaya, girmansa kamar
girman dutsen Uhudu. Wanda aka yi mata (gawa)
salla ya koma gida bai je aka rufe ta ba, yana da yankin lada guda xaya
girmansa kamar dutsen uhudu.[156]
Hakqi
ne na xan uwa Musulmi idan ya rasu a raka shi ya zuwa maqabarta. Wasu Malamai
suna ganin dole ne gaba xayan Musulmi su raka shi kamar dai yadda hadisin Muslim
ya nuna haqqin Musulmi ga xan’uwansa guda shida ne. A cikin haqqin; in ya rasu
ka raka gawarsa.[157]
Wani
hadisin Manzon Sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam cewa ya yi, “Ku raka gawa,
rakata yana tuna maku lahira.”[158]
Malamai
dai ma’abota ilimi sun ce raka gawa zuwa
Maqabarta Faradhul kifaya ne ba dole ba ne, ba sai kowa ya rakata ba. Amma da
za a je baki xaya to ya fi dacewa da alheri, kuma shi ne abin da aka fi so. Xaukar
ta da raka ta ba dole ba ne kowa ya yi, sai dai sunna ce mai qarfi.[159]
SIFFAR YADDA AKE XAUKAR
GAWA
1.
Bayan an gama yi wa gawa wanka sai a naxe ta a likafani kamar yadda bayani ya
gabata, a sa ta a cikin makara fuskanta na kallon sama, sannan a rufe gawar
idan gawar ta mace ce a rufe makarar baki xaya. Haka aka yi
ga Fatimatu Zahara’u ‘yar Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
da Zainab bintu Jahashi Ummul Mumin.[160] amma
namiji ba za a yi masa yadda aka yi wa mace ba.
2.
Ana so masu xaukar gawa su zama mutane huxu mustahabbi ne ko kuma su
kai shida amma huxun dai shi ya fi. Yin hakan sunna ce ya zama mutane huxu,
hadisin ibn Masud ya nuna mana haka [161].
3.
Mutane huxu za su xauki gawar biyu a
gaba biyu a baya. Yin haka ita ce sunna.[162]
4.
Umurni
ne in an xauki gawa a yi sauri da ita. Manzon Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam
ya yi umurni da a riqa sauri da gawa idan an xauke ta.[163]
5.
Ba a zama har sai an saka ta cikin
qabari.[164]
6.
Ana son waxanda suke raka gawa su raka ta
suna masu qasqantar da kansu ga Allah suna
masu tunananin Rasuwa.
7.
Ba a Zama
idan an xauki gawa har sai an saka ta a qabari.[165]
8.
A wuya ake sa gawa idan an xauke ta. Wannan
ita ce sunna kamar yadda Abi-Sa’idu
Kudiri ya kawo hadisin da ke nuna haka.[166]
Mata ba sa raka gawa ya zuwa maqabarta
sai dai ya halasta su raka ta ya zuwa waje a yi mata salla amma zuwa maqabarta bai halasta a gare
su ba.[167]
Ya
halasta mai raka gawa ya wuce gabanta ko bayanta duk sun tabbata ga Manzon
Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam sai dai biyo bayanta shi ne mafifici wato a
sa gawa a gaba masu rakata suna biye. Wato tana gaba kuna biye. Domin ladar bin baya
wajen raka gawa kamar kun yi salla ne a cikin jam’i. Idan kuwa kuka
shiga gabanta, ladarku ladar wanda ya yi salla shi kaxai ne.[168] Zamu
iya fahimtar bin bayan gawa shi ya fi da a shiga gabanta.
Ya
halasta a hau keke ko mashin ko doki ko jaki wajen raka gawa amma dole ka jira
mutane su yi gaba sannan ka biyo baya kar ka
hau abin hawanka, haka ya faru zamanin
Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa
sallam an kawo masa abin hawa sai ya qi hawa. Bayan da jama’a suka wuce sai ya
biyo bayansu a kan abin hawansa sai aka tambaye shi sai ya ce
bai dace ba in hau abin hawa alhali malai’ku na qasa (Wato su ma suna raka ta
kuma bayanta suke bi). Bayan da suka
wuce sai ya biyo bayansu.[169]
SHIN XAUKAR GAWA A KAN
ABIN HAWA YA HALASTA?
Xaukar
gawa a kan abin
hawa, wato a keve mota ta musamman domin xaukar gawa ya zuwa maqabarta kamar
yadda waxansu garuruwa suke yi, babu ko shakka yin haka ba shari’a ba ne kuma
kuskure ne babba ya sava wa abinda shari’a ta koyar kamar ta hanyoyi kamar haka:
1.
Al’ada ce ta kafirai xaukar gawa a mota.
Kuma Musulunci ya umurce mu da mu sava wa kafirai. Kuma bai halasta koyi da su
ba, ko ta ko’ina. Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce wanda ya
kamanta kansa da wasu mutane yana tare
da su.[170]
2.
Kuma xaukar gawa a mota bidi’a ce cikin
ibada ta sava wa sunnar da ta ce a xauke ta a wuya/kafaxa haka hadisi ya ce. Amma sanya ta a cikin mota bidi’a ce
kuma hadisi ya nuna mana dukkan bidi’a vata
ce. Sai dai lalura.
3.
Tanasa a samu qarancin masu raka ta wanda
sunna ta umurci da a raka ta.
4.
Ta kore ma mutane tuna lahira na wajen
rashin xaukar ta a kafaxa kamar yadda hadisi ya nuna.
Ibn Abidin ya ce xaukar
gawa a dabba makaruhi ne in ba da uzuri mai qarfi ba, kamar nisan maqabarta ya ce
babu laifi a sanya ta a jaki a kai ta mutane na bin ta a qasa amma banda mota.[171]
Ibn Taymiyya shi ma ya ce
bai dace xaukar gawa ba a dabba ba. Xaukar ta a wuya ita ce Sunna. [172]
ABUBUWAN DA SUKA HARAMTA A RAKA GAWA DA SU
A
kwai abubuwan da suke haramun ne raka gawa da su ko kuma ana tafiya ana yin su,
duk ba su halasta a yi su ba. Yana da kyau
‘yan’uwa mu kiyaye domin dacewa da koyarwar Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam da kuma nema wa mamaci alheri. Duk lokacin da aka yi sunna wajen
sha’anin gawa, yana shafar gawar, haka ita ma bidi’a in aka aikata ta sharrin ta
zai iya shafar mamacin. Don haka ya dace
a kula. Ga abubuwan da shari’a ta hana a
raka gawa da su kamar haka:
·
Raka gawa da wuta ko garwashin wuta.[173]
Kamar yadda Indiyawa suke yi. Wannan babu savani cewa haramun ne raka gawa da
wuta ko bakin wuta. Haka ita ma fitillar qwai ta shiga cikin wannan hukunci da
kyandir da duk abin da zai xauki sunan wuta.[174]
·
Raka gawa ana zikiri shi ma haramun ne.[175]
·
Raka gawa ana karatun qur’ani shi ma
haramun ne.[176]
·
Raka gawa ana Allahu Akbar shi ma haramun
ne.
·
Raka ta ana waqa da kixa da sarewa irin
yadda Kiristoci da masu bin addinin Shi’a suke yi da Sodoji suke yi shi ma bai
halasta ba. Wannan shi ne mafi muni da sharri, a raka gawa ana waqa da kixa wannan
a fii yake koyi ne da kafirai maqiya Musulunci.[177]
·
Raka ta ana surutu shi ma bai halasta ba,
abin da yake daidai raka ta ana yin shiru.[178]
·
Bai halasta Musulmi ya raka gawar Kafiri
ba.[179]
·
Kuma shi ma Arne bai Halasta ya raka Musulmai
ba.
·
Babu kyau shiga maqabarta da takalmi ko
tsakanin qabari.[180]
QABARI
Wajibi
ne rufe gawa ko da kuwa ta Kafiri ce shi ma za’a rufe shi saboda xan Adam yana
da daraja ko da Arne ne, Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya sa an
rufe manyan kafirai da aka kashe a yaqin Badar.[181]
Dole
ne rufe mutum idan ya rasu bai dace a bar shi a fili ba tare da an yi masa qabari
ba. Sannan ba a rufe Musulmi a Maqabartar Arna ko kafirai a maqabartar Musulmai
ba kafirai za’a rufe su a Maqabartar su ta Arna Musulmai a tasu ta Musulmai.
LOKUTAN DA BABU KYAU A BISNE
GAWA
Manzon
Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya hana rufe matattu a waxannan lokutan:
ü Lokacin
da rana ta ke fitowa.
ü Lokacin
da rana ta ke tsakiya.
ü Lokacin
da rana zata faxi ta yi ja-jawur.
ü Babu
kyau rufe gawa da daddare sai dai larura mai qarfi.[182]
Ba a rufe mutum a gida, abinda sunna ta nuna
shi ne rufe mutum a maqabarta kamar yadda Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi
wa salam ya riqa yi wa sahaban sa. Ba a sami wani sahabi da ya ce a rufe shi a
gida ba. Don haka rufe mutum a gida bai halasta ba.
·
Babu kyau rufe mutum a masallaci, haramun
ne.[183]
Kuma
duk inda mutum ya rasu anan ake rufe shi haka shari’a ta nuna. Manzon Allah ya ce
qasa ta tsarkake kowa, duk inda mutum ya rasu a nan a ke rufe shi ba za a ce
sai an dawo da shi gida ba. Duk garin da ka rasu a nan za a rufe ka, hadisin Huzaifatu Yaman ne ya faxe shi.[184]
IDAN MACE KIRISTA TA MUTU
DA CIKIN MUSULMI[185]
Idan
mutum musulmi ya auri kirista sai ta mutu da cikin Musulmi, to ba za a kai ta maqabartar
Arna ba ba kuma za a kai ta ta Musulmai ba, za a rufe ta tsakanin Maqabartan
Musulmai da ta Arna. Sannan kuma bayanta yana kallon Ka’aba(gabas), yadda shi kuma jaririn ko jaririyar
da ke cikin nata zai fuskanci alqibla.[186] (idan
da ciki)
YADDA AKE YIN QABARI
Ana
so a yi qabari da zurfi da kuma faxi a kuma kyautata shi ba a so a yi qabari
mara zurfi kuma mai qunci Manzon Allah Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya
yi umurni da a yi qabari mai zurfi wajibi ne. An Samo hadisi daga Hisham wanda
yake nuni a kan
wajabcin gina qabari da zurfi da kuma faxi.[187]
wata ruwayar a gaban manzon Allah sal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ake gina qabari, sai ya ke
umurtar masu gina qabarin da su faxaxa shi kuma su kyautata shi.[188]
Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
ya ce, “Ku faxaxa wajen kansa (gawa) kuma ku yalwata wajen qafafuwansa.[189]
Zamu
fahimci kuskuren masu gina qabari a yau yadda suke daidaita qabari wajen qafa
da kai da ciki duk suna yin su dai-dai. Yin haka kuskure ne ya kamata mu gyara,
da kai da qafafuwa su fi faxi kamar yadda Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa
sallam ya yi umurni da a yi. Kuma yana da kyau a ce masana addini su ne suke
ginin qabari, yin qabari da zurfi da faxi shi ne sunna, sai mu gyara. Allah ya ba
mu ikon gyarawa. A qalla ana so zurfin qabari ya kai kamar qirji ko cibiya kuma
ana yin qabari a jere wato a yi a layi..
Bayan
mun ga ana so a yi qabari da zurfi da
kuma faxi, qin yin qabari da zurfi da faxi sava wa addini ne. To sannan kuma
yana da kyau mu gane qabari ya kasu
kashi biyu, akwai:
1.
Lahadu
2.
Shuqqu
·
Lahadu shi ne qabarin da za a gina shi
da faxi da zurfi sannan a qwaqule bangon gabas (Qibla). A bangon qibla za a sanya
mutum, wannan shi ne lahadu.
·
Shuqqu shi ne qabarin da za a gina tsakiyarsa ko kuma mu ce wanda ake ce ma uwa
da ’ya (Shi ne qabarin da aka saba yi a qasar Hausa suna ce masa uwa xiya).
WANNE NE MAFIFICI?
Ba
shakka Lahadu shi ne mafifici, kuma shi Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
ya yi umurni da Musulmi su yi wa matattun musulmai idan sun rasu.
Lahadun
shi ne aka yi wa Manzon Sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam.
Sahabi
Sa’ad bn Abi Waqqas ya faxa a yayin rashin lafiyarsa ya ce, “Idan na mutu ku yi
mani Lahadu, kuma ku sanya mani bulo (Tubali) kamar yadda aka yi wa Manzon
Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam[190].
Babu
shakka Allah yana zava wa Annabinsa sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
abinda ya ke mafifici, don haka da ya rasu
aka gina masa qabarin Lahadu kamar yadda
Sahabi Annas ya labarta mana. Ya ce da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ya rasu akwai masu sana’ar ginin qabari a Madina, xaya yana Lahadu xaya
kuwa yana Shuqqu. Sai suka yi istikara a kan
Allah ya zava masu wadda ya fi. Sai suka aika, sai kuwa Allah ya sa saqo ya ishe
mai yin Lahadu, sai aka yi wa Ma’aiki Sallal Lahu layhi wa alihi wa sallam
Lahadu.[191]
A
wata ruwayar Manzon sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Lahadu ne
namu mu Shuqqu kuwa na wanxanda ba mu ba”[192].
Babu
savani kan qabarin
Lahadu shi ne mafifici shi ne kuma ya kamata duk Musulmi ya yi wasiyya da in ya
mutu a yi masa. Amma in babu halin yin lahadu babu laifi in aka yi
Shuqqu.
MATASHIYA
Babu
laifi ba ne sai dai ba haka aka so ba, a yi wa mutum Shuqqu. Yana
da kyau mai karatu ya duba littafin Imamun Nawawi ya yi bayani mai daxi mai
kuma gamsarwa.[193]
·
Yayin da za a saka gawa a qabari ana karanta
wannan addu’ar:
بسم
الله ، وعلى سنة رسول الله،أو :ملة رسول الله صلى الله عليه وسلم
Ko kuma ka ce:
باسم
الله ، وبالله على ملة رسول الله صلى الله عليه وسلم
Sunna ce a shigar da
gawa qabarin ta ta qafa (ta fuskar qafar kabarin ba ta kai ba). Babu kyau a ajiye
gawa a yamma sannan a xauko ta a sanya ta qabari, yin haka sava wa koyarwar
Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ce.[194]
Ana saka gawa ta vangaren dama jikinta na fuskantar qibla.[195]
·
Ana saka gawa a hankali ne ta tsagin dama tana mai kallon qibla.[196]
·
Dangin mamacin (gawa) ke saka ta a
qabari, idan mace ce kuma mijinta ya
nemi taimakon babanta ko yaranta. Amma bai kamata wani ya saka gawa qabari ba
in dai ba dangin gawar ba ne sai dai in babu kowa daga cikin dangin.
·
Wanda ya sadu da iyalinsa a daren da ya
gabata bai halasta ya saka gawa qabarin ta ba, ko da kuwa matarsa ce.[197]
·
Amma in ba su kiyaye qa’ida ta sunna ba
gara a sami waxanda suka san yadda ake yi a sunna su saka ta a qabarin.
ME
AKE RUFE QAVARI DA SHI?
Yana
da kyau koda yaushe mu yi aiki da koyarwar Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa
sallam, yin haka shi ne tsira kuma shi ne zai kai mu ga nasara.
Zamanin
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam abinda ake rufe qabari da
shi shi ne tubali ko bulo, haka hadisin Sa’ad ibn Abi Waqqas ya nuna da wasu ruwayoyi
ingantattu, amma banda tukunya. Kuma ya tabbata za a iya sa ganye a rufe qabari
da shi ko itace banda tukunya. Sanya tukunya ba shari’a ba ne al’ada ce.
Kuma
ya tabbata za a iya sanya ciyawa, domin lokacin Fathu Makka Manzon Sallal Lahu
alayhi wa alihi wa sallam bayan an ci Makka da yaqi wato bayan Fathu Makka ya hana
sare itatuwa saboda Makka harami ce. Sai Abbas ya ce, “Manzon Allah sallal Lahu
alayhi wa alihi wa sallam banda Iywa (wata irin ciyawa ce wadda ake Asabari da
ita)?” Sai Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce banda ita(Iywa). Abbas
ya ce, “Domin muna rufe mattattun mu da ita kuma muna rufin xaki da ita.”[198] Ishara,
ashe da ita a ke rufe qabari. Ya kamata mu gyara, mu koyi yadda sunna ta koyar
ba tukunya ba. Allah ya bamu ikon gyarawa.
Bayan
an sa bulo ko tubali ko itace ko ciyawa, sai a tura qasa sau uku ta vangaren
kansa (gawar), haka Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yake yi.[199]
ü Haramun
ne saka mutum cikin akwati a rufe shi cikinsa, wannan koyi ne da kafirai.[200]
ü Kana
iya sa dutse a qabarin xan’uwanka don ka gane qabarinsa saboda zuwa ziyara a
gare shi, amma ba zaka sa sunansa ba, wannan haramun ne rubutu a qabari.[201]
ü Xaga
qabari misalin tiqa xaya kar ya wuce tiqa xaya, haka hadisin Jabir ya yi mana
bayani.[202]Manzon
Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
ya hana xaga qabari ya wuce tiqa xaya tsakanin sa da qasa. Ya umurci sahabi
Aliyu Allah ya qara masa yarda da ya je ya daidaita duk qabarin da bisan sa ya wuce tiqa xaya.[203]
Idan
ka kalli qaburburan mu za a ga sun sava wa koyarwar Manzon Sallal Lahu alayhi
wa alihi wa sallam. Yadda ake xaga shi ya yi bisa wannan kuskure ne, yana da
kyau mu gyara. Ba dole ba ne duk qasar da aka gino sai an mayar da ita.
Imamul
Qurxubi ya yi magana mai gamsarwa kuma mai kyau kan rashin halascin qabari ya wuce tiqa xaya
tsakaninsa da qasa. Ya ce duk qabarin da ya wuce tiqa xaya tsakaninsa da qasa a
baje shi ya koma tiqa xaya tsakaninsa da qasa. Yana
da kyau mai karatu ya duba suratul Kahafi a Tafsirinsa.
RABA QASA
Akwai
wani abu da aka saba da shi a qasar Hausa wajen ginin qabari. Idan aka zo ginin
qabari zaka ga ana raba qasa, Jar
qasa da Baqa wato qasar sama daban
na sama da ban wannan aiki ba dai-dai ba ne bidi’a ce. Ya kamata mu gyara domin bidi’a komin qanqantar ta
sharri ne, kuma sava wa Annabi Sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ne. Shi ya
koyar da mu yadda ake yin qabari bai kuma ce a raba qasa ba.
Haka
nan babu kyau yin ma qabarin siminti ko gini, koyi ne da kafirai.
RUFE MUTANE BIYU A
QABARI XAYA
Babu
laifi in an haxa mutane biyu ko fiye da haka a qabari xaya, an samo ruwaya daga
Jabiri ibn Abdullahi ya ce Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya
kasance yana haxa mutane biyu a cikin likafani xaya. Sai ya tambayi wanda ya fi
karatun qur’ani, sai ya fara sa shi a lahadu sauran kuma su biyo bayansa.[204]
Babu
laifi haxa mutum biyu ko fiye da haka a
qabari xaya in buqatar haka ta taso.
HAXA MACE DA NAMIJI A
QABARI XAYA
Babu
laifi idan aka haxa namiji da mace a qabari xaya saboda lalura. An samo Asari daga
Wasilatu ibn Asqa’i Allah ya yarda da shi ya kasance idan zai rufe mace da namiji
a qabari xaya yana sanya namiji a bangon qilba (Gabas), sai kuma ya sanya mace
a bayan namijin.[205]
Shi
kuma Imam shafi’i ya ce haxa namiji da
mace a cikin qabari xaya bai kamata ba, sai
dai in lalura. ya ce in dai lalura ce to babu laifi sai a haxa amma namiji ya kasance a gaba ita kuma a baya.
Sai a sanya turvaya wadda zata raba tsakanin shi da ita.[206]
ME AKE YI BAYAN AN GAMA
RUFE GAWA?
Addu’a
bayan an gama rufe mamaci, ana tsayawa a
yi masa addu’a. Yin addu’a sunna ce kuma wannan addu’a a tsaye ake yi ba a zaune
ba. Ana so gaba xayan jama’a su kalli gabas, kuma duk wanda ya je maqabarta ake
so ya yi masa addu’a, ba wai a keve
waxansu mutane daban ba a ce su ne wai zasu yi masa addu’a ba. Yin haka bidi’a
ce a zavi waxansu daban da za su yi addu’a. Manzo Sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ya kasance idan an gama rufe gawa yana tsayawa yana yi mata addu’a,
kuma ya kasance yana umurtar sahabbansa da su tsaya su yi mata addu’a. Sai dai
kuma kowa yana yin ta ce ne daban ba a yi cikin jam’i ba, yin addu’a cikin jam’i
babu kyau bidi’a ce.
Abin
baqin ciki yau zaka ga masu da’awar cewa su Ahlussuna ne zaka ga in an gama rufe gawa suna yin addu’a cikin jam’i. Wannan
gaskiya abin kunya ne a ce mai danganta kansa da sunna yana addu’a a jam’i
bayan rufe gawa, alhali kuma ba ya yin
haka a masalaci bayan gama Sala. Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam
yana cewa ku riqa roqa wa xan’uwanku gafara ku roqa masa sabati yanzu za’a
tambaye shi.[207]
Sahabi Sa’ad bn Abi Waqqas ya ce wa
yaransa idan na rasu ku tsaya a qabarin kuna
yi masa addu’a kwatankwacin yadda za a yanka raqumi a fexe shi a raba
namansa. Ya ce ku yi haka kuna yi ma ni addu’a.
Allah
kaxai ya san bakin da yake na kirki, don haka keve waxanusu wajen addu’a ga
gawa bidi’a ce. Ana so kowa ya yi tasa
addu’ar haka sunna ta tabbatar. Ba a samu Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa
sallam ya yi addu’a a jam’i bayan rufe gawa ba, su ma sahabbai ba a samu ba, to
ina muka ga mu mu yi a jam’I, kuma muna da’awar sunna? Allah ya ba mu ikon
gyarawa.[208]
DAFA ABINCI GA DANGIN
MAMACI
Musulunci
ya koyar da tausayawa hatta ga dabbobi. Har ila yau kuma yana daga cikin
tsausayawa da kyautatawa a dafa abinci a aika da shi gidan da aka yi rasuwa. Yin
haka sunna ce kuma kyautatawa ne kuma akwai lada mai yawa. An samo hadisi daga
AbdulLahi ibn Ja’afar ya ce Manzon Sallal Lahu alyihi wa alihi wa sallam ya ce,
“Ku dafa wa iyalan gidan Ja’afar abinci domin haqiqa abin al’amari ya same su mai shagaltar da su ya zo masu.[209]
Haka nan ma an samo daga Nana A’isha Allah
ya qara mata yarda, ita ma ta kasance tana dafa abinci ga gidan da aka yi
rasuwa. Ta ce na kasance na ji Manzon
Sallal Lahu alyihi wa alihi wa sallam yana umurta ta da yin haka (wato dafa abinci ga gidan da aka yi
rasuwa).[210]
Wannan
sunnar ta xan yi rauni. Ya kamata a raya ta, ko ma don samun lada. Ga kuma qara
soyayya ga juna da qara danqon zumunci ga kuma raya umurnin Manzon Sallal Lahu
Alaihi wa alihi wa sallam.
Amma
banda masu zaman amsar gaisuwa, su ba za
a ba su wannan abincin ba. Domin su zaman bidi’a suke yi. Mun sani cewa
zaman amsar gaisuwa bidi’a ce, zaman amsar
gaisuwa harmun ne. Za mu ga bayani a
gaba in sha Allah.
YIN WA’AZI A MAQABARTA
Ya
tabbata yin wa’azi a maqabarta yayin rufe gawa ko bayan rufe ta domin a tunatar
da mutane Rasuwa, kuma su gane su ma zasu zo wannan gida, kuma aikin su ne
kawai zai bi su. Haka kuma a tunatar da su abinda zai biyo bayan Rasuwa. Babu laifi
a wannan lokacin ko da an zauna, amma a kiyaye kar a zauna a qabari. Kuma ana so mai wa’azin ya
kalli gabas. Hadisi ya zo da ga Manzon Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam
ya yi wa’azi wajen rufe gawa a maqabarta, ya kuma tsoratar game da a azabar
qabari. Ya ce mu nemi tsari daga azabar
qabari[211].
Gaskiya
a halin yanzu muna tsananin buqatar tunatarwa a maqabarta kuma ga shi Sunna ce yin
haka. Don Allah muna roqon duk wanda zai iya tunatarwa to ya tunatar da mu, musamman
game da yadda mutane suka manta da Rasuwa, Yana
da kyau mai karatu ya duba hadisin da Annabi Sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam
ya tunatar a maqabarta.
ABUBUWAN DA SUKA
HARAMTA BAYAN AN RUFE GAWA
1.
Fidda’u shirka ce kuma faxa ne da
koyarwar Annabi sallal Lahu alaihi wa alihi wa salam.
2.
Addu’a a cikin taro a maqabarta.
3.
Yin gini a qabari.
4.
Yi wa qabari siminti.
5.
Kunna fitila a qabari.
6.
Karatun qur’ni ga gawa a maqabarta ko a
gida bidi’a ce kuma jawo wa wannan mamacin bala’I ne.[212] Haka
nan ma yin haka sava wa Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ne, domin ya
hana karatu a maqabarta wani hadisin cewa ya yi, “Ku karanta suratul Baqara a
gidajenku. Kada ku maida gidanku Maqabarta”[213].
ishara a fili ba a
karanta qur’ani a maqabarta domin ya ce kada ku maida gidanku maqabarta. Ashe a
fili yake ba a karatun qur’ani a maqabarta.
Wata ruwayar cewa ta yi, “Ku yi sallar (Nafila) a gidanku kada
ku maysr da gidajenku maqbarta”.[214]
Sheikh Ibn Abiy Hamzah
ya ce, “Karatun qur’ani a maqabarta bidi’a ce ba sunna ba ce.[215]
Sheikh Dardin Ya faxa
yake cewa a cikin littafin sharhus sagir ya ce abin qyama ne karatun qur’ani ga matattace ko a maqabarta domin ba shi cikin
aikin salaf abinda yake aikin magabata yi wa gawa addu’a ba karatun qur’ani ba[216].
Haka nan ma ya zo a cikin Hashiyatil Adawi da
ke nuna haramcin karatun qur’ani a maqabarta ga gawa.
Imam Ahmad ibn Hambal
ya ce karatun qur’ani a maqabarta bidi’a ce. Wannan ita ce maganar baki xayan
Sahabban Manzon Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Ya cigaba da cewa haka nan ma karatun qur’ani ga gawa shi ma bidi’a
ce.[217]
Sheikh Istanbuli shi ma
ya ambata cewa karatun qur’ani a maqabarta bidi’a ce. Yana
da kyau mai karatu ya nemi litattafin Sheikh Ahmad Abdussalam Asshaqiriyu wanda
Istanbu’i ya yi ma ta’aliqi.[218]
Imamu Shaxibi ya faxa
cewa karanta qur’ani a gaban gawa ko a maqabarta bidi’a ne.[219]
7.
Yanka a wajen qabari shirka ce duk wanda ya yanka
kaza ko rago ko sa a maqarbarta ya yi shirka Allah ya shiryi masu yin wannan
mummunan aikin.
8.
Kiran Sunan wanda ya rasu a ce ma shi ya
faxi kalmar shahada, yin haka bidi’a ce.
9.
Rubuta sunan matacce a jikin qabari bidi’a
ce kuma koyi da kafirai ne.
10. Xibar
qasar qabari domin neman tuburraki shirka ne.
11. Bayar
da sadaka a maqabarta bidi’a ce.
12. Yin
ta’aziyya a maqabarta bidi’a ce.
ME KE AMFANAR MUTUM
BAYAN RASUWARSA?
A
kwai abubuwan da shari’a ta bayyana mana ko bayan mutum ya rasu suna amfanar sa yana qabarinsa, ana rubuta
masa lada ga wasu daga cikin su kamar haka:
1.
Addu’a: Wannan addu’ar ta iyalinsa ce ko
abokansa ce ko yaransa.[220] wani hadisin kuma Manzon Sallal Lahu Alaihi wa
alihi wa sallam ya ce, “Addu’ar da mutum ya yi ga xan’uwansa bai sani ba, karvavviya ce.[221]
2.
Biya masa bashin da a ke bin sa.
3.
Biya masa azumin da a ke bin sa.[222]
4.
Aikin alherin da mamaci ya yi yana
amfanar mamaci.[223]
5.
Sadaqatul Jariya (Wadda ya gina
masallaci ko islamiya ko ya gina rijiya ko ya shuka itacen da ake shan ‘ya’yansa).[224]
6.
Ilimin da wani ya koyar mai amfani.
7.
Wanda ya bar Qur’ani ko ya bayar da
kyautar sa.[225]
8.
Yin ma mahaifa ko mamaci aikin Hajji,
ladan na zuwa gare su.
9.
Yin layya ga mahaifa bayan mutuwar su
lada na zuwa gare su.
Waxannan su ne abubuwan
da idan mutum ya same su yana qabari, to ana rubuta masa lada. Muna roqon Allah
ya ba mu samun su.
TA’AZIYYA
Ya
tabbata a shar’ance idan mutum ya rasu a
yi wa dangin mamacin ta’aziyya, ana yin ta’aziyyar ne da kalmomi masu daxi da
za su faranta wa wanda aka yi masa rasuwar rai. Ba ma sai rasuwa ba, duk abinda ya faru da wani xan’uwa musulmi
na musiba duk ya tabbata ana yi masa ta’aziyya da kalmomi masu daxi da zasu
faranta masa zuciyarsa da kuma lallashin
sa da ya yi haquri ya qara yarda da qaddara.
Manzon
Sallal Lahu Alaihi wa alihi wa sallam idan zai yi wa wani ta’aziyya yana cewa;[226]
إن لله ما أخذ ،
و لله
ما أعطي ، وكل شئ عنده إلى أجل مسمى
Kuma ka kira sunan mamacin ka ce Allah ya rahamshe shi Allah ya ba shi
aljanna. Ka dai faxi kalmomi masu daxi waxanda suka dace, kuma ba a qayyade ta’aziyya
ba a ce kwana uku ko sati xaya. Duk lokacin
da a ka yi rasuwa har shekara, ya tabbata in ka haxu da wanda a ka yi wa rasuwar
to kana iya yi masa ta’aziyya. Maganar iyakance ta’aziyya da kwana 3 wannan magana
ba gaskiya ba ce ba kuma koyarwar Manzon Allah salla Lahu alayhi wa alihi wa sallam
ba ce.
ZAMAN AMSAR GAISUWA
Yana
daga cikin abin ban takaici da baqin ciki zaka ga jama’a sun shimfixa tabarma a
kofar gida suna amsar gaisuwa. Kuma abin ban mamaki har da waxanda suke danganta
kansu da sunna, sai ka rasa ina suka samo irin wannan aiki na zaman amsar gaisuwa.
Yanzu abin ya koma har da shimfixa rumfa ( canoe fee) mutane suna zaune suna
gulma da hirar siyasa, ka rasa inda suka samo wannan xanyen hukunci.
An
tambayi Imamu Ahmad Ibn Hambal me
zai ce game da masu zaman amsar ta’aziyya idan an yi rasuwa, sai ya ce, Wannan
aikin maguzanci ne.” Ya yi inkari mai
tsanani.
Imamu
Shafi’i shi ma ya ce wannan abin qyama ne. haka shi ma Auza’i ya ce Sahabi Abduahi Bajali ya ce, “Mun kasance mu
na qirga zaman amsar gaisuwa in an yi rasuwa, xaya daga cikin abubuwan da Manzon Sallal Lahu
alayhi wa alihi wa sallam ya hana. [227]
Imamun Nawawi
ya ce a cikin majmu’u, “Zaman da mutanen suke yi domin amsar gaisuwa idan aka yi rasuwa a gida ko masallaci ko wani
waje daban, ya ce yin haka abin qyama
ne.[228]
Imamu Shafi’i
: ya faxi rashin asalin zaman amsar gaisuwa.[229]
Sheikh Abubakar Jabir aljaza’iri ya faxa cewa zama a
gida domin amsar gaisuwa bidi’a ce, ya nuna yin haka jahilci ne.[230]
Sheikh Ja’afar Mahmud
Adam
Allah ya ji kansa da gafara amin ya faxi
acikin Tafsirin sa a cikin suratu Ahzab cewa zaman ansar gaisuwa ba addini
bane al’adace kuma ta sava ma koyarwar
Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam, ya qara da cewa bidia ne kuma ba daidai ba ne ya kamata duk musulmin kirki
ya nisanci zaman ansar gaisuwa, har ya kawo misalin lokacin da aka kashe
sayyina Hamza Manzon Allah sallalLahu
alayhi wa alihi wasallam bai zauna ya anshi gaisuwa ba haka lokacin da Nana
Khadijah Allah ya qara mata yarda ta rasu manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam bai zauna
amsar gaisuwa ba, Sahabbansa ba su zauna ansar gaisuwa ba bayan ya rasuwar Annabi sallalLahu alayhi wa
alihi wasallam ba. Nemi kaset karatunsa na suratul Ahzab Allah ya jiqan Sheikh
Ja’afar Mahmud Adam Allah ya gafarta masa.
zaman amsar gaisuwa ba addini ba ne, kuma
yanzu zaka ga an mayar da shi wajen cin mutuncin jama’a da hirar banza da gulma da hirar siyasa. Mutane
ba sa tunanin maganganun da suke yi sun manta da Allah zai tambaye su
maganganun da suke yi. Allah ya ba mu
ikon gyarawa amin.
Sheikh Hamidi Fakqi
ya ambata a ta’aliqin da ya yi wa Bulugulmaram, ya ce zaman amsar gaisuwa kwana
3 ko fiye da haka ba addini ba ne bidi’a ce ta jahiliyya (Maguzanci ne), bidi’a
ce da alfahari da riya da qarya.
Ibn Qaym
shi ma ya nuna babu kyau zaman amsar
ta’aziyya idan an yi maka rasuwa, ya kuma nuna yin haka bidi’a ce.[231]
Sheikh
Usaymin yana ganin bai kamata mutum ya
je inda aka shimfixa tabarma ana amsar gaisuwa
ba. Ya ce, “Kada ka je ka, bari in ka haxu da shi, sai ka yi masa ta’aziyya
domin kada ka taimaka wa bidi’a.
Sheikh Usaymin ya
yi Magana mai gamsarwa da take nuni da haramcin zama a kofar gida ko masllaci
ko wani waje domin ansar ta’aziyya a duba fatawar sa za a qaru sosai.
Kuma
in ka tambayi Malamai za su gaya
ma cewa ba inda aka ce a zauna akofar gida a karve gaisuwa tun daga Qawa’idi har Muktas haka kuma littafan
Hadisai ba inda aka yarda mutum ya zauna yana ansar gaisuwa in aikai masa
rasuwa.
وأحسن
الهدي هدي محمد
ADDU’A
Addu’ar
uku da bakwai da ta arba’in da ta
shekara duk ba addini ba ne bidi’a ce,
ko ka ce asalin wannan addu’o’in daga maguzawa yake, mu tambayi tarihin. ‘Yan
bidi’a suna yin addu’ar 3 da 7 da ta arba’in don neman abinci ne su ma sun san cewa ba shi da asali. Abin da
yake daidai ko da wani lokaci yaran kirki yana ma mahaifansa addua.
KAMMALAWA
Wannan
shine xan abin da Allah Ya hore man in
yi magana akansa wanda ya shafi hukunce-hukuncen Janaza ina roqon Allah ya
amfar dani da ‘yan uwa na musulmai baki xaya, kuma ina roqon ‘yan uwa da muji
tsoron Allah mu gyra aiyukan mu, mutuwa ko da wani lokaci tana iya zuwa wa xaya
daga cikin mu. Duk yayin da xan uwan mu ko ‘yar uwar mu suka rasu mu dage muyi
masu janaza yadda Musulinci ya koyar mu daina barin waxanda ba su san shari’a
ba su riqa yni ma gawa surkulle. In muka yi janaza yadda musulinci ya tsara,
shi mamacin yana samun lada kuma muma muna samun lada amma in muka sava muka yi bidia zamu haifar ma xan uwan mu da
matsala Allah ya kyauta amin. Aqarshe ina
roqon duk wanda yaga kuskure ko gyara qofa a buxe take kuma ina mai farin ciki
da gyaransa, har ila yau ina roqon ‘yan uwa da su yi man addua ta alheri ni da
mahaifana Allah ya ji qansu baki xaya Allah ya albarkaci zuri’ar su amin. Na gama rubuta wannan littafin cikin daren 25
Ramadan 14329.
Za
a iya samun sauran littattafan dana rubuta a mudawwanata ta yanar giza-giza http://harunaabubakarshika.blogspot.com
ina roqon addua ta alheri ga duk wanda ya karanta littafi na nagode.
والله تعالى أسأل أن يجعل هذا العمل مقبولاً، مباركاً، خالصاُ لوجهه الكريم، وأن
ينفعني به في حياتي وبعد مماتي، وأن ينفع به كل من انتهى إليه؛ فإنه سبحانه خير
مسؤول، وأكرم مأمول، وهو حسبنا ونعم الوكيل، ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي
العظيم، وسبحانك اللهم وبحمدك
أشهد أن لاإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك
Harun
Abubakar Shika
08030582333-08054533361- 08020900001
[1]
Tirmidhi.
[2]
Tirmidhi.
[3]
Matarsa ce ta ke zuwa ta nemo ma su abinci na tsawon ciwon da ya yi ita ta yi
ta wahala da shi tsawon shekara goma sha bakwai. Wannan yana nuna mana yadda
matayen qwarai suke haquri da mazajensu su ma mazajen suke haquri da su wannan
yana daga cikin siffar mataye na qwarai, haquri, shi ma miji ana so ya fi
matarsa haquri haka ake so. Matayen magabata
suna taimaka wa mazajensu ba tare da sun yi masu gori ba. Wannan shi ne abin da ya kamaci dukkan matayen Musulmi. Yana
da kyau wanda zai yi aure ya nemi mai addini ba mai karatu ba, domin manzon
Allah sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam cewa ya yi a nemi mai addini yana
da matukar mahimmanci. ‘Yan’uwa a lura da wannan wajen neman aure a duba mai
addini shi zai sa ka sami mai bin Allah wadda ta san mutunci mai girmama na
gaba da sanin ya kamata mai biyayya mai
godiya ba rainuwa da kuma jin maganarka. Allah Ya sa mu dace amin. Wasu da dama
suna ruxuwa idan sun ji mace ta iya karatun Qur’ani sai su xauka ita ce siffar
da ake nufi, wannan kuskure ne. Ya dai kamata ‘yan’uwa su tambayi malamai
siffar matar da Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya ce a aura, haka
kuma da shi ma irin namijin da ya kamata mace ta aura, domin a na samun matsala
wajen aure. Ya kamata malamai su yi bayani sosai a kan
wannan nuxuqan duba littafi na haqqoqin
‘ya’ya a Musulinci da kuma dalilan da kan
kawo lalacewar tarbiyya. duba
suratul Anbiya’i za ka ga qissar ciwon Annabi Ayyub.
[5]
Daga baya Allah Ya ba shi lafiya sannan kuma Ya mayar ma sa da yaransa waxanda
suka rasu Allah Ya ba shi waxansu, kuma Ya ba shi dukiya mai yawa. Wannan duk
sakamakon haquri ne. Wata rana ya je rafi yana wanka sai Allah Ya sa sama ta
kama yin ruwan Zinariya (wato ruwan kuxi) sai ya riqa Tarawa,
sai Allah Ya ce ma shi bai wadatu da ni’imarsa ba? Sai ya ce masa babu mai
wadatuwa da rahamarKa Ya Allah.
duba Bukhari zaka ga Qissar.
[6]
musulim
[7]
Bukhari da Mulim
[8]
Bukhari da Muslim
[10]
Ahmad.
[11] Abu
Dauda da Tirmizi.
[12]
Siilatus sahiha 1633.
[13]
Muslim. Wannan mutumin da ya sha zuman a karan farko ya warke amma ya qi
faxi, xan uwansa ya gayama Annabi sai Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi
wa sallam ya ce a qara ba shi aka qara bashi ana uku Manzon Allah sallalLahu
alayhi wa alihi wa sallam ya ce Allah ya faxi gaskiya cikin xan uwanka ya yi
qarya.
[14]
Silsilah 1053.
[15]
Muslim.
[16]
Tufatun zaqarin na Shawkani.
[17]
Bukhari.
[18]
Bukhari. Wannan yana xaya daga cikin dalilin da ya sa likitoci suke wa mutum
qarin ruwa idan an kai mutum ranga-ranga, kai ma idan kana fama da zazzavi mai
tsanani kana iya wanka da ruwan sanyi zaka warke da yardar Allah.
[19] Zadul Ma’ad da Dibbun Nabawi
[20]
Muslim.
[22] Sifatus safawa 264.
[24]
Majmu’ul Fatawa 269/24.
[25] Abu
Daud.
[26]
Bukhari.
[27]
Muslim da Abu Dauda.
[28]
Zadu Mustaqni’i Ilimin likintanci wani ilimi ne na musulmai ba na Arna ba
ne, kafirai ba su fara karatun likitanci
ba sai da suka je qasar Andulus (Spain) daular
musulunci a wancan zamani suka koya, musulmai suka koya wa Arna likitanci haka
nan ma ilimin Andasa wato ilimin Qere-qere dukkan waxannan nau’o’in ilimin
kafirai a Andulus suka koya. Amma abin baqin ciki yau Kafirai sun mamaye wannan
ilimin har wasu ‘yanbana bakwai suna ganin ilimin Boko kafirci ne wannan
kuskure ne Allah ya shiryi waxan nan yaran
su gane cewa ilimin Boko ba
na Arna banne.
[29]
Adabul Shariah na ibn Muflihi
[32]
Bukhari.
[34]
Yana da kyau ‘yan‘uwa su kiyaye shiga
gidajen jama’a, wannan bala’i ne kuma laifi ne shiga gidajen jama’a ba tare da
izini ba, ko da ka yi sallama sai ka jira an ba ka izini kafin ka shiga,
haka Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi
wa sallam ya koyar da mu. Haka nan ma haramun ne qanin miji ya shiga xakin
matar wansa sai da izinin yayan nasa, idan kuma baya nan to haramun ne kai qaninsa
ka shiga xakin matar. Allah ya ba mu ikon gyarawa amin.
[35] Bukhari.
[36] Hajjaj bn Yusuf saqafi shi ne ya sa aka soki Sahabi mai daraja Abdullahi bn Umar Allah ya
qara masa yarda da wani masoki mai dafi, ba don komai ba sai don zalunci da mugunta, Abdullahi bn Umar ya yi
wa Hajjaj magana ne ranar juma’a a kan ya tsananta wa jamá’a wajen huxuba har la’asar, sai ya sa aka soke shi. Wannan sukar ce ta zama sanadiyyar Rasuwarsa. Bayan an soke
shi ne daga baya ya zo gasshe shi don
yaudara, sai shi kuma Abdullahi bn Umar ya ce ba ya so, shi ya sanya Shamsudden
Zahabi a cikin littafinsa Siyar ya faxi miyagun maganganu
a kansa ba don komai ba sai don ya kashe
sahabai da bayin Allah nagargari har a
qarshe yake cewa, “Muna qin sa ne saboda Allah ya ce ’’ mugu xan ta’adda
azzalumi xankama karya jabberi’’ ya dai
sossoke shi. Mai karatu yana da kyau ya karanta tarihinsa a cikin SIYAR A’ALAMUN NUBALA shafi
343/4.
[38]
Muslim.
[39]
AbuDauda 309 da Ahmad 21833.
[40]
Bukhari 1356 ba a tsayawa a tsakiyar
mara lafiya sai dai wajen kansa.
[41] Abu
Ya’ala fi Musnadihi 83/7 yana da kyau
idan mutum zai je gasshe da mara lafiya ya je masa da wani abin sha ko ci
wannan ta’ada ce ta musulunci.
[43]
Muslim da Zadul Ma’ad: Wannan ya na nuna
wa likitoci yadda ake so su yi wa mara
lafiya, ba a ba shi tsoro da ciwonsa komai tsananinsa, haka musulunci ya koyar.
Idan ka tsorata mara lafiya ko wane irin
magani ka ba shi ba zai yi masa tasiri ba, domin kai ma ka sa masa wani ciwon
na damuwa a sakamakon tsorata shi da ka yi. Manzon Allah salla Lahu alaihi wa
alihi wa sallam ya kasance yana ce wa mara lafiya, “Za ka warke kuma za ka yi
rayuwa mai tsawo nan gaba.” Don Allah likitoci da masu jinya su kasance masu
faranta wa marasa lafiya, su kasance suna ba su labarin waxanda suka warke ba
tsoratar da su ba da cewa wannan ciwon
ba a warkewa ba, yin haka babu kyau, shi ya sa ake so masu addini su karanta
wannan farnin.
[44]
Bkhara 5659 da Muslim 1628 da Abu Dauda
3104.
[45]
Attamhid 277/24.
[46]
Kitabul Jana’iza na Usaymin Zadul
Mustaqari).
[47] Abu
Dauda 3072 da Silsilatu Sahiha 714.
[49]
Haqqul Ikwa na Abu Ammar Mahmud almisri.
[50]
AdabulShariah 190/2 da Haqqul Ikwa na Abu Ammar Mahmud almisri 68
[52] Abu
Dauda.
[54] Al
,Ubudiyya na ibn Taymiyya.
[58] Zadul Ma’ad.
[59]
Bukhari.
[60] Suratl baqara 155-157.
[62]
Ahmad.
[63]
Sahihu Jami’u 1676 da Ahmad 1063 da Abu Dauda 4753.
[64]
Nasa’i 1828.
[65]
Kitabul Jana’iz na Nabil Muhammad 34-35.
[66]
Muslim 919.
[67]
Bukhari 651.
[69]
Ahmad 357 da Nasa’i.
[70]Ahmad
(6582-6646) Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa salam ya
ce, “Babu wani mutum musulmi da zai mutu
ranar juma,a ko yini Juma,a face Allah ya kare shi daga fitinar qabari.”
[71] ولا تحسبن الذين قتلوا في سبيل الله
أمواتا ، بل أحياء عند ربهم يرزقون . فرحين بما آتاهم الله من فضله ، ويستبشرون
بالذين لم يلحقوا بهم من خلفهم ألا خوف عليهم ولا هم يحزنون . يستبشرون بنعمة من
الله وفضل ، وأن الله لا يضيع أجر المؤمنين
[72]
Muslim 7/51.
[74]
Muwadxa 232-233/1 da Abu Dauda 26/2.
[75]
Bukhari 33/6.
[79]
Bukhari 93/5.
[84]Ahkamu
Jana’iz na Nabil Muhammad Mahmud 76.
[85]
Kitabu Muslim liQurxubi 756-758/3 da Sharhu Nawawi ala Sahih Muslim. 66-67/13
da FathulBari 43/6.
[86]
Kitabul Jana,iz na Muhammad Mahmud
Nabil 78.
[87]
suratul Baqara 155-156.
[88]
Bukhari da Muslim.
[89]
Baihaqi 334/3 da Ahmad 297/6.
[91]
Ahkamu Jana’iz Abu Ammar 15-16.
[92]
Bukhari da Muslim.
[93]
Wasu malaman suna ganin qwal-kwabo bai halatta ba in ba wajen aikin hajji ba,
domin manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ba ya yin qwal-kwabo
kuma bai tava yi ba. Shi ne ya sanya ma
Sheikh Usman ibn Fodiyo a cikin IhyausSunnah ya ce qwal-kwabo bidi’a ce abar
zargi.
[94] Aske gemu haramun ne a Qur’ani, da Hadisi, da
maganganun Sahabbai, da gaba xayan mazhabobinmu guda huxu, da malam
Fiqihu, duk sun bayyana cewa aske gemu
haramun ne. Don haka masu aske gemu su ji tsoron Allah su bari, Ibnil Jauzi a
littafinsa “Talbisul Iblis” ya ce duk laifi idan ka yi barci ba a rubuta maka
zunubi, ya ce amma banda mai aske gemu. Mai aske gemu yana barci ne kuma ana
rubuta ma shi zunubi.
[95] Najashi Sarkin
Habasha ne ya musulunta ne a wajen sahabin manzon Allah Sallal
Lahu alayhi wa alihi wa sallam “Jaafar
ibn Abi Xalib.” Ya zauna a Habasha har ya rasu bai ga manzon Allah Sallal
Lahu alayhi wa alihi wa sallam ba amma ya yi imani da shi, da ya rasu Mala’ika
Jibril ya zo ya gaya ma sa ya rasu , sai ya gaya wa Sahabbai Najashi ya rasu
suka fito suka yi ma sa sallah saboda ba a yi masa sallah ba a can Habashar.
[96]
Muslim 920 Abu Dauda 3102.
[97]
Musim 920.
[98] Bukhari 1241 da Musim 942.
[99]
Tirmizi 1078.
[100] Na 5,6,7,8,9
ka duba Muguni Nabidin 2/451 da
Furua 2/192 da 21194.
[101]
Bukhari 2291 da Nasa’I 1961.
[102] Ahkamul Jana’iz na Abduahi bn Jaruallah bn
Ibahim 13-15.
[103]
Zadul mustaqani,i.
[104]
Muslim 919 Aljanu suna son xaki ko
gidan da ya ke akwai hoto ko kare shi ya
sa in za a cire Aljanu a jikin namiji ko mace sai an cire hoto kafin yin
ruquya. Ana cire hoto domin in akwai
hoto mala’ikun rahama ba za su zo ba
kuma ko bayan an cire aljanu a
jikin mace suna dawowa jikin wanda aka cire
wa in dai akwai hoto a xakin, ya dai tabbata xaukar hoto da liqa shi a
gida ko xaki haramun ne. Ba a fara shirka a bayan qasa ba sai ta sanadiyar hoto
wannan sananniyar magana ce a wajen malaman tauhidi ruwaya da ga ibn
Abbas, duba littafina Sharuxxan Hijabi a
Muslinci.
[105]
Kitabul Jana’iz na Nabil ibn Muhammad
Mas’uds.
[106]
Kitabul Janaiz na Nabi bn Muh’d Mahmud.
[107]
Usaymin Jana’iz 4.
[108]
Karuwanci masifa ce, duk matar da ta
mutu tana zina ba ta tuba ba Allah sai
ya qona ta. Karuwanci shi ke kawo masifa da rashin albarka da cututtuka waxanda ba a san su a baya ba, iyaye su ji tsoron
Allah su kula da tarbiyar yaransu musamman mata, kuma abin da zai maganin
karuwanci shine rage tsadar aure da aurar da yara da zarar sun balaga kada a
jira a ce sai sun gama makaranta, barin su zuwa wani lokaci shi ke kawo
lalacewarsu iyaye a ji tsoron Allah a gyara.
[109]
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce wanda ya sha guba ya
kashe kansa zai tashi da wannan gubar da ya sha a hannunsa ranar tashin qiyama
Allah zai azabtar da shi a cikin Jahannama, Allah ya kyauta. Masu shan fiya-fiya
domin su kashe kansu sun ji sai su ji tsoron Allah su gyara, wasu malaman ma
suna ganin duk wanda ya sha wata guba ya kashe kansa ya mutu kafiri.
[111]
Kitabul Janaiz na Jarullah bn Jarullah.
[112]
Usaymin a Zadulmustaqani,i kitabul Jana’iz.
[113]
Abiy Shaybah 3/247.
[114]
Bukhari.
[115]
Bukhari1254/Musim 939.
[117] Usaymun fatawa
[118]
Minhaju Muslim.
[119]
AhkamuJana’iz na nabil bin Muhammad 81-120.
[120]
Al’ummu na Imamu Shafi’i 248/1 da
Majmu’u 5/187 da Ahkamu Jana’iz na
jarullah 16.
[121]
Almusanaf Abiy-Shaybah 3/248.
[122]
Mugmy 2/463.
[123] Bukhari.
[124]
Kitabul Jana’iz na Jarullah 17.
[125]
Bayhaki 3/398 da ibn Abiy shaybah 3/413.
[126]
Muhallah 5/122 da Majmu’u 5/178.
[127]
Mukhtasar da Gayatul Muntaha1/254 da
BugayatusSalikin 1/232da fatawan Hindiyah 1/157.
[128]
Bayhaqiy 3/398 da Hakim 1/386.
[129]
Tirmizi 2/132 da Abu Daud 62-63).
[130]
Bukari
[131]
Ahkamu Jana’iz na Muh’d Hassan 121
[132]
Ahkamu Jana’iz na Muh’d Hassan 121.
[133]
Ahmad 40/6 da Bayhaki 399/3.
[134]
Bukhari 1263 da Muslim 941. Maganar da ake cewa za a yi wa gawa hula da rawani
da riga bai
tabbata ba, magana ce mai rauni raunin kuma mai tsanani duba Fatawar Usaymin.
[135]
Mulim 943.
[136]
Ahmad 14131 da sahih Jami’u Albany.
[137]
Bukhari 1276.
[138] Bukhari.
[139]
Bukhari 1277 da ibn Majah 3555.
[140]
Muhalla ibn Hazam 5/122) fikhussunna linnisa 45.
[141] Tanbihu Afham 496
[143]
Zadul mustaqani da Ahkamu Jana’iz na Nabi 151 da Ahkamul Jana’iz Usaymin.
[144]
Ahkamul Jana’iz na Jarullah 1.
[145]
Qibla Ahkamul Jana’iz na Abu Ammar.
[146]
Muslim 224.
[147]
Bukhari 756 da Muslim 394.
[148] Bukhari 1335Nasa’i 1998.
[149]
Bukhari 1317 da Muslim 964.
[150] Limamin da zai ma gawa sallah ya gaya ma jama’a abin da ake karantawa tun daga
kabbaran farko har zuwa na huxu
[151]
Hadisai ingantattu sun tabbata da suke nuna duk sallolin manzon Allah sallal
Lahu Alayhi wa alihi wa sallam na nafila da farilla da ta gawa hannunsa a qirji
yake sanya su, ba ya sakin hannunsa kuma haka ya koyar kuma ya umurci sahabbai
da su riqa sanya hannunsu a qirji. Su ma shugabannin mazahabobin mu
guda huxu su ma duk sallolinsu hannunsu a qirji suke sanyawa. Wasu jama’a
marasa adalci suna cewa wai mazhabar
malikiyya ta umurci da a saki
hannu wajen sallar farilla ta nafila kana iya sanya hannunka a qirji. Wannan
magana gaskiya rashin adalci ne da kuma qirqirar qarya ga Imam Malik domin shi
dai Imam Malik baya sakin hannu wajen salla. Bil hasali ma ya ruwaito hadisai
guda biyu a babban littafinsa Muwaxxa da suke nuna tabbatar da sa hannu a qirji
wajen salla. Ibn Abdulbar ya yi magana mai
gamsarwa cikin littafinsa Attamhid sharhin da ya yi wa Muwaxxa ya tabbatar da
cewa Imam Malik ba ya sakin hannunsa a wajen sallah. Ya kawo wata qissa ta
Imam Malik da wani mugun sarki Walid
inda ya sa a ka yi wa Imam Malik
dukan tsiya, da ya zo salla sai ya saki hannunsa, da ya gama salla sai
xalibansa suka ce masa mun ga ka yi abin da Annabi bai tava yi ba kuma kai ma
ba ka tava yi ba. Sai ya amsa masu da cewa ba ya iya riqe hannunsa ne saboda dukan da aka yi masa. Wannan ita ce ranar da Imam Malik ya tava sakin hannunsa
sabo da dukan da aka yi masa. Imam Assubki shi ma ya tabbatar da cewa Imam
Malik ba ya sakin hannunsa a wajen salla
shi ma ya kawo qissar Walid da Imam Malik: Duba DINUL KHALIS, shi ma mai
littafin Irsalil Malik ya
kawo hujjojin da suke nuna cewa
sakin hannu ba koyarwar Imam Malik ba ce domin shi ma ba ya sakin
hannunsa. Kuma malaman hadisi sun yi
raddi ga masu danganta kansu da Imam Malik
da suke sakin hannu a farilla
amma a nafila su yi qablu, wato su sanya
hannunsu a qirjinsu. Sai malaman hadisi
suka ce mene ne dalilin da ya sa ba sa yi a farilla domin dukkan su ai salloli
ne. Muna masu addu’a ga masu cewa wai suna bin Malikiyya da su riqa sanya hannunsu a qirji domin haka ne karantarwa Annabi sallal Lahu
alayhi wa alihi wa sallam da Imam Malik. Masu bin addinin Shi’a ne suka ce sanya hannu a qirji yana vata salla, haka
Ayatullahi Khomen ya ce a cikin littafinsa TAHRIRUL WASILA. Ya faxi haka ne don
qiyayya da gaba ga AhulSunnah, shi ya sa duk xan Shi’a ba ya yin qablu. Wannan
magana ce sananna a wajen masu bin addinin Shi’a, kuma bai kamata Ahlul Sunnah
su riqa koyi da masu bin addinin Shi’a ba. An samu wani mugun xan bidi’a ya yi
sharhin AHDHARI sunan sharhin HALLUL MASA’IL. A cikin littafin ya kawo
hadisin qarya da wai ya ke nuna ana iya yin salla a saki hannu. Wannan kuskure
ne Allah ya shirye shi. Wasu kuma suna cewa akwai hadisi a NAILUL AUDAR littafin Shaukani amma da zaka duba zaka ga shi
Shaukani yana ganin wajibi ne sanya
hannu a kirji wajen salla. Maganar sakin hannu a sallar Farilla maganar
mai MUKTASAR ce ba maganar Annabi sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ba ce,
ba kuma maganar Imam Malik ba ce. Karantarwar Annabi da Imam Malik ita ce qabzu
a cikin sallah kowace sallah. Wannan maganar ita ce mai Askari ya goyi bayan ta
haka shi ma mai FATHUL JAWAD ya ce a sharhin Askari ya kawo hadisin ibn Kuzaima
da ya nuna sallar Annabi sallal Lahu Alayhi wa alihi wa sallam ita ce
yin qabzu ba sakin hannu ba, Allah ka
ganar da mu amin.
[152]
Dari Qudini 191 da Hakim 360/1 da Bayhaqi 43/4.
[153]
Tsakanin Sahabi Aliyu da Sahabi Umar Allah ya qara masu yarda babu matsala
tsakaninsu abin da ya ke tabbatar da haka shine yadda Sahabi Aliyu ya aurar da
‘yarsa Ummu Khulsum ga Khalifa Umar Allah ya qara masa yarda kuma ta kasance
matar Umar har ya bar duniya kuma ranar da aka kashe Sahabi Umar Sahabi Aliyu Allah ya qara masa yarda ya
girgiza girgiza mai tsanani kuma Sahabi Umar har addua yakeyi ya ke cewa ya
Allah kar ka zaunar dani garin da babu Sahabi Ali, wannan ya nuna mana qaryar
masu bin addinin Shia da suke sharri ga sahabi Umar, Allah ya shirye su amin.
[154] Nasa’i
[155] Muslim
[156]
Muslim 945.
[157]
Muslim.
[158]
Ahmad 3/27 da Bukari Fil Adabu/Mufrad518.
[159] Ibn
Abidin 1/624 da Fahul Bari 3/113.
[160]
Kitatul Jana’iz Nabi 226.
[161] Ibn
majah 16.
[162]
Zadusmustaqani’i.
[163]
Bukhari 1315 da Muslim 944.
[164]
Bukhari 1310 da Muslim 959.
[165]
Bukhari 131.
[166]
Bukhari 1/314 da Nasa’I 1/41.
[167]
Majmo’ul Fatawa 5/270 da Jamiu ahkhmu Nisa’i na Mustafha Adawi1535. Kiristoci da masu bin addinin Shi a su ne
matayensu su ke raka gawa har maqabarta wannan ko aiki ne na kafirai, wannan
kuma a bayyane ya ke domin musulmin Najeriya sun ga yadda masu bin addinin
Shi’a suka yi wa wani xan uwansu da aka
kashe wajen zanga-zangar da suke yi a Zariya inda mata suka raka gawar
wanda aka harbe har maqabarta, suna raka ta suna waqa suna buga ganga mazajen
su kuma na rawa har maqabarta yadda dai Kiristoci da Yahudawa suke yi. Idan
mutum bai san masu bin addinin Shi’a ba, idan ya ga wannan janazar zai rantse
da Allah kiristoci ne ko wasu maguzawa ne. Wannan da ma ba sabon abu ba ne
domin duk wanda yake kallon gidan talabijin na ALMANAR ya san yadda ‘yan
Shi’an Hizbullah na Labanon suke yi yadda Kiristoci suke yin Janaza su ma haka
suke yi. Muna roqon Allah ya
shiryi masu bin Addinin Shi’a su gane cewa Shi’a ba addini ba ne.
[168]
Bayhaqifi Kubra 3/25 da Ahkamul Jana’iz
na Albany
4).
[169]
Abu-Dauda 3177 da ibn Majah 148.
[170]
Muslim.
[171] Ibn
ABidin 723.
[172]
Majmu’u Fatawaa 5/270 abin da ya ke gaskiyan labari shi ne bai halasta ba a sa gawa a mota a kai
ta ba sai dai inda wata lalura mai qarfi.
[173]
Ahmad 2/427 da Abu Dauda 3171.
[174]
Muslim 121 da Ahmad 4/199 da ibn majah 1487 da Bayhaqi 3/395.
[175]
Bayhaki 4/74.
[176]
Azkar na Imam Nawawi 303.
·
[177] Azkar na Imam Nawawi 303. Mai
karatu ya nemi faifan CD na Janazar da masu bin addinin Shi’a suka yi a Zariya
zai ga koyi da Kiristoci a fili yadda shugabansu ya yi limanci salla. Duk wanda
ya ga wannan janazar zai qara sakankancewa a kan masu bin addinin Shi’a ba su da banbanci
da Kiristoci.
[178]
Azkar na Imam nawawi da Ahkamu Jana’iz na Albany.
[179] Koda wajen aikin ku xayane bai halasta ka
raka wannan Kafirin ba domin addininka ya hanaka, in kuma ka rakata ka nuna
addininsu daidai ne Allah yasa mufi karfin zuciyar mu amin.
[180] Abu
Dauda.
[181]
Bukhari 3/3979 da Muslim 4/294.
[182] Abu
Dauda 3149 da Muslim 831 Ahmad 3/593.
[183]
Ahkamul Janaiz na Muhammad Hassan, ba mamaki wani mara sani ya ce to ai ga
gawar Annabi Sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam a masallaci. To duk wanda ya
faxi wannan maganar alama ce ta ba ya zuwa makaranta, domin asalin qabarin
Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam yana xakin Nana A’isha ne. Qabarin
Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam bai shiga masallaci a sai bayan
duk Sahabai sun rasu, Tabi’ai ma sun rasu, sai Sa’id bin Musayib kawai ya rage
a cikin Tabi’ai shi ma ya yi suka mai tsanani a kan sanya qabari cikin
masallaci. Amma waxannan sarakunan su ka
qi jin maganarsa saboda su ba malamai ba ne. Don haka haramun ne rufe mutum a
masallaci.
[184]
Muslim.
[185]
Musulunci bai hana ka ka auri Kirista ba ko Bayahudiya wannan hukunci ne
tabbatacce. Sayidina Umar ne ya so ya hana sahabbai ,su kuma su ka sava masa
har sahabi Huzaifa ya auro Kirista. Ya ce ba wai ya na son ta ba ne sai dai don
ya nuna wa Sayiddina Umar kar ya haramta wa
mutane abinda Allah bai haramta
masu ba. Shi ma sahabi Usaman ya auri
Kirista don ya nuna ma Sahabi Umar kar
ya haramta abin da Allah da Manzonsa ba
su hana ba. Shi Umar hujjarsa akwai mata musulmai da suke neman masu
auren su, don haka su ya kamata a gama
da su kafin Kiristoci. Shi ma xansa yana cikin masu hana auren Kiristoci. Babu
laifi don mutum musulmi ya auri Kirista sai
dai ba kowa ba, sai wanda ake sa
ran za su iya musuluntar da ita ba wai yanda mutanen banza suke yi ba, bayan
sun gama fasiqanci da Kirista daga baya
su aure ta ba, ba irin waxannan
ake nufi ba. Kuma su ma matan Kiristocin sai masu kamewa ba ‘yan iska fasiqai
ba. Yana da kyau mai karatu ya duba littafin
ALQADHI ABUBAKAR IBN ARABIY ALMALIKI ALANDALUSI
AHKAMULKUR’AN Saratul Ma’idah zai ga bayanin da ke nuna halascin auren
Kirista.
[186]
Mugni Ibn Qudama 2/563.
[187]
Abu-Duda 3215 da Nasa’I 2011 da Tirmizi 1713 da ibn Majah 1570.
[188]
Muskah 1703.
[189]
Ahmad 22955 da Abu Dauda 3332.
[190]
Muslim 966.
[191] Ibn
Majah 1557 daAhmad 3/99.
[192]
Abu-Dauda 3207 da Nasa’i 2009.
[193]
Majamu’ul Sharhul Muhazab 5/287.
[194] Abu
Dauda 3195).
[195]
Muhallah 5/173.
[196]
Muhallah 5/173.
[197]
Bukhari.
[198]
Bukhari.
[199] Ibn
Majah 1565 da Irwa’u Ghalil 751.
[200] Masu bin addinin Shia cikin akwati suke rufe
wanda ya mutu.
[201] Abu
Dauda 3207.
[202] Ibn
Habban 2170 da vayhaqi 3/410.
[203]
Musim.
[204]
Bukhari 1343 da Nasa’I 2771 da ibn Majah 15141.
[205]
Abdu Rak 7378 da Jamiu Ahkmun Nisan a Mutapha Adawi 1/556.
[206]
Al’uMmu 1/245.
[207] Abu
Dauda.
[208]
‘Yan bidi’a ne ke yin addu’a cikin jam’i bayan sallolinsu da kuma maqabarta. Koda yake a da ba sa yin
addu’a a maqabarta, daga baya ne suka gane gaskiya sai kuma suka haxa da bidi’a
ta yadda suke yi cikin taro su keve waxansu su ce wai su ne za su yi addu’a ga
wannan mamacin. Abin da sunna ta koyar da mu kowa ya yi tasa. Kada mutum ya
shiga tsakanin bawa da ubangijinsa. Haka
sahabi Umar ya ce. Muna fatar jama’a zasu gyara kowa ya yi wa gawa addu’a, kuma
ana so a daxe ana yin addu’ar ga mamacin. Sannan kuma alqibla ake kallo
wajen yin addu’ar.
[209]
Ahmad 2/204.
[210] Bukhari
5417 da Muslim 2216.
[211] Abu
Dauda)3753 da sahih Jami’u 1676.
[212]
Kitabu Jana’iz na Nabi Muhammad 263.
[213]
Muslim.
[214]
Tirmidzi da Nasa’I da dhiyaul Maqadisi.
[215]
Madakal.
[216](Sharhus
sagir 1/180.
[217]
Hukumul qiratu alall Amwatu 24.
[218]
Hukumu Qiratu qur’an ala Amwatu.
[219]
Fatawal Shaxibiy 210.
[220]
Suratu Hahar 10.
[221]
Musim 2733.
[222]
Bukhari 1952 da Musim 1147.
[223] Abu
Dauda 3511 da Nasa’I 7/341.
[226]
Bukhari 1284 da Muslim 923.
[227] Ibn
Majah 1612 da Ahmad 666.
[228]
Almajahmu’u 5/306).
[229]
Alummu 1/248).
[230]
Mindaju Muslim 266).
[231]
Zadul Ma’ad.